Bayan wata d’aya Soyayyar Maryama ta hana Habib sakat, duk yanda yaso ya ya k’ince ta ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar tunkarar ta zuwan sa uku gidan da k’yar ya samu ya shawo kanta ta amince da soyayyarsa Iya tafi kowa farin ciki da wannan soyayyar.
Ranar asabar da azahar bayan ya fito masallaci ya wuce gidansu ya tarar yayyinsa duk sunzo bayan sun gaisa yace “yanzu Aunty Aisha kuna gida baku fad’a mun ba da banzo ba shikenan bazan ganku ba?”
“A to auta ya zamuyi kayi wuyar gani ba ka zuwa wajanmu shikenan mu ne zamu ta binka muna gaba da kai?”
Sosa kansa yayi kafin yace “Kuyi hak’uri Allah aiki ne yamun yawa shiyasa amma zan dinga k’ok’arin zuwa Insha Allah.”
Aunty Fa’iza tace, “Da dai yafi tunda ita ‘yar mulkin taka bata so muna zuwan mata gida.”
“Kuyi hak’uri Aunty.”
Aunty Halima tace, “To idan ba mu yi ba dukanta zamu yi ya dai kamata wallahi kayi k’ok’arin gyara gidan ka. Yanzu abun kunya Yaya Mujaheed bai tab’a ganin matar ka ba wannan ko a hanya ya ganta bazai ce matar k’aninsa bace, ko sha’awar matar Yaya baka gani mai kirki da haba haba da ‘yan uwansa amma taka in banda rashin mutunci ba abun da ta iya.”
Aunty Aisha ta karb’e “Abun haushin ma yanzu shekarar ku uku da aure ko b’atan wata bata tab’ayi ba wama yasani ko wani abun tayi dan karta haihu tunda dama irinsu duniya ce a gabansu ba yara ba.”
Hajiya da ke zaune kan darduma tana lazumi ta tsawata masu. “Kai ya isa hakanan dan Allah kunzo kunata magana akan abunda ba ku da maganinsa addu’a ya kamata kuyiwa d’an uwanku Ubangiji Allah ya sauya masa gidansa ni bana son k’ananan magana.”
“Ki yi hak’uri Hajiyarmu mun daina Insha Allahu.”
Sukayi maganar lokaci d’aya Habib ransa duk ba dad’i fatansa Allah yasa Maryama ta zame masa alkhairi ta kula dashi da familin sa.
“Uhm,” ajiyar zuciya yayi kafin yace, “Dama maganar da nazo da ita akwai wata da munka kai k’arshe har iyayenta sun nemi na turo iyayena.”
Hajiya ta zuba masa idanu tana nazarinsa kafin tace, “Habib aure na biyu da k’urciyar ka d’ayarma ya ka k’arasa da ita.”
“Hajiya dan Allah kisa albarka wata k’ila wannan d’in itace sauyin da muke masa addu’a.”
“Yayarsu ba ina k’i bane Habib nawa yake ina zai iya da mata biyu.”
Haka suka sata gaba da magiya har ta amince suna cikin maganar Baba ya dawo shikam baija ba ya sanya albarka tare da alk’awarin zai tura ‘yan uwansa a nema masa auren haka Habib ya bar gidan ciki da farin ciki.
Bayan ya mayar da budurwarsa gida ya dawo gida kai tsaye d’akinta ya nufa a fusace ban d’aki ya jiyo mutsinta hakan yasa ya shiga ban d’akin ya tarar da ita tana yunk’urin amai gashin kanta ya janyo da k’arfi.
K’arar wahala tasa cikin rashin tausayi ya janyo ta zuwa cikin d’akin yana masifa, “Wato ke gaki ‘yar iska nayi maki umurni ki k’ibi wato kece ta Allah mu kuma ‘yan iska ko? To zakici uwarki yau.”
Belt d’in wandonsa ya ciro ganin haka yasa tayi baya tana fad’in, “Dan Allah kayi hak’uri wallahi bank’i dan sab’awa umurnin ka ba lokacin sallah ne yayi shiyasa.”
Bai saurare ta ba ya dinga dukanta kamar ya samu jaka tun tana kuka da yi masa magiya har tayi shiru ko motsi batayi sai da ya gaji dan kansa sannan ya kyaleta. Idanunsa ne suka kai ga k’afafunta yaga jini na zuba kamar anyanka k’aramar dabba da sauri yayi baya yana fito da idanu firgice.
“La ilaha illallahu muhammadu Rasulullahi S.A.W Fahad me zan gani kasheta kayi?”
Firgici ya joya yana kallon k’ofa ganin wacce ke tsaye ya matuk’ar d’aga masa hankali a tsoraci ya jefar da belt d’in dake hannunsa yana zarar idanu.
Da dare bayan ya gama shirin bacci ya nufi d’akinta zaune ya tarar da ita tana sana’ar wato kallo zama yayi kusa da ita kafin yace “hutawa kike?”
“Uhm” ta bashi amsa a tak’aice ba tare da ta kalleshi ba cikin murmushi yace, “Ki kashi tv magana nake so mu yi.”
“Ai kunne ke ji ba ido ba dan haka ba ruwan ka da TV kawai kafad’i maganarka.”
Sanin idan zasu kai yaushe ba kashewa za tayi ba yasa yace, “Shikenan dama zan fad’a maki ne ki shirya tarbar k’anwa nan da wata d’aya Insha Allah.”
Kallonsa tayi cikin mamaki tace “wai kana nufin Safiyya ko Sarat d’ayansu zata dawo gidannan?”
Murmushi yayi kafin yace, “A’a ba su nake nufi ba ina maki maganar zan k’ara aure.”
Firgice ta mik’e tsaye cikin tashin hankali tace, “Aure? him wasa kake.”
“Ba zancen wasa a maganata dan kinsan bamu tab’a irin wannan wasan dake ba.”
“Wai tashin hankali ai wallahi baka isa ba uban kuturu yayi kad’an dan bamuyi zaka mun kishiya ba!”
Mik’ewa tsaye yayi tare da rik’o hannunta ta fizge hannun da karfe tana harararsa bai damu ba yaci gaba da magana cikin lallashi, “Na sani ba mu yi zan maki abokiyar zama ba, amma kinsan ban tab’a yi maki alk’awarin bazan k’ara aure ba ko? ki kwantar da hankalinki ki fahimce ni ba wai zan yi aure ne dan na daina sonki ba, a a kin sani narasa abubuwa da yawa age…”
Cikin masifa ta katse shi, “Kaga Adana duk wasu maganganun ka dan basu da tasiri awajena. Fahimta kuma har abada ba zan yi ba aure ne baka isa ka yi ba idan kuma ka kuskura ka yi wallahi ka aurowa kanka tashin hankali da bala’i acikin gidannan! Wato munafukai sun zugoka ko? to wallahi sun janyo maka bala’i ihim!”
Duk yanda Habib ya so ya lallasheta tak’i sai k’ara hawa take kamar zata dake shi. Hakan yasa yabar d’akin, biyo shi tayi tana masifa da sauri ya fad’a d’akinsa tare da saka key. Ranar kam Ruk’ayya tamkar mahaukaciya ta koma batayi barcin kirki ba bata bar Habib yayi ba.
Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)