"Nace me ka yi wa 'yar mutane?” ta sake jeho masa tambayar cikin tsawa.
"Ummy nifa ba abunda namata nima haka na shigo na ganta."
K'arya kake Fahad wallahi idan nagano wani abun ka mata wallahi ba zakaji dad'ina ba maza kamata mu wuce asibiti!"
Jiki asanyaye ya d'auketa ya kaita Mota Ummy ta shiga sai fad'a take masa shi dai bai ce da ita komai ba, fatansa su isa asibiti karta mutu ya shiga uku da Dady.
Suna zuwa emergency suka nufa da sauri, likitoci suka karb'eta. Ganin yanda jini ke zuba, aka. . .