Skip to content

Ma’aurata | Babi Na Takwas

Bookmark

No account yet? Register

<< Previous

“Nace me ka yi wa ‘yar mutane?”  ta sake jeho masa tambayar cikin tsawa.

“Ummy nifa ba abunda namata nima haka na shigo na ganta.”

K’arya kake Fahad wallahi idan nagano wani abun ka mata wallahi ba zakaji dad’ina ba maza kamata mu wuce asibiti!”

Jiki asanyaye ya d’auketa ya kaita Mota Ummy ta shiga sai fad’a take masa shi dai bai ce da ita komai ba, fatansa su isa asibiti karta mutu ya shiga uku da Dady.

Suna zuwa emergency suka nufa da sauri, likitoci suka karb’eta. Ganin yanda jini ke zuba, aka rubuta magani Fahad ya je ya sayo. Bayan sun bata taimakon gaggawa cikin taimakon Ubangiji, ta farfad’o daga suman da tayi. Bayan an sa mata k’arin ruwa, likita ya nemi ya ga mijinta. Fahad yabi bayansa zuwa office.

Bayan sun zauna, likitan ya dube shi. “Am ina mai baka hak’uri mun yi iya k’ok’arinmu na ganin cikin bai fita ba, amma Allah bai yarda ba cikin ya zube sai dai abun da ya bamu mamaki shatin duka da muka gani ajikinta, wanda ina kyautata zaton sanadin dukan ne yasa cikin ya fita.”

Fahad tunda ya ji tayi b’ari ya ji bak’in ciki sosai dan Allah yayi masa son yara duk sai ya ji ya k’ara tsanarta. “Me yasa zata masa laifin da zai sa ya daketa? Gashi ta yi masa asara gudan jininsa mtsw!”

Likita ya k’wank’wasa tebir da ke gabansa wanda ya dawo dashi daga tunanin da ya fad’a. Fuska ba walwala yace, “OK ba komai Dr duka da kake magana banda masaniya kuma ba sai ka fad’awa Ummy zancen dukan ba zan bincika.”

“OK Allah ya bata lafiya zamuyi mata wanken mara amma kafinnan muna so tayi photo da test d’in jini saboda mu tabbatar idan jininta baiyi k’asa ba.”

Zaune ya tarar da Ummy bakin gadon da aka kwantar da Fad’ima ta zuba mata ido idonta tab da k’awalla.

“Ummy ya jikin nata”?

Harara ta watsa masa kafin tace, “Me likitan ya fad’ama?”

Nan ya yi mata bayani kamar yanda likitan ya masa sai dai ya b’oye mata zancen dukan.

Wayyo Ummy harda hawayen ta saboda bak’in cikin rasa jika ko jikanyarta kafin daga bisani ta yi mata addu’ar Allah ya bata lafiya ya kawo rayayye mai albarka.

Gyara tsayuwarsa yayi tare da dafa k’arfin gadon yace “Ummy ya za ayi da zancen hoton naga tana barci?”

“Eh bari za ayi sai ta farka tunda ai ko cikin asibitin sunayi”.

“To ko zan maida ke gida ne sai na dawo?”

“A’a zan zauna da ita yayarku ma na nan zuwa.”

Haka ya zauna asibitin ba dan ransa yaso ba sai dan ganin idanun Ummy.

Habib da wuri ya shirya ya bud’e k’ofarsa a hankali kamar wani marar gaskiya addu’ansa Allah yasa har ya bar gidan kar ya had’u da Ruk’ayya.

Yana kaiwa k’ofar da zata sada shi da harabar gidan tasha gabansa tana jijjiga jiki kamar wata sabuwar kamu.

Turus ya yi tare da furta, “Ya salam” a hankali yanda ba zata ji ba.

Murmushi yayi kafin yace, “Hajjaju antashi lafiya?”

Cikin harara tace masa, “Da ban tashi ba zaka ganni anan”.

“Oh Allah ya baki hak’uri ni zan tafi wajan aiki a taimaka abani hanya”.

“Ai wallahi ba inda zaka har sai ka zab’a ko ni ko shegiyar”.

“Zab’e ki ke so nayi?”

“Eh” Ta yi maganar tana harararsa.

“Ok to muje falo sai na fad’a maki zab’ena.”

Da saurinta ta juya zuwa cikin falon ba tare da tace masa komaiba yana ganin ta bar k’ofar ya fita da gudunsa ya rufeta ta waje. Tana ganin haka, ta dinga ihu tana jefa masa zage ta uwa ta uba. Baima san tana yi ba tuni yabar gidan.

Sai dare ya dawo yana cire kayan jikinsa zai shiga wanka ta fad’o d’akin ba ko sallama. Ta fara magana cikin masifa, “Wato ga mahaukaciya marar wayi ka gudu ka barni to wallahi nid’in walki nake dai dai da k’ugun kowa shege ka fasa!”

“Waike me kika d’auke ni? karki ga ina maki shiru kice zaki zageni aure ne, ke baki isa ki hanani yi ba. Ki je ki yi duk abunda zakiyi d’in tunda baki san lallami ba mtsw!”

Ya shige toleit yabarta tana ciccika tabar d’akin zuciyarta kamar ta fashe ba tare da ta sake cewa komai ba dan ta tsorata da yanda ya hayayyak’o mata.

D’akinta ta shige tana kuka kamar wacce aka aikowa sak’on mutuwa. Abun haushi tasan ko zuwa gida tayi Babanta ba barinta zai yi ta zauna ba ballatana ya goyi bayanta “Mtsw kai wani uba kam suna dai ya tara.”

Tana cikin tunanin ta ji ringin d’in wayarta tana dubawa taga Kubura ce. Da sauri ta d’aga kiran tare da k’ara fashewa da kuka.

Kubura tace “Kwantar da hankalinki ki daina kuka munafukin ya zo ya fad’awa Malam wai zai k’ara aure. Malam sai murna yake da yaga na fara masifa, ya ce duk na yi wani abun gami da wannan auren abakin aurena. Wannan yasa nace zan kira ki kar ki tashi hankalinki. Aure dai ko bisimillah ya yi wallahi idan ta zo ban ce ki d’aga mata k’afa koda masukar allura ba. Kina jina”?

Ruk’ayya ta ja numfashi kafin tace “Eh ina jin ki.”

“Ki rik’i abun da zan fad’amaki sosai daga shi har ita karki bari suji dad’in auren”.

Haka ta zauna ta yi ta kitsawa ‘yarta mugayen shawara sai da ta tabbatar ta kwantar mata da hankali sannan sukayi sallama.

Kwanansu d’aya asibiti aka sallame su bayan likitan ya tabbatar da babu matsalar komai. Kai tsaye gidan Dady suka wuce bayan ta huta taci abinci.

Dady ya kirasu d’akinsa. Kallon Fahad ya yi cikin b’acin rai yace, “Kai me kayiwa ‘yata har yayi sanadin cikin jikinta ya zube?”

“Dady nifa ba abunda na mata haka na dawo na tarar da ita.”

Ummy tace “k’arya kake Fahad belt d’in da na gani a hannunka uban me kake da shi sannan ga tabon duka ajikinta bayan ba haka muka kaima ita ba, a ina ta same su?”

“To Ummy gatanan ku tambayeta ku ji idan k’arya na fad’a”. Yayi maganar yana mai hararta ta k’asan ido.

Sunkuyar da kanta ta yi aranta tana jin “Inama zata iya tona masa asiri in ma Abbanta da Inna basu mata kashedi da ta zamo mai rufawa mijinta asiri ba inama zata iya rufe ido karta kalli karamcin Yayan Mahaifinta da matarsa ta fad’a masu aibun d’ansu hak’ik’a da ta fad’a ko dan fitar da kanta daga uk’ubar Yaya Fahad.”

Maganar Dady ce ta dawo da ita daga dogon tunanin da ta fad’a.

“Fad’ima fad’amun gaskiyar abunda yake maki a zamanku da shi da abun da ya faru jiya.”

Gumi ya fara tsattsago masa jiki fatansa Allah yasa kar Fad’ima ta fad’awa iyayansa ya shiga tara.

Muryarta ya tsinkayo tana fad’in, “Ba komai Dady lafiya k’alau muke zaune. Jiya kuma ruwane suka zube na manta ban goge ba zan fita santsin ruwan suka jani na fad’i”.

Cikin harara Ummy tace, “ba zaki fad’i gaskiya ba ko Fad’ima?”

“Da gaske nake Ummy.”

“Ai shikenan tunda ba zaki fad’a ba anaso akwato maki ‘yanci shegen zurfin cikinki zai cuceki wallahi”. Ummy ta yi maganar kamar zata maketa.

Dady yace, “Tunda kunk’i ku fad’a gidan dai da matsala gani zamu yi komai daren dad’ewa. Ina mai maku nasiha da kuji tsoron Allah wallahi aure da kuke gani ba abun wasa bane. Duk wanda ya zalunci wani Allah ba zai barshi ba.”

Sosai yayi masu nasiha kafin ya sallame su Ummy taso abar fad’ima ta k’ara jin sauk’i Dady ya hana haka suka tafi zuciyarta fal da tsoro.

Ranar asabar aka d’aura auren Habib da Maryama Ango kam baki yak’i rufuwa.

Ruk’ayya ba wanda ta gayyata rufe sashinta ta yi har ‘yan kawo amarya suka gama hayaniyarsu suka waste.

Tanajin shigowar Habib da abokanansa zuwa sashin amarya ta fito d’akinta da sauri ta nufi  b’angaren amarya da mugun nufinta.

Habib kuwa yaso ya fara  zuwa wajan uwargida sai dai tsoron karta  dizga shi a gaban abokanansa yasa dole ya hak’ura idan abokanan sun tafi sai ya je.

Ta ku Aisha A. Yabo (Fulani)

Next >>

How much do you like this post?

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found this post interesting...

Follow us on social media to see more!

nv-author-image

Aisha Abdullahi Yabo

Share the post on social media.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.