Tana son ta masa tambayar me yake son sakata yi ta kasa, gabadaya ma ji ta yi tana mugun tsoronsa ganin yadda ya kafeta da idanuwansa da suka sha bakin kwallli, ga nadin kansa sai ya zame mata kamar irin yan taaddan falasdinawa da take ganin ana nuna su a TV, sai kawai ta sunkuya da kwandon a hannunta, ta mika hannunta za ta tabo tarin kashin rakumar ta ji ta kasa tsabar kyankyami, ta sake dagowa ta kallle shi ya daga mata girarsa da ke cike da gashi yana ma ta nuni da ta kwashe.
Deluwa sai hawayen takaici. . .