Skip to content
Part 5 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Deluwa A Saudiyya

Matarr Malik Abdul’aziz (Jeddah)

Anan jirginsu Deluwa ya sauka.

Ga Deluwa bacci take ta shara abunta sai da taji wani rugugu, tukunna tasan da saukar jirgin, ranta ya ɓaci da bata samu damar ɗan muttsika ko da farar hoda za ta ɗan ƙara mata kyawu ba, duk da hakan bata ɓata lokaci gurin zaro turarenta lailatus sahara ta feshe jikinta dashi , sa’annan ta ƙara gyara zaman tabaran dake fuskarta, ta ɗan goga man leɓe a manyan laɓɓanta masu kama da an tauna ganda, tukunna ta miƙe tsaye tana tunanin kamar a kusa da ita ta aje akwatin kayanta. To tana ina, ba dai an sace ba? Kai sata har a jirgi? Kamar dai ance ɗaga kanki, ta kalli jakar a kantar saman kujerarta, tai sororo tana duban jakar, ita dai ba tsayi ba, bare ta ce ita ta ɗora ta.

Qyat! Ta yi ƙwafa, sai kuma ta kame kugu tana kallon jakar, aranta tana ambaton ‘duk wanda ya ɗora min ita sama, ya zo ya ɗauko min kuwa, wallahi idan ba haka ba in kwana cikin jirgin nan.’ 

Ɗai-ɗai take kallon matafiyan na ta sauko da ƙanƙanan jakunkunansu suna ficewa, ita ko ko oho, ta ƙara jan tsaki wanda yaja hankalin ainihin balarabiyarta mai fentin ‘yartsana, ta taho da hanzari tasa hannu ta sauke mata jakar, tana kallonta da murmushi ta ce (Sadik habiby ana…”) 

“Dakata malama!” Deluwa ta katse ta da hanzari tana jijjiga jiki,

“Wallahi kinji na rantse yadda kika ɗora min ita sama, haka zaki sauke min ita har ƙasan wancan tsanin naku, (matattakalar jirgi) ɗauki maza mu wuce ba na son dogon yare!” Wani ɗan baƙin bahaushe da ke ƙoƙarin fita, ya juya ya fashe da dariya, ya lna mamakin yadda ‘Yar Wadar ke ba da ummarni ga balarabiyar gabanta.

Balarabiyar ta ƙara faɗaɗa murmushin fuskarta, cikin rashin sanin me take faɗi ta ƙara dafa kanta a karo na biyu ta ce “(Allah yaddakal Afiya)” ta juya kamar za ta karye tabar wajen. Deluwa wani daɗi ya ratsa mata ƙoƙan kanta, ta ma manta da masifar da ke cinta, kawai taja akwatin ƙiiii itama tabi layin masu tururuwar fita daga jirgin. Faskekiyar fuskarta na ɗauke da yalwataccen murmushi da ita daga gareta, takai ƙoluluwar farin ciki ke nan…

Sakamakon wasu da yawa in zasu kalleta tana irin wannan murmushin, to kuwa babu abinda zai hana su fashewa da kuka.

Cikin salon takunta na wadanni take sauka daga mattakalar jirgin xuwa lokacin data sauko gabaɗaya tana ƙarewa gurin kallo, wani sanyin ni’ima da ƙamshi ke ratsa sassan jikinta, kai ga mamakinta fa ita har ƙamshin jikinta ta ji ya fara sauyawa ya koma tamkar na balarabiyar data dafa mata kai, wani farin ciki ya sake lulluɓeta, nutsuwa ta wadaci zuciyarta, nutsuwa Irin wacce ba ta misaltawa.

Ta fara taku ɗai-ɗai kan saramit sai kuma can cikin hanzari  tabi hanyar da taga jama’ar da suka sauko tare na bi. Sai dai fa tunda ta shiga gurin tantancewar ‘ya’yan larabawa ke kallonta suna fashewa da kuka, dan haka Alla-alla take agama mata abinda za’ai ta fice, Su kansu larabawan dake aikin dube-duben viza da fasfot, sun tsorata da ganin Deluwa, bawai don tana wada ba, a’a, yanayin shigarta shi yafi ruɗa hankali, ba dai wanda yai ƙoƙarin furta mata wani abu, har aka gama abinda za’ai ta tafi, tunda ba ta da Awo, hanya kawai ɗan Balaraben dake gun ya nuna ma Deluwa ta wuce ba tare da ya ko kalli guntuwar akwatin ta ba.

Bayan fitowarta daga Matarr ɗin kai tsaye gefen titi taja ta tsaya tana ƙarewa gidajen dake kusanta kallo, a ranta fata take wataran su mallaki irinsu itada ‘yan uwanta Wadanni. Ta ɗan saki dariya me kama da an mari ɓera, kana kuma ta gintse fuska haɗe da faɗin “NA SHIGA UKU!”

kwata-kwata Deluwa ta manta Saudiyya ba irin Nijeriya ba ce, ba wanda ta sani ba wanda ya santa anan, haka Alhaji ce mata ya yi tana sauka ta kira shi zai sa wani ya kama mata hotel,  to ita ina ma tasan hanyar hotel ɗin, ina kuma taga hanyar kiran Alhaji?

haka ba tasan kome daga yarensu ba sai Kalmar HAMMAM BUKHAR. Ta kuma san

BINtun-yarinya Da WaLadun-yaro, ‘ina na dosa?’ ta tambayi kanta

‘Hammam bukhar mana’, wata zuciya ta sanarta hakan, kai tsaye ta yi ɗan murmushi, ‘sai dai Hammam Bukhar ɗin, na tabbata duk balaraben dazan tambaya yasan da shi.’

Cikin kwarin gwiwa ta matsa can kusa da wani dan Takzi, akwai alamun fasinja yake jira dan yana jingine da motar ya juya baya, sallama ta masa bata jira ya amsa ba ta ce..

Dan Allah Malam kasan Hammam Bukhar anan? ” Saurayin da ‘yar dariyarsa ya juyo jin bai san yaren ba da ambaton, “Maza taqul?”(me kake cewa) Lokaci guda saurayin ya buga wani ihu haɗe da an dungure sau uku a jere kana kuma ya baje a gun a sume, ba kome ya ja haka ba sai arba da faskeken kan Deluwa da ya yi, da kuma kankantarta a matsayinta na Wada, take jami’an tsaro kamar an watso su suka kewaye Deluwa, yayin da wasu sukayi kan ɗan balaraben saurayin. Ga jami’an tsaro an rasa jarumin da zai taɓa Deluwa dukkansu kallonta suke a razane suna mamakin ganin yanayinta, haka dukkansu sun auna ta da manyan bindigogin hannunsu suna zare idanu, wasu a cikinsu gani suke kamar wani mugun dawan ne ya arto daga gidan Zoo, shi ya sa kawai jira suke ta yunƙura ta ji ruwan alburusai, Deluwa kuwa tsurewa ta saka ta sandarewa a gurin, kamar a mafarki take ganin abun cikin rawar murya take ambata musu “Hammam Bukhar fa nike tambayarsa, wallahi ba abinda na masa” ka ji Deluwa da karfin hali wai ɓarawo da rance gidan ɓarawo.

Kai tsaye wani cikin Askarawan ya fara zungurin Deluwa da tsinin sandarsa alamar su tafi motarsa, da dabara a kasa ƙeyar Deluwa a gaba har zuwa gurin motarsu, ba wanda ya yi ƙoƙarin taɓa ta har ta shiga bayan motar suka datse, nan Askarawan suka ɗin cikin motar.

Wata mota ta ‘yan jaridu suka rufa musu baya suma…

Deluwa A Sijin (prison)

Kai tsaye  _FARHIN JEDDAH_ aka wuce da Deluwa, babban Sijin ke nan na ƙasar saudiyya, wanda daga shi kai tsaye za’a dunƙulaka zuwa ƙasarka idan ya zama na baka cika sharuɗansu ba.

Ga Deluwa ba tasan inda aka dosa da ita ba, bare hankalinta ya tashi. Don haka ko bayan fitowarta daga bayan motar hankalinta kwance yake musamman ganin kyawun wurin ga sanyin ni’ima yana ratsa ta a zuciyarta harta fara raya mata ƙila _HAMMAM BUKHAR_ ɗin masu zungurorin bindugun nan suka kawota.

Tunaninta ya canja ne lokacin da motar ‘yan jaridu ta ƙaraso kusa da ita nan da nan suka fito suna ta ɗaukanta a hoto sunayin larabcinsu, har an fara haskawa live a ALJAZEERA, dan kai me karatu da ka kunna tv ɗinka a ranar 30/12/2030 tashar ALJAZEERA, to tabbas za ka ganta cikin Yan sandan Saudiyya ana ta tafka Larabci. Ita dai abu ɗaya ta fahimta a maganar tasu kalmar( Walad )da suke yawon ambatonta dashi, nan ta sahihance larabawan nan a Namiji suke ɗaukarta ba Mace ba, don haka ta ƙara gyara zaman ɗan siririn gyalen da ke kewaye a wuyanta gami da ƙara gyara zaman tabaronta tana kallonsu, ‘yan guntayen hannayenta maƙale a ƙirjinta irin na ‘yan mata, ji ta yi an bushe da dariya, dan su kansu larabawan burgesu ta yi ganin yadda ta ƙara gyara tsayuwarta ba tare da tsoro ba, babu alamun ma tasan inda aka kawota.

Nan wani Babba daga cikin Askarawan ya duƙa sosai a ƙasa yadda tsayinsu zai kai.

“Ya ya sunanka, dawa kake tare? Me ya sa ka zo kai ɗaya?” Ya tambaya cikin harshen larabci.

Deluwa ta yi zuru tana dubansa cikin baƙin tabaranta ba tasan me yake

nufi ba, Don haka ta yi shiru.

‘Muryar ɗan balaraben gwanin daɗi ta faɗa a ranta,’

‘Ina ma…’ ta yi shiru kamar tana jin kunyar faɗi..

Ina ma ya amince ya aure ni, da daga ranar ko wanka na daina, in don ƙamshi ne aiko hular larabawa ƙamshinta daban yake, ta ɗan rufe ido cikin tabaranta tana hango kyakkyawar ɗiyar da za ta haifa ita da balaraben dake duƙe kusa da ita, kai harta gano su suna yawo ƙasa-ƙasa tare da daukar hoto. 

Zungurar da ta ji an mata ne ya dawo da ita daga mafarkinta.

A karo na biyu yasake tambayarta:

“Abuk Wain ?” (Ina Babanka )

Deluwa ta yi shiru tana tunanin inda ta taɓa jin kalmar  “Abu” tunaninta ya bata yana tambayarta ne cikin ‘yan uwanta akwai Abu? 

Cikin hanzari Deluwu ta ce; “A’a Malam! ‘yan uwana daga Ila sai Sirajo sai kuma Yusuf, wallahi duka dangina babu Abu ma.” Ta faɗa da ɗan murmushi a fuskarta me kama da damammen gayan tuwo.

Askarin ya dubeta cikin rashin fahimta. ( Ya Walad inta minyatu balad?) (Daga wane garin kake? ) Deluwa tunanita ya bata yana

Tambayarta inda za ta ne, don haka cikin fara’a ta ce HAMMAM BUKHAR nazo ai kuma naga ma kamar nan kuka kawo ni ta faɗa tana kwantar da baratolin kanta.

Ɗan Balaraben Askarin ya miƙe cikin ƙosawa da rashin fahimtar yaron dake gabansa, yabawa wani Askari umarnin ya shige da yaron cancikin sijin din bangaren yaran pakistan amma, ya kuma kawo masa jakarta su duba takardunta. Nan da nan Askarin ya taso, kai tsaye duƙawa ya yi ya  sunkuci Deluwa ya aza a kafaɗa ya doshi cikin sijin ɗin da ita.

Deluwa ta dinga wutsil-wutsil tana ambaton “macece ni Malam! Sunana Saratu Malam Na Allah, wallahi haramun ka taɓa ɗan banza kai ya ji laushin jiki, yaga jiki a cike ba irin na figaggun matanku ba! Kai ka sauke Ni na ce!! Wayyo Chibunzu!”

<< Mafarkin Deluwa 4Mafarkin Deluwa 6 >>

2 thoughts on “Mafarkin Deluwa 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.