Skip to content
Part 6 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

“Ka taɓan ƙirji ban yafe ba! Ɗan iska, wayyo matancina, wallahi ni ma sadaki na sisin gwal ne, ka sake ka taɓa ni sai ka biya ni da duk abinda ka mallaka, na faɗa maka ni ba ‘yar iska ba ce!” Garin ya zunkuɗata gwiwar hannunsa ya shafi tudun ƙirjinta da ba a ganewa, ta kuwa daddage ta kwantsama ihun da ya saka shi ƙanƙame ta ya tsaya cak!

Yana haki yana yafito wasu Askarawa da ke can gefe dan su taimaka masa, cikin hayagaga ta ce, “ka sauke ni na ce maka da ƙafata!” Inaaa! Deluwa an makaro, tuni ya hantsilawa waɗannan Askarawan ƙafafuwanta shi ya kama hannayenta suka ci gaba da tafiya da ita a haka har suka jefata ɗakin wasu yara sa’aninta, amma ba ga shekaru ba, ga tsayi. Kai tsaye Askarin ya jawo ƙofar sijin ɗin ya garƙame bayan ya watsa mata harara, sai hucin nauyin Deluwa da yaƙushi da ya sha yake yi.

Yaran guda goma dake cikin dogon ɗakin mai ɗauke da gadaje goma sha biyu, waɗanda takwas a cikinsu suka kasance ɗiyan Pakistan, sauran yara biyun kuma baƙaƙe ne, za ka iya sakasu a ‘yan Africa ne haihuwar Sa’udiyya. Suka dubi Deluwa tana goge hawaye gami da tuntsirewa da dariya dukansu da alamun tsaurin ido da tsantsar fitina a tare da su, cikin dariya wani yaro mai ɗan doguwar ƙeya cikin masu kama da hausawa ya taɓo wani yaron kusa dashi yana faɗin “Bukr ga ɗan garinku ya zo”, yaron da aka ambata da Bukr, wanda ba zai gaza shekaru goma sha biyu ba ya ɗan ɗago da idanuwansa yana kallon Deluwa, cikin yaren hausa ya cewa ɗayan yaron. “Wannan ai ɗan wadane irin wanda Abbu ke ba mu labari.”
Sai kuma ya karkace ya zaro wata sigari gami da kunnata da wata ‘yar munafakar Ashana da ke ɓoye ƙasan wandonsa…

Miƙawa Deluwa ya yi yana faɗin “ka daina kuka, sha wannan tabar ko ka ji sauƙin baƙin cikin abinda waɗannan yan iskan Askarawan suke yi, haka suke yi, kai dai karka sake ka gaya musu ƙasarka ko da sun tambaye ka, kuma karka nuna musu ka na da wanda ka sani anan, don kansu zasu zo su fiddamu gabaɗaya, ka kuma ɓoye Jawazz ɗinka (fasfot), duk ranar da ka bari suka gani za su mai da kai garinku kome nisansa.”

Deluwa da ta yi sororo tana ƙarewa ɗan yaron da bai fice ta haifo shi ba, ɗauke da kwalin taba a hannu, ba abu mafi mamaki ma sai ganinsu a gurin da ta tabbata yanzu kurkukune duba da yadda wasu ƙarafe da aka zarƙafe su da ankwa suka kewaye su, ta ɗago a razane tana duban yaron ba ki buɗe.

“A mai da ni ƙasarmu fa ka ce? Bantan bala’i! Uwar ubansu ma ta yi kaɗan!”

Ta sami bakinta na furta hakan cikin gaggawa… Sai kuma ta yage baki tana mai rushewa da ihun kuka…

*****
A can wani ƙauye da ke tsakanin Makkah da Tayib (Hadasham) cikin wani mulmulallen ginin dutse mai ɗan karen kyau, wasu maza biyu ne zaune suna kallon juna. ɗayan wanda ya fi nuna alamun tsufa sosai, ɗan yalolon balarabe ne fari fat! Ya tara gashin gemu har ƙasan ƙirjinsa kusa da cibiya, idanuwansa a runtse, hannunsa na bisa wani fai-fai, saman fai-fai tarin yashi ne mai matuƙar laushi yana ɗaukan ido, ɗayan hannun nasa kuwa Alƙaluma ne guda biyu da aka sassaƙa su da Iccen tamar hindi, yana haɗa su lokaci guda suna ɗan ƙara.

Ya jima a wannan halin, can dai ya buɗe manyan idanuwansa ya sauke su akan farin mutumin dake kallonsa.” Annur!” Ya kira sunansa cikin kakausar murya.

“A yau dukkan matsalarka ta zo ƙarshe, don kuwa labarin da na taɓa ba ka shekara biyu da suka wuce, yau ga wacce labarin ya ƙunsa ta sauka a birnin Makkah”

Ya tsura masa ido yana kallonsa, tattausan murmushin fuskarsa ya gaza ɓuya.

“Alhamdulilah Abuya! A wacce unguwa take, yanzu in tashi in je mata?”

Tsohon ya yi ɗan murmushi yana dubansa.

“Dai na gaggawa Ya Annur, a yanzu haka tana sijin ɗin jiddah, dole sai ka yi haƙuri nan da kwana bakwai, wanda ya yi daidai da ranar da za a fito da dukkan yaran da ba su da kowa a garin, a watsa su cikin garin Makkah”

Ya yi shiru, sai dai fuskarsa na nuna alamun tarin tambayoyi da yake son yiwa Abuya.

“Karka damu Annur, alƙalumana basu taɓa nuna mini ba daidai ba, wannan yarinyar da nake ta ganinta kan lamarinka, ina mai tabbatar maka ita ce za ta haifa maka ‘ya’ya da jikoki, sai dai…”

Ya yi shiru yana saukar da idanuwansa ƙasa, “tashi ka tafi, nan da kwana shida ka dawo, akwai abinda zan baka”

“Na gode Abuya” Ya furta gami da miƙewa, har ya kai bakin ƙofa, ya ƙare sautin muryarsa.

“Karka manta, ka yi haƙuri da dukkan abinda zaka gani gun yarinyar, don ina yawan ganin wani duhu, musamman idan na matsa kan son ganin bayyanar fuskarta.”

Ya tsaya tsam! Kamar ya tsorata da zancensa, sai kuma ya juya da hanzari ya fice daga gurin.

Wanene ANNUR?

Annur ɗan Asalin ƙabilar Hausawy ne, don kuwa kakansa da ya haifi babansa,
ɗan asalin Nijeriya ne, Jihar Zamfara cikin ƙauyen Galadi. Yawo ne irin na mutanen da ya kawo shi ƙasar Saudiyya, har Allah ya haɗa shi da wata balarabiyar Yemen, bayan an kai ruwa rana na cewar ba za ta auri wanda ba ɗan ƙabilarsu, da shi ke Allah Ya rubuta sai an yi، sai gashi anyin. Daga nan fa zama ya kama shi a saudiya har zuwa lokacin da aka haifi mahaifin Annur, Sabeer. Daga Sabeer bai ƙara haihuwa ba, duk kuwa da uban aure-auren da ya yi, yana saki, har dai Allah Ya ɗauki ransa. Ya bar matarsa ɗaya Naahid, da kuma ɗansa.

Ta ɗauke ɗanta ta koma can ƙasarsu Yemen, dole iyayenta suka haƙura da fushin suka riƙe su. To bayan Sabeer ya girmane fa, ya ce shi zai zo saudiyya ya fara aiki, don kuwa can in da suke a Yemen talauci ya musu ƙatutu, dole badon uwar na so ba ta haƙura ta barshi. Tunda kuwa ya zo saudiyya Allah bai ƙaddara saduwarsu ba, har itama Allah Ya ɗauki abunsa.

A nan saudiyyar ya ci gaba da zama har zuwa lokacin da ya haifi auri uwar Annur, wacce take Bafulatana ‘Yar Marke dake jihar Jigawa Nijeriya. Wani Abin mamaki shi ma, tunda Allah Ya bashi Annur, bai ƙara ganin kwansa ba, har gashi yanzu Annur ya tasamma shekaru Arba’in a duniya, abunda dai sun canfa gadone rashin haihuwar tasu.

Don kuwa tun Annur na da shekara Ashirin da Biyar Babansa ya masa Aure da wata ‘Yar ƙawar mamansa, amman har aka shekara biyar, ita ko ɓarin wata ba ta yi ba, haka ya dinga aure-aure ya na saki, cikin shekara goma sha biyar, ya auri mata takwas amman shiru kake ji shaho ya ci shirwa.

Dole ta sa ya bazama bin malaman Tsubbu su duba masa, ko shi ba zai taba haihuwa ba ne. Kowane Malami da abinda zai ce masa. Akwai wani Malami da ya taɓa zuwa gurinsa, can wani jeji dake tsakanin Iran da Saudiyya, ce masa ya yi.

“Tabbas Aikina na nunamin cewar zaka haihu, sai dai a duk sanda zan duba naga abinda zaka haifa, sai ya nuna min (K’irdun) biri, don haka nake ba ka shawarar da ka haƙura, don kuwa haihuwar ba alheri ba ce gareka”.

Tashi ya yi a hargitse ya shaƙe malamin bayan ya gama koro masa jawabi, ya za’ai mutum ya haifi biri? Tun daga lokacin yasha Alwashin sai an binciko masa abinda zai haifa, har dai ta hanyar wani Abokinsa ya samu ganin Malam Abuya, wanda shi ne kaɗai ya kwantar masa da hankali da tabbacin akwai yarinyar da zata zo nan da wasu lokuta, ita ce matarsa, za kuma ta haifa masa abinda zai kawo masa jikoki, sai dai ya rasa gane duhun dake lulluɓe da yarinyar.

Tun daga lokacin baya kwana goma sai ya leƙa gun Malam Abuya ya ji ko tazo, malam ya yi ta kwantar mai da hankali, har dai yau Malam da ya tabbatar masa da saukarta a _Makkah._

Hmm!

Ko wa ce ce ?

Cikin kuka ta ci gaba da cewa bayan ta matso sosai kusa da yaron “Wallahi ba zata saɓu ba, idan za su kashe ni ko filin jirgi ban zuwa bare cikin jirgin” Ta ɗan numfasa “Dan Allah yaro gaya min yadda za ai na fita daga gurin nan yanzun nan!”

Yaran biyu suka dubi juna lokaci guda, cike da mamakin jin muryar mace na fitowa daga bakin wadan da suke tsammani namiji ne. “Au wai dama ke ta mace ce, kuma kika yarda aka kawo ki cikin mu?”

“Haba yaro to me kake so na ce musu ? Har sunana na faɗi amman wannan mummunan ɗan sandan ya mini banza, ka ganni fa” ta miƙe sosai tana juyawa, yaran suka ƙyalkyale da dariya lokaci guda, sai kuma mai ɗan doguwar ƙeyar ya yi sauri ya gimtse dariyarsa gami da take tabar hannunsa yana mai kallon ƙofar ɗakin nasu.

Wani ɗan gajeren balarabe ne ya shigo, hannunsa ɗauke da ƙaton tire na Abinci (siniya), a kowane kwano da ke kan tiren ɗauke yake da rabin kaza gashasshiya har guda goma sha ɗaya, yana muzarai ya aje shi gaban yaran, sai kuma ya sunkuya yana fidda ko wane ɗaya, yana ajewa gaban yaro guda, har ya iso kan Deluwa. “Kai ne sabon baƙon da aka kawo yau ko?” Deluwa ta masa banza, bai san damuwar dake shaƙe da ita za ta iya hanata cin Abincin ba ma, ga mamakinta ɗaga idon da za ta yi sai ga Bukr ya zura hannu aljihun gefe na wandon balaraben, a hanakali ya zaro kwalin sigari, suka hada haɗa ido da Deluwa ya ƙyafta mata ido, ya koma baya da sauri ya figi kaza gami da dannawa a baki. Ɗan balaraben ya miƙe cikin rashin damuwa da amsar Deluwa ya fice daga ɗakin yana mai rufo ƙofar.

A hankali ta sadda kai tana kallon Abincin, ji take kamar ba za ta iya ci ba, duk kuwa ƙaunarta da kaza, ‘wallahi bazan koma ko Nijer ba ballantana Nijeriya’ ta ƙara maimaitawa a zuciyarta, sai kuma ta sadda kai hawaye na zuba, ji take kamar ta shaƙe kanta ko ta huta da baƙin ciki.

Yaro Bukr da ke zaune yana kula da damuwarta ya taso kusa da ita “(Ukhty)..” A karo na farko ya kira ta da ‘yar uwarsa, “karki damu, na miki alkawarin ko ban fita daga nan ba ke kam sai kin fita” ta ɗago tana kallon ɗan yaron da ke mata wannan zancen “karka faɗi min abinda bazai yiwu ba yaro, idan har suka maidani ya zan yi ? Shi ma fasfot ɗin nawa yana cikin jaka, kuma jakar na hannunsu, ba ka tunanin zasu duba? Ƙila dama haka Allah Ya ƙaddara mini, ita rayuwa dama ai haka take kamar kaza, wataran idan ta baka kwai, wataran kashi za ta sambado maka” Ta fashe da rishin kuka tana mamakin yau ta tuno ƙaddara a karo na farko a rayuwarta.”

“To ki ci abinci tunda ba za ki yarda za ki fita daga nan ba,” ya furta yana mai toshe kunnensa na yadda muryarta ke masa amsa kuwwa cikin kunne.

Ta tsurawa abincin ido, sai kuma tasa hannu a hankali ta gutsiri kaɗan, ta sauke ajiyar zuciya gami da lumshe mitsi-mitsin idanuwanta sa’ilin da daɗin abincin ya ratsata.

<< Mafarkin Deluwa 5Mafarkin Deluwa 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×