Skip to content
Part 8 of 9 in the Series Mafarkin Deluwa by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Ya ɗago da jajayen idanuwansa da suka rine da hawaye yana kallon dattijon dake gabansa Allahu Dammar hayatak ya Abuya ka ha’ince ni, Azzalumi macuci, Wallahil Azim sai ka dawo min da dukkan abinda ka karɓa a hannuna da kuma Raƙuma na, ya ƙara fashewa da wani hargitsattsan kukan, yana buga hannuwansa saman kansa, lalle baƙin cikin da yake ciki a wannan lokacin baya faɗuwa. Amman ga mamakinsa bayan shuɗewar wasu lokuta yana kukan da furta kalmar tsinuwa gare shi, ba tare da samun wani da zai rarrashesa da kalmar haƙuri ba, balle ma zuciyar ta rage zafi, Abuya ya ɗago kai fuskarsa cike da murmushi yana kallonsa, wanda hakan daya gani ne ya saka shi gintse kukansa ya koma kallon Dattijon.

“Ana Aasif ya Annur! Wannan shi ne baƙin duhun da ire-ire na suka sha faɗa maka, yayin da wasu suke ƙara ƙarairayinsu kan sirrataccen duhun, lalle idan ba na mantawa kai da kanka ka faɗa mini akwai Malamin da ya taɓa faɗa maka abinda za ka haifa da duk matar da za ta haihun ma Biri ne, to kuwa shakka babu duk Alƙalamin da ya kawowa wancan Malamin wannan lamari lalle ya kasa siffanta abinda ya gani ne.” Ya ɗan nisa yana kallon Annur da ya yi satato yana kallonsa har yanzu akwai tarin ɓacin rai a kan fuskarsa…

Kana ya ɗan da, “Yanzu abinda zan faɗa maka ɗaya ne, idan har zaka ji shawarata lalle ba zaka yi nadama game da lamurana ba kamar yadda kake ƙoƙarin yi yanzu, shin kana biye da ni na faɗa maka?…” Ya ci gaba ba tare da jiran amsar Annur ba.

“Tunda har buƙatarka kan haihuwa take bakan mace ba, lalle ka yi haƙuri ka tara da wannan wadar a matsayin matarka, idan yaso a lokacin da ka tabbata ta samu ciki sai ka ajeta a inda kasan ba za ta taɓa tafiya ba, saboda kaidin Mace, koda kuwa keji nema to ka saka ta a ciki, harta haifa maka abinda zata haifa sai ka karɓe abunka ita kuma ka sallameta ta tafi, kaga a nan mun ɓata abinda aka ƙaddaro maka(wa iyazu billahi)!

Ya yi tsai! Yana kallon Malamin  fuskarsa na nuna kamar ya yadda da wannan tsarin kamar kuma bai yarda ba, can kuma sai ya yi sauri ya gintse sa’ilin da idanuwansa suka ƙara hasko masa ita sanda take saukowa daga benen Funduk ɗin, muryar Bukr na masa kuwwa har yanzu a cikin kunnuwansa da zuciyarsa wacce bugunta bai daidai ta ba…

‘Akhee ai gata can ma tana saukowa…’  Ya yi saurin runtse idanuwansa, ba ya son yana ma tuna juyawar da ya yi a hargitse ba tare da ƙara kallon Bukr dake binsa da kira ba, ya tabbata ikon Allah ne kawai ya kawo shi nan inda yake zaune. Ya sauke idanuwansa Abuya, suka haɗa idon ya sake runtse yana jin baƙin cikin kasantuwar abinda zai faɗa…

“Ba ka tunanin idan nabi wannan gugurwar shawarar taka, idan ta tashi haihuwar ta haifo mini irinta, ba ka tunanin na ɓata nasabarmu? Haka na zamo abin dariya ga matan da na shika, abin yiwa nuni cikin alhali abin dariya ga Abokaina? Kai wai ba ka ma tuna idan har ta haifi irinta yaron ko yarinyar ba za su yafe mini ba na auren uwarsu tana matsayin wada da na yi ba? Mummuna ce ya Abuya! Tsananin munin da babu irinsa a kaf nahiyarmu! Biri ya fita kyau, na tabbata gorilla ya fita kyawun gani! Magana da ita za ta iya saka ni suma! Zama kusa da ita zan ji kamar an dunƙule ni ne an jefe a rijiya gaɓa dubu! A haka  kake so na tara da ita? Kashe ni kake son yi?”

Abuya ya saki wani busasshen murmushi yana mai sake kai hannunsa kafadar Annur, ya ce, “karka yanke hukunci kan abinda baka gani ba, kar kuma ka zartas da abinda baka sani ba, kar kuma ka yi hasashen abinda bai taɓa faruwa a ƙissoshin baya ba balle a yanzu. Duk wanda aka halitta a duniyar nan tamu zai iya kome! Idan na ce kome ina nufin har wanda baya da ƙafa da hannu zai iya saƙa tabarma da bakinsa da dungulmin kafaɗunsa da ikon Allah!

Dan haka za ka iya kome idan ka sakawa kanka iyawar! Tashi ka tafi ya Annur, hakan ba za a yi shi ba, ba kuma a yi nufin yin shi ba, ba zai faru ba, ba zai taɓa nuna alamun faruwar ba, maza jeka ka fara shirin aure da matarka.”

Wata kibiya ta soke shi acan cikin zuciya, ji yake kamar ya shaƙe bushasshen dattijo Abuya a duk lokacin da ya furta masa kalmar _matarka_, ya ƙuta yana mai mamakin yadda Malamin nasa ke jujjuya dukkan kalmominsa, kamar ba yanzu ya ce masa an canja ƙaddararsa ba…

A yanzu kuma ya daɗa sahihance masa ikon Allah ke jujjuya komen. Jin kansa na shirin tarwatsewa da tunani da tarin damuwa ya saka shi miƙewa tsaye yana tangaɗi, a haka ya fice daga wurin a cikin idanuwansa babu abinda yake ji da gani sai wani kyakkyawan yaro fari tas me kama da shi yana ɓangala mishi dariya da daddaɗan sauti.
*****

Ƙirrrrrrrrrrr! Ƙaran tangaraho ɗin gefen gadon da take kwance ya fara rinni kamar zai fasa mata dodon kunne. A haka ya katse mata dogon baccin da take yi cike da mafarkai na shirme. Ta tashi da sauri tana muzurai, sai kuma ta saki dogon tsaki sa’ilin da ta kula da abinda ke ƙaran “Aikin banza kawai, ko uban me zan musu da suke tashina da ranar nan oho, ni fa wallahi na gaji da wannan larabcin nasu, zan fa fara zagin uban mutum idan ya ƙara tashina da wani banzan ihu, wai shi garin nan dole ne sai da talho a ɗaka?”

Ta finciko wayar gami da sakawa a kunnenta cikin bala’i za ta fara magana, ta ji muryar Bukr yana faɗin “Ukhtee buɗe mana ƙofa kin yi baƙo, tun ɗazu muke danna _jarass_ ƙinki buɗewa, wane irin bacci kike haka?”

Da sauri ta danƙwafar da wayar tana tunanin wane irin baƙo kuma? Ko dai yaron nan ne ya kawo mata yara, kai daga ji me muhimmanci ne to amma wa ta sani a garin? Ta dai kauda wannan tunanin ta miƙe da sauri, har ta kai bakin ƙofa, sai kuma ta dawo gun mudubin ɗakin ta tsaya gabansa tana kallon kanta tana murmushi, sai taga fuskarta ta yi fayau, mini-minin idanuwanta sun yi haske maimakon ja na me barci, kai ita fa sai taga kamar ta rage da duhu ma sai dai kuma kanta kamar ya ƙara girma. Ga mamakinta sai ta sami kanta da dangwalo farar hoda ta shafa, ta ɗan goga man leɓe, ta fesa turarenta, kana ta isa ƙofar ta buɗe tana mai faɗin “ku shigo”.

<< Mafarkin Deluwa 7Mafarkin Deluwa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×