Skip to content
Part 2 of 2 in the Series Mahaukacin So by Fatima Ismail Abdullahi

“Haba Mama dan Allah, hakurin ki ne ya sa matar nan take mana haka , basa da wani iko da Laila, domin a yanzu bata da wani uba da ya wuce ni .”

Nasir yayi maganar cikin bacin rai

Mama ta ce .

“Nasir bana san tashin hankali, dole gobe zan mayar musu da yarinyar nan, idan ya so tai shekara biyu sai su dawo da ita , ba shi ke nan ba .”

Nasir ya ce .

“Nima zan iya rainon shekara biyun ai , gaskiya babu inda za a kai ta .”

Mama ta mike tsaye cikin bacin rai tana cewa.

“Kai mahaukacin ina ne wai Nasir, to wallahi gobe dole za a basu yarinyar nan ko kana so ko baka so , baki daya shekarun naka nawa suke , tunda aka haifi yarinyar nan ka haukace mana a gida . To Allah ya kai mu goben zan kawo karshen komai .”

Tai tsaki ta shige daki.

Nasir ya karbi Laila a hannun Ummi, yayin da wasu hawaye suka zubo masa .

Har dare yayi Nasir yana cikin takaicin gobe ta yi .

Domin duk wata mafita ya duba domin ganin an bar masu Laila a gidan amman ya rasa yadda zai yi .

Haka da dare ya yi Ummi da Mama suka shige daki da Laila suka kwanta , shi kuwa Nasir yana falo zaune ko abinci ya kasa ci .

Washe gari da safe

Wajejen hantsi Inna na zaune tana hutawa tana tunanin yau za a kawo mata jikarta

Anan kuwa Ummi tunda Allah ya sa ta kula cewa Laila bata nan hankalinta ya tashi , ta duba duk gidan amman bata ga Laila da Nasir ba

Hakan ya sa ta tashi Mama a bacci take fada mata

Nan ita ma hankalinta ya tashi matuka

“To kira shi a waya mana , ko ya tafi kai musu ita .”

Mama ta fada

Ummi ta ce .

“Wallahi Mama wayarshi a kashe tun d’azu.”

Mama tai ajiyar zuciya tare da fadin

“Oh ni Nasir ina ka shiga .”

Ta fita ta nufi dakinsa, koda Mama ta kula da yanayin dakin sai ta ga kamar Nasir ya debe kayansa

Da sauri ta koma dakin su ta duba kayan Laila, ta ga riga guda biyu ce kawai a cikin akwatitinta

“Innalillahi Ummi ba dai Nasir guduwa ya yi da yarinyar nan ba .”

Ummi taji gabanta ya fadi , ta kalli Mama da cewa

.”kamar ya Mama me kika gani wai .”

Cikin tashin hankalin nan Mama ta kara mata da cewa .

“Na duba dakinsa kayanshi basa nan , kuma dubi kayan Laila.”

Cikin faduwar gaba Ummi ta sa hannu cikin akwatin ta ga rigunan Laila guda biyu sai wata takarda da akai rubutu da fensir a ciki .

Da sauri ta dauki takardar tana zaro ido tana kallon Mama

“Shi ne ya aje takardar ko , karanta muji .”

Ummi cikin jin tsoron abin dake cikin takardar ta zura mata ido da nufin fara karanta wa .

“Mama ku yafe ni , ni na tafi da Laila, sai wata rana karku neme ni , kar kuma ku d’aga hankalinku , idan da rabo zamu gana watarana babata . Sako daga Nasir.”

Abin da Ummi ta karantowa Mama ke nan

Mama hannayenta guda biyu ta dora a kai cikin tashin hankali tana cewa.

“Innalillahi wa inna’laihir raji un. Yanzu abin da Nasir zai mana ke nan , wannan wanne irin mahaukacin yaro ne .

Innalillahi wa inna’laihir raji un.”

Mama ta sauke hannayen kasa tare da zama a bakin gado cikin wani yanayi

Dogon numfashi Ummi taja , sannan ta aje shi cikin matukar takaici da tunanin irin abin da Nasir ya aikata musu

“Yanzu ni me zance zanin aro ya bata .”

Mama ta fada tare da fara kuka

Ummi ta durkusar da gwiwowinta kasa a gaban Mama , sannan ta dafa kafar mahaifiyar tasu cikin rarrashi ta fara magana.

“Dan Allah Mama ki dena wannan kukan , in sha Allah duk inda Yaya Nasir ya je da Laila zasu dawo.”

Cikin sabon kukan takaici Mama ta ce .

“Yi shiru Ummi kar zuciya ta buga , yanzu ina zansa rai na idan wannan zancen ya fita.”

Ummi ta durkusar da kai kasa , yayin da wasu hawaye suka gangaro mata , domin tasan tabbas abin da Nasir ya yi ba abin da kuda zai bi bane , dole Mama ta shiga tashin hankali.

Har wajejen 12 na rana , su Mama suna cikin wannan tashin hankali, duk sun kira wasu daga cikin ‘yan uwa , da suke tunanin Nasir zai je amman babu labari.

Anan ita ma Inna sai mita take yi, har Bahijja ta gaji da ji

“To yanzu dan Allah Inna yaushe garin ya waye , ai tunda suka ce zasu kawota , zasu zo ai .”

Inna ta maida mata da cewa .

“Shiru kike ji makad’i ya fad’a rijiya ai , gaskiya abin ya ishe ni haka .”

Bahijja tai ajiyar zuciya tare da gyara zaman yaron dake kafarta mai kimanin shekaru biyar da haihuwa

A lokacin wata ‘yar Innan ita ma ta shigo gidan me suna Rabi .

Yaron mai suna Mahmud ya tashi daga kafar Ummi da gudu ya nufi Rabi , ita kuma tasa hannu ta dauke dan nata sama .

Murmurshi Bahijja tai tana cewa.

“Lallai Mahmud ka kyauta .”

Mahaifiyar Mahmud ta ce .

“To kinga lefinshi , dan gatan babanshi .”.

Ta karasa maganar tana kallon Inna da cewa .

“Inna har yanzu basu zo ba ne .”?

Inna ta dauke kanta , dariya ce taso kama Bahijja, domin wani abin idan Inna tai yana matukar bata dariya .

Kallon Inna tai tana cewa.

“Inna ke fa kina da jikoki , da zaki bar musu Laila, kinga Mama bata dasu .”

Kawai Inna ta fashe da kuka tare da face majina da gefen zaninta tana cewa.

“Allah ya jikanki Batula , Allah ya miki rahma , saboda ita nake son rike wannan jaririyar.

Allah ya jikanki Batula.”

Duk sai jikinsu ya yi sanyi , yadda suka tuna ‘yar uwar su .

Bayan sallar magari ba Mama ta dukufa da addu’a ,

Domin har yanzu babu labarin Nasir

Bayan Mama ta idar da adduarta, ta kalli Ummi da ke gefe ta yi tagumi ta ce .

“Kira kanin mahaifin ku Alaji Bashir, kiji wanne hali ake ciki .”

Cikin mutuwar jiki Ummi ta nufi daki domin dauko waya .

Washe gari

“Zancen banza , zancen wofi , kamar ya Nasir ya bata tare da Laila.”?

Inna tai maganar cikin masifa , Bahijja dai tai shiru , hakan ya sake ingiza Inna tana cewa.

“Ai zancen duniya ba ya buya , tun jiya abin ya faru amman baza su iya sanar damu ba , Allah wadaran sirikai irin wannan wallahi

Aikin banza aikin wofi .”

Ta sake kallon Bahijja da ita ma abin ke dukanta tana cewa.

“To yanzu wanne hali ake ciki , shi kanin baban nasu Bashir me ya yi akai?”

<< Mahaukacin So 1

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×