A daren yau ma kuka Mama take ta yi , carbinta na hannunta Ummi ce take rarrashin ta da cewa . "Mama ki yi hakuri dan Allah, kinji abin da malamai suka ce , suna cikin koshin lafiya , kuma kin san Baba Bashir zai cigaba da kokarin ganin Nasir ya dawo , ki dena kuka ." Mama cikin wannan kukan ta ce . "Ki bari kawai Ummi , Nasir ya yi abin kunya , kiji irin maganganun da mutane suke yi , ba kuma sa duba cewa Nasir kanin mahaifin Laila ne , amman wasu har cewa suke yankan kai zai shiga da ita , wannan wacce irin masifa ce ." Ta. . .