LITTAFI NA DAYA
“Hauwa’u Idris.” Nayi maza na mike tsaye tare da amsawa saboda tun kafin ya kira sunana dama na riga na harhada littattafaina, na zuba su a cikin Jakata.
Ya waiwayo ya zub. mun ido sannan ya ci gaba da kallon dogon littafin da ke ajiye a kan teburin gaban nashi, wanda yake littafin sunayen dalibai ne wadanda suka biya kudin Makaranta, da kuma wadanda ake bi bashi.
Ya ci gaba da kiran sunayen daliban daya-bayan-daya duk wacce ya kira kuma to zata tashi.
Sai da ya gama kiran sunayen ne sannan ya waiwayo ya kalle mu ya ce, “To tsayuwar me kuma ku ke yi a nan?
Cikin sauri kowacce ta fara nufar inda yake, tana fada mishi uzurinta, wata ta ce,
“Malam Babana yayi tafiya ya ce na bada hakuri kafin ya dawo, sati mai zuwa.
Wata ta ce “Malam ni Babana ya ce ayi hakuri kasuwa ce tayi gardama, zuwa wata mai kamawa. Cikir sa’a kuma duk wacce ta kawo uzurinta yana sauraronta tare da ba wata dama.
Sai dai ni kam ban ma doshi inda yake ba, don kuwa a wannan karon ban san me zan cewa Malam Ali ba.
Ya waiwayo a karo na biyu ya sake kallona “To ke tsayuwar me ki ke yi a nan? Ko kuwa kina da wani abin da ki ke son fada ne?”
Na ce, “A’a a hankali ya ce ai ke ko ma me za ki ce mun a wannan karon babu abinda zai sa na saurare ki.
Ni na dade ko ma na ce tunda nake a cikin Malamtaka ban taba haduwa da dalibar da ke cin garabasar karatu irin naki ba. Haba! Wane irin abu ne wannan?”
Na rataya Jakata na juya tare da kokarin
fita a cikin ajin, cikin sanyin jiki lokacin da naji an kira sunana cikin sauri, na amsa tare da juyawa.
Sadiya Tanimu ce dalibar da ke zaune a kujerar da ke bayana. “Ba ni littafina da ki ka karba dazu.”
Na dora Jakata a kan bencin da ke gabana na fara kokarin binciko mata. Littafin na darasin English (Turanci) da na ara a safiyar yau don kwafar rubutun da aka yi a lokacin da bana nan.
Malam ya ce, “Uhum, ba ka ji abin ba, zata tafi miki da littafi. Allah dai ya sauwake irin wannan abu to wai idan uba bai tsaya yaga ya ilmantar da ya yanshi a wannan zamani ba me zai yi mishi ne na gata kuma? Da irin wannan wahalar banzan da ki ke yi na kullum kina cikin wadanda ba su biya kudin makaranta ba dama aure aka yi miki ki ka huta don ban san yadda za a yi kici jarrabawar gama makaranta ba a irin wannan tambelen da karatunki yake yi.”
Ni halina da Hausawanmu kenan wai ba za su tsaya suga sun biyawa ya’yansu kudi sun yi karatu ba, amma idan an tashi aurensu sai kaga mata ta sunkuya karkashin gado tana zaro ‘yan marofiya da masu hannun katako.”
Yan aji suka kwashe da dariya, yayinda na mikawa Sadiya littafinta na kama hanyar barin ajin.
“Ki hutar da kanki kada ki dawo, don kuwa sai dai idan ban gan ki ba ko a ina ne kuwa za a kore ki gida.
In tsaya cewa maganar Malam Ali bata 6ata mun rai ba ma to zance ne, kuma ku san kullum haka yake yi mun, idan yazo ajinmu koran kudin Makaranta ba zai bar ni da takaicin koran kawai ba, sai ya bini da bakaken maganganu.
Ni kuma ba abin in yi zuciya na ce na daina zuwa ba tunda idan na ce haka ba zan yi karatun ba kenan, don kuwa ba biya mun din za a yi ba.
Duk wadannan takaicin da nake sha lada ne akan a ce an fara jarrabawa, ranar da duk wani dalibi yake. dokin zuwanta saboda lokaci ne na nuna bajinta da kuma gwaji kan abin da aka koyar da kai da kuma gane irin fahimtar da ka yi. Sai dai ni takan zo mun ne cikin tsananin fargaba, don kuwa rana ce ta babu sani babu sabo, idan har ana binka ko da kwandala ce daya to babu ko shakka za a kore ka gida.
Na rinka bin Malamai kenan ina kamun kafa wadanda za su tabuka mun wani abu ma wadanda babu wani taimako da za su yi mun ba.
Wani lokaci ma kaga an bar wasu sun shiga ajin jarrabawar wata kila saboda su din kudin zango daya ake bin su, ko kuma. Wasu sauran canji da ba su gama biya ba.
Ni kuma a hana ni ko wani Malami ya tausaya yasa baki sai ka ji Malam Ali yana cewa ai ko an barta ta shiga da alkawarin biya ba biya zata yi ba.
Ana binta bashin da ya kai na shekaru uku, don haka barta nan kawai ta karaci zamanta ta tafi.
Idan har akwai wani abu da nake burin yin shi a rayuwata, to kuwa karatu ne, sai dai ina ji ina gani abin yana nema yafi karfina.
Babana ba shi da karfi, ba zai iya biya mun kudin Makaranta ba, haka nan bai ciyar da gida ba. Har a yanzu da muke mu bakwai ‘ya’yan Mamanmu, shi din albashinshi a wurin da yake aiki bai fi Naira dubu goma sha biyar ba a wata.
To da me ya ciyar damu, da me ya biya mana kudin Makaranta da kuma sauran hidindimu na rayuwa? Ta kai ma shi kanshi ya hakura da karatun kannena maza ya saka su a sauran wurare irin su, koyon dinki da kuma kanikanci don ganin ya maida hankalinshi kan nawa karatun ni kadai amma abin ya gagara.
Don kuwa da albashin nashi kafin wani watan ya zagayo an lamushe shi a bashi. Dan sauki-saukin da muke samu to na
sana’ar dinkin da Ummanmu take yi ne inda wani lokaci takan samu tayi cikon cefane har ta adana mana dan abinda muke hidima da shi na sallah.
Idan shekara ta zagayo babban abu guda daya kuma mai muhimmanci a wurinmu gaba daya shi ne muna da kwanciyar hankali da nutsuwa tare da addini mai yawa a cikin gidan namu. Don haka zama muke yi cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
Na kamo hanya don komawa gida zuciyata cike da kunci, don kuwa wani irin nisa ne a tsakanin gidanmu da makarantar wanda kuma a kullum da kafa nake zuwa nake kuma dawowa.
Sannan a mafi akasarin lokuta na kan tafi ne ba tare da nayi karin kumallo ba, don kuwa na kan kasa hakurin jira don kada nayi latti.
Tafiya zan kuma tafi ne ba tare da ko sisi ba har sai na dawo ne zan ci abincin da na samu an yi.
Ina karyo kwanar unguwarmu na hango Abdussamad zaune kan dakalin shagon askin dake makwabtaka da gidan su.
Wani irin faduwar gaba na samu, nan take na juya na koma ta daya hanyar duk kuwa da cewar ita din tafi nisa zan iya cewa kusan kullum aka koro ni kudin Makaranta, to sai na ganshi matukar ba komawa tashi Makarantar yayi ba.
Na kane da niyyar na share shi nayi kamar ban ganshi ba, don haka na sunkuyar da kaina na ci gaba da tafiyata har na dan gota su.
Sai naji ya ce “Barka da dawowa, ranki shi dade. Cikin wayancewa na ce “Af, ai ban ganka ba ne. Tare da dan murmushi. Ya mike ya nufo ni tare da kakkabe wandonshi yayinda yake karasowa inda nake. Ya dan tabe baki tare da cewa.
“Da dai kamar ban sanki ba ne ki ka fada mun haka, to dana yarda.
Na fara gaishe shi bayan mun faraa tafiya yana amsawa. Na ce, “Ashe baka koma ba har yanzu?”
Ya ce, “A’a na koma jiya dai na sake dawowa da yamma saboda wani yajin aikin da Jami’o’i suka fara satin can da ya wuce.”
Na ce, “Cabdijam! Abin dai babu dadi.
Ya ce, “Eh to, kusan hakan, kin san yanzu babu ranar komawa dai kenan halin yajin aikin kasar nan, idan ba matukar sa’a muka ci ba sai mukai watanni biyar nan gaba zaune Gwamnati bata dauki wani kwakkwaran mataki a kai ba.
Tunda su babu ruwansu, don talaka ne a matsala tunda mu ne muka cika cikin Jami’o’ i kasar, su nasu suna can Turai suna karatun cikin kwanciyar hankali, mu kuma muna nan muna gwagwagwa.Karatun da zai dauke ka shekaru hudu idan ba matukar sa’a kayi ba sai ya kai ka shekaru shida kana yi ba ka gama ba. Shi yasa ai tun yanzu muke muku addu’a komai ya gyaru kafin zuwan naku lokacin, sai dai banga alamar ke za ki yi nisa ba, nafi zaton aure za ki yi da alama.
Na kalle shi na ce, “Uhum! Sai anjima.” Na shiga gida saboda karasowar da muka yi kofar gidan mu. Akwai mutunc1 mai yawan gaske a tsakanina da Abdussamad, don kuwa duk shariyata da mutane suke magana akai, shi kam muna gaisawa har ma mu dan yi hira, saboda shi ko na wuce shi to zai yi mun magana har ta kai ma ba na ma iya wuce shin.
Makwabcinmu ne sosai, haka nan Babana da Babanshi suna mutunci sosai a tsakaninsu. Nayi sallama na shiga gida, yan kananan kannena ne suke wasa a tsakar gida da alama Umma ta hana su fita zuwa kofar gida ne.
Tasi’u da Sabi’u, a guje suka taho suna rige-rigen karbar Jakar Makarantana. Na mikawa Tasi’u saboda nasan Sabi’u ba iya dauka zai yi ba, na kuma yi mishi dabara ta hanyar daukanshi na cilla shi sama na cabke.
Don kada ya saka mun rikici muka karasa shiga dakı, suna yi mun hirar su ta shirme Umma tana zaune a kan tabarma a tsakar dakinta, yanka take yi na atamfa.
Na tsugunna nayi mata sannu da gida, ta amsa ba tare da ta tambaye ni dalilin dawowana ba, don ta riga tasan abinda ke dawo da ni a irin wannan lokacin.
“Shiga ki tube kayan Makarantarki ki saka na gida, ga dumame nan sai ki diba kici. Na ce, “To. Sai dana gama cinye dumamena daa muka ci tare da su Tasi’u sannan na sake hada kwanukan da sukalalacena wanke na sake gyara gidan, na wanke bayan gida sannan na sake dawowa wurin Ummana ce, “Umma za a dora wani abu nea wuta?
Ta ce, “Dan saurara dai tukuna muga dawowar Auwalu ko?” Na ce, “To.” Na mikena shiga dakina dake tsakar gida na
dauko littattafaina na Makaranta don na dan yi bita.
Har karfe daya na rana shiru Auwal bai dawo ba, hakan ne ya sani sake tashi na shiga cikin kicin dinmu na dauko dan sauran garin kwakin da ke ajiye don na jika musu.
Na kawo sugar na saka na mika musu cokala sannan na dauki buta don yin alwalar sallar Azahar.
Haka rayuwarmu take a gidanmu, kusan kullum muna kwanciya ne da daddare ba tare da mun san abinda zamu ci idan gari ya waye ba.
Haka nan idan safiyar tayi muka samuu muka karya kumallo, to ba ma sanin abin da zamu ci idan rana tayi.
Saukin abin ma shi ne, yanzu Auwalu ya kawo karfi yana kuma matukar taimakawa.
Auwalu shi ne wana da nake bi, shi ne kuma da na fari a wajen Iyayenmu baki daya.
A yanzu haka makanike ne a cikin babbar kasuwa, sai dai har yanzu ba kwarewa yayi ba, amma yana matukar samun’ alheri ba kadan ba.
Saboda sa’ar da yayi na haduwa da shugaba na kwarai, illa ko yau ma shi ne ya shigo da cefane a hannunshi don haka na shafa fatiha cikin sauri na fito na karbe shi.
“Akwai itace ne? Na ce, “Bari na duba. Na leka kicin din na ce, Akwai, amma dai babu yawa.
Ya juya ya fita, yayinda ni kuma na fara kacaniyar dora girkin, ya sake shigowa da itace kai biyu a hannunshi ya zuba tare da miko mun Naira ashirin.
Ki bai wa Tasi’u ya sayo miki maggi, ni na manta ban siya ba. Na ce, “To.” Ya juya da niyyar komawa wajen aikinshi.
Tuwon masara nayi tare da miyar kubewa danya, saboda ita na gani a cikin cefanen, ta kuma yi dadi da yawa na tuka don mu samu na dumamen safe.
Na kwashe na adana na kowa tare da rufewa na janye itacen na dora ruwan wankana a kan garwashin sannan na kawowa Umma nata.
Sai da nayi wanka na yiwo alwalar sallar La’asar, don kuwa zan iya cewaa yanzu dabi’ata ce hakan saboda kusan kullum abincin yamma muke yi.
Na idar da sallar La’asar na jawo kwalbar maina da Auwalu yake kawo mun mai kamshi.
Duk da ba wani mai tsada ba ne, shafa shi yana sani naji ni’ima saboda kamshin shi.
Na murza hoda da dan kwalli na jawo atamfata na daura sannan na fito nazo inda Umma take na zauna don naci nawa abincin.
Muka dan fara hira wacce yawancinta akan Makarantata ce. Tace “Sai ki yawaita addu’a, Allah ya zabar miki mafi alheri a ciki, ko karatun idan zai yiwu. ldan kuwa ba mai yiwuwa ba ne to sai kiyi aure a kai ki dakinki kema ki nutsu ki zauna a wuri daya.
Babban burin Iyayena bai wuce na ganin nayi karatu ba, ko da kuwa wacce irin wahala za su yi don ganin hakan.
Hakan ne yasa da Umma tayi mun wannan maganar gabana yayi matukar faduwa, ta soma hakura kenan ko ya ya?
Na ce, “Umma aure fa ki ka ce?
Ta ce, “Eh shi na ce idan karatun ba zai yiwu ba menene amfanin zaman gidan tunda kin riga kin isa auren.
Shi ma Babanku ai ya na ga ya fara hakura tunda naga an kwan biyu ba tare da yayi maganar Makarantarki ba.
Jikina yayi matukar yin sanyi, dafin maganar Umma sai dai ban ce mata komai ba, don ba maganata ba ce tunda ba zan iya tuna ranardas wata magana makamancinyar wannan da ta danganci aure ta hada ni da ita ba.