Skip to content
Part 11 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Abulkhairi ya falla a guje ya tafi don yi mishi oyoyo din da ya saba. Yana daukanshi ya shigar dashi cikin daki ya kulle ya dawo.

Me na gaya miki a kan mutanen nan iye? Na fara ja da baya saboda matsowar da yake yi da kuma abinda na gani a idonshi na tashin hankali.

Ni kuma a yanzu babu abinda nake tsoro irin dukan Ishak, sai dai ban tsira ba. Duka sosai ya lakada mun ya tara mun jini a ido.

Kwana nayi ina kuka, haka nan Abulkhairi duk da kin barin shi yazu gurina da yayi ya shiga dakinshi da shi ya rufe kofa.

Na fara gajiya da irin wadannan abubuwan har gashi yaro ya fara fahimtar wasu abubuwa ya tayaka kuka.

Da kyar na lallaba da asuba na shiga bayangida na gaggasa jikina, har da fuskata na dawo alwala nayi sallah.

Lokacin ne shima ya bude kofa ya fito don zuwa Masallaci.

Har da gari ya waye bai bar Abulkhairi yazo wajena ba, da kanshi ya ba shi abin karyawa ya yi mishi wanka ya sa shi a mota ya tafi da shi, ban san inda suka tafi ba.

Ko girki ban iya yi ba sai tea da na wuni sha saboda mummunan ciwon daa jikina yake yi mun, ba su dawo ba sai karfe hudu na yamma.
Yana sake Abulkhairi dakina ya nufo a guje.

Ina kwance gwalandin magana yana tambayata wai Babanshi ne ya dake ni to nayi hakuri kin ji Mama.

Ban ce mishi komai ba amma duk kokarin hana hawayena zuba da nake yi bai fasa gangarowa ba.

Ya shigo dakin ya rike hannun Abulkhairi yaja shi suka sake fita, na ci gaba da kukana.
Idan na bari Ishak yana yi mun irin wannan dukan wanda jinýa take biyo bayanshi anya zan kai labari kuwa?

Ya sake shigowa dakin rike da leda a hannunshi ya zauna a kan stool din gaban dressing mirrow yana ciro abubuwan cikin ledar.

Robar abincin ne na take away sai gasasshiyar kaza sai magunguna. Tashi kici abinci, ban ce mishi komai ba, amma ban iya daina kallonshi ba.

Abulkhairi ya matso, “Mama tashi.” Yasa hannu yana girgiza ni ban motsa ba.

Ya fita ya dawo da robar swan ya kama
ni zai daga ni na fizge hannuna na koma na sake kwanciya.

Shima fita yayi bai sake ce mun komai ba. Na sake fashewa da wani sabon kukan, babu irin tunanin da bai zo mun raina ba.

Ya zama dole na hemi mafita abinda kawai zuciyata take kara jaddada mun kenan.

A hankali sai na samu sauki na ci gaba da hidimomina, sai dai idona har yanzu bai washe ba. Zazzabi sosai ne ya kama Abulkhairi wanda yasa Ishak ya sauke mu a asibiti don ganin Likita. Muna zaune muna bin layi a sashen yara sai kawai naga Sadiya Tanimu cikin mamaki na rike baki ina kare mata kallo sanye take da fararen kaya na jinya wato Nurse na ce, Sadiya kada dai ki ce mun kin zama Nurse?

Ta ce, a’a haba ce miki aka yi abin babu wuya, ina dai shirin zama wannan ita ce shekarata ta farko.

Na ce, Au to koda dai naji. Ta ce, ai sshekara biyu kenan rabon da muga juna kin tuna?
Sai lokacin ne na tuna zuwanta na karshe wajena da abin da ya faru tsakaninta da Ishak. Na dan yi murmushi na ce haka ne fa ba mu sake haduwa ba.

Ta sunkuya daidai inda Abulkhairi yake ta mika mishi hannu tare da cewa “Hi handsome ya ka ke? Ya ce, Salamu alaikum Babana yake cewa.

Ta ce, To ko kuwa ya ce, Eh to ce to ka gani kenan akwai ‘bambanci. Ta mike ta gyara tsayuwarta ta ce, yaron ki ya mun kyau gashi da wayo na ce baki yi aure ba?

Ta ce, Eh to muna kan hanya na ce to Allah ya ba da na kwarai. Ta kara zuba mun ido tana kallona ta ce, Kin san wani abu ne?

Mijinki exactly mijin Sister ta shi yasa abinda ya yi mun bai bani haushi ba. Idan ya tashi dukanta itama sai idonta ya bar jini, na ce kai! Sadiya kenan baki da dama ce miki nayi dukana yayi jini ya taru mun a ido? Ni ciwon ido nayi.

Ta dan tabe baki kamar dai yadda ta saba ta ce, Oho dai ni na gaya miki nasan maza irin su. Abu daya za ki yi ki taimaki kanki ki koma Makaranta shi kanshi wataran idan aka ce ya buge ki ba zai fara ba.

Shi yasa wani lokaci ma ko son tunanin aure bana yi saboda irin wannan tauye hakkin.
Ai ba haka aka ce ayi auren ba. Ban cewa Sadiya komai ba amma dai ina ganin shawararta zan bi to ta ina? Ni dai nasan ba karamin yaki za a yi da Ishak ya bar ni na koma Makaranta ba.

Sai da muka gama ganin Likita sannan na kira shi a waya yazo ya kai mu gida.

Muna zaune da dadare bayan mun gama cin abinci na kwashe kanukan duk da faduwar da gabana yake yi.

Ban fasa yi mishi maganar ba cikin hanzari kuma ya dakatar da ni irna so in tabbatar miki da komawarki Makaranta ba zai taba yiwuwa ba.

Nayi shiru zuwa wani lokaci na ce kayi hakuri ka gaya mun sharuddanka na yin karatuna ba zan kaucewa dokarka ba, ka ji?

Na tambaye shi ya mike ya zauna ya zuba mun ido, Kina son yin karatu? Cikin sauri ya ce, To ga zabi zan baki.

Sai kiyi wanda ki ka fi so, babu matsala duka zan yi miki. Za ki zauna ne kiyi zaman aure shi kadai ba tare da kin yi karatu ba ko kuwa za ki bar zaman aurenki ki koma karatu?

Gabana ya yi mummunan faduwa, na dago kai na kalli Ishak da ya zuba mun ido yana kallona.

Wacce irin tambaya ce wannan? Ishak yana nufin kenan idan har zan zauna da shi ba zan koma Makaranta ba, haka zan yi ta zama dashi da halayenshi?

Ya raba ni da “yan uwana, ya raba ni da kowa haka nan kankanin abu idan nayi ya rufe ni da duka tamfar an aiko shi.

Amma hakan bai ishe shi ba ya tsare ni da irin wadannan tambayoyin saboda rainin hankali.
Ina son aurena duk da irin abubuwan da nake fuskanta, to amma idan na zabi auren nashi ai zai ga kamar naji tsoro na kuma ba da kaina ban kuma san abinda zai biyo bayan hakan ba.
Haka nan shi idan ya matsu da auren ai sai ya bar ni na ci gaba da karatuna saboda nima na samu mafita kan matsalolina, kenan dama ce ta zo mun.

Ya ce, Ke fa nake jira. Wanne ki ka zaba? Na ce, “Karatu. Ya ce, “To babu laifi. Ya koma ya kwanta.

Na hau gado na kwanta a raina ina tunanin babu mamaki nima nan da yan watanni kadan na koma na ci gaba da makarantata.

ldan na gama kuwa na tafi na zama nurse har yanzu ban canza buri ba. A haka barci ya dauke ni.

Da sassafe na shiga dakin Ishak don na gaishe shi ya gama amsawa na mike don fara shirin abin karyawa.

Ya ce, Zo. Na dawo na sake zama. Ungo wannan. Na karba, takarda ce ina jiran ya yi mun bayanin wanda zai zo ya karba ko wani abu makamancin hakan.

Sai na ji ya ce, “Zabin ki ne nakaratu don haka kije kiyi na sauwake miki.” Bai jira amsawata ba ya juya ya fita a daki.

Ina zaune a wurin kwakkwaran motsi na kasa yi, sauwakewa saki kenan ko me? Sai dai har a yanzu ban bude takardar na ga abin da ke cikinta ba. Ya sake shigowa dakin ya ganni a inda nake zaune.

Ya ce Kije “gida kiyi musu bayanin komai.” Na mike na dawo dakina na dauki hijab da Jakata nasa hannu na dauki Abulkhairi da har yanzu yake barci na saba shi a kafadata na fito falo zan wuce ya ce, Zo Hauwa’u.

Nadawo ya ce, “Sauke shi. Nayi sokoko ina kallonshi ya sake cewa “Sauke min shi. A lokacin da ki ka yi zabin da ki ka yin ba ki kalle shi ba, yi kawai ki ka yi ba tare da kin yi tunanin wasu abubuwa masu girma za su biyo baya ba.

Abulkhairi dana ne ni ke da cikakken iko a kanshi, don haka ajiye mun shi. A hankali ya mike har inda nake yazo yasa hannu ya dauke shi a kafadata ya shimfide shi tare da dan jijjiga shi a hankali ganin yana kokarin farkawa na dawo gida cikin wani yanayi da baya kwatantuwa.

*****

Umma tana ganina ta ce “Lafiya ki ka bugo irin wannan sammakon haka? Ina yaron?”

Na ce, Yana tare da Babanshi. To lafiya dai ko? Ta sake tambayata na ce, Eh Baba nake son gani.

Ta ce, Ikon Allah, to ai yanzu ya tafi sai dai ko ki yi sammakon zuwa da safe, ko kuma ki dawo da yamma. Neman wuri nayi na zauna ba tare da na ce mata komai ba. Ta sake bina da kallo ta tashi ta kawo mun abin karyawa ta ce, To ga shi nan ki karya ko?”

Duk da ban ci komai ba na fito daga gida ban ji wani alamar yunwa a tare da ni ba.

Ina kallon Umma tana ta harkokinta da yaran da suke zuwa siyan kaya da kuma su Tasi’u. Itama ta Iura ta gane ba zan yi magana ba ta rabu da ni.

Sai dai a duk lokacin da nayi nufin kallon inda take sai naga itama ni take kallo. Zuciyata tana ta kaiwa da komowa. Ban taba tunanin zabin da nayin zai zamo haka ba. To me Ishak yake nufi kenan?

Babana bai dawo gida ba sai wajen karfe biyar na yamma, yadda dai ya saba dawowa kenan. Yana ganina ya ce, “A’a Hauwa’u ce yau a gidan? To ina abokin nawa?

Na ce mishi yana gida Baba. Na durkusa na gaishe shi. Ban yi mishi wata magana ba sai da ya ci abincin shi ya samu nutsuwa sannan na mika mishi takardar da Ishak ya bani wacce har a yanzu din nan ban iya budeta naga abinda ke cikinta ba.

Cikin nutsuwa ya budeta ya fara karantawa. Babana duk da yake Masinja a Banki ya iya karatu da rubutu daidai gwargwado.

Inna lillahi wa inna ilaihir-raji’un. Abin da ya biyo bayan karatun nashi kenan.

Yayi shiru na kusan mintina biyar sannan ya ce, Ikon Allah! Me ki ka yi mishi da zafi haka Hauwa’u da yayi nufin yanke miki irin wannan hukunci mai tsanani? Ba zai yi miki saki daya ko biyu ba sai ya yi miki uku gaba daya.”

Na dafe kirji da sauri na ce “Uku Baba? Yau na shiga uku! Tuni na fashe da kuka. Mikewa nayi cikin sauri da nufin fitowa a gidan na koma gidan Ishak. Babana ya ce Ina za ki je? Na ce, “Baba zan dauko Abulkhairi ne.”

Ya ce, “Dawo kawai Hauwa’u, ba shi ya karbe shi ba? Na ce, “Eh Baba ai cewa ya yi nazo nayi muku bayani ne kafin na koma na karbe shi.”
Ya ce, “A’a bar mishi danshi kawai kiyi hakuri. Wata rana za ki ga kamar ba ayi ba, ki daure ki zama Jaruma ki yawaita addu’a, Ubangiji yayi miki zabin miji nagari da zai zamo miki alheri fiye da wannan da ku ka rabu.”

<< Mai Daki 10Mai Daki 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×