Skip to content
Part 12 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Cikin sanyin jiki na koma dakin Umma na hau kan shimfidar na sake zama. Ita kuwa tana ta harkokinta na kokarin ganin ta karasa abincin daren da take yi. Ban taba sanin haka abin zai zamo ba, yanzu duk wannan zaman da muka yi da kuma hakurin da na rinka yi a haka auren zai kare?

Lallai Ishak ya wuce sanina, don kuwaban taba zaton zai yi mun hakan ba. Ko da ya bani zabi kuma na dauka karkari ya yi mun saki daya ne ba uku ringis ba. Hakan ya yi ne don ya nuna mun dama can ni ce na damu da zaman ba shi ba.

Auwalu ne da kanshi ya shiga dakina na da ya tsaftace shi ya gyare shi tsaf ya sayo sabuwar katifa waya takwas da zanin gado da filo guda daya ya ajiye ya shimfida leda a tsakar dakin don na dan ji dadin zama a ciki.

Kwanaki biyun da nayi a gida ba masu sauki ba ne ko kadan don kuwa kwtaa-kwata bana barci.

Babu abin da yafi damuna irin kwace Abulkhairi da Ishak yayi da dai a ce yayi mun sakin ne sai ya bar ni na taho da dana to da abin ya zamo mai dan sauki a wurina.

Shi kenan shima yanzu nasan yana Kaduna wurin Yaya tare da su Anas da Rukayya. Ina zaune ne a gida amma ko tsakar gida ba fitowa nake yi ba ballantana naa taya Umma wan1 aikin gida. Idan har nasa kafata a waje to kuwa wanka zan yi ko wani uzuri ko kuma alwala.

Ko abinci Tasi’u ne ko kuma Sabi’u suke kawo mun na kasa sakewa ko kadan naji dadin zuciyata. Itama Umma harkokinta take yi ba tare da ta saurare ni ba don kuwa har a yau dinnan bata ce mun komai a kan maganar ba ballantana ta tambaye ni abinda ya hada ni da Ishak yayi abinda yayin.

Ranar da na wayi gari kwanana bakwai a gidan ranar ne dan aika ya yi sallama ya dire mun akwatunana wadanda su ne kadai abinda na mallaka a gidan Ishak.

Komai na same shi ne a can ya kuma miko mun zungureriyar envelop ya ce in ji Ishak din. Na koma daki na zauna na bude wata ‘yar gajeriyar wasika ce, ga abinda ya ce:


Hauwa ‘u,

Ina fata kina nan lafiya?, Ga kayanki a bayar a kawo miki, don nasan kina da bukatarsu. Wannan kudin kuma kiyi amfani da su wajen ganin kin koma Makaranta tunda na gane hakan yana da matukar muhimmanci a rayuwarki, tunda ki ka zabe shi a kan aurenmu.

Ina so ki san zan zamo mai taimako kwarai ta fannin karatun naki a duk sanda ki ka bukaci nayi hakan. Ina miki fatan alheri. Abulkhairi yana gaida Mamanshi.

Na gode.

Na bude daya envelop din, rafa ce ta dubu daddaya guda daya.

Na mayar a ajiye na fara duba kayana, duk wani abu da na mallaka a idanshi ya saka mun a cikin akwatuna set daya mai shida.

Sai saitin Encholac guda daya mai uku. Na jawo babbanalbum dina wanda hotunan Abulkhairi ne kadai a ciki na bude hotonshi na karshe na fara gani wanda aka yi mishi shi a ranar da ya cika shekaru biyu a duniya.

Nasa hannu na shafa fuskarshi da ke murmushi a hoton ko sai yaushe zan sake ganinshi, sai Allah.

Hawaye suka yi ta zubo mun. Ya zama dole na wartsake na fuskanci al’amuran da ke gabana.
Ba zai yiwu nayi ta zama cikin kunci don kawai Ishak ya sake ni ba. Rayuwata yanzu ne take farkon ganiyarta, tunda ko a bana shekaru ashirin da daya ne da ni, auren kuwa shekaru hudu.

Wartsakewa nayi na fito tsakar gida na fara taya Umma hidimar gidan da kuma harkokinta na saye da sayarwa. Irin su bayar da abu idan an zo siye, karbar kudi da kuma bayar da canji, muna kuma yan hirarrakinmu.

Su Tasi’u ma ganin na dan soma wartsakewa murna suka rinka yi. Bini-bini su zo su zauna a inda nake suna yi mun magana.

Babana yana dawowa da yamma sai da ya gama cin abinci sannan naje na same shi.
Na sake gaishe shi sannan na kawo mishi batun bukatata na son komawa makaranta, don ganin na ci gaba da karatuna.

Shiru yayi yana kallona, kallon da yake yi mun shi ne yasa ni ta kara shiga taitayina tun kafin naji abinda zai ce.

Ke! Kina cikin hayyacinki kuwa? Anya wani abu vai shiga kwakwalwarkii ba? Idan ma kin kaso aurenki ne don ki koma Makaranta, to ki kwaan da sanin hakan ba zai yiwu ba, shashashar yarinyar kawai, wacce ta ke nema ta mayar da kanta wata iri.

Tun kafin ki gama Iddah har kin fara kokarin neman abin yi saboda ke addinin ba damuwa ki ka yi da shi ba ko? Tashi ki bani guri na sha iska.”

Idan na ce ban shiga mawuyacin hali ba ma to nayi karya. Duniyar tayi mun wata iri. Nayi ta kokarin ganin na sake jikina nayi hidimar gabana amma abin ya gagara.

Don kuwa ko na dan manta kuma na dan lokaci ne sai naji kamar wani abu ya muntsini zuciyata.

Ko da ba wani jin dadin zama da Ishak nake yi ba sai na fahimci dakina shi ne cikakken ‘yancina.

Sai nake ganin kamar na rasa komai babu Abulkhairi wanda a kullum kewarshi take sanyanına rasa sukuni.

Tsananta wa kana aikace-aikace da nayi sai yake debe mun kewar zaman tunane-tunane wadanda ba za su amfane ni da komai ba.
Kullum na idar da sallar asuba sai kawai na fito tsakar gida na wanke ta kwal na wanke mana bayan gida na ciccika randunan ruwa.
Nayi wanke-wanke nayi wanki sannan na dora abin karyawa.

Yaya Auwalu da kanshi sai da ya ce, aikin ya yi yawa na rage. Murmushi kawai nayi ban ce mishi komai ba. Idan nayi wanka sai na dora mana abincin rana nayi na dare, Umma kuwa tana harkar kasuwancinta wanda kullum kara bunkasa yake yi. Yanzu gidan ba a rashi kamar da. Dan albashin Babanmu da kuma sana ar Umma wani karin rufin asiri ne a gare mu baki daya.

Ga Yaya Auwalu da a yanzu saukin abubuwan da ya samu na gida yasa yake ajiye mana hatsi a maimakon kullum a yi ta awo.

Don kuwa a yanzu shima oga ne na kanshi duk da dai ba rabuwa yayi da maigidan nashi ba.
Duk da hakan dan kankanin lokaci ne kawai sai na zube nayi baki. Ganewan da nayi in ba matukar hankali nayi ba zan canza gaba daya yasa nayi tsaye don ganin na kula da kaina ta wurin cima da kuma gyaran jiki.

Iddahta ta cika ne ana gab da fara Azumin watan Ramadana mai albarka, bai fi saura sati uku ba.

Zuciyata sai kaiwa da komowa take yi akan na sake samun Babana a kan maganar Makarantata.

Babu mamaki a yanzu tunda na gama Iddah ya yarda amma ina matukar jin tsoro don kuwa wani abu makamancin wancan bai taba faruwa tsakanina da shi ba.

Ina zaune a kan shimfidar tabarmar da nayi a tsakar gida ina taya Umma kullin gishiri.

Yayin da take gete tana lissafin kudin cinikinta na ce “Umma ko za ki taimake ni ne ki yiwa Babanmu maganar Makarantata tunda a yanzu babu wani nauyi a kaina.”

Ta ce, “A wane dalili?”

Nayi shiru ina tunanin abinda zan fada mata don gamsar da ita zamana a haka ba shi da wani amfani.” Sai ta ce, “Kina so né na taimaka miki ki bijirewa maganarshi? In yaso kenan nima sai nasa ran wata rana zai kafa doka-ki taimaka a karya dokar ko?

To ba zan iya ba. Babanku burinshi a yanzu na ki samu miji ne kiyi wani auren, ki zauna a dakinki cikin rufin asiri. Yanzu da da ba daya ba ne. da da yake burin ganin kin yi karatu to ya wuce.

Yanzu ke ba yarinya karama ba ce, koda ba ki da yawan shekaru a kanki yanzu kuwa burinshi bai wuce na ganin kin zauna a dakinki kin nutsu kin samu mijinki da zai kula da al’amuranki ya kuma tausaya miki.
Ba wanda zai nemi wulakanta ki ko tozarta ki ba, karatu ga budurwa ba dole ba ne ballantana ga bazawara.

Wani irin faduwar gaba naji da Umma ta kira ni Bazawara.

Nan da nan sai maganganun Umma suka zamo tamfar fami a zuciyata, nayi wunin ranar ba tare da na yi wani kuzari ba.

Shi kenan ta faru ta kare wai an yi wa mai dami daya sata. Aurena ya mutu a kan karatuna gashikuma karatun yana nema ya gagara. In ba wani ikon Allah ba. Dare ya yi nisa bacci ya ce bai san idona ba sai juyi nake yi a kan ‘yar katifar tawa.

Zamana da Ishak ya rinka dawo mun a raina rashin yanci na walawa da mu’amalla da fargaba a kowanne lokaci.

Kamar ba aure ba. In ban da ma zuciya banga abinda zai sa har sakin da yayi mun ya daga mun hankali ba.

Matsalar daya ce, Babana da yaja yatsaya akan ba zan koma Makaranta ba. Ba dai a gidanshi ba. Idan na auri wani mijin yaga zai bar ni na koma Makaranta.

“Yo wannan a tsakanın mu. Haka kawai naji zuciyata tana bani shawarar zuwa birnin kudu nayi Azumin Ramadan a can.

Don haka tun kafin Babana ya fita naea anar da shi, na kuma yi sa’a bai hana ni ba.

Ya ce,”Yaushe ki ke son tafiya? Na ce, “Ko zuwa nan da kwanaki uku.” Ya ce, To.” Ya shiga daki ya fito ya ce, To ungo rike kiyi kudin mota sai kiyi manejin su.

Na ce, Lah, Baba ai ina da kudi, ya ce eh karbi dai ki kara. Nayi godiya. Umma ta shiga kokarin hada mun kayan tsaraba irin su omo, sabulun wanka, sabulun wanki, sugar, maggi da dai sauransu tunda Su karkara ne.

Shiryawa nayi don zuwa kasuwa saboda siyayyar da zan yi na tafiya.

Kwalliya sosai nayi ban kuma san dalilina na yin hakan ba. Doguwar riga na saka mai fadi sai dai girmanta yabi jikina saboda santsi da laushinta.

Hannunta shima mai matukar fadi ne amma ya tsinke a daidai wuyar hannun. Rigar ribi biyu ce samanta bulu ce mai shara-shara da ake iya ganin na kasanta wanda yake ja.

Sai adon da aka yi ana saman shima da jan zare da kuma hannun rigar. Na dauka jan gyale na yane kaina dashi na saka jan takalmi da kuma karamar jaka itama jar kala.

Na kalli kaina a madubi na tuna ranar da Ishak ya kawo mun rigar da kuma uban tashin hankalin da na gani a ranar.

A dalilin bakin da ya dawo ya same ni da su wadanda suka zo daga Birnin Kudu, kannen Babana.

Nayi saurin kawar da tunanin lshak daga cikin raina, don gudun samun matsala, na kamo hanyar fita a dakin, a zuciyata ina addu’ar samun miji mai hali sabanin na shi, wanda zan yi mu’amalla ta kwanciyar hankali da shi cikin farin ciki da jin dadi.

Shi yasa kuma a yanzu ko kadan na daina jin haushin irin sakin da Ishak ya yimun, fatana kuma shi ne ya zamo mun alheri.

Na fito tsakar gida Umma tana bina da kallo. Zuwa can ta ce, “Yanzu nan wannan kwalliyar duk ta zuwa kasuwan ce?”

Nayi murmushi, na ce “Ta yi yawa ne Umma?”
Ta ce, “A’a je ki Allah ya tsare.” Na ce, Amin. Ina Tasi’u ya raka ni? ta ce, “Na aike su gidan Mama Tambaya su bi min bashina, amma sun kusa dawa ma.”

Na ce, “To bari na gani ko zan gansu a waje. Tun ranar da na dawo gidanmu da takardar sakin aurena ban kara leka koda kofar gida ba ne ballantana nasa kafata na fita.

Hakan ne yasa ni tsayuwa a kofar gidan ina bin layin da kallo, ina kuma wasu yan tunane-tunane a raina.

Na irin yadda unguwar ta canza gaba daya tun daga lokacin aurena shekaru hudu da suka wuce zuwa yau dinnan. Karab! Sai kawai muka yi ido hudu da Abdussamad wanda daga ganin irin kallon da yake yi mun na gane ya dade yana kallona bá tare da na ganshi ba.

Sauri nayi na sunkuyar da kaina ga barin kallonshi, sai dai hakan bai hana ni ganin canjin da ya samu ba. Ya kara tsawo yayi haske sosai sannan yayi ‘yar kiba daidai ba mai yawa ba.

Wacce ta sanya shi ya yi kwarjini, ba kadan ba. In da da hali to da na fasa. Fitan da nayi niyya.
Sai dai zai yi mun wata fassara haka nan dole na gayawa Umma abinda ya hana ni fita tunda har mun yi sallama.

Wuce shi nayi, nayi tafiyata bayan nayi iyakacin kokari na ganin tsananin kallon da yake yi mun bai harde ni na fadi ba.

Tafiya nake yi ina tunani a raina nasan Abdussamad ya ji maganar mutuwar aurena.
Don kuwa a unguwarmu kaf babu wanda bai ji ba. Wani babban shagon saida kaya na shiga saboda daukan hankalina da shagon yayı.

Rabon da wani abu ya kawo ni kasuwa tun kafin aurena da Ishak, don kuwa shi baya ba ni kudin komai kawowa yake yi.

Wani dan saurayi ne ya karaso inda nake tsaye saboda girman shagon yasa na kasa fahimtar inda zan dosa.

Barka da zuwa Hajiya, me ki ke so? Lokacin ne na fara kallon yadda aka kakkasa shagon gefen takalma da jakunkuna daban, haka na leshi haka na atamfa, haka na material da kuma shadda.

Na dawo da kallona ga yaron saboda kada na bata mishi lokaci, duk da akwai masu sayar da kaya a shagon irin shi masu yawa na ce atamfa.

Ya ce, “Babba ko karama?” na ce, “Kanana za ka bani guda hudu.” Ya ce, To ga wuri zauna bari naje na kawo miki.”

Na zauna a kan kujerar da ya bani ina kallon mu’amallar kasuwanci yadda take tafiya a shagon da irin mutanen da suke shiga suke fita.

Yaron ya dawo rike da atamfofi guda hudu na duba na ce, “Sun yi.” Na mika mishi wata na ce ya karo mun irinta guda daya.

A raina kuma ina tunanin wadanda zan baiwa. Kakata Baba Ladi da kishiyoyinta guda biyu, sai matan Yayun Babana biyu.

Sai kuma kanwar Babana. Ya dawo na tambaye shi kudin ya fada, nasa hannu a cikin jakata na mika mishi yayi godiya. Yana saka mun a babbar jakar su ta shagon mai dauke da suna da adireshin shagon.

Yana kuma tambayata ko za ki duba gefen mu na takalma ne? kamar naki sai kuma na bishi ina dubawa.

Wani takalmi yayi matukar daukan hankalina, na dauke shi ina dubawa na tambaye shi kudin ya fada mun. Na mayar na ajiye yana gaya mun ai da kin dauüka Hajiya “zai matukar yi miki kyau, saukinshi na fada miki, in kin duba da kyau. za ki gane asalin takalmi ne dan Italy.
Na ce, Eh na sani wani lokaci nazo na saya amma ba yau ba.” Na fito daga shagon don ci gaba da siyan abubuwan da nake bukata na káina.

“Hajiya! Hajiya!! “

Nayi maza na waiwaya saboda wani mutum da yayi mun alama da cewa ana kirana.

<< Mai Daki 11Mai Daki 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×