Skip to content
Part 13 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Yaron da nayi sayayya a shagonsu ne.

“Lafiya? na tambaye shi. “Ki zo in ji Maigidana.”

Na ce, Maigidanka kuma?” ya ce, Eh. gabana ne ya yi mummunan faduwa.

Na ce, Ina ce na baka kudinka? Na tambaye shi saboda tunanin da yazo mun raina.

Ya ce, Eh ban san dai dalilin kiran naki ba, ki dai taimaka din kizo tunda kin gani nima dan aike ne.”

Juyowa nayi na biyo bayan yaron nan zuwa shagon su.

Mutumin yana zaune a can wani kebantaccen wuri da aka tanada a shagon, amma daga wurin kana iya ganin duk wani abinda ake yi a cikin shagon.

Kammalallen mutum mai kwarjini mai matsakaicin hasken fata da tsawo. Kamalar shi ce tasa na dan rusuna a lokacin da zan gaishe shi.

“Lafiya yanmata, kiyi hakuri fa naga kamar kin dan damu ina fata ban takura ki ba ko?”

A lokacin ne naji na dan sake saboda tunane-tunanen da nake tayi a zuciyata, na game da kiran Wata alfarma nake nema kiyi mun.”

Na ce, Kamar ta me fa? ya ce Lambar wayarki za ki taimaka ki bani.

Nayi shiru saboda yadda abin ya yi mun wani iri. Don Allah. Lafuzzan shi da ya yi amfani da su suka hana ni bijirewa bukatar tashi.

Don kuwa ban san mu’amalla ta roko a tsakanin mace da namiji ba.

Yayi godiya na juyo na wuce, yaron nan yana ta harkokinshi ya ce sai anjima
Hajiya, na ce Yauwa.

Ban wani dade a kasuwar ba na gama siyayyata na kamo hanyar dawowa gida. Sabanin dazu da Abdussamad yake tsaye a kofar gidansu a yanzu tsaye yake a kofar namu gidan, hannayenshi duka biyun zube cikin aljihunshi.

Babu yadda zan yi na shiga gidan ba tare da ya kauce hanya ba. Ban san me zan ce mishi ba, hakanne yasa naja na tsaya don ya fahimci ina da bukatar shi din ya kauce mun a hanya.

Ban ga alamar yana da niyyar yin hakan ba, na daga ido na kalle shi shima ni yake kallo kuri kamar bai taba ganina ba.

Ban ce mishi komai ba amma sai nayi nufin rabawa ta gefe na wuce. Ya sake tarewa.

Hakan yasa na fahimci neman magana yake yi, don haka na juya kallona ga wasu yara can gaba da mu da ke guje-guje suna wasan ojiyo jiyo.

“Dama nasan wata rana zata zo, ranar da zan fuskance ki gani ga ki don na gaya miki cewa a wancan lokacin zabin da ki ka yin kuskure babba ki ka tabka.

To gashi ko lokaci mai tsawo ashe ba za a yi ba ranar zata zo. Mata irinku masu kwadayi da kallon kyalkyalin mota a mafi akasarin lokuta abin da ke faruwa da su kenan.

Ba zan mance bakin cikin da ki ka sa ni ba, bakin cikin da da kyar na samu ya bar ni, bakin cikin da ya yi mun sanadin abubuwa masu yawa.

To amma na gode Allah ko ba komai kema yanzu gashi nan kin gani ya gama cin amfaninki ya kore ki ya mayar da ke tokumbo ‘yar kwatano.”

Ganin da nayi Abdussamad ba shi da niyyar tsayawa da maganganun banzan da yake ta jero mun yasa ni dakatar da shi cikin sauri.

Na ce, Kayi kuskure da ka dauka tokumbo bata da daraja, don kuwa akwai wata tokumbon da ta fi sabuwa daraja.

Misali, Tokumbon mota kirar America da kuma Tokumbon mota kirar China kaga kamar yadda kwarin su ba ya zama daya haka ko da suke na hannu farashinsu ba daya ba ne.

Kuma ka godewa Allah da ya taimake ka ya rufa maka asiri da a lokacin ba ka tunkare ni da wata magana ba.

Don kuwa da jinyar bakin cikin da kayi ka warke da kyar da har yanzu kana yi bata kare ba, don kuwa babu abinda zan yi da kai ko a da can ballantana a yanzu da aka yi iska asirin kaza ya budu.”

Naja mishi wani dan banzan tsaki sannan na ce da ka ke cewa naga mota nabi kyalkyali kudi banza ne?

Kaima kayi mana kaga kenan har a yanzu kai din ba tsarata ba ne. Na raba ta gefenshi na wuce na shiga zauren gidanmu.

Na dan tsaya sai da na dan ji nutsuwa saboda barin da jikina yake yi sannan na shiga gida.
Ban so haka ya shiga tsakanina da Abdussamad ba, amma ko ma dai menene shi ya fara.

Sammako nayi don kuwa karfe goma na safiya na isa tasha tare da rakiyar Yaya Auwalu.

Karfe uku daidai kuwa muna tasha. Sammani shi ne yaron wan Babana da yazo daukana a tasha.

Saboda dama tun da motarmu ta tashi a tasha nayi waya na sanar da su zuwana. Saurayi ne da zai kai shekaru ashirin ko zuwa da biyu. Ba karamar karba na samu ba daga wurin Kakata Baba Ladi da sauran kishiyoyinta ba.

Baba Jummai da Baba Iya da kuma sauran matan gidan baki daya. Babana mutum ne mai dangi, don kuwa maza ne da su sosai haka nan yawancinsu daga mai mata biyu sai mai uku ko hudu.

Da wuya matuka kaga mai mata daya sai dai ko yaro. Haka nan ‘ya’ya ne da su masu dumbin yawa.

Wasu daga cikinsu suna zaune ne a cikin gidan da iyalinsu, yayin da wasu da suka sanmu hali sun yi nasu a waje sun tare.

Don haka gidan su Babana babban gida ne na gandu.

Kakata Baba Ladi ita ce mata ta biyu a wurin mijinta, Dattijuwa ce da a kalla ta doshi shekaru tamanin a duniya, amma saboda irin kirar karfi da Allah ya yi mata har yanzu din nan da karfinta.

Uwargidanta ta dade da rasuwa, haka nan ma Maigidan gaba daya don kuwa mu ba mu ma san shi ba.

Kafin nayi wanka na ce zan rama sallolina da aka biyo ni tuni kwanukan abinci sun kusa cika tsakiyar dakin Baba Ladi.

Na idar da sallah itama tana miko mun furar da ta dama mun da hannunta, tana cewa “Fara shan wannan ki warware yan hanjinki tukunna.”

Na ce, To. Ina shan furata tana tambayata labarin Ummana da ‘yan uwana ina gaya mata.

Ta ce, Ikon Allah! Ashe ke kuma wannan aure naki haka ya kasance? Na ce, Eh Baba Ladi ki taya ni da addu’a hakan ya zamo mun alheri.
Ta ce, To amin hakan ne kam yafi amma wai! Alamar tana jinjina abin mutuwar aure ai ba karamin al’amari ba ne.

To shi ina dan naki yake? Na ce, Ya karbe shi. Ta fara zata yi magana na ce “Baba Ladi bar maganar Ishak bana so.”

Ta kalle ni ta ce, To na bari ‘yar, nan, maganar dai kam babu dadi. Na ce, Yauwa ashe kin gane kenan.

Na jawo kwanon kwadon zogalen da na gani ya bani sha’awa saboda wadatar kuli-kuli da su tumatur a ciki na fara ci.

Ta ce, “To ba kin gama idda ba har yanzu ba ki fara zawarwa ba ne? na ce, Na fara to ina suke? Na ce suna nan.

Na mike na fito saboda a yanzu babu abinda na tsana irin naji ana kirana bazawara.

Da alama hirarmu da Baba Ladi ba za ta rinka yin tsawo ba. Dakin Baba Jummai na shiga duk da mutanen gidan sun zo mun gaisa nayi nufin kuma na zaga su gaba dayansu.

Baba Jummai jika take yi da ni sosai. Ta kalle ni tana balla goronta ta ce, To ke kin je in kashe aurenki, ga mazan naki duk sun kare sai kawai kiyi zamanki a nan muyi ta lallabawa.
Nayi dariya na ce mata, Kada ki damu, kwanan nan zan ballo miki wani darjeje ki sha gara har ki ture.

Ta ce, Wayyo yan nan gamu nan dai. Daga nan dakin ta hudunsu na shiga Baba Iyalele kafin na gama zaga gidan Magriba tayi.

Don haka daga nan alwala nayi na wuce dakin Baba Ladi don yin sallar Magriba.

Harkokina nake yi cikin walwala da sakewa ga iyayena maza kowa ya fita kasuwa ko gona ya dawo zaka ji ana ina.

“Hauwa Kulu?

Kowa da irin tsabar da yake riko mun. Da safe kuwa to zan yiwa Baba Ladi aikin gyaran wurinta na tsabtace shi.

Na cika mata randunan ruwanta na kuma wanke mata kayanta na sakawa.

Haka ma sauran abokan zaman nata. Matan gidan kuwa zaka ji suna ina Kulu take ta taya mu kaza…ina jin Baba Iya rannan tana korafin basa barina ina hutawa amma ni kam ko a jikina.

Sammani kuwa babu inda bai zaga dani ba a cikin gari, gidajen yan uwa na waje da kuma yan kananan kauyukan da yake kai kwan kaji.
Kafin na cika sati biyu sai kawai aka fara sallama wai ana kirana zance. Wasu ko sunana ba su sani ba sai ka ji yaro ya shigo wai ana sallama da bakuwa.

Haushi ya kama ni ba kadan ba, ban san yadda aka yi naja wa dan aikan wani dan banzan tsaki ba na ce, Je ka ka ce ba zan zo ba, kada kuma su dame ni.

Baba Jummai ta rarumo muciyar tukin tuwonsu ta nufo ni wai zata fasa mun kai.
Inna Hadiza matar kanin Babana ta ce, Haba Baba, ai sai ki nakasata. Ta ce, To ba shi kenan ba magana sai ta kare.

Ja’irar yarinya kowa yayi sallama ta yi tsaki kin kaso auren naki ne ki zo ki zaune wa mutaneki rinka jawo musu maganganun mutane da ba a iyar musu sai sun tanka?

Ina ce gayar gidan Malam Akawu kwanaki da aurenta ya mutu washegarin da ta gama lddarta aka daura mata aure da mijin da ko ganinshi bata taba yi ba saboda ta san darajar iyayenta.

To ki raba ni da wannan rashin mutuncin da ki ke yi wa mutane, idan ba so ki ke nasa iyayenki su nemo miki miji a garin nan su aurar da ke ba.

Tsit nayi jikina a sanyaye kuma na shiga daki na kwanta don nasan zata rina.

An kama azumin watan Ramadan ne ranar Jumma’a saboda ganin watan da aka yi a daren Alhamis.

Don haka wayewar garin sai ta zamo daban. Yau aikin duk na azumi ne masu surfe suna yi masu daka suna yi.

Nima ba a bar ni a baya ba, sai dai sabanin yadda nayi zato ba a je ko ina ba na ajiye tambayar saboda bororon da hannuna ya fara yi sai na koma tankade.

Ranar da aka yi ukun azumi tashi nayi da nufin yin abinda zan yi buda baki da shi da kaina.

Alele da kuma soyayyiyar doya da miyar kwai don kuwa su kunu kawai suke yu sai abincin gida.

Baba dan Juma ne ya ba da kudin da aka yi mun cefanen kayan da babu a gida.

Zama nayi nai abincina mai rai da lafiya na bi ‘yan tsofaffin na basu sannan nayi alwala na zauna ina jiran a kira sallah.

Wayata ta fára kara kamar ba zan dauka ba, saboda magana ma wahala take yi mun.

Don kuwa ba karamin jin azumin nake yi ba. Na yi sallama daidai na kaita kunnena.

“Ranki shi dade barka da shan ruwa.” Na ce, “Ai mnu nan bamu sha ba tukunna, wanene mai magana?”

“Ahmad ne.”

Na dan yi shiru ina tunani, to ni kuma ina nasan wani Ahmad? Na ce, Kayi hakuri ban gane ba.”

Ya ce, Mutumin da ki ka yi sayayya a shagonshi kwanakin baya. Na ce, Au, haka ne ina wuni?
Muka fara gaisawa, ya ce Nayo ta so na kira to wani uzuri ne ya same ni shi ne dalili na kuma kira ne a yanzu don na nemi wata alfarma da fatan kuma ba za a ki yi mun ba? Na ce, mecece alfarmar da ka ke nema? Ya ce, So nake a bani izinin zuwa gida.

Na ce, Aiya, ai bana ma gari. Ya ce, Eh naso nayi zaton hakan da ki ka ce mun ku ba ku sha ruwa ba, kina wane gari ne yanzu haka?”

Na ce, Ina Birnin kudu. Ya ce, Au ki ce kusa da garinmu kenan. To sai yaushe ki ke ganin za ki dawo?

Na ce, Gaskiya sai gab da sallah ko ma bayan sallah. Muka yi sallama da shi na ajiye wayar.
Ni shaf na ma manta da shi gaba daya. Baba Ladi ta ce, To shi kuma wannan wanene?

Na ce, Wani ne. Naja bakina nayi shiru, ta ce Kya dai ji da gulmarki.

Ina zaune a sashen kannen Babana muna aikin abincin buda baki wayata tayi kara.
Na dauka ina dubawa, Ahmad ne. tun bayan da müka yi waya da shi kwanai takwas kenan cif, ba mu sake ba sai yanzu da ya kira ni.

<< Mai Daki 12Mai Daki 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.