Bin ta da kallo suka yi cikin mamakin irin yadda ta dangwarar da kula, wannan kuma wacece?
Ina dan murmushin da ban san na meye ba na ce, yarshi ce.
Fu Suka hada baki Yarshi? Na ce, Eh, ita ce ta biyun tana da wa yana Makaranta dankaci ke ki ce akwai babbar magana, haka suke sakaka babu tarbiyya.
Ban sake cemusu komai ba mikewa nayi na shiga kicin na debo plates da cokala na dawo sai ga Larai ta shigo dauke da wata kular da kato kular ruwa mai famfo alamar abin sha ne a ciki.
Ta gaisa da su Baba Ladi sannan ta juya ta tafi. Na bude kular miya da taji naman kaji ta ukun kuwa kunun aya ne mai kauri.
Na zuba musu na mika musu sannan nima na zuba naci sosai saboda yunwar da ke damuna.
Sai da muka gama cin abincin ne Baba Iya ta ce “To kai mu wurin uwar mijin taki mu gaisa ko ‘yannan.”
Na mike suka bi ni. A bakin kofar dakin muka yi sallama ban shiga ba sai da ta ce a shiga.
Karba sosai tayi musu sannan suka fara tattaunawa a kan al’amuran aure da halayya na ya’yan zamani na rashin kunya da fitsara har suka kawo kan danta tana basu labarin rasuwar da mahaifinshi yayi ya bar mata su tun bata fi shekaru talatin ba a duniya.
Ya barta da Ahmad da Yayarshi Kausar da a yanzu take aure a Kano wurin dangin Babanta, da aure-auren da ya yi guda hudu mata biyu suka haifan mishi ‘ya’yanshi Zaidu da Zainaba.
Sai kuma wata ta haifi Ziradat da Zinatu, sai wasu biyu da ba su haihu ba.
A raina na ce, “Dankari! To me yasa bai taba gaya mun cewa ni ce matarshi ta biyar ba?”
Na kawar da wannan tunanin daga cikin raina, ko bai gaya mun yawan matan da ya aura ba ai ya gaya mun yana da ‘ya’ya hudu.
Shi kenan magana ta kare. Hira sosai suka yi sannan suka taso muka dawo sashena. Hajiya ce tasa aka mayar da su Baba Ladi gida bayan nayi musu kyaututtuka daga cikin kayan aurena.
Kwalliya sosai na sake tsalawa da yamma shadda danya da aka yi wa wani irin dinki na Senegal ruwan kofi na saka, na saka dan kunne fashion ruwan zaren jikin shadar.
Na feshe jikina da turaruka sannan na kunna bumer na saka na daki yabi gidan gaba daya. Karfe shida daidai naji tsayuwar mota a wurina.
Na leka, Ahmad ne. Na dawo na zauna ina jiran naga shigowarshi ban ji ba, har aka yi magriba aka yi Isha’i sannan ya shigo dakin. Yana kallona ya ce “Wow! Allah na gode maka da kayi mun baiwa da samun Hauwa’ u a matsayin mata ka bani zaman lafiya da ita ka albarkace mu da albarka da ka ke yi wa ma’aurata.
Murmushi na rinka yi har ya iso in da nake ya jani zuwa jikinshi ya rungume ni yana rada mun a kunnena ke baki iya yiwa mijinki oyoyo ba ne?
Rike hannuna yayi ya jani zuwa wani wuri da ban kula da shi ba a gidan. Kofa ce ya budeta muka shiga.
Babban wuri ne, don falon yafi nawa. Duk wani abu da ke falon faci ne tas tun daga kujeru har zuwa labule.
Falon ya matukar kawatuwa ba kadan ba, bai bar ni a nan ba cikin dakinshi ya wuce da ni. Wanka za ki taya ni nayi.”
Na gwalo ido ina kallonshi, ya ce “Ko ba za ki iya ba?
Nayi shiru, murmushi yayi ya soma cire kayan jikinshi na kawar da kaina zuwa kallon wani wawakeken hoton da ke manne jikin bangon gadon shi na wani irin ruwa da ke zubowa daga wani tsauni zuwa wani dan koramai masu tsuntsaye.
Kafin na juyo har ya shiga bayan gidan dakin. Mintuna kadan ya sake fitowa da tawul daure a kugunshi yana goge jikinshi da wani.
Dauko mun kaya a cikin wardrop din gabanki. Na bude ina dubawa.
An kakkasa kayan kashi-kashi, under wears, kayan barci, jallabiya da tract suit alama na babu kayan fita a wurin na ce wacce zan dauko maka?
Ya zubo hannayenshi ta kwibina tare da dora kanshi a kan kafadata har ina shakan kamshin man wankan da yayi amfani da shi da ke jikinshi.
Ya ce, “Kamshin turarenki mai dadi Hauwa’u. Ban iya ce mishi komai ba don ban saba irin wannan mu’amallar ba.
“Idan ba ki san wacce za ki ba ni ba, to bar shi haka mana kawai ba shi kenan ba, dama ai ba fita zan sake yi ba.”
Na jawo wata rigar barci da ke can sama saboda ya sassauta rikon da yayi mun, na ce “To ga wannan. Ya ce, “To juyo ki saka mun.
“To ai saika sake ni tukuna zan iya saka makan.” Na juyo ina saka mishi rigar tun daga hannu har na daure mishi belt dinta.
Yayi murmushi ya ce, “Hauwana kenan.” A falon shi muka zauna yana kallon labarai yana yi mun yan hirarraki ya ce, “So nake na dan takura miki kadan.”
Na ce,”Wacce irin takura kuma?” Ya ce, To ban sani ba ko ba za ki ji dadin ta ba, so nake daga gobe na fara cin abinciki. Idan ki ka yi mun haka zan ji dadi.”
Nayi murmushi “Nima hakan yafi mun ai, kamar na gaya mishi haka sai na fasa. Ya ce, “Ba ki ce komai ba.”
Na ce, yadda duk ka ke so haka zan yi.” Ya ce, “To na gode.”
Washegari daga fitan shi sai ga cefane rigigif babu abinda babu, kaji, kifi, nama, tumatir, komai dai na bukatar gida.
Wayata na dauka na kira shi na ce, “Za a yi na rana ne da za a kawò maka?’
Ya ce, “A’a Hauwa’u wannan Hajiya tana sawa a kawo na dare kawai za ki yi.”
Na ce, “To me za ka ci da daddaren? Yayi shiru zuwa can ya ce, Na baki zabin yau dai kam ko meye ki ka yi zan ci.”
Tsayuwa nayi ina kallon cefanen da aka yi, na rasa yadda zan yi na fara tamfar wacce bata taba girki ba.
Karaf na tuno da littafin Momin Hindu, shi na dauko na bude ina dubawa amma na kasa zaben abinda zan yi.
Da kyar na iya zaben wani da na gani ina dubawa meat ‘tagine’ sunan ne ya yi mun dadi, har nake dubawa ganshi ba mai wahala sosai ba.
Sannan akwai kayan hadin gaba daya, yanayin yadda naga girkin a hoto. Na fara hada kayan amfanin nama, mangyada, yaji, tattasai, attarugu, albasa, tafarnuwa, gishiri, maggi, karas, citta, bawon lemon tsami, tumatirin gongoni da ruwa.
Nan da nan na hada abubuwan na rangada miyata mai wani irin kyau da sha’awa. Na daukó ledar cous-cous na dafa saboda ganin da nayi da shi zai dace.
Na kira Momin Hindu ina bata labarin abincin da nayi. Tayi murmushi ta ce, “To saura abin sha.” Na ce, To ai ban san me zan yi na sha ba. A gajarce ta gaya mun.
Ina gamawa na shiga bayan gida nayi wanka.
Yau ma kwalliya nayi ta materia ya kuma yi mun kyau sosai. Na yane jikina da babban gyale na dauki babban food flask din da na zubawa Hajiya abinci a ciki na dauka nayi sallama a bakin dakin na shiga, bayan an ba ni izinin shiga.
Na ajiye abincin a gefe na zauna. Ta kalli food flask din ta ce “Ai ba sai kin rinka sako abinci ba don ba ci suke yi ba, sannan ga Larai nan idan muna bukatar abu zata rinka girkawa, mijinki kawai ban da mu.”
Na kai kamar mintina goma na tashi na dawo wajena, na kalli agogo har yanzu karfe shida bata yi ba.
Na gyara kwanciyata a kan doguwar kujera na kunna TV ina kallon CCTV Documentry da ake yi akan wani kabarin tsohon Sarkin Kasar Sin da ya mutu shekaru dari biyar da suka wuce.
Yau ma Ahmad bai shigo ba sai bayan sallar Isha’i. A dakin shi na ajiye mishi abincin saboda wankan da yake yi.
Ya fito yana goge jikinshi da tawul, ya samu na ciro mishi riga da wando na hutawa masu sauki.
Ya dan yi murmushi yana kallona tare da amsa gaisuwar da nake yi mishi.
Yasa hannu ya dauki kayan da na ajiye mishi akan gadon yana sakawa, ya gama ya riko hannuna.
“Muje ki bani abinci.” A kasa ya zauna a kan kafet yana duba wani sako da ya shigo wayarshi, ni kuma ina zuba mishi abinci a plate.
Na gama na tsiyaya mishi coconut juice din da nayi mishi na fara mika mishi.
Ya karba ya dan yi murmushi ya ce, “Bismillah zan fara cin abincin amarya. Nayi murmushin jin abin da ya ce. Ya kai juice din bakinshi ya kwankwade ya ajiye kofin a kasa.
Ya kalle ni na dauka madara ce, na ce a’a ba madara ba ce, ya ce To menene’? Na ce Juice din kwakwa ne.”
Ya sa cokali ya fara cin abincin gaba daya muka yi shiru sai da ya cinye abincin tas sannan ya ce, “To masallah Allahu, na gode Hauwa u.
Allah ya yi miki albarka, ya kuma ba mu zaman lafiyamai dorewa.
Abinci yayi kyau.”
Nasa hannu na kwashe kwanukan na fitar na kai kicin, sannan na dawo na zauna. Ya fara magana, “Tunda ki ka zo ban samu wani lokaci na zaunar da ke don nayi miki magana dangane da al’amuran gidana ba.
Amma duk da hakan dai nasan kin ga abinda ki ka gani na zahiri. Akwai mahaifiyata wacce idan kin lura za ki gane ba ni da wanda nake girmamawa nake kuma so fiye da ita.
A rayuwata ita kadai ce na mallaka ina nufin mallakar da ban taba wayar gari na gane na rasata ba.
Ina yi mata soyayyar da bana yiwa kowa shi a duniya Hauwa’u, don kuwa nasan itama tana yi mun fiye daa hakan.
Babana ya rasu ne ya bar ni ban fi shekaru biyar ba a duniya, amma kuruciyarta bai sa ta barni zuwa wani mijin ba.
Sai ta zauna da ni da Yata don ta tarbiyyantar da mu, ta ilimantar da mu ta hakura ta sadaukar da jin dadin rayuwarta.
Don haka duk wani abu da ki ka ga nayi a yau ko na zama a yau din nan to da bazarta ne. Ina rokonki daki taimake ni ki zauna lafiya da ita.
Zan iya yin hakuri idan ki ka saba mun, amma ina da gajen hakuri ta fannin sabawa mahaifiyata.
Sai abu na biyu, nasan kin ga yara to ina so ki san ko ni da nake ubansuu Hajiya bata yardar mun ta bani yancin shiga harkarsu ba.
Idan kin ga wani abu da suka yi miki da bai yi miki dadi ba, to na roke ki da kiyi hakuri, idan kuma kin ga ba za ki iya ba to ki jira ni na dawo ko menene a lokacin sai ki fada mun.
Ina yi miki wannan maganar ne saboda ni nasan kan gidana, na kuma san matsalar da ke cikin shi. Ina so ki taimake ni na samu nutsuwar da nake bukata a cikin gidana.”
Na yarda da duk abubuwan da mijina ya gaya mun da kanshi ya kuma roke ni a kai ina kuma iyakacin kokarina wajen ganin na biya mishi bukatunshi.
Gara nake shirya mishi kullum mai dadi, daga cikin littafin girkina a kullum kuma bai gajiya wajen yaba mun.
Haka nan baya gajiya da yabon kwalliyata, don kuwa kullum a cikinta nake safe da yamma, matukar yana gidan.
Ina son mijina ina kuma son zama da shi. Zama nake yi na yanci da walwala. A yanzu ne kuma na gane me ake nufi da zaman aure.
Zama na hakika ba mai cike da kunci ba. Zama na sanin hakki da yancin dan Adam.
A yanzu ne nasan so nasan abinda kalmar take nufi don abinda nake ji a game da Ahmad.
Shima burinshi a kullum bai wuce na ganin ya faranta mun ba. Da matukar wuya ya dawo gida ba tare da ya riko mun wani abu ba, wanda zan yi amfani da shi don kaina ba don shi ko wani ba.
Iyayena kuwa yana mutunta su tamfar nashi. To abinda nake so kenan na kuma samu, zan kuma jurewa zama da ya’ yanshi da mahaifiyarshi kamar yadda ya ce, don na tabbatar mishi matsayin shi a wurina.
Watana biyu cif, Ahmad ya ce na shirya a kai ni gida wuni. Cikin doki ranar na kama shiri. Tsaraba sosai yayi mun wanda zan tafi dashi tamfar wacce take nesa.
Nayi sallama a kofar dakin Hajiya na shiga a gefe na durkusa na gaya mata zuwana gida.
Ta ce, Eh mijin naki yazo ya gaya mun. Allah ya kiyaye hanya, ki gaida manyan naki. Na fito na shiga mota.
Bala direba ya tuka muka tafi. Babu wanda bai yi murna da ganina ba.
Umma ta ce, “Haka fa Allah ke lamarinsa, ki duba ki gani wannan auren naki nutsuwarshi ma daban.”