Skip to content
Part 16 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Wajen karfe uku Ahmad ya kira ni a waya. Na dauka “Yaushe ki ke shirin zuwa gida ne?

Na ce, “Ina ce wai ko za ka bari ne na yi sallar Magriba tukuna daidai lokacin dawowarka kenan.”

Ya ce, “To abincina fa? Ko zan zauna da yunwa ne yau tunda nayi karambanin yi miki gwaninta?

Nayi maza na ce, “A’a yallabai mu tafi.” Ban iya tsayawa jiran Babana ba na kama shiri.

Tasi’u ne yake ta magana yana cewa, Zai bini yaje yaga gidana, Umma ta ce, Aa a wane dalili ka bari dai a kai ku wani lokacin.” Ba tare da wata fargaba ba na ce a hada musu kayansu shi da Sabi’u.

Wurin Hajiya muka fara shiga, na gaisheta. Su Tasi’u ma haka, na mike zan fito ta ce mun, “Zo mana. Na dawo na sake tsugunnawa ta ce, Su waye wadannan? Tana nuna su da baki.

Na ce Kannena ne.

Ziradat ta leko daga cikin dakinsu ta kalli su Tasi’u ta ce, Wai!

Sannan ta kwashe da dariya. Ta ce, Lallai kuwa. Na tashi bayan ta bani umarnin tafiya, na dawo sashena amma ina jin wani abu a raina maras dadi.

Muka shigo falona sannan na kara bin yaran da kallo wadanda tuni suka bi lafiyar kujera suka zauna. Ni nasan mu ba masu kudi ba ne. Amma daidai gwargwado Umma tana iyakacin tawajen ganin ta tsaftace danta babu kazanta a tare da shi.

Tsarguwar da nayi ita ce tasa na leka na kira Bala direba na ba shi kudi na ce ya sayo mun kaya daidai nasu Tasi’u set bibbiyu wadanda zan yi musu amfani da shi.

Aikina na fara yi gadan-gadan saboda kada na makara. Abinci mai kyau sosai nayi mishi. Sai da na gama sannan nayi wa su Tasi’u wanka na saka musu sababbin kayansu nima nayi wankan nayi alwala, sannan nayi kwalliyata.
Ka’idar Ahmad shi ne, yana dawowa zai shiga wurin mahaifiyarshi, idan aka yi sallar magriba ya dawo zai shiga suyi hira.

Daga sallar Isha’i ne zai shigo wajena, don haka yau ma hakan ya yi.

Yana ganin su Tasi’u ya sai murmushi.
“A’a’a, ke ki ce yau muna da manyan baki a gidan nan, amma ba ki sanar dani ba, ai da na shigo da kayan tsaraba. To yanzu me ki ka ba su na saukan baki?”

Na bude baki zan yi magana ya ce, “A’a bar su kawai su bani amsa. Suka fara lissafa mishi abubuwan da suka ci tun da suka zo.

Sai da suka gama ya ce, “Ba ta ba ku sweet ba, ba ta ba ku Ice Cream ba kenan kun ga bata iya karbar baki ba.”

Ya jawo wayarshi daga aljihu ya kira Bala direba ya ba shi kudi ya ce yaje ya siyo mishi Ice Cream da candy.

Sannan ya kalleni, “To baiwar Allah ya ya ki ka samu gida? Nayi murmushi har cikin zuciyata na ce,

“Lafiya lau yallabai, kowa yana gaisheka tare da godiya mai yawa, sai dai ban ga Baba ba saboda gudun kadana makara.”

Ya mike ya nufi hanyar sashen shi ina bin shi har muka shiga. Ya tsaya a bedroom din shi yana tube kayanshi, ni kuma na wuce bayangida ina hada mishi ruwan wanka a kwarmi.

Ya ce, Ki koma wurinki kawai saboda yaran nan na ce to. Ban dawo ba sai da na ajiye mishi dukkan abin da zai bukata idan ya fito daga wankan.

Na dawo dakin inda na bar su Tasi’u suna nan inda suke, kallon cartoon din da na saka musuna Kiddies world suke yi har yanzu.
Ban dade da dawowa ba Bala ya shigo da aiken da aka yi mishi babbar leda cike da kayan kwalama.

Ya ajiye ya juya na kira shi na debi mai yawa na ba shi saboda sanin da nayi yana da yaya suna kuma zaune ne a boys Quarters din gidan.

Godiya sosai yayi ya juya. Na bai wa su Tasi’u wanda za su iya ci na kai saura fridge na ajiye saboda Ice Cream din kada ya narke.

Ganin da nayi hankalinsu ya yi nisa yasa na koma wurin Ahmad ya gama shirinshi har ya fito falon yana kokarin fitowa na ce, “Ai abincinka nazo na baka ya ce mu koma wurinkina ci a can, na ce to.”

A falona yaci abincin shi muka ci gaba da hirar mu, su Tasi’u ma suna harkokinsu har suka yi barci. Na dauke su naje daya dakin nawa na kwantar da su na dawo in da Ahmad yake.

Ya jawo ni jikinshi ya kwantar da ni a kan kafafunshi yana shafa gashin kaina.

“Tun da ki ka zo gidan nan ina kallon ki ba ki taba yin kitso ba.” Na ce, Ai ban san inda za a yi mun kitson ba ne a unguwar nan.”

Ya ce, “Eh mai yi ma su Zainab tazo tayi miki gobe. Na ce, “To.”

A dakina muka kwana ya ce saboda su Tasi’u kada a bar su su kadai. Sammako sosai yanzun nake yi saboda karyawar Ahmad tunda na lura ba son shayi da biredi yake yi ba.

Pizza na mishi na hada mishi da ruwan lipton saboda complain din da yake yi akan tebar shi da take kara habaka.

Duk da na gaya mishi ni bana ganinta. Sai da na sallame shi ya tafi sannan na dawo na shirya su Tasi’u cikin sababbin kayansu muka karya muna ‘yar hirarmu cikin raha da ban dariya suna bani labarai. Su na tambaya abinda zan girka musu suka fadaa na shiga nayi musu muka ci tare sannan na dauko Ice cream din su na jiya na ba su suka sha suka ce mun za su je wasa a waje.

Kamar na hana su sai dai naga kada na takura su tunda yara ne.

Tashi nayi na nuna musu wurin da yara suke wasa sannan na dawo dakina na hau gado na kwanta.

Ban dade sosai da kwanciya ba sai ga dan aika daga kasuwa Ahmad ya aiko shi da sakon su Tasi’u. Na karba ina dubawa.

Kaya ne masu asalin kyau yan kanti set uku-uku, sai takalma sandals na asali.

Na ajiye kayan na leka don na kira su daga nesa na hango su a kan lilo, don haka na dawo na bar su suka ci gaba da wasan su.

Ni kuma na shiga kicin don fara shirin abincin dare. Ihun da nake jiyowa ne yasa ni saurin fitowa, don kuwa ya yi mun kama da na Tasi’u.
Sai dai kafin na fita waje har sun shigo dakin cikin tsananin rudewa na kwallara kara tare da fadin “Inna
lillahi wa inna ilaihi raji’una.”

Jini ne kawai har ya rine rigarshi gaba daya. Waje nayi da gudu saboda rudewa.

Daga nesa Bala direba ya hango ni ya taho cikin sauri “Lafiya, lafiya?

Na ce, Zo ka gani. Na taho dakin har ya zauna a kasa cikin saurin shi ya sunkunci Tasi’u nima na bishi a mota ya saka shi zuwa asibiti.

Ban jira dawowansu ba bin su nayi. Ba karamin jin ciwo Tasi’u ya yi ba, don kuwa sai da aka yi mishi dinki a keyarshi a ka yi dressing din wurin aka yi mishi allurai sannan muka dawo gida wajen karfe shida da rabi na yamma.

Har dakina Bala direba ya kawo shi kan kujera ya ajiye shi. Muryar shi har ta dishe saboda kuka. Na tsaya a kanshi ina kallon shi saboda tausayin da ya bani.

Na koma bandakina na dauko sandar goge-goge na goge duk jinin da ya mannu a tayels din na saka dettol na sake gogewa sannan na shiga kicin cikin sauri don na dan yi wa Ahmad abincin da zai ci.

Sai dai ko dorawa ban yi ba sai ga motarshi ta shigo gidan, duk da haka ban fasa ba saboda nasan ba wurina zai wuto ba.

Cikin kankanin lokaci na yi mishi fried rice da coleslaw salad, sannan na dawona dauki Tasi’u da barci ya riga ya dauke. Naje nayi mishi wanka da ruwa mai zafi saboda ya ji dadin jikinshi, na hada mishi tea na ba shi sannan na ba shi magungunan da Likita ya ba shi.

Naje na kwantar da su ban wani bar su suka tsaya kallo ba.

Ahmad ya shigo lokacin ne nake wanka amma kafin na fito ya tafi dakinshi, don haka sai kawai na bi shi can.

Shi ma wankan na samu yake yi don kuwa dabi’arshi ce vin wanka, da zarar ya idar da sallar Isha’i yana cin abincin shi yana dan kallona.

Zuwa can dai ya kasa yin shiru ya ce, “Menene ya faru ne amarya?

Na ce “Me ka gani? Ya ce, “Ba haka na saba ganinki ba. Kamar nayi shiru don kuwa abin da zuciyata take ta gaya mun kenan sai dai na kasa.

Abin kawai da na sani shi ne, Sabi’u ba zai yi mun karya ba, don kuwa yana wurin da abin ya faru ya kuma tabbatar mun da Ziradat ce ta wurgar da Tasi’u akan liie ya ji wannan ciwon.
Na share hawayena da na gama yi mishi bayani, ya ce “Yanzu yana ina? Na ce, Ya yi barci. Mikewa yayi ya taho dakin da nake kwantar da su har yanzu wata irin ajiyar zuciya yake yi.

Duk da nisan da barcin shi ya yi ya zuba mishi ido yana kallon lafcecen bandejin da aka toshe ciwon da shi, ya juya ya fita.

Shiru naji bai dawo ba, na mike zan fita sai na hango shi yana tahowa daga sashen Hajiya, duk da ban san me ya faru ba gabana ne ya fadi da na kalli fuskarshi.

Na kauce na ba shi hanya ya shige daki ya kwanta, ni ma kwanciyar nayi ban ce mishi komai ba, tunda shi ma bai ce mun ba.
Washegari sai da ya gama shiri zai fita ne ya kalle ni.

“Kiyi hakuri Hauwa’u, zan so ki dauke shi a matsayin tsautsayi duk da dai nasan ganganci ne kawai irin na yara.”

Na ce, “Babu komai.” Ya fita, Na shirya kamar kullum na shiga sashen Hajiya don na gaisheta.

Kallon kawai da ta yi mun ne ya yi matukar sanyaya mun jikina.

Na gaisheta ta amsa sannan ta ce, Ko da wasa kada ki kuskura ki kara kai karar yaran nan wurin Babansu na gaya miki kada ki kara.

Ba a yi mun haka, kada ki shiga gonata saboda bana son abinda zai sa na saba miki. Tashi ki bani wuri.”

Dawowa dakina nayi, nayi sumukwi nayi tsit saboda sanyin da jikina ya yi.

Ban yarda na mayar da su Tasi’u gida ba kamar yadda naso nayi sai da ya ji sauki sosai har aka cire mishi bandejin.

Ahmad kuwa siyayya ya yi musu mai ban sha’awa har da Kekuna ya ba su, sannan yasa Bala ya mayar da su gida.

Na riga na saba duk ranar Litinin da Alhamis Hajiya tana Azumin nafila, tunda nazo kuma duk da cewar da tayi na daina saka mata abinci idan nayi bai sa na fasa yi mata girkin abincin buda baki a wadannan ranakun ba.

Tun tana hanawa har tayi shiru, kasancewar yau Alhamis sai na shirya mata farfesun danyen kifi mai hadi sannan nayi mata lafiyayyen alcle na ganye da kunun gyada na danyar shinkafa.

Na hada wuri daya ina nufin dauka na kai sai ga wayar Ahmad ya aiko dan aike na ba shi takardar da ya bari a kan bed side din shi da ke cikindakinshin.

Hakan ne yasa nayi waya sashen su don Larai tazo ta dauki abincin, sai aka ce bata nan, don haka na ce Zainab tazo ta dauka. Na shiga na dauko wa dan aiken sakon shi na ba shi, sannan na dawo na ci gaba da harkokin abincina.

Sai da na kammala komai nayi wanka nayi kwalliya tare da sallar Magriba sannan na fito wurin Hajiya don nayi mata sannu da shan ruwa.

Ina shiga Ahmad yana fita saboda sallamar da aka yi da shi a waje.

Na durkusa gefe na gaisheta tana amsawa kamar kullum yanayinta ta kuma yi mun sannu. Na mike zan fito sai naji an kira sunana.

Na waiwayo da sauri don ganin mai maganar. Tun da nazo gidan yau ne naji Zainab tayi magana da ni.

Tana rike da kofar dakinsu da hannu daya yayin da dayan kuma take nuno ni da shi.

“Kada ki kuskura ki sake yin waya ki ce a turo ni ki aike ni kin ji na gaya miki. Ba na daukan raini idan kin lura za ki gane tunda ki ka zo gidan nan ban taba shiga harkarki ba.

Idan me aika ki ke so, to gayawa wanda ya ajiye ki ya nemo miki.” Ta juya ta koma dakin da ta fito. Ina tsaye a bakin kofar dakin ko ina a jikina sai tsatsafo da gumi yake yi.

Murmushi Hajiya tayi ta ce “Kai Zainab kenan, ina dai yi miki addu’a Allah ya shirye ki. Je ki abin ki Hauwa’u rabu da ita.”

Na juyo na dawo daki raina a cushe. Har lokacin da Ahmad ya shigo na rasa yadda zan yi na saki raina.

Duk wani abinda na saba yi mishi na mishi sai dai da muka kwanta Juyawata nayi na rabu da shi, don kuwa abin har yanzu yana cina.

Yayi tambayar har ya gaji wai na gaya mishi abinda ke damuna na ce babu komai. Ya ce, haka kawai ki ke mun irin wannan abin.

Nayi shiru naga zai ja mun wata matsala na ce mishi ba ni da lafiya, ya ce Idan ba ki da lafiya ba za ki yi magana ba sai kawai ki juya mun keya?

Juyowa nayi na ba shi hakuri, sannan aka zauna lafiya.

Duk wani kokari da nake yi na gani ban shiga sabga r ‘ya’yan Ahmad ba nayi shi, amma hakan bai sa sun bar ni ba tare da su suna shiga tawa harkar ba.

Babu ma dai shaidaniya irin Ziradat, haka kawai yarinyar bata kwanta mun ba. Gara Zainab bata kallon inda nake bata yi mun magana amma ita ko baki nayi to sai tasan yadda tayi ta yi musu abinda ransu ya 6aci.

Duk wanda tayi wa rashin mutuncinta hakuri nake ba shi tunda ko a gaban Hajiya ne hakurin zataa bayar sai ko bin su da take yi da addu’ar shiriya.

Ba ni da wata matsala daga wurin mijina, muhimmmin abu kenan a wajena.
Wata irin iska mai karfin gaske aka yi da daddare, wacce ta bugo satelite dish din sashen su ya fado kasa.

A lokacin nan Ahmad baya nan, don haka ba a gyara ba. Tun da abin nan ya lalace sai suka dawo kallon su wurina.

Ziradat da Zinatu safe, rana da dare a dakina suke wuni, ba na sawa ba na hanawa.

Sannan ga su da ciye-ciye duk abinda suka ci kuma to a wurin za su yar da bawon shi ko kuma su bar kwanon a wurin ko da wacce irin shara ko gyara na yi wa gun.

Ban taba daga ido na kalli abin da suke yi ko na gaji nayi musu magana ba.

Abin dai da na sani shi ne, ya kusa wucewa tunda maigidan ya dawo a jiya da daddare bayan tafiyar da yayi ta wajen sati biyu.

Na gama aikina tas da yamma na gyara dakina da na Ahmad na duba babu wani abin da zan yi.

Don haka nayi wanka na gyara kaina, nayi kwalliya ta burgewa sannan na dawo falona da yake ta kanshi na zauna ina kallon programme din (Ask Huda) da ake yi a Huda TV. Kan wata tambaya dangane da jinin Haila da ake amsa ta wacce ta dade tana daure mun kai.

Sai kawai Zinatu ta shigo dakin nan da sauri ta dauki remote ta canza zuwa kidsco wai zata ga cartoon.

Wani gululun takaici ya taso min, ban san yadda aka yi na daka mata tsawa ba.

Na ce, “Meye haka? Dalla can mayar mun inda ki ka same shi.”

Iyakacin abinda na ce kenan yarinyar nan ta tayi jifa da remote dinnan ya daki bango ya wargaje.

Sannan ta falla a guje tana kurma wani irin ihu, sai ka ce wacce ya yanke wa wata gaba a jikinta.

Wani sabon takaicin ya sake kama ni, ganin remote din ya ki aiki na tattara shi na aj1ye.

<< Mai Daki 15Mai Daki 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.