Skip to content
Part 17 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi


Na shiga dakina na bi lafiyar gado ina ‘yan sake-sakena.

Larai ce tayi sallama ta shigo, wai in je Hajiya tana kirana. Na fito bayan na lullube jikina da gyale.

“Me ya hada ki da Zinatu ki ka bugeta?” Na kalli yarinyar yadda ta takure a jikin kujera har yanzu kuka take yi.

Na ce, “Hajiya ban bugeta ba.” Na fara kokarin yi mata bayanin abin da ya faru.Ta ce,

“Dakata! Kin ga yadda muka fara zama cikin fahimtar juna? To ba na so wani abu ya shigo daga baya, don idan nayi niyyar daukan mataki akan mutum abin ba ya yi mishi kyau.
Kada na sake jin an ce ko kallon banza kin yi wa wani da a cikin gidan nan, ballantana har ta kai ga kin saka hannu a jikinsu.

Ki zauna a matsayinki su zauna a matsayinsu. Ni bana dukan yarana tunda ubansu ma a haka na tarbiyantar da abina.

Duk wanda ya ce ba zai yi hakuri da su a haka har kafin su fahimci kan al’amarin duniya ba, to sai yasan nayi.

Ba na so, kada kuma na sake jin don sun je wurinki sai kiyi mata haka har tana sulewa saboda razana? Ai nan gidan ubanta ne tana da ikon shiga duk inda take so ta wala.”

Na dawo dakina nayi alwala nayi sallar magriba har aka yi Isha’i ban tashi daga wurin ba.

Don haka na mike nayi sallar Isha’I tare da shafa’i da wutiri. Motsin
Ahmad naji a wurin shi ne na dauki abincin shi na kai mishi.

Ina ajiyewa ya ce, “Me ya hada ki da Zinatu ki ka yi mata irin wannan dukan? Wato kin gane ko? Ni da ki ke gani ina matukar tsoron tashin hankali.

A waje ban huta ba, babu abin da nake bukata irin na shigo gida dan hutun da zan yi da iyalina na yishi cikin kwanciyar hankali da farin ciki ba.

Menene haka? Tun farko na gaya miki kiyi kokarin zama ba tare da wani abu ya hada ki da wani yaro ba, saboda nima hakuri nake yi da su.

Hajiya kuma ina matukar kokarin ganin bacin rai, bai same ta ba ballantana a ce sanadina ne,”

Naga fadan nashi zai yi yawa saboda wani abu bai taba hada ni da shi makamancin haka ba, a tsawon zaman da nayi a gidan na watanni shida.

Na ce, Ban fa bugeta ba.” Ya watso mun ido “Ba ki bugeta ba? Na ce “Na rantse maka ban bugeta ba.”

“Me ki ke nufi kenan? Kina so ki ce mun Mahaifiyata tayi miki karya?”

Nan da nan na fara kuka saboda jin inda ya mayar da abin. Nan take kuma fadan yafi na dah wai na karyata mishi uwa. Ga gaskiya nan kiri-kiri jikin yarinya ya rure har zazzabi ya rufeta amma kina karyata mahaifiyata.

Mara kunyar yarinya, tashi ki ba ni wuri.”

Na tashi na dawo dakina nayi kuka har na gaji, idanuna suka yi luhu-luhu saboda rashin barcin da ban yi ba.

Na gama abin karyawa kamar ba zan shiga sashen nashi ba, tunda korata ya yi jiya sai naga kada na karaka kaina matsala.

Na dauka na kai mishi na ajiye na juyo abina, tunda a da wannan damar tayin gaba da wani ina dai bin doka ne kawai. To da haka wanna ya wuce.

Ba karamin taka tsantsan nake yi da yaran Ahmad da mahaifiyarshi ba, saboda ina son aurena.

Gashi kuma cikin kankanin lokaci sai na mallaki abubuwan kadara irin Su,gold da zinari saboda yawan tafiyar da yake yi. Kuma shi mai sakin hannu ne. matsalata a kullum ba daga shi ba ne sannan babu fashi sai dai idan bai yi tafiya ya dawo ba sai an ce nayi kaza nayi kaza.

Ita kuma Hajiya ta ce aja mun kunne, to garin aja kunnen sai ya zama tashin hankali, ina batawa mahaifiyarshi rai.

Sannan babu damar nayi musun ban yi ba sai laifin nawa yayi yawa, na karyata mahaifiyarshi, don haka kullum a haka muke.
A daidai wannan lokacin ne ta bayyana ina dauke da juna biyu har na shiga wàta na uku.
Hakan ne ya matukar takura ni naa kasa yin Azumin watan Ramadana, saboda tsananin laulayin da nake yi.

Ba Ahmad ba ma har Hajiya a wannan lokacin ta sassauta mun, don haka babbar matsala a yanzu laulayina ne da kuma yaran.

Tunda yanzu ba barina suka yi da karata wurin Babansu duk da laulayin da nake yi bai hana ni kiba na murje ba.

Shirin sallah sosai ake yi don kuwa gidan ma a cike yake da mutane ‘yan uwan su da suka zo daga kauye da kuma babban dan Ahmad Zubair. Wanda yanzu ne muka san juna da shi.
Shi kam babu laifi yana da hankali don Aunty ma yake kirana. Haka nan nima duk da sanin da nayi suna buda baki a wurin Hajiya hada mishi nake yi da Babanshi.

Sannan ganin shi yasa hatta Zainab ta saurara da wasu abubuwan ballantana su Ziradat. Zama yazo yayi yana gaya mun abubuwan da yake so nayi mishi, na sallah saboda bakin abokanshi da za su kawo mishi ziyara.

Na ce, To ka bari mana idan nayi na Babanku sai na diban maka a ciki.

Yayi godiya sosai, take kuma farin cikinshi ya bayyana, ya tashi ya tafi.

Bai dade da fita ba na fita don zuwa sashen Hajiya kai mata farfesun kodar da Ahmad ya aiko ya ce nayi mata da hannuna.

Na isa bakin kofar tun kafin nayi sallama naji Ziradat tana cewa, “Ai munafuka ce tunda gashi har Hajiya ma yanzu ba ta yarda idan mun ce mata tayı mana wani abu.

Ni a matan da Babanmu ya aura duk ita nafi tsana. Hajiya ta ce,
“Um’um Ziradat na fa kwabe ki da irin wannan maganganun.”

Shi kuma Zubair cewa ya yi “Ni banä son irin wadannan maganganun ban san abinda yasa Baba yake biye muku ba.

Menene laifin wannan matar? Ko harkar mutum bata shiga ba za ku taba barin Baba ya zauna lafiya da mata ba. Shi kuma ku ke sakawa a matsala.”

Sallama nayi na ajiye mata na fito na dawo wurina, a raina na ce kwaji da shi, ni kam nawa auren daram in Allah ya yarda.

Shiri sosai nayi na sallah mutanen gidan kaf na basu abinci da abinsha da su kek din da nayi ba tare da nayi la’akari da Hajiya tayi ba.
Makwabta baki daya sai da na zagaya su da abinci. Ahmad ne kuma ya taso keyar su Zainab suka kai mun rabon.

Gidanmu ma duk da ya aike musu da nama cikin babban baho saboda yankan da yayi da kuma shinkafa da tumatur kwando bai hana ni kai musu abincin sallah ba wannan kuwa Bala direba na aika.

Da yamma ne baki abokan harkar Ahmad suka zo gidan hakan ne yasa sashenshi ya cika dankam ba kadan ba.

Nima gagarumar liyafa na shirya musu sinasir da farfesun kafar saniya sai dambun nama da kek da manyan donghnut na asali mai ridi.
Sai kwalayen juice wanda na hada musu duka a cikin wani madaidaicin kwando na Rafia da nayi rafin dinshi da wata ‘yar leda da aka rubuta iyalan gidan Alhaji Ahmad Rufa’I suna muku barka da Edil Fitr.

Kuma gaba dayansu ya wadace su. Shima abin yayi mishi dadi ba kadan ba.

Ya shigo dakina lokacin da nake shirin shiga wanka har yanzu fuskarshi a washe take ya sa hannu ya dauke ni yana cewa bari nima na taya ki wankan irin wannan gajiya da ki ka yi haka.

Duk da dai ni da yunwa ki ka bar ni na ce, “Haba yallabai na dauka ai yau ba za ka ji yunwa ba.”

Dariya yayi ya fita bayan ya gaya mun yana jirana idan na gama shiri.

Doguwar riga na saka mai gyale na dauko abincin a babban tire na nufi falon shi na waje don a nan na jiyo shi alamar ya sake yin wasu bakin.

Ni kuma ba zan iya jiran tafiyar su ba tunda na gane yana jin yunwa.

Wani irin santsi ne ya debe ni gaba daya na zame na kife a kasa tire yayi nesa ya kife abubuwan ciki suka tarwatse.

Karar fashewar abu da salatin da nayi ne yasa Ahmad tahowa wurin cikin sauri har ya karaso inda nake.

Ba iya motsawa ba sa hannu yayi ya dauke ni zuwa cikin dakinshi tunda daga inda nake nan dinne ya fi kusa.

“Sannu Hauwa’u.”

Sai dai ko amsawa na kasa yi saboda wani irin gigitaccen ciwo da nake jiwowa daga gadon bayana yana hadowa har gabana zuwa marata.

Ya juya yana kiran Larai don tazo ta kwashe barin da aka yi yana kumna gayawa Hajiya.
Durkusawa nayi saboda murdawan da yake yi mun da irin azabar da na ke sha.

Ahmad yana shigowa tare da Hajiya daidai lokacin dá naji kamar fitsari yana zubo mun. Hajiya ce ta fara salati tana karawa, wannan wane irin mummunan faduwa ki ka yi ‘yannan. Ai jini nake gani.”

“Jini Hajiya?” Ahmad ya fadi
daidai ya kara matsowa inda nake cikin sauri ya dauke ni zuwa mota muka tafi asibiti.

Jinin da ya zuban ya yi yawa, don haka cikin ya lalace wankin ciki aka yi mun aka sallamo ni da magunguna muka dawo gida wajen karfe sha biyun dare saboda cewar da Ahmad yayi a sallamo ni mu dawo gida.

Cikin dan kankanin lokacin da abin ya faru nayi wani irin ramewa saboda bakar azabar da na sha.

A daren Hajiya tazo duba ni ta kuma hado mun da abincin da ta girka mun, tuwo miyar kuka ta ce na ci na sha maganina.

Ba karamin jjjaga Ahmad ya yi da barin da nayi ba, don kuwa shi mutum ne mai son haihuwa.

A yanzu kuma Zinatu ita ce karamar ‘yarshi, wacce a bana ya ce mun shekarunta takwas.
Hakanne yasa ni daurewa nayi niyyar wartsakewa duk kuwa da abin da ke damuna a zuciyata.

Da safe ma Hajiya ta shigo ta gaishe ni, haka Larai da Bala direba de matarshi sai Zubairu.
Wajen karfe tara ne Ahmad ya sake shigowa ya kalle ni, ganin ina zaune a ukan gadon “Har kina iya tashi? Na dan yi murmushi na ce, “Ai naji sauki. Ya zuba mun ido tare da kamo hannayena duka biyu ya rike a nashi hannuwan yana dan matsawa.

Yace, Kin dai daure Hauwa’u ba kin ji sauki ba, ki taya ni addu’a Ubangiji ya ba mu. wasu masu albarka.” Na ce, “To amin.”

Yayi shiru zuwa wani lokaci ya ce “Ina son zama da ke Hauwa’u. Ina rokonki ki kara hakuri da duk wata matsala da ki ke fuskanta a tare da ni ko wai nawa.”

Ban fahimci inda maganar tashi ta dosa ba, amma sai na dan yi murmushi kawai.
Duk kokarina bai wuce na ganin na nunawa Ahmad cewa naji sauki ba.

Na dan daure na yi kwalliya na sanya doguwar riga na fito ina lallabawa zan shiga dakin, shi ne naji maganar Zubair.

Kamewa nayi na kasa shiga.

“Na rantse Baba naga lokacin da Ziradat ta saka ai ba zan yi maka karya ba, amma ina gaya maka ne don kada wata rana suyi abinda yafi haka.”

Ahmad ya ce “To kai Zubairu me yasa da ka ganta ba ka ce komai ba?”

Ya ce, “Ai ni ban san da wata manufa tayi ba. Na juyo. na dawo dakina saboda na fahimci wani muhimmin abu ne duk da dai ban san ko menene ba.

Wajen La’asar na rinka jiwo ihun yaran, sai dai n1 kam ban je ba, don ban san abinda yake faruwa ba kumna babu ruwana ko ma menene.

A dakina yau ma na kwana sai dai tare da Ahmad.

Washegari matar Bala direba ta dawo gaishe ni tana zaune a kan kujera muna yar hira saboda mutuntani da matar take yi da kuma kokarin shiga sabgata yasa nake dan hira da ita.

Don ba za ta wuce sa’ata ba. “Oh ni ‘yasu, wadannan yara kuma ashe sune.”

Na ce, Su ne kamar ya ya?

Wadanne yara? ” Nayi mata tambayoyin a tare kuma lokaci daya.

“Au, jiya ba ki jiyo ihunsu ba? Ai Baban ne ya yi musu duka ba na wasa ba, don wansu yaje ya gaya mishi cewa ita wannan shu’umar ita ce ta saka miki abu ki ka fadi.”

Nayi shiru ina kallonta saboda jin abin da take fada, abin dai ya yi matukar bani mamaki, sai dai duk da haka ban tanka ba don tsoron halin mutane.

Shiru nayi a kwance ina tunani me nayi wa wadannan mutane haka?

Ahmad ya shigo ya nemi wuri kusa da ni ya zauna.

“Ya ya Amarya me ke faruwa ne?” Ban ce mishi komai ba sai zuba mishi ido da nayi. Ya jawo ni jikinshi yana cewa.

“Kin san fa tunda wannan ya fita to aiki ya koma baya, sabon zubi kumna zamu yi yanzu.”
Daurewa nayi na ce mishi “To, amma dai ai ba yanzu ba ko?” Ya ce,

“Eh to, ko gobe tunda Likita ya ce bari ba a wuce kwana uku, ko ba haka ba?”

Wartsakewa nayi saboda farantawa maigidan rai na nuna mishi naji sauki don hankalinshi ya kwanta.

Haka nan kuma abubuwa sun matukar yi mun sauki ba kadan ba, tunda dai yanzu zan iya ganin Ziradat a hanya ba tare da ta ja mun tsaki ba.

Abin har mamaki nake yi, wai ‘yar karamar yarinya mai shekaru goma sha uku ce ta ke irin wannan abin.

Lokacin komawan Zubair Makaranta ya yi, don dama hutun nasu ba mai yawa ba ne.

Tambayar shi nayi abinda yake so nayi mishi na tafiya. Ya yi shiru yana ‘yan tunane-tunane.

Ya ce, Ai ba na so ne Baba ya ji zai ce na cika fitina, tun da ana siya mun komai.”

Na ce, “To fada mun ba zan bari ya ji ba.” Ya ce, “To ina son kek irin wanda ki ka yi da sallah.”

Na ce, “Sai me?” Ya ce, “Ko shi kadai aka yi mun Aunty na gode. Na ce, “To shi kenan.

Cefane sosai nasa aka yi na kira Larai muka yi aikin tare. Cincin nayi mishi mai yawa, nayi mishi kek na sassaka su a leda daidai saboda kada su bushe tunda Makaranta ce.

Sai dambun naman da nayi mishi cikin babbar roba fara.

Ana gobe zai tafi na ba shi tsalle ya rinka yi kamarzai yi ya ya don murna.

Sallamaa muka yi mai dadi ya kumaa roke ni idan Babanshi zai je mishi visiting na raka shi muje tare, na ce to.

Da yamma ne Ahmad ya shigoo bayan ya kai shi Makaranta ya dawo na kawo mishi ruwa mai sanyi yasha sannan ya yi hamdala ya ce “Zubairu ya ce na sake yi miki godiya.”

Ban saurare shi ba kicin na koma na hado mishi fruit salad na kawvo mishi, ya karba yana sha ya ce “To ni ina nawa dambun naman?”

Na kalle shi na gane da gaske yake yi na ce “Ban ajiye maka ba saboda ya ce ba ya so ka sani.”

Ya dan yi murmushi ya ce, “Haka ya gaya mun, to amma kuma sai ya kasa yin shirun ya fada mun da kanshi.

Kin san alheri komai kankantarshi yawa ne da shi, to ballantana irin wannan.”

Na ce, “Kai dai don Allah bari zuga ni, ai ba da kudina nayi ba a cikin cefanen gida na saka.”

Ya ce, “Ko ma dai ya ya ne ai cefanen gida idan wata ce ba za ta yi ba, ina so kuma na gaya miki cewa ba Zubairu ki ka yi ma ba ni ki ka yi ma, zan kuma tabbatar. ban mance alherinki ba.”

<< Mai Daki 16Mai Daki 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×