Ina zaune na tasa abincin da aka aiko mun daga gidan Yaya Auwalu a gaba zan fara ci. Itama Samahatu kullum sai ta zubo min abinci na daban duk da na gida da take aikowa a babban food flask wanda wani lokaci ko abincin dare ba ma yi saboda yawanshi.
Sannan ga laulayin ciki da ya tasata a gaba, hakan ne yasa idan na dawo na samu nata shi nake ci. Idan kuma naci shi to shi kenan na koshi saboda ni dama ba mai cin abinci ba ce.
Baba Ladi ta leka gefen gadonta ta jawo kwano lafiyayyen kwadon zogale ne a ciki, ta miko mun. Na dan yi murmushi saboda nasan duk tana yi ne don ta birge ni, ta nuna mun tana sona. Hakan kuma kan sa naji dadi a raina. Na ce, Baba Ladi Babanmu yana kawo miki zogale ne saboda matsalarki. Likita ne ya ce ki rinka cin zogale sosai saboda yana magani, amma idan aka kawo miki maimakon ki zauna ki ci ya ishe ki sai ki raba biyu ki ajiye mun rabi, ni din da lafiyata kalau. Ta ce, “eh nasan lafiyarki kalau ci ki kara lafiyar ‘yar nan ai ni tausayinki nake ji ke da ki ka saba cin dadi a gidan mazan da ki ka aura.
Ke dai ina miki addu’a Allah ya kawo miki wanda za ki huta fiye da su.”
Nayi dariya na ce “Haba Baba Ladi, ai wannan addu’ar taki bata yi ba. Cewa za ki yi Allah ya kawo mun wanda zan zauna lafiya a gidan shi zama na din-din-din wanda zai yi hakuri da halayyata da dabi’ una masu kyau da marasa kyau.
Ni a ganina wannan shi ne mafi alkairi a gare ni. Na mike gidan Yaya Auwalu na nufa don duba matarshi. Ina rike da kwanon da Umma ta bani na kunun tsamiya da ta dama mata saboda ganewan da tayi bata cin abinci ya zauna mata.
Nayi sallama a bakin kofar na shiga. A kwance na sameta shame-shamc a kasa. Cikin sauri ta gyara zama tana daura dankwalinta, na ajiye mata kunun ina gaya mata sakon Umma tana dan murmushi cikin jin nauyi. Ban saurare ta ba kicin dinta na shiga na dauko kofi na tsiyaya mata na mika mata ta karɓa. A raina ina tunanin mu’amalla mai sauki irin wacce ke tsakanin matar Yaya Auwalu da sirikarta Umma.
Ban jima a gidan ba na fito bayan na gaya mata zan zo gobe nayi mata kitso, saboda kanta dake tsefe.
Ina tafe ina tunanin rayuwar da nayi a gidan Ahmad da mahaifiyarshi, da kuma shi kanshi.
Da mahaifiyarshi dai kowa ya sani babu sauki amma da shi wata irin rayuwa da kowacce mata zata yi mafarkin samu.
Yanzu kuma ko ina zan fada sai Allah, don kuwa a yanzu ko kwanakin baya da ya kira ni gaisuwa kawai muka yi ya dan tambaye ni abubuwa. Saboda jin labarin komawata Makaranta da Yayi, da alama shima ya hakura. Kirana kawai yake yi saboda mutunci.
Nasiba ita ce kadai yarinyar da nake mu’amalla da ita a makaranta. Jininmu ya hadu ne ba don halinmu yazo daya ba. Nasiba ‘yar gaye ce sosai Irin yan gayun nan da basa kunyar gayensu. Wadanda yafa gyale ko saka hijabi bai dame su ba, yar gata ce sosai daga irin suturun da take sakawa na fahimci hakan.
Duk da irin bambancin da ke tsakaninmu muna jin dadin mu’amallar mu don kuwa tana da matukar kamun kai ba kadan ba.
Mu’amalla ta da ita ya sanya ni na kara jin dadin karatuna, don kuwa komai tare muke yin shi.
Amma har da irin sabon da muka yi da juna ban san komai game da ita ba, kamar yadda ita ma bata san komai game da ni ba.
Ta dai tambaye ni yarana na ce daya, don haka ita kallon matar aure take yi mun. Karatu sosai muke yi ba tare da wani wasa ko kuma yaudarar kai ba, har aka zo rubuta Jarrabawa.
Bayan yan gwaje-gwajen da aka yi mana wanda tun daga nan muka fara ganin irin kokarin mu da kuma ta inda zamu yi gyara.
A komai kusan muna tafe ne da Nasiba sai dai a wasu darussan ta fini haka nima a wasu na fita. A duk inda dayanmu kuma yafi daya, to a nan zai rinka koyar da dan uwanshi.
Hakan ya yi matukar taimakon mu ba kadan ba. Ranar da zamu fara jarrabawa kuwa har Babana sai da na gayawa, ya taya ni da addu’a ya kuma jaddada mun a kullum shi din cikin yi mun addu’a yake. Zai kuma kara a kan ta da. Na ce to na gode
Baba. Cikin sauki muka yi jarrabawarmu muka gama ba tare da mun fuskanci wani tsanani ba.
An kuma ce wai Juma’a mai kyau daga Laraba ake ganeta. Muna rike da hannun juna ranar da muka yi hutu zamu rabu, Nasiba ta ce “amma dai kin san ba ki da kirki ko?” Cikin murmushi na ce,”Na sani mana Nasiba.”
Ta yamutsa fuska tana kallona, ta ce “Amsar da za ki ba ni kenan don wulakanci?
Na ce, “To ai kin ga ke ce ki ka fada kin ga kuma na san ba za ki yi mun karya ba.
Ta ce, “To tunda muke da ke ba ki taba tunanin ya kamata ki tambaye ni ta inda gidanmu yake ba, ballantana in saka ran wata rana zan ganki. Kullum haduwar Makaranta rabuwar Makaranta. Ni kuwa a yanzu din nan da nake ko da ban taba zuwa gidanku ba har kalan fentin shi na sani. Don kuwa komai yana cikin zuciyata.” Nan take naji kunyar Nasiba ta kama ni, don kuwa nasan gaskiyarta kawai ta fada.
Na saka hannu a cikin jakata na dauko biro da ‘yar takarda na ce “Kiyi hakuri Nasiba na yi kuskure, amma rubuta mun a nan.”
Ta watso mun wata zabgegiyar harara sannan tayi tafiyarta ta bar ni a tsaye a wurin.
Sai da nayi wanka naci abinci na wartsake gajiyata sannan na dauko wayata na rubutawa Nasiba don gajeren text message.
“Kiyi hakuri kawata ban kyauta ba, amma ki saurare ni zan ba ki surprise.
Miss you so much.”
Ranar da aka wayi gari satinmu biyu da hutu ranar Samahatu ta haifo santalelen yaro.
Ina rike da yaron a hannuna bayan an sallamo su daga asibiti sun dawo gida, bakina ya ki rufuwa saboda murna.
Shi kuwa Yaya Auwalu sai kaiwa da kawowa yake yi. Iyayen Samahatu sun so su dauketa ba a yardar musu ba. Don haka kullum Inna Hadiza ce mai zuwa ta yi mata wanka ta yiwa jariri.
Kwanaki uku da yin haihuwar sai ga Nasiba. Duk da na sanar da ita maganar haihuwan ban yi zaton zata zo ba, rungume juna muka yi cikin murna.
Wurin Umma na fara kaita suka gaisa, na kaita wurin Baba Ladi, sannan na shigar da ita asalin dakina. Na ajiye mata abubuwan ci da na sha muna yar hira tana ta dan kalle-kallenta sannan takalle ni cikin mamaki.
“Yanzun nan Hauwa’u dama ba ki da aure amma ba ki taba gaya mun ba? Gaskiya ke ba mutuniyar kirki ba ce.”
Na ce, “To kiyi hakuri a yadda dama naso ki gane kenan. Tayi tsaki ta dauki kunun ayarta ta fara sha.
Muna ‘yar hirarmu tana ciye-ciyenta na abubuwan da na ajiye mata. Ta ce, “Amma gaskiya kina da zurfin ciki, koda yake ba zan ga laifinki ba. Don kuwa mutanen yanzu ba abin yarda ba ne, balle kaje kana bude musu sirrinka. Bayani na yi wa Nasiba na komai game da ni, zamana a gidan Ishak da kuma Ahmad da yadda aka yi auren ya mutu.
Tayi shiru jimawa kadan ta ce “Gaskiya maganin matsalar kenan komawan da ki ka yi makaranta. Sai ayi ta addu’ar samun salihin miji a gaba da za ki yi zamanki lafiya da shi.”
Na ce,”Addu’ata kenan nima.”
Zukekiyar riga mai kyau da sabulai hadi da turmin atamfa ‘yar Ingila Nasiba ta bai wa Samahatu da na kaita ta yi mata barka. Umma ma tsaraba tayi mata sosai, dangin kuka, kubewa busassa, daddawa da su citta. Sannan ta kulle mata yajin daddawan maijego duka ta ce, ta kai wa mahaifiyarta ta kuma yi murna sosai. Babu wanda bai yaba da nutsuwar Nasiba ba a gidanmu.
Mun yi shagalin suna sosai da sosai, yaro ya ci suna Abdurrahman saboda darajar sunan. Hutunmu ya kare cikin kankanin lokaci saboda dadin shi da múka ji. Shiri sosai na sake yi don himmar fuskantar zangon karatu na biyu, wato second semester a makaranta. Duk wani abu da nasan zai taimake ni, kuma na tanade shi.
Sammako nayi saboda dokin da nake yi na tafi makaranta, duk da sanin da nayi cewa a yau din rana ce da aka bude mafi akasarin dalibai ba su zo ba. Haka nan malaman ma wasu ba a satin suke fara shiga aji ba. Kan gurin da na saba zama ni da Nasiba naje na karkabe mana na zauna, tare da jawo wani littafi na turanci don ya dan debe min kewa mai suna (Jane Eyre) ina karantawa.
Lokaci ya tafi ba kadan ba jifa-jifa kuma ina dagowa don amsa gaisuwar abokan karatuna da suke ta shigowa ajin.
Na kalli agogon da ke daure a hannuna don ganin lokaci saboda ganewan da nayi lokaci ya tafi. Karfe takwas ne har da rabi amma Nasibata ba ta zo ba. Na dauko wayata kenan da nufin na kirata sai ga mallam ya shigo.
Mallam Zakariyya shi ne Malamin da yake daukanmu GNS wacce madda ce da ta zama wajibi akan kowanne dalibi na makarantar. Koda kuwa me kake karantawa, sanin halin shida na yi ne yasa na mayar da wayar na ajiye.
Ya isa gaban allo yana rike da marker a hannunshi. Ya rubuta test a jikin allon. Gabana ya yi mummunan faduwa na juya don kallon sauran ‘yan tsirarun ajin suma sai zazzare idanu suke yi alamar bani kadai ba ce a cikin rudani sai dai babu wanda ya tanka. Ya rubuta mana tambayoyin shi yaja gefe yana nade da hannayen shi a kirji yayin da yake bin mu da kallo.
Na yago takarda na rubuta suna, course (madda), department da kuma matriculation no, nayi gaggawan rubuta abinda na sani daidai gwargwado. Sannan na jawo wata takardar duk da faduwar gaban da nake yi bai sa na fasa abinda nayi niyya ba. Nasiba na rubuta ma duk kuwa da sanin halin shi da nayi. Muna gamawa ya karba sannan yayi mana dan karatun da zai yi mana ya fita.