Skip to content
Part 24 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Ban cewa Mallam komai ba har ya yi shiru. Ya kalli agogon hannunshi ya ce, “yanzu karfe uku ne, ina ganin gara na hanzarta don kada lokacin sallar la’asar ya riske ni a nan.

Zan samu alfarmar sauke ki a gida? Na ce, “A a ba yanzu zan tafi ba.”

Yasa hannu a aljihu ya ajiye kudi masu dan auki a kan hannun kujerar da nake zaune a kai.

Ya ce, “Ki yi kudin mota don Allah a kula yin dare ba shi da kyau.”

Ban sake yi ma Nasiba maganar Mallam ba, ita ma bata yi mun ba.

Wata hirar kawai muka yi har ta rako ni nas mota don dawowa gida.

Tsakanina da Mallam Zakariyyya kuwa kullum yana kirana a da safe sai dare duka kuma gaisuwa ce kawai sai ko dan maganar karatu.

Ba a dade ba bayan nan muka koma makaranta.

Da farko dai naji nauyin abubuwa musamman yadda zan fuskanci malam a aji.

Amma shima sai na gane ya basar, don haka nima sai na shanye. Sai kawai na dauka babu wanda yasan zance in ban da Nasiba.

Bamu fi sati biyu da komawa makaranta ba sai kawai kwatsam Babana ya saka daurin aurena da mal’lam, abinda yayi matukar dukan zuciya ta.

Na kasa sanin dalilin da yasa har yanzu zuciyata ta kasa sakewa da lamarin shi, mutumin da kowa yasan ba shi da wani aibu.

Haka nan ba ni da wani hujja na kin shi. Wunin ranar ban iya tabuka komai ba.

Haka nan washegari ban tashi da niyyar zuwa makaranta ba. Umma tana ta kallona har ta gaji ta ce “Ni yau baku da makaranta ne ko?”

Na ce, “Muna da shi, ba na dai jin dadi ne kawai.”

Waya ya yi mun yana shaida min zuwan shi.

Na zurma hijabina na fita. Kasancewar dare ne bayan sallar Isha’i a zaune a motar shi na same shi.

Muna gaisawa ya fara tambayata dalilin da yasa ban je makaranta ba.
Na ce “haka kawai,” da alama kuma amsar ba ta yi mishi dadi ba. Saboda shirun da yayi na dan wani lokaci kafin ya ce.

“Nasan an yi miki bayanin komai na game da saka ranar aurenmu da aka yi, ina kuma fata babu matsala ko?”
Nan ma shiru nayi ban ce komai ba, don ban san abinda zan ce ba.

Idan ma da matsala wannan duk daga baya ne don kuwa ba zai yiwu Babana ya zartar da hukunci a kaina. Na nuna mishi cewa shi din bai isa ba.

“Lokacin da aka saka ba mai tsawo ba ne, don haka ina so ki fadi abubuwan da kike da bukata da kuma shirye-shiryenki gabadaya. Tunda ai kin san sati biyu ne ko?”

“Ni gabadaya ba ni da wasu shirye-shirye duk abinda aka yi kawai ya wadatar” ya ce, “To babu laifi.”

Kusan duk shirye-shiryen da ake yi na auren Nasiba ce mai yi wanda ya dangance ni sauran shirye-shiryen gida kuwa duk su Umma ne suke yi.
Da alama kuma da gaske suke yi. har kudin kayan lefe Nasiba ya baiwa ta narko siyayya ba na wasa ba.

Ganin irin hidimar kashe kudin da yake yi yasa na rubuta mishi text a gajarce.

Ina fata ka san na yi aure biyu a baya?

A take kuma ya turo min da amsa.

Na sani akwai matsala ne?

Don haka sai kawai na rabu da shi.
A makaranta kuwa satin da maganar ta bazu sai da naji kamar kada na sake zuwa.

Kowa maganar yake yi rakwacam babu tsari, wasu ma cewa suke yi dama shi ne ya daure mun gindin cin jarrabawar da nake yi.

Duk inda na zauna kuma idan mutum yazo mace ko namiji sai ka ji ya ce amarya congratulations muna taya ki murna fa wani idan ya tsaya a nan, wani sai ya kara don neman bugun cikin, yayin da wasu kuwa gaskiyarsu suke fada taya ni murna suke yi.

Shi kuwa duk yadda ya yi da ni na gaisa da abokanshi naki yarda.

Don kuwa nasan abokan nashi ba za su wuce malamanmu ba.

Idan da don ta ni ne da ko ‘yar walima ba ayi ba, to amma Nasiba ta ki.

Gayyata sosai ta yi, yan makarantarmu kuwa sun amsa gayyata, ga kuma taron dangi da abokan arziki. Amma komai na dangin abinci da na sha sai da ya ragu.

Ana daura aure kuwa a washegari aka kai ni gidan Mallam. Har a wannan lokacin kuwa da aka watse a ka barni daga ni sai Nasiba, zuciyata a kuntace take.

“Da kin yi hakuri kin saki ranki ni fa nafi zaton tsoro ne ya hana zuciyarki ta sake.

Kuma gaskiya ne a tsoracen nake don kuwa ban san bayan auren me zai biyo baya ba, haka nan shi wannan auren shi ne na karshe ko kuwa shima matsala za ta taso ne a sake sakina? Bayan na fara sakewa na mayar da gidan, gidan zamana? Idan da a yadda naso ne to da zan dau lokaci ban yi wani auren ba.

Don kuwa babu abinda naki irin a zauna zaman kirga mun aure.

Nasiba bata tafi ba sai da Mallam ya shigo bayan an idar da sallar Isha’i.
Da kanshi kuma ya mayar da ita gida bayan yayi mata godiya.

Duk yadda nayi zaton abin zai zamo sai naga ba haka ba, don kuwa cikin kankanin lokaci sai malam ya sauya mun tunanina.

Don kuwa sai na gane shi mutum ne mai wani irin rarrashi da saukin kai.

Da sassafe na tashi na dan yi abubuwan da zan yi irin su wanka, na kuma kintsa kaina cikin yadin shadda gizna, doguwar riga mai laushi.

Nasa gyale mahadin ta na rufe jikina. A falo na zauna ina karewa falon kallo.
Yayi kyau ba kadan ba, ba wai tsadar kayan ba sai dai kyan tsarin da aka yi mishi ne zai bai wa mutum sha’awa.
Komai na cikin shi kore ne mai haske. Kama daga kan labule, kujeru, centre rug har door mat dan sirkin ba mai yawa ba ne.

Ban dade da zama a wurin ba malam ya shigo. Sanye da jallabiya fara sol a jikinshi.

Kusa da ni yazo ya zauna a kan doguwar kujerar da nake.

Na dan takura kadan saboda yanayin zaman da muka yi. Ya ce, “Amarya an tashi lafiya? Na fara gaishe shi yana amsawa ya ce, “kiyi hakuri kin tashi ba ki ganni ba na tsaya ne a masallaci meeting na committee kan wasu yan abubuwa da ke tasowa a unguwa.

Ina fata babu matsala dai ko? A hankali na ce “Eh.” Ya ce, “To an gode, Allah za ki zo wuri na ne mu karya gabadaya ko?”

Na ce, “To.” Yana gaba na bishi a baya zuwa inda ya kira sashen shi.

Tankamemen falo ne kawatacce da kujeru masu kyau sai tibi na bango babba, sosai na zauna akan daya daga cikin kujerun, shi kuma ya shiga wata kofa ya dan dade kafin ya fito.

Fitowar shi babu dadewa wata mace ta shigo doguwa ba sosai ba, yar siririya wankan tarwada, don kuwa na fita haske sosai sai dai kyakkyawa ce sosai. sannan ‘yar gaye a kallon da nayi mata da bai fi na dakiku biyu ba.

“Sannu Hauwa’u an tashi lafiya?”
Ba sai wani ya tsaya yi mun bayanin komai ba, take na fahimta amma duk da hakan sai malam ya ce.

“Hauwa’u ga Amina nan ‘yar uwarki ce.”

Ta karasa kusa da shi ta dan zauna a gefe tana mishi magana da ban san me take fada ba.

Na ji ya ce, “A a ba na so. Ta waiwayo ta kalle ni.

“Ina kwana Hauwa’u, an tashi lafiya ko?” Sannan ta sake fita sai ga ta da manyan kula guda biyu take kuma ta fara zuba abinci tana ajiyewa.

Sai da ta gama zubawa sannan ta ce na zo muci.

Muna zaune muna ci kowa dai da nashi, sai dai na kasa sakewa ko kadan babu abinda nake so irin na koma dakina su kuwa suna ta dan hirar su.
Ya kalle ni “ya ya dai Hauwa’u, akwai matsala ne?”

Na ce, “A’a babu.” Amina ta ce, “ƙila kunyata take ji ko don dai nasan wannan kunyar ba ta Darling ba ce. Tunda ba yau aka fara ganin juna ba.”

Ni kuwa wani irin abu nake ji a zuciyata ba ɓacin rai ba, haka nan ba haushi ba.

Amina ta gama cin abincinta ta mike ta fita ta bar ni rike da plate a hannu.
“Ƙokarta ki ci abincin nan ko babu yawa.

Abinda ya fara fada mun kenan, bayan fitarta.

“Ko kuma kin fi so na ba ki da hannuna?”

Na dago ido zan kalle shi, na kasa saboda kallon da yake yi mun. ban iya ci ba don haka na hakura na ajiye.

Ya mike ya isa gaban fridge din dakin ya dauko robar fresh milk da dogon kofi yazo kusa da ni a kasa ya zauna ya tsiyaya ya dauka ya nufi bakina zai ba ni da kanshi.

Na girgiza kai na karba da hannuna bai hana ni ba sai kawai ya sake mun ya ce, “to amma fa ki shanye duka kafin na dawo daga dauko yara daga Islamiyya.”

“Kin san yau lahadi da safe ake zuwa.” Na ce, “To. Ina so na koma dakina.” Ya ce, “A’a ki zauna a nan idan kuma barci ki ke ji ga daki nan ki shiga.”

Bai fi mintina talatin ba da fita sai gashi ya shigo, yara guda uku suna binshi a baya maza biyu da karamarsu mace.

Dukkansu suna ba shi labarin abubuwa ya zo ya zauna ya ce, “To ba ku gaisa da Mamanku ba?”

Gabadayansu suka fara gaishe ni a tare cikin fara’ata nima na amsa. Ƙaramar ta ce, “Baba ita ce sabuwar Mama ko?”
Ya ce, “Ita ce Ummulkhairi ashe kin gane ta kenan? Ta kada kanta alamar eh, ya ce “To kuje ku huta ku cire kayan makaranta ku ci Abinci.”

Suka ce, “A’a Baba mu a nan zamu ci. Ya bude musu ido ya ce, “Kai ku tafi ku ba ni wuri na ce.”

Karamar tasa kuka, ta juya tabi yan uwanta suka fita
“Ina ganin ya kamata ki kwanta ko?”

Ban ce mishi komai ba don kuwa ba zan iya musu da shi ba.

Kwanana biyar a gidan Nasiba ta dawo. Na Harare ta lokacin da naga shigowarta, na ce don wulakanci yau ne kika ga daman zuwa?
Ta ce, “A to ban yi kokari ba kenan, ai da cewa na yi sai kin yi sati biyu.”
Na ce, “To ai sai ki koma.

Ta isa gaban fridge din dakin ta ciro lemon kwali ta zauna tana surkawa da ruwan sanyi saboda bata son za ki sosai.

Amina tayi sallama. Gabadaya muka amsa sallamar, ta nemi wuri ta zauna suka fara gaisawa da Nasiba. Sannan aka shiga hira gabadaya.

Ta kai mintina goma sannan ta tashi ta fita. Nasiba ta ce da alama dai matar nan za ayi zaman kalau da ita? Na dan yi murmushi muka shiga wata hirar tana tambaya ta ranar da zan koma makaranta.

Na ce, “Na jira ne ya ce mun mu tafi to har yanzu bai ce ba.”

Nasiba ta ce, “Kenan za ki jira ne sai ya ce ki tafi, ina ce kwanaki uku yayi a dakin nan ya fita?
Na ce, Eh mana, to da nawa ki ke so yayi? Ta ce, “A’a ba wannan ba ne ma, ki dai sa ni ne cewa ya kamata idan ku ka zauna kiyi mishi maganar komawarki makaranta.

Kasancewar yau kwanakina biyar ne a gidan to kuma a dakina malam yake.
Don haka kokarina shi ne na ganin nayi mishi maganar makaranta na tunda na kusa kwanaki goma ban je ba. Don tun kafin daurin aurenmu na daina zuwa.

Muna zaune a falo dukkanmu hira ake yi tunda a can muke cin abincin dare gabadayanmu.

Sai dai ni kam duk hirar da suke yi ban iya tsoma musu baki, idan ba saka ni a ciki aka yi ba.

Hankalina a zahiri yana kan shirin da ake yi ne a TV sai dai a badini ba haka ba ne.

Ban saba ganin mace tana yiwa namiji abubuwa haka a gabana ba.
Na kasa sakin jiki da irin mu’amallar malam da matar shi.

Na sani tare na same su amma da sai su rinka bari idan ba na nan suyi abinsu.

Gyara zamana nayi a kan kujera na rufe ido nayi kamar ina barci ne.
Zuwa can naji ya kira sunana. Shiru na yi ban amsa ba.

“Amina ya kamata ki je ki kwanta dare fa ya fara yi, goma ta wuce.”

Shiru ta yi bata amsa ba zuwa can na dan ji shisshikar kuka shi kuma yana cewa “menene kuma? Me aka yi miki na kuka?”

“To Darling ya ya ba zan yi kuka ba don Allah wai har an yi lokacin da ni zaka kore ni a dakinka saboda ka matsu da wata ni kuma na isheka ko?”
“Haba Amina, wannan wace irin magana ki ke yi haka? Ki na so ki tsokalo magana ne kawai.”

“Idan kinga ba za ki tafi ba zauna mu kwana duka a nan. Magana ta kare.”

<< Mai Daki 23Mai Daki 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.