Skip to content
Part 26 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Ban kuma taba fasawa ba. Ko wurin cin abinci muka hadu sai ta kai ta kawo ne magana ke hada mu.
Idan bata ga dama ba kuwa ko nayi mata ba ta amsawa.

Ta daina shisshigin zuba mishi abinshi ranar girkina, ko shisshige mishi da take yi.

Shirin jarrabawa ta bata hana ni hidima da mijina ba, don kuwa a yanzu ne ma nake jina na fara auren.
Na gama hada abinci a falo na fara zuba mishi salad saboda azumin da ya yi.

Ya fara ci na kai hannu zan dauki cokali sai naga ta rike, na ce barı mana na gama zuba mishi sai na baki.
Kan na ankara sai kawai naga ta fauce shi a hannuna ta ce, to duk maitakarki sai na zuba nawa, jarrababbiya kawai.

Bude baki na yi galala ina kallonta, shi kuma cikin bacin rai ya ce, “ya ya haka? Me ye haka kuma daga magana sai ki zage ta? To ba na so.”

“Eh mana ai dole ka ce ba ka so sai kawai ta fashe da kuka. Muna zaman zamanmu ka dauko masifa ka kawo mun cikin gida.”

“Duk abubuwan da take yi mun kana gani ba ka ce komai ba, saboda ba haka kawai ta barka ba, da haka muke?”

“Ta shiga tsakaninmu ko kallon arziki baka iya yi mun sai idan bata nan har ta kai ma zata wulakantani a gabanka, kuma ka goyi bayanta.”

Tana kukanta ina rike da cokali a hannuna na kasa komai saboda takaici, shi kuma salad dinshi yake sha tamkar ba a yi wani abu ba.
Ya kalle ni idan ba za ki iya zuba mun abincin ba ajiye ki ba ni wuri.
Inda zan iya da ajiyewa nayi na tashi, to amma ba zan iya ba.

Na zuba mishi na kammala mishi komai na mike na tafi dakina na zauna a bakin gado.

Maganganun Amina suna dawo min ban taba jin mutumin da yayi mun irin wannan zagin ba.

Kala malam bai ce mata ba saboda bani da mutuncin da zata zage ni ayi mata magana.

Washegari kicin na fara shiga na hada abin karyawa na dauka zan shiga naji su suna magana, da alama kuma ba ta dadi ba ce, na karasa dakin na zauna a kasa na gaishe shi ya amsa a dake.
Na hada mishi nashi na mika mishi ya zuba mun ido, nayi gaggawar sunkuyar da kaina.

“Gargadi na karshe da zan yi miki shi ne, na kada ki sake zuba mun abinci ki tashi ki bar ni da shi a wurin, shashashar yarinya kawai.”

Na ajiye a gefe na tashi na shiga cikin bedroom din shi don na gyara, sai dai raina a matukar bace.

Na gama abinda zan yi na fito na same shi yana ce mata ba za ta yi ba. Idan kinga za ki yi girkin da zaku ci da rana shi kenan.

Idan kuma kin ga za ki iya tilasta ni sa ta yi miki girkin da zaku ci don kawai tana amsa sunan matata sai mu gani tunda na fahimci ba kya jin maganata. Ni dai na gama shirina na fito muka tafi.

Makaranta kowa a shirye yake don fara jarrabawa, kuma mun fito lafiya ba tare da matsala ba.

Na biyo office din malam ba shi da alama zai tafi yanzu, na ce ko zan tafi ne saboda mun gama jarrabawa.
Bai kalle ni ba nima ban kara cewa komai ba. Ba mu dawo ba sai wajen karfe uku.

Amina bata yi girki ba na shiga dakina ina kokarin neman abinda zan ci saboda wata irin gigitacciyar yunwa da ta kama ni.

Shayi na hada na sha wanda take kuma ya burge mun ciki, nayi ta kwara amai babu kakkautawa.

Nayi wanka na saka jallabiya na shigo kitchen jikina a mace na dauko indomie na yara na dora a wuta cikin sauri ta nuna na ci na dan ji dadi.
Sannan na koma nayi la’asar kafin na dawo na dora abincin dare.

Duk abinda nayi kokartawa kawai nake yi saboda wani zazzabi da ya rufe ni. Na hada komai na kai mishi yadda muka saba.

Na zuba mishi abinci har yaci ya gama Amina bata zo ba, ya kalle ni, “ke ba za ki ci ba ne?” Na ce, Ba na jin dadi ne. ya ce “Allah ya sauwake, amma da kin daure kin ci ko babu yawa.”
Ban yarda na ci ba don kuwa zuciyata ba a nutse take ba.

Wajen karfe dayan dare na tashi saboda murdawan da cikina ya ke yi, na shiga bayan gida wani aman ne ya sake kubuce mun, nayi ta yi.

Motsin da naji a bayana bai sa na juya ba, don na san malam ne. na wanke jikina na dawo daki na kwanta.
Ban wani jima ba na sake komawa. Tun ina aman abubuwan da na ci da rana har sai da na koma kakarin aman kawai nake yi.

Amma babu abinda ke fita. Nayi matukar galabaita.

Wajen karfe hudu saura kwata, Mallam ya dauke ni zuwa asibiti, tun kan mu isa naji ni a jike, abinda na dauka fitsari nake yi saboda wahalar da nayi.

Sai dai ina fitowa daga cikin motar hasken fitilun dake harabar wurin suka haskake mana jinin da ya wanke illahirin kayan jikina.

Cikin wani irin firgita nayi luuu zan yi kasa ya yi saurin rike ni. Daukata yayi ya shigar dani asibitin take kuma Nurses da Likita suka yo kaina.
Gwajin farko aka tabbatar mana ciki ne, kuma ya fita. Wankin ciki aka shigar dani, shi kuma ya juya ya tafi, don fara kiran sallar Asuba.

Sun so su rike ni amma naki yarda, don haka muka dawo gida wajen karfe goma.

Jarrabawar ranar dai ta wuce ni. Abin da na ce wa Mallam kenan, sai dai bai ce mun komai ba, tukinshi kawai yake yi.

Muna dawowa gida kuma ya sake shiryawa ya fita don zuwa wurin aiki. Labarin da Nasiba taji ne yasa ta zuwa bayan gama jarrabawarta.
Ta zuba mun ido cikin mamaki. “Kinga yadda ki ka zabge kuwa yau kawai?
Gaskiya kin ji jiki Hauwa’u, sannu.” Ina kwance na amsa. Sai lokacin ne Amina ta shigo a’a kun zo ne? Nasiba ta fara gaisheta.

Suka gama gaisawa sannan tayi mun sannu da jiki ta fita. Sai da Mallam ya dawo Nasiba ta tafi.

Har cikin dakina ya shigo ina kwance a kan gado na saboda rashin karfin da nake dashi.

Na dan yunkura na żauna ya ce, Yaya jikin naki. Na ce da sauki. Ba ki da matsala?Na ce, Eh sai ta rashin karfi, ya ce eh ai sai a hankali wannan kuma. Don kin zubar da jini da yawa, ga kuma aman da ki ka kwana kina yi.
Na dan daga tafin hannuna ina kallo, shima ya rike yana dan latsawa.

To amma Hauwa’u me yasa kina da ciki har kin shiga wata na uku ba ki taba gaya mun ba me ki ke nufi da hakan da ki ka yi?”

Yanayin tambayar tashi ta yi mun wani iri. Na ce, “ban san ina da shi ba. Abin da na sani kawai shi ne, na kan tashi da zazzabi da safe, amma baya ga haka ba na jin komai.

Sai aman da nayi jiya, shi kenan. Ya ce, to Allah ya ba ki lafiya, na ce amin. Muka canza maganar zuwa can kuma sai ya sake cewa, ina fata kin san da cewa maganar karatun ki ba zai shafi al’amarin aurena da ke ba ko?”

Na dan kalle shi zuwa can na ce, “kana zargin wani abu ne?” yayi shiru na dakiku kafin ya ce, a’a bana yi. Na ce “to nayi maka alkawarin ba za ka taba ganin wani abinda baka so ba game da maganar karatuna ba.”

Ya ce, to na gode, ya yi mun sai da safe sannan ya fita.

Duk da rashin karfina na lallaba naje makaranta a washegari don jarrabawata. Shima kuma yana jirana a waje lokacin jarrabawar ina gamawa ya dauko ni ya dawo da ni gida. Bai ce sai ya gama ayyukanshi ba.

Duk abinda nake yi daurewa kawai nake yi saboda yadda zuciyata take cunkushe.

Babu abinda ya tsaya mun irin ganewan da nayi har yanzu ban rabu da matsalar mahaifar da na samu a gidan Ahmad ba.

Yanzu me zan yi a kai? Zan sami Mallam nayi mishi bayani ne ko kuwa yaya? Yamma ta yi, ban hassala kome ba saboda tunane-tunanen da ke damuna gara nayi aikin da ke gabana kawai duk da rashin karfin jikina.

Na shiga kicin saboda na dora abincin dare na samu Amina a ciki tana yi don haka na dawo dakina na sake kwanciya.

Don haka a kwanaki biyun nan in banda jarrabawata ba na leka ko ina, ko wurin cin abinci ba na zuwa.
Shi ne dai yake shigowa ya dan yi mun hira ya tafi saboda tunanin da yake yi na rashin karfin jiki ke damuna.

Duk da jarrabawata ban ji kunyar shirya lafiyayyen abinci ba, ranar da kwanana ya zago na yi kwalliya mai ban sha’awa cikin yadin material baki da pink mai rawa dinkin doguwar riga ya kuma bi jikina ya manne saboda yaukin yadin.

Ni kaina nasan ya matukar yi mun kyau, don ya karawa hasken fatata kyalli. Na feshe jikina da turare. Sai da nayi sallah sannan na shiga falon.

A yanzu Amina ta daina yi mun shisshigin makalkale Mallam ranar girkina, don haka ko ba na wuri sai nazo nake yi mishi abubuwan da yake bukata.

Na shiga falon yana ganina ya dan saki murmushin da ban san ko na meye ba a cikin biyu, na ganin jikina yayi kwari ne ko kuma na mai yaba kwalliyar dayar mu ba ne a gaban mu ko zai yaba miki kwalliya to sai kun kebe don gudun cin fuska.

Na karasa gaban shi ina zuba mishi abinci na gama na zuba mishi abin sha na gyara zan zauna ya ce ke fa?
Kamar nayi magana sai na fasa na dauki plate ina zubawa Amina ta ce ai da ka barta kawai kila bata jin ci ne. ka san illar bari yawa ne da ita ballantana wanda a ka jawo shi da karfi. Ai ma an auna arziki da abin ya tsaya a haka, ga yar makwabtan nan namu da suka shigo duba ki shekaranjiya ai garin haka ita har yanzu bata sake haihuwa ba. Don an ce mahaifarta ta samu matsala kawai fa akan tana Jami’a itama kamar dai nakin nan.”

Na kalli inda Mallam ke zaune yana cin abinci sai dai fuskarshi ta canza gaba daya, na zuba abincin na ja gabana zan fara ci.

Ta fara kokarin ci gaba da zancen na ce, Amina ya isa haka. Ta kalle ni ta ce, “au, ya isa kuma kada nayi miki nasiha don na taimake ki?”

“Ai ni ‘yar uwa na dauke ki don kuwa ni ko kishi da ke ba na yi.” Mallam ya ce, “ta dai ce ya isa haka ina ganin da sai kiyi shiru.”

“To ai shi kenan tunda dai duk bakwa son zancen. Ita gaskiya kasan daci ne da ita Darling, amma tunda ba ka so shikenan.”

Ta dan yi murmushi ta kalle shi, “Darling sai da safe.” Ina rike da cokali da abinci a plate ina dan coccokalawa amma na kasa ci saboda bacin rai.

<< Mai Daki 25Mai Daki 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×