Skip to content
Part 3 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Duk yadda na kai da daurewa da na zauna gaban Umma zan yi mata magana sai kawai na fashe da kuka.

Ta ce, “Menene kuma na kuka?” Ta tambaye ni fuskarta a yamutse. Na ce “Umma daga zuwa biyu sai kawai maganar aure, ko gama saninshi bamu yi ba, sannan karatuna fa?”
Tayi shiru ta ci gaba da saka maballan gar da na samu ta gama, an kai kamar mintina biyar sannan ta fara yin magana.

“Babanki ba shi da halin daukar dawainiyar Makarantarki, kema kin san da haka. A yanzu ma da ki ke Makarantar secondary abin ya gagara ballantana kin shiga wacce ki ke burin yi ta koyon jinya.

Idan da kina da zurfin tunani kema ya kamata ace kin fahimci hakan. ke kadai ce a cikin ku bakwai ki ke ka ratun nan, amma a biya miki kudin Makaranta ma abin ya gagara.

Babanku yana zuwa wurin aikin nan da yake yi ne kawai ba wai don kudin da ake ba shi ba tunda a yanzu ba biya ake yi ba sai don kawai kada ya zauna a gida ba tare ya yana da abin yi ba.

Ba kuma zai yiwu ya ce takamar ke da shi kuna son kiyi karatu ya yi ta ajiye ki a gida ba, ke mace ce. Kin kai lokacin aure tunda kuma shi ya ce ya yaba da kamalar mutumin. Ina ganin shi kenan magana ta kare, ya kuma yi alkawarin zai tsaya yaga kin yi karatun da ki ke son yi.

Na tashi na dawo dakina na kwanta saboda yanayin da jikina ya yi mun, aure a yanzu? Babu abinda ke zagaya mun kwakwalwata irin ko wata guda ban yi da sanin mutumin ba.
To amma tunda dai yayi alkawarin zan yi karatu shi kenan magana ta kare, dama burina kenan idan na samu hakan kuma zan yi murna.

Bayan nan ban sake zuwa Makaranta ba saboa abinda Babana ya ce kenan a jinkirta aga yadda maganar zata kaya.

Na ci gaba da karatun a dakina. Sati biyu ne kawai bayan nan iyayen Ishak suka zo an sasanta da su har an daidaita lokacin aure don suma suna son shi da gaggawa.

Sun kuma zo da kayansu na na gani ina so. Tun daga lokacin da maganar aurena ta yadu ban sake ganin Abdussamad na gaishe shi ya amsa ba wani lokacin ma yana hango ni yake kaucewa.

Ban san abinda yake nufi ba, don haka nima sai kawai na share shi.

Shirye-shirye na nima nake yi da iyakacin karfina tunda dai ba zance bana son Ishak ba, kamar yadda ba zan ce ina son shi ba.

Babban burina dai da nake hangowa kamar nishadi. Ishak da kanshi ya shaidawa iyayena ba ya bukatar wata doguwar dawainiya da ta danganci kayan daki, shi gidanshi akwai komai. Don haka shirin da Umma ma take yi ya dan yi sauki kokarinta kawaina ganin ta hada mun kayan kicin ne ta kuma saya mun sabon Keke gau a kwalinshi.

Tunda nima ta koya mun dinki na kuma iya daidai gwargwado. A shirye-shiryen da aka yi mun a gida kuwa har da na zuwan garin ma garin Babana Birmin Kudu, duk kuwa da suma za su zo bikin.

An yi mun shirye-shirye masu yawa daga gida amma duk da haka sai da Ishak ya kawo kudi masu yawa ya kara mun.

Zan iya cewa tun da aka fara maganar aurena da shi al’amarin da yanayin gidanmu gaba daya ya canza, don kuwa duk zuwan da zai yi zai kawo kudi masu dan dama ya bani. Haka nan ba zai rasa abin amfani da zai sauke mana ba. Tun da farko da Babana yana karba ya hana ni am fani da kayan da yake bani.

Amma da aka zo magana tayi karfi sai ya bar ni har da kayan da yake kawo mun na zannuwa yana karba yanzu duk ya dawo mun da su.

Ni kuma na kai an diddinke mun su, ina ta kwalliyata gwanin sha’awa. Wani lokaci sai nayi tunani na ce to a waje ma ya wadata ni haka ina kuma ga naje gidan shi.

Kwanaki uku kawai nayi a birnin kudu duk kuwa da yawan ‘yan uwan Babana da ke garin saboda gabatowar bukina na gaiyato kawayena irin su Sadiya da wasu daga cikin ajinmu da na san muna mutunci da su.

Na kuma gayyato Lubabatu kanwar Abdussamad da muke unguwa daya da su gashi kuma dama tare muka tashi tunda sa’o’i muke.
Ina zaune a dakina ina shafa mai na mai tsada Ishak ne ya ke saya mun shi wanda a yanzu ya mayar mun da jikina tamfar wacce aka ciro daga cikin kwai saboda laushi da kyau.

Dama gani ba fara ba haka nan ba baka ba. Kalar jikina ita ce tafi daukar hankali, amma ba ya ga haka bani da tsawo sai dai kuma idan ba tsayuwa kusa dani kayi ba zai yi wuya ka gane haka, don kuwa gabo6ina suna da zubin na dogayen mutane.

Lubabatu ce tayi sallama ta shigo ta zauna muna gaisawa tana tambayata shirye-shiryena, ina yi mata bayani, zuuwa can ta ce, “To ai gaskiya Hauwa’u ni dai hakuri za kiyi ba zan samu zuwa ba shi yasa naga da ki ga shiru ban zo ba gara na gaya mii kawai.

Na ce, Saboda me Luba? Ta ce, “to Yaya Abdussamad ne ya hana ni ya ce, idan kuma nazo to zai lauki kwakkwaran mataki a kaina.
Nayi shiru ina dan tunani a raina na rasa abin da na yiwa Abdussamad da yake sa shi yin irin wadannan abubuwan da yake yi mun a wannan lokacin.

Na ce,To babu komai Luba na gode, amma kin san wani abu? Ni fa ban san abinda na yi wa Abdussamad ba, amma zan shigo gidan naku dan anjima kadan.

Ta ce,A’a rabu da shi kawai. Ni na riga na fahimce shi, shi a tunaninshi sauraron shi da ki ke yi Jira yake yi ya gama karatu kuyi aure. Wanda Umma ma ta gaya mishi ke mace ce ba tun yanzu ba to bai yarda ba.”

Yaushe za’a ce ke kin jira shi, shi da yake aji uku na Jami’a a yanzu ko bautar kasa bai je ba, ballantana har ya samu aiki kuyi aure?

Na ce, “Duk ba haka ba ne ma Luba, ni bai taba ce mun yana sona ba, mutunci ne kawai na dauka a tsakani.”

Ta ce, “Tabdijam! Ke kenan amma kowa ya sani.”

Bayan tafiyar Luba shiru na yi ina tunani ban san abinda ya hana ni fahimta ba sai a yanzu ne nake fahimtar wasu abuubuwan.

To amma koda na gane hakan tun farko ko kuma ace shi ya gaya mun da kanshi zai yiwu na jira shi? na yi wa kaina tambayar.

A take kuma na baiwa kaina amsa ba zai yiwu ba don kuwa a yanzu ma auren nawa ya dauro ne saboda wasu dalilai.

Da dai ace muna da wadatar da zan yi
karatuna ne ba tare da wata matsala ba to da sai in ce zan yi ta jiran Abdussamad har ya yi karatunshi ya gama muyi aure. Don kuwa wane mutum na ce bana sonshi dan gaye ne.

Duk da iyayenshi ba masu kudi ba ne Abdussamad dan gata ne. Haka nan shi ne dan farin namiji a gidansu.

Nayi maza na cire tunaninsu shi da kanwarshi a cikin raina, na ci gaba da harkokina, saboda hakan shi yafi mun. Kayatacciyar walima aka shirya ana gobe daurin aurena. Babu abin da bai ji ba a wurin walimar.

Ana cikin walimar ne kuma ‘yan uwan Ango suka iso da La’asar aka farata ba a gama ba sai gab da sallar Magriba. A wurin su Sadiya nake jin labarin irin kawataccen kayan auren da aka yi mun. Kamar zan yi dokin gani sai kuma naga to ma nawa ne, dokin me kuma.

Na tsaya cewa Ishak ya kawata bikin nan ma tamkar na bata ne. Nayi kwalliya iri-iri ba a magana.

Ranar Asabar da aka daura aure aka kai ni gidan aka watse saboda wadanda suka zo daga wasu garuruwa da za su koma a ranar Lahadi don samun damar komawa wuraren aikin su wadanda suka saura daga yan biki kawai, yan uwan Umma ne da yan uwan Babana wadanda a gidanmu suke.

Na bude idona ina kallon dakin shiryayyen daki na zamani irin wanda mafarkina bai taba nuna mun shi a matsayin nawa ba. takaice dai gidan yayi matukar haduwa daidai da rayuwar ‘yan boko.

Bani kadai ba nasan Ummana da Babana ma za su samu nutsuwa a yanzu. Naci amarcina yadda ya kamata, abin ba a cewa komai ga kuma karin nutsuwa da na samu ta bangaren abinci da kuma wurin zama sai abin ya hadu ya sani nan da nan nayi wani irin canzawa, nayi kyau ba kadan ba.

Kullum idan ‘na tashi nake tsabtace gidana na fara da abincin karyawa wanda shayi ne da biredi wani lokaci ya ce da kwai zai ci wani lokacin kuma ya ce da sauran farfesun dare zai ci.

Kasancewar kusan kullum yana kawo kaji ko kuma kifi ko nama ya dai danganta da abin da yake so sannan na fara gyaran dakin kwanciyarmu wanda kullum na gyara shi sai na tsaya na kare mishi kallon saboda sha’awar da yake bani.

Kullum kuma burina Umma tazo ne taga inda nake kwana amma har yanzu wajen watana daya shiru bata zo ba. Sai na tsabtace toilet din da ke cikin bedroom din na kalkale tiles din bango zuwa na kasa yayi tas, sannan na fito falo. Nan ma haka kafn na shiga kicin, nan ma na gyare shi na goge tiles din shi nayi wanke-wanke na goge cabinet sannan na fito na wanke tsakar gidan nan tas.

Nasa sandar goge-goge nayi mopping din ko ina. Bana gajiya saboda yadda yin hakan yake yi mun dadi a cikin raina. Bayan duk na gama hakanne sai kuma na dauko kayanmu da muka cire na wanke su na goge.

Ban cika yin abinci da rana ba saboda baya dawowa da rana sai dare, don haka sai kawai na sha shayi ko dan wani abumai sauki sai da daddare ne nake yin girki. Kullum cikin raina dai ina tsara yadda zan rinka tafiyar da al’amuran gidana ne, idan na koma Makaranta.

A yau kuma nayi nufin yi mishi maganar tunda idan ba batan lissafi nayi ba, to ina cikin wata na uku ne da aure.

Sai da na gabatar mishi da abincin shi shinkafa da miya da salad na ajiye mishi kunun zaki a gefe, sannan na koma na zauna na ci gaba da kallon abinda ake yi a TV.

Ishak ba mutum ba ne mai hira zan iya cewa abinda aurenmu ban sani ba ko da can kafin auren ban lura na gane hakan ba ne. Kullum dai idan zai dawo to ka’idarshi zai yi guzurin Jaridar da zai karanta ta ranar kafin zuwan shi wurin kwanciya.

Idan kuma ya kwanta ranar ba shi da bukata ta to zai yi juyawar shi ne ya kalli bango nima nayi tawa kwanciyar ban kuma taba daukan hakan a matsayin wata matsala ba.

Idan kuma ranar sati ne to kuwa haka zai wuni yana kallon Jaridar shi ta sati, idan kuma yamma tayi to zai fita ba zal dawo ba sai sha daya ko da rabi idan ya yi dare kuwa har sha biyun dare.

To zan iya cewa wannan ita ce babbar matsalata da shi amma nauyinshi ya hana ni yi mishi magana.

Sai dai maganar makaranta ta ce a yau nayi nufin yi mishi magana saboda tafiyar lokaci.
Saida ya gama cin abincin shi na kwashe kwanukan sannan na dawo na zauna can gefe na ce mishi cikin ladabi.

“Don Allah ina so ne nayi maka wata magana idan ba za ka damu ba.” Ya dan kawar da Jaridarshi daga kan fuskarshi ya
ce, “Uhum ina jin ki.”

Na ce, Dama maganar Makaranta ta nake so nayi maka don yanzu na kai wata shida bana zuwa kada lokaci ya yi ta
tafiya.”

Yayi shiru zuwa wani lokaci da har na fara gundura da shirun nashi sai da ya daga Jaidar ya ci gaba da dubawa sannan ne ya ce “Ba yanzu ba.”

Na ce, Na’am!” saboda yanayin da amsar tashi tazo mun. Na ce miki ba yanzu ko da matsala ne?”

A hankali na ce, “A’a babu.” Ya ce,

To madallah.” Sannan ya ci gaba da kallon Jaridarshi. Daki na shiga na kwanta. Sai dai na kasa hana kaina kukan da yazo mun.

Ba yanzu ba sai yaushe? Sai dai ba zai yiwu nayi mishi irin wannan tambayar ba.

To waye zai tambayan mun shi? Ai sai daina din don kuwa ni ce nake zaune tare da shi. Hakan ne yasa ni mikewa daga kan gadon na fito falon na sake neman wani wuri na zauna.
Na ce To yaushe ka ke ganin ya dace kenan na koma Makarantar? Ya janye jaridar daga fuskarshi ya zuba mun ido yana kallona.

“Ke! Tashi ki bani wuri, ke kuma wacece da za ki yi mun titsiye? Shashashar yarinya kawai.
Wadanda ya zamarwa dole ma ba su tsaya sun ga kin yi karatun ba ballantana ni.”

Mikewa na sake yi na hau gado na kwanta. Har aka kira assalatu ban runtsa ba, kuka kawai nake yi kukan sharbe.

Wane irin abu ne kuma haka meke faruwa ne? Shin me Ishak yake nufi? Na mike daga kan gadon na nufi bayan gida nayi wanka sannan na dauro alwala.

Har yanzu barcin shi yake yi cikin kwanciyar hankali. Nayi sallolina na nafila raka’a biyu sau uku sannan na zauna na dan yi karatun Kur’ani kafin aka fara kiran sallah.

Lokacinne ya tashi ya shiga bayan gida yayin da ni kuma na tada sallar nafila ta raka’atul fijri, sannan nayi sallar asubahi.

Na durkusa na gaishe shi kamar yadda na saba sannan na shiga kicin don kokarin yin abin karyawa kada ya makara.

Ba tun yauba na sha yin tunanin shiga gidajen makwabta da muke unguwa daya da su saboda mu’amalla da Jama’a.

Ban kuma samu damar yin hakan baa duk kuwa da cewar su sun shigo ba sau daya ba ba sau biyu ba. Haka nan ma yayan su.

Baran ma dai Hindu wacce nasan ko bata gime mun ba to zamu yi sa’a da ita don a yanzu a SS 2 take kenan da muna tare a Makaranta.

Don haka ko a yau da nayi nufin na sha kunun gyada da safe sai na tashi domin na leka sudaga nan kuma na samu wanda zai siya mun gyada da kamu.

Ban yi hanzarin tambayar Ishak ba amma a a raina sai na kuduri aniyar idan ya dawo daga wurin aiki sai na sanar da shi. Na fito na rufe ko’ina na cikin gidan. Sannan na nufi gian su Hindu wanda yake kallon namu gidan nayi kyakkyawan sallama a tsakar gidan wanda hakan yasa Momy mahaifiyarsu ta leko.
“A’a’a Amarya ce yau a gidan namu? To shigo daga ciki mana.” Na bita muka shiga falon na zauna a kasa ta ce “A’a zauna a kan kujera mana.”

Na mike na gyara zamą a kan kujerar sannan na gaisheta cikin girmamawa ta amsa tare da yin yar hira kadan wacce mafi yawancinta kan al’amuran gida ne.

Na ce, Hindu bata nan ko? Ta ce, “Eh ba su dawo daga Makaranta ba, saboda tana tsayawa lesson.”

<< Mai Daki 2Mai Daki 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×