Skip to content
Part 4 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Ban. wani tsaya bata lokaci ba na mike don dawowa gida har kofar gida ta rako ni da yar leda a hannunta ta miko mun nayi godiya na nufi gida ina tunanin inda zan samu abin da na fito nema.

Wanda ba zai yiwu kuma na kara yin gaba ba. Wani abin mamaki shi ne ban lura na hangi motar Ishak ba sai da nazo shiga gida.

Wani irin mummunan faduwar gaba ne ya same ni sai dai kawai sai naga to ai ba nisa nayi ba sai nayi mishi bayani.

Na shiga dakin cikin murmushi na ce,
“Lah ban yi zaton zaka dawo yanzu ba, shi yasa… ” kan na gama maganata ya ce
“Dama idan na fita yawon ki ki ke tafiya? Iye? Inà ki ka je? Na ce miki daga ina ki ke, kaga mun shegiya ‘yar matsiyata.

Raina yayi mummunan baci na ce “A’a ni kada ka sake zagina ka hada da iyayena, me nayi da zafi haka?”

Ya ce, “An zage su matsiyata me za ki yi iye na ce me za ki yi idan an zage su su din banza su din wofi.”

Wannan shi ne na farko kuma na karshe na gaya miki idan ki ka kuskura ki ka sake fita na dawo gidan nan ba kya nan sai nayi miki abinda ba ki yi zato ba.”

Ya juya ya fita ina jin shi ya sa kwado ya rufe gidan ta baya. Na zauna a wuri nayi kuka irin wanda ban taba yi ba a rayuwata.

Dama haka auren yake? Na san iyayena talakawa ne wadanda ba su da komai amma ba haka yana nufin Ishak ya zage su ba ne tamkar sun dauke ni sun ba shi ni auren da ko wata biyar bai yi ba.

Tausayin Babana ya sake kama ni, mutum mai kokari da bai taba zuwa kofar gidan wani neman taimako ba, ya dogara ga Allah ne da kuma dan abinda yáke samu a wurin aikinsa.
Hakanne yasa mutanen unguwarmu har da ma su kudin suke matukar girmama shi. Na lallaba na mike da nufin shiga kicin nayi girkin abincin dare. Na kuwa samu ya kawo wani cefanen abinda a yau ya daina birge ni.
Na dauko na fara rarrabawa, ina ajiye komai a wurinshi, na zaro ledar da naji danshi, kifi ne manya masu kyan gaske guda uku.

Na bude frizer na ajiye guda biyu na fara gyaran dayan da alama shi yake son ci da daddare.

Farfesun kifi nayi mishi wanda bai yi romo mai yawa ba, sai nayi coconut fried rice na ajiye a food flask ganin har na gama bai dawo ba duk kuwa da daren da nayi saboda makarar da nayi wajen farawa.

Har nayi sallar Isha’i shiru bai dawo ba. Bai saba yin dare a waje ba idan ba kwanakin sati ba ne wato Asabar da Lahadi.

Tun ina sa ran dawowan shi har na hakura na hau gado na kwanta. Can cikin dare na ji motsin shi. Na mike na same shi tsaye yana cire riga da niyyar canzawa don kwanciya.

Na fito falo na dauko abincinshi na kawo mishi, bayan nayi mishi sannun da ko kallona bai yi ba. Na ajiye abincin da farfesun na koma gefe na zauna yadda na saba yi. Ya gama shirin shi ina tunanin zai zauna yaci abincin ne sai kawai naga ya hau gado ya kwanta.

Na dan daure na ce ba za ka ci abincin ba ne? Bai ce mun komai ba duk kuwa da nasan idonshi biyu saboda haka sai na tattara na kai kicin na zuba cikin wani abin na saka a fridge don gudun kada ya lalace.

Na dawo dakin na gyara na sake kwanciya sai dai a yanzu kam ban samu yin barcin ba. Kan kace meye wannan sai na fara jin saukar numfashin Ishak yau ma haka na kwana ban yi barci ba.

Sai dai duk tsawon lokacin tunani nake yu na ya kamata naje gida naga iyayena haka nan na sanar musu da abinda yake faruwa.

Hakanne yasa da na gama gaishe shi da safe na roki ya bani izinin zuwa gida bai babi amsa ba haka nan bai tsaya karyawa ba yayi ficewarshi.

Da wani bacin ran na wuni wanda yau duk da dadin da gyaran gidan nan yake yi mun yau haka ya zauna sai da naga la’asar tayi sannan na mike don shirin abincin dare.

Shaf, na mance da abincin jiya da Ishak bar ci ba, don haka na nufi kofar gida don na samu yaran da zan baiwa abincin. Sai dai a kulle na ganshi ta baya. Sai kawai na dawo na kama aiyukana. Kamar yadda jiya bai dawo ba sai tsakar dare haka nan yau ma.

Sannan bai ci abincin ba ya sake kwawo mishi ba. Gari ya waye na sake yi mishi maganar zuwa gida yau ma bai ce mun komai ba, ya fita ba tare da ya karya ba.

Na dai lura idan nace zan zauna ina kunci da bakin ciki to zan nakasa kaina, sai kawai na nemi samun saukin damuwata ta wata hanyar. Ni ba ma’abociyar kallon fim ba ce, amma yau sai na shiga laluben drawer da ke jikin TV stand din don neman kaset din kallo.

Na yi dace da wani mai suna Why did I get married too?’ sunan shi ne ya dauki hankalina da na saka kuma sai na samu kaina da nutsuwa don yin kallon. Kawaye ne guda uku sai dai kowacce da irin matsalar aurenta. Na dan ji dadin yin kallon don ya rage mun damuwa.

Ban ki yin abinci ba don ganin ba ya ci kuma ina ta tara shi a fridge. Tuwo nayi miyar kubewa bushasshiya na ajiye kamar yadda na saba.

Ban kwanta ba zama nayi na jira dawowarshi. Shima yau bai vi dare sosai ba, don kuwa sha daya da kwata ya dawo. Babu irin tunanin da ban vi ba amma ina kasa sanin abin yi a kan matsalar.

Zaman aure da nayi ba mai yawa bane ballantana har nayi wayon zama da miji. Amma sai na kudure a raina a yau idan ya dawo zan san abin yi akai shi ne kuma na ba shi hakuri.

Ganina da yayi zaune a falon bai tsaya ba wucewa yayi zuwa cikin daki yadda ya saba.
Na bishi na sake yi mishi sannu, sannan na tsugunna a gefe na ce don Allah idan na yu maka laiti ne ka yafe mun abinda nayi maka. Ba kuma zan sake ba da ikon Allah.”

Wannan magiyar da nayi mishi ita ce tasa shi ajiye rigar barcin da ya dauko zai saka ya kalle ni.

To kenan har kin isa na zage ki ki rama. Iye! Ke kuma wacece a cikin mata?

Duk da bacin ran da maganar tashi ta sa ni wacce a take kuma na kasa danne hawaye da suka fara zuba a idona. Hakuri na ke ba shi kafin daga baya ya ce ya wuce amma kadá ki sake ko da wasa.”

Hakan bai sa yaci abincin ba, amma bai dame ni ba. Na hau gado na kwanta.

Washegari na lura ba shi da niyyar buga sammako irin na sauran kwanakin.

Don haka na shirya mishi abin karyawa. Ya fara ci kenan ya kalle ni Na baki mintina goma kI shirya na sauke ki a gida.”

Ban san sanda na fara godiya ba, duk da cewar mintina goman ba isa na za su y ba.

Na riga nayi wanka don haka atamfata na dauko Exclusive na daura da gyalenta da set din takalmi da Jaka ‘yan taly, sai yan canji na da ba su fi Naira dubu daya ba.

Da wasu yan abin kwalam da nake ajiyewa idan ya kawo sun ban sha’awa na karewa dakin kallo na rasa abinda zan kaiwa Umma.
Don haka na bude akwatin aurena da zannuwa suke ciki na dauko mai kyau na fara nadewa ban san ya shigo ba ya ce,

“Me za ki yi da ita? “

Na rasa abinda zan ce, ya ce, to mayar. Na sake budewa na mayar gwiwata a sanyaye.

A kofar gida ya ajiye ni na shiga rabona da gidanmu watanni biyar. Haka na Umma da Babana. Gani na rinka yi kamar ba ni ba.
Haka nan Umma ta rinka ina ta ka saka da ni. Ta zuba mun ido ko kyaftawa bata yi. Ni kuwa kunya duk tà kama ni.

Farin ciki mai yawa Umma ta nuna na ganina. Ita ma na ganta tayi kyan gani ba kadan ba.
Na bude Jakata na ciro ma su Tasi’u Bueno cakulet da biskit kwali biyu na mika musu suna ta murna, wanda iyakacin kuma abinda na riko nusu kenan.

Ni ce na tashi yau ma nayi mana girkin rana muna ta yar hirar mu da Umma. Wacce ganin irin murnar da take yi ne
yasa ni kasa gaya mata mnaganar da ke cina a cikin raina.

Wato maganar makarantata. Ba zai yiwu na dakushe mata wannan farin cikin da take ciki na ganina ba. Karfe hudu da rabi daidai sai ga sallamar dan aika wai na fito na dauko gyalena na zo inda Ishak ke hakimce a cikin mota na dan risina ta gefe na ce “Ai na dauka zaka shigo ku gaisa da Umma ne ko da ba za ka bar ni na jira dawowan Babana ba.”

Ya ce, A’a ba zan shiga ba, fito kawai. Na ce, “To.” Na koma na ciro “yar naira dari taran da nake ta nuku-nuku na kasa bai wa Umma, na mikawa su Tasi’u nayi wa Umma sallama na fito zuciyata kamar ta fashe. Muka iso gida ya ajiye ni ya juya, ni kuma na shiga kicin da nufin dorà abincin dare.

Tunani nake yi na yadda zan rinka taimakon iyayena, don kuwa ba zai yiwu na zauna a haka ba. Ishak ba ya bani ko sisi zan iya cewa tun bayan aurena a shi sile biyar bata shiga tsakanina da shi ba. Haka nan duk wani abu na amfanin gida shi ke kawowa bani da wata hanya da zan bi na samu kudi da zan iya yi musu wani abu. Ya zama mun dole nasan abin yin.

Tun daga ranar da na samu matsala da Ishak kan zuwana gidan su Hindu ban sake ba, sai dai da yake ya daina kulle ni bayan na roki yayi mun hakan, to ita takan shigo.

Mafita daya ce shi ne na dan rinka taimaka musu da dan abinda za su ci wanda shi kam ina da shi, don haka da Hindu ta shigo na roke ta ta gayawa Mominsu ina son aikanta gidanmu. Na debi shinkafa mudu biyar da suk, taliya da cous-cous, man gyadan (Turkey) da soyayyen nama da sauran abubuwan amfani na hada mata rigijif ta kai ta dawo.

Yauwa zuciyata tayi mun dadi naji sanyi na dan yi wani abu. Sai dai babban abin takaicin shi ne, bayan kwanaki biyu kawai da faruwar hakan sai naji wa’azi a Rediyo ana yi na matar da ta yi wa miji kyauta da abinci ba tare da ya sani ba, irin hukuncinta.

Sai dai har idan ta tabbatar da shi din ma zai yi hakan, to sai tayi da nufin Allah ya ba shi ladan.

Nayi shiru a raina ina tunanin to shi zai yarda da hakan ko kuwa shisshigi nayi? Ba zai yiwu na gaya mishi ba kada na ballo wa kaina liki, tunda dai an ce haramun ne gara kawai na nemi hanya da zan nemi naawa ita ce ta hanyar dinki tunda na iva, kuma ina da keken yin dinkin. Sannan unguwarmu sabuwar unguwa ce, da alama za a samu alheri idan mutum ya ce zai yi wata sana’a.

Washegari asabar don haka Ishak yana gida da rana. Sai da na gama aikace-aikacena na gida sannan nazo falon da yake na zauna na fara yi mishi magana kan tunanin da nayi na dinki tunda na iya.

Amsar da ya bayar a gajarce ce, ita ce idan ina gidanshi to ba zan yi dinki ba. Ba zai lamunci irin wadannan abubuwan na nuna karanta ba. Ba ni da abin fada, don haka naja bakina nayi shiru. Kamar yadda shima ya yi. Bani da wani abu da nake yi da ya wuce aikin gida da girki.
Wannan a yanzu nake rayuwa akai babu abinda yafi damuna irin tsayawar karatuna.
Ba zan ce Ishak ya yaudareni da iyayena ba, don kuwa matsayin shi ya wuce hakan mijina ne. Sannan babu wanda zai kalle ni ya ce Ina da matsala don kuwa a bayyane yake na samu canji. Kana kàllona ka san ina cikin wadata. Sai dai to iyavena fa? Wannan shi ne babbar matsalata.

Yau ma zama nayi da nufin jiran dawowar Ishak na nemi izinin zuwa gida a washegari don kada ya ce ban fada mishi da wuri ba. Ina matukar kewar Babana saboda zan iya cewa tun da aka yi aurena rabona da shi, a yanzu kuma wata na bakwai nake ciki.

Na jira shi har na gaji na hau kan doguwar kujerar dake dakin na kwanta.

Bai shigo ba sai karfe goma sha biyu daidai.
Na mike zaune saboda jin motsin da nayi na kuma yi mishi sannu’ ya amsa: Ban tsaya zancen kawo mishi abinci ba don kuwa ma a yanzu idan ya dawo ba yaci ko na kawo mishi. Ban yi mishi maganar ba sai da ya kammala shirin kwanciya sannan na fara kokarin yi mishi maganar.

Bai bar ni ba saboda dago mun hannu da yayi alamar dakatawa. Wai ke ba ki da wata magana ne sai ta gidanku? Mits! Yayi tsaki ya yi kwanciyarshi.

Sai mutum ya wuni aiki amma idan ya dawo gida a maimakon a barshi ya huta wai sai a tasa shi a gaba da surutan banza.

Ya ja abin ruhuwarshi ya kwanta. Na riga na saba da dabi’un Ishak, don haka a yanzu ba su cika damuna ba.

Washegari har na gama mishi shirinshi na karyawa da sauran abubuwan shi na tafiya aiki a raina ina tunanin zai yi mun maganar zuwana gida da nayi mishi bai ce komai ba ya tafi.

A duk lokacin da ya tafi aiki na kan dauki wayata na kira Hindu ta taya ni hira, hakan ne yasa muka yi wata irin shakuwa ba kadan ba.
Hindu wayayyiyar yarinya ce ba kadan ba, haka nan yanayin irin gidajen da muka tashi ma ba daya ba ne.

Don kuwa kamar yadda nake “yar talaka ita kuwa ya ce ga babban Ma’aikacin Gwamnati, Mominsu ma wayayyiyar mace ce.

Wunin da nake yi da ita a cikin gida yayi matukar taimaka mun kwarai da gaske kan al’amurana. Ban taba zama na
fada mata wani abu game da mijina ba, amma sai ta gane hakan. Wanda yasa ta yi mun magana, ban saurari abin ba don ganin da nake yi mata na cewa ita din ko da muke kusan sa’o’in juna ita ba macen aure ba ce.
Haka nan kullum Umma tana gaya mun na rike sirrina. Don haka ko da ta yi mun magana murmushi kawai nayi. An dan dade kafin na samu Ishak ya bani izinin zuwa gida. na zaune cikin motar daidai ya tsaya a kofar gidanmü na ce mishi “Ko za ka bar ni ne zuwa dare donn na gaisa da Babana?”

Bai ce komai ba, nima kuma ban sake yin magana ba.

<< Mai Daki 3Mai Daki 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.