Skip to content
Part 7 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

Karfe goma daidai ya shigo gidan. Nayi mishi barka da sallah ina kallon shi ga zatona zai yaba kwalliyata tunda ko da ba dabi’arshi ba ce yin hakan.

Ai kuma yau sallah. Bai ce mun komai ba har na gama shirya mishi abincin shi.

Ya ce “Da kin bari sai sun zo muci tare.”
Na ce, Ai ba ka da tabbacin lokacin zuwan nasu tunda yanzu ne ma aka sauko daga Idi, kaci ko babu yawa zai rage maka yunwa.” Sai dai na daure ne kawai nayi mishi wadannan bayanan.

Don tuni zuciyata ta fara hankoron fushi. Na shiga daki na zauna a bakin gado naga abin bai yi mun ba. Na gaji da abubuwan ko in kula da Ishak yake yi mun ko ma meye zai faru kawai ya faru a yau dinnan.

Ban san lokacin da na ganni zaune kan kujerar da ke gabanshi ba.

Na kare mishi kallo yana cin abincin shi cikin nutsuwa kana kallon shi ka san ba shi da matsala. Ya dago ya kalle ni Yaya lafiya?
Kullum salon tambayarshi kenan. Ban ce mishi komai ba ban kuma daina kallon nashi ba.
Kina da matsala ne? ko wani abu yana miki ciwo. Wani tunani yazo mun cikin raina da kuma yasa na fasa yi mishi magana na mike da nufin komawa daki.

Hauwa’u na juyo tare da amsawa. A tun farkon zamana da Ishak zan iya kirga adadin lokutan da ya kira sunana.

Zo ki kwashe wadannan kwanukan na gama.” Na zo ina kwashewa., Dan sassaucin da na samu na mu’amalla ni kaina nasan don juna biyun da nake dauke da shi ne wani lokaci ya kan tambaye ni akwai matsala ne ko kuma wani abu yana yi miki ciwo?

Haka nan ya rage yawan dadewa a waje karkari ya kai karfe goma shi kenan.
Na gama kwashewa da karin gyaran wurin na dawo dakina na kwanta don dan samu na huta ayyukan da na kwana biyu ina yi.

Ya shigo dakin sanye da farar singilet da wandon kayan da ya cire ya miko mun kudi bandir din Naira dari sababbi fil da su.

Na mika hannu na karba ina jira yayi mun bayanin abinda za a yi. Ya ce, “Ki ajiye barka da sallanki ne. in tsaya cewa kudin nan sun yi mun dadi ma bata baki ne.

Sai dai kan nayi mishi godiya aka fara buga sallama. Ya juya ya shiga dakinshi don dauko rigar shi da ya tu6e.

Ni kuma na jawo gyalena mahadin material din jikina na yafa na fito har ya
ba su izinin shigowa. Lallai kam bakin Ishak da yawa.

A can gefe na zauna müka gaisa da su. Ban tsaya kallonsu ba amma nasan sun kusa goma. Ban iya komawa ba lokacin daa na shiga kicin tunanin yadda zan yi na kat musu sa’a shima ya fito ya zo kicin din.

Bani abincin kawai ba sai kin shiga ba tunda kun gaisa. Ya fara kwasa yana shigarwa sannan na hada Plate-Plate da kofuna na sake mika mishi ya shiga.

An dai kai kamar mintina talatin na motsin plate da cokula kawai nake jiwowa,
yayin da nake zaune a single dakin dake tsakar gidan. Kafin daga baya hira ta barke. Ina sauraronsu kowa da abinda yake fada game da abincin yayin da ake sakawa wasu waigi.

Hira sosai şuka shiga yi daga baya da ta kunshi wajen aiki da kuma wasu al’amura. Koda nake kwance a kan gadon dakinnan na kasa barci duk kuwa da irin gajiyar da nayi saboda muryar Ishak da nake jiyowa,
Da yadda yake dariya da wasu abubuwa. Mamaki ya kama ni, dama yana hira da mutane da ni ne.bai yi ko kuwa ya ya?

Ba su tashi tafiya ba sai wajen azahar suka fita gaba daya don yin sallah, bayan sun nemi nazo muyi sallama ya ce musu nayi barci.

Na dawo dakin na sake gyara shi tsaf kamar ba a yi komai a ciki ba, sannan nayi sallah na hau gadona na sake kwanciya.

Ishak bai dawo ba sai wajen hudu da rabi. Na mike na bishi dakinshi baya ciki alamar yana wanka na zauna a bakin gadon ina jiran fitowar shi.

Tunda ya fito nake bin shi da kallo har ya sanya short da jallabiya fara sol, sannan ya sake kallona.

Ga wannan suka ce na baki goron sallah. Yana miko mun kudi na kalli kudin a hannunshi da yake miko min, sannan na kalle shi shima ni yake kallo.

“Ya ya dai akwai matsala ne?” Na ce, “Eh akwai, wannan ma da ka bani da safe gasu nan na dawo maka da su bana so.”

Ba karamun kada shi maganata tayi ba, don tsawon zamana da Ishak ban taba amsa mishi magana ba ballantana nayi jayayya da shi.

Kuka na fara yi a daidai lokacin da na fara magana. “Ni ba zan iya irin wannan rayuwar ba. Dama abinda yasa nake ta hakuri na dauka haka ka ke, haka dabi’arka da halayyarka suke. To ashe ni kadai ka ke yi ma.”

Ya ce, “Wacce irin banzar magana ce wannan, ke lafiyarki kuwa?” Na ce,
“Lafiya kalau, na dai gaji ne. Ban taba saka kaya a gidan nan ka ce yayi kyau ba. Ban taba yin girki kaci ka ce yayi dadi ko bai yi ba, ban taba yin wani abu da nufin na burge ka ka yaba mun abinda nayi baa. Ni a kullum a wajen ka a kushe nake. Bana gwaninta a wajenka sai kuskure. Ni kulluma wajen ka mai laifi ce ni.

Ba ka ganin nawa da mutunci saboda ni, babu wani mutum da zai shigo cikin gidan nan da sunan wurina yazo ba tare da ka wulakantashi ni kuma ka bata min ba…”

“Ke dakata! cikin tsawa ya dakatar da ni. “Ita ce ta turo ki ki zo ki titsiye ni? Kina nufin kin isa ki sa ni nayi abinda ban yi niyya ba?

Wannan abin da ki ka zo ki ke yi ba zai sa na canza daga dokata ta kada wani ya shigo mun gida ba ko wanene ba tare da yardata ba.

Kuma tunda yanzu na kara gane aibun hakan nasan abinda zan yi kenan har kin fara bin shawarwarinsu ne kina titsiye ni akan abin da bana so. To babu laifi.”

“Ba titsiyeka nayi ba, kuma ni babu wani wanda yasan abinda muke yi ballantana har ya bani shawara a kan abinda zan yi. Amma wacce irin rayuwa ce wannan?

Za ka iya zama da abokai kuyi hira kuyi dariya tare amma ni matarka ta aure ba ka da lokacina?

Idan gari ya waye ka fita ba zan sake saka ka a idona ba sai wani wayewar garin? Amma ni kana saka mun takunkumi na yin mu’amalla har da ‘yan uwana, to… kafin na karasa tuni ya dauke ni da marin da na kife a kasa.

“Ki rinka fahimtar lokacin da mutum yá gundura da abu.” Ya watsar mun da kudin a wajen ya dauki mukullin motarshi yayi waje.

A hankali na mike na goge hancina da naji alamar ruwa-ruwa yana biyowa, jini ne. Ban ci gaba da kukan da nake yi ba sai dai duk da gargadin da zuciyata take yi mun kan abinda nayi nufin yin ban fasa ba. Wannan karon shi ne karo na uku da Ishak yake dukana, Jakata na dauko har na fito na nufe ko’ina sai na tuna ko kudin mota ba ni da shi.

Dawowa nayi na bude dakin Ishak har yanzu kudin suna watse a kasa na sunkuya na dauki gudan dubu guda uku a kudin da bakin shi suka ce ya bani na sake shig dakina na dauko kaya set daya na sake fita. A gidan bayan na rurrufe ko ina na tafi gida.

Ba karamin mamakın ganina suka yi ba, don kuwa ban gaya musu zuwana ba. Babana muma yake yi daga ganinshi kuma na san ya dan samu canji, don kuwa yayi fes da shi.

Umma atamfar da nayi mata ce a jikintą, haka nan su Taşi’u. Umma ta zubo mun abinci ta ce “Ga shi nan duk da dai daga gidanki yake.” Na dan yi murmushi na ce “Umma ba ni, naki mana na ci,”

Ta ce, “Tuwo ne miyar taushe.” Na ce, “Eh bani kawai.” Cin abincin nayı sosai sannan na sha kunun zaki. Ta ce, “Amma ai ba yau muka yi da ke za ki zo ba ko? Lafiya dai ko?”

Na dan yi shiru ban ce wa Umma komai. “Idan akwai wani abu kiyi magana mana, naga kamar ranki a bace yake.”

Na rasa ta inda zan fara yin maganar nan take kuma na kama kuka, sosai da sosai. Sai dai na kasa cewa Umma ga matsalata.

Ta ce, “To ko nayi, iki magana da Babanku ne? Na girgiza kai na ce, “A’a.”

Ta ce “To ki share hawayenki kiyi hakuri kowacce mata da ki ka gani, da irin matsalarta.
Shi aure haka yake, kina hango na wani nee wani kuma yana hango naki. Ki daure ki zamo mai sirri a tsakaninki da mijinki.

Babu mai ganinki ya ce kina da matsala kwata-kwata, tunda mijinki ba gaza miki ba, bai kuma yi tsari ba a ce tun yanzun kin koyi kai kararshi ba ki iya warware wa kanki matsalarki ba tare da wani ko wata ya fahimta ba.

Ki tashi ki koma kada ki dade kuma ya zama matsala, tunda dai da’alama ma ba ki sanar da shi zuwan ki ba.”

Sai da Umma tayi wannan maganar ne naji gabana ya yi matukar faduwa. Na koma gida idan Ishak ya dawo kuma muyi ya ya kenan?
Ban bari Umma ta fahimci halin da nake ciki ba, dauko kudin dake Jakata nayi na bata biyu na baiwa su Tasi’u canjin kudin mota ta dari takwas na rage kudin da za su mayar da ni gida.

Fitowar da zan yi kenan na hango motar Ishak ta karyo kwanar unguwarmu, cikin sauri na koma gida.

Umma ta ce “Lafiya?” Na ce, “Gashi nan zuwa shima.”. Ta ce, “To, to Allah Yaasa kalau. Umma ce da kanta tayi mishi shimfida suka gaisa.

Sannan aka kira Babana da ke tare da wasu daga cikin makwabtanshi suna tattaunawa. Gaisuwa sosai suka yi sannan ya kawo goron sallah ya baiwa su Tasi’u.

An dan jima kafin ya nemi na fito mu tafi. Bai ce mun komai ba har muka iso gida, daidai an fara kiran sallar Magriba. Bayaan gida na wuce nayi alwala na fito don bada farali.

Shima a dakin shi yayi sallah. Ban fito ba don kuwa na riga na kudurawa rainaa zan zauna ne da lshak irin zaman da yake so muyi da shi, tunda dai haka ya zaba.

Lekowa yayi dakina ya kira ni na shiga yana tsaye. “Kwashe mun kudin nan. Na sunkuya na kwashe su gaba daya..

Ya ce, “To zauna.” Na nemi wuri a kasa na zauna. Tashi ki zauna a bakin gado.
Nayi kamar yadda ya ce shima yazo bakin gadon kusa da ni ya zauna.

<< Mai Daki 6Mai Daki 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×