Skip to content
Part 9 of 28 in the Series Mai Daki by Hafsat C. Sodangi

LITTAFI NA BIYU

Sadaukarwa

Sadaukarwar littafin ta Iyayena ce, Alhaji Chindo Muhammad Sodangi da Hajiya Fatima Musa Sodangi, Ubangj ya saka muku da alheri ya kuma kara muku lafiya amin.

Tukuici

Tukuicin littafin naki ne; Khadija Chindo Sodangi (Mrs Nasiru Idiris)

Jinjina

Jinjinar littafin taki ce Amarya ba kya laifi (Maman Umar) Zuhuriyya Ibrahim (Mrs Lawal Chindo Sodangi), Ubangiji ya raya Umar da Imani.

Fatan Alheri Gare Ku

Fatima Abdulkadir Kazaure
Hafsat Iliyasu Unguwar Rimi

Khadija Usman Nasarawa
Nafisatu Ibrahim Muhammad
Fatima Ahmad Shehu Kaduna
Maryam Muhammad Gusau, Zamfara
Umaima Abubakar Umar
Maijidda Uba Magaji

Na gode, Ubangiji ya saka da alheri
amin.

Kuna Raina

Hajiya Maryam (Mami) Dan Hassan
Hajiya Jamila Ibrahim Na-Bature
Hajiya A’ isha Balarabe (Jazan)
Ubangiji ya bar zumunci amin.

******

Wahala dai irin wacce nayi ta ranar ta wuce a zauna fada. Babu wani na makwabta da zan tuntuba don ba ma zan iya mikewa ba balle na ka1 ga zuwa wani wuri.

Na kai awa biyu kafin ciwon ya sake ni, na kokarta na ja jikina na hau kan doguwar kujera na kwanta. Wasu hawaye ma su dumi suna bin kuncina. Ban kai mintina goma a haka ba sai ga shi ya shigo ko kallonshi ban yi ba balle nayi mishi sannu. Ya ya akwai matsala ne? ban ce mishi komai ba, kukana kawai nake yi.

Ganin haka yasa shi ya ajiye ledar da ya zo da ita ya wuce ni ya shiga dakinshi. Bai fito ba haka nan nima ban tashi don yin sallar Magriba da Isha’i da ban yi ba har wajen karfe goma na dare. Ya fito falon yana kalloa “Na tambaye ki ko kina da matsala ne kin yi mun shiru,

Amma kin zauna kina kuka wai ke wane
irin hali ne da ke ne?” Ya kalli ledar abincin da ya ajiye a kasa yayi tsaki. “Idan ba za ki ci abincin nan ba wuce kije ki kwanta. Na mike a hankali tare da rike gefen cikina da ke mun wani irin ciwo na lallaba a hankali na hau kan gadona na kwanta.

Wata kila yanayina da ya gani ne yasa shi biyo ni dakin. Hauwa’u menene damuwarki? Ina kuka na ce “Umma nake so ka kira mun.” Ya ce, “Umma kuma? A wane dalilin zan yi hakan?:

Na ce, Ba ni da lafiya ne. nayi mishi bayanin abinda ya faru da baya nan da kuma ciwon da gefen cikina yake yi mun. Fita yayi zuwa dakinshi ya dauko mukulli ya sa hannu ya dauke ni zuwa wurin motar shi, muka tafi asibiti.

Likita na duba ni ya ce haihuwa ce, duk da akwai sauran kusan sati uku kafin (E.d.d) dina ya cika. Nakuda kamar za a yi

kamar ba za a yi ba shiru ka ke ji kamar an shuka dusa. Har gari ya waye ya leko dakin yana shaida mun zai je kiran Umma, don shi ma ya je ya shirya yayi wanka na ce To.

Umma ce tazo ta tsaya a asibitin. Da kyar da taimakon Allah da na Likitoci na haihu wajen karfe uku na rana na samu. Santalelen yaro, jajir da shi.

Ba mu dawo gida ba sai washegari saboda hutu da suka ce na samu da kuma dalilin zubar jinin da nayi Umma ta nemi Ishak ya bar ni na koma gida don yin jego bai yarda ba, don haka dakina aka mayar da ni.

Mutanen unguwar mu sun zo mun barka ba kadan ba, har ma da wadanda ban sani ba. Sanin halin Ishak da nayi ne yasa da aka fara maganar kawo mai yi mun wanka na ce su bari a tuntube shi tukunna. Ilai kuwa sai cewa yayi Yayarshi ce zata zo. Bayan kwana biyu kuwa sai gata ta iso.

Mata mai saukin kai ni kuma nayi sabo da ita ne ta yawan wayar da suke yi da Ishak ta ce a bani mu gaisa. Suna sosai aka yi ta bangarena iyayena da ‘yan uwana sun yi mun irin nasu kokarin, sun kuma yi mun gata ta wajen zuwa dubani da jariri. Haka nan yan uwan lshak suma sun zo ba kadan ba. Don haka bikin suna mai gamsarwa sosai aka yi. Yaro kuma yaci sunan Baban Ishak wato Abdullahi, amma an yi mishi lakani da Abulkhairi.

Abinci kala-kala aka yi ta kawowa da aka yi odar su babu kuma wanda zai ce bai gamsu ba. Yaya ce da kanta ta tashi washegarin sunan tunda asuba ta fara aikin tsabtace gidan. Kafin takwas na safiya kuwa tamfar ma ba a yi komai a cikin shi ba.

Mu kuwa tuni mun yi wanka daga ni har jarii Abulkhairi. Ta shigo har cikin dakin da nake zaune ta fara karyawa muna dan hira tana tambayata “Kin ga kayan naku kuwa? Na dan yi murmushi. Ta ce Hauwa’uu kenan, hala ke ba kya halin naku ne na zamani? Na ce, Yaya meye halin zamani?

Ta ce, Rashin kunya mana wai ku nan a dole kun waye? Yaya ce da kanta ta ware mun kayan da Ishak yayi mana.

Kaya ne sosai ba wai masu dumbin yawa ba, amma dai masu daraja ne kwarai baran ma na jaririn wanda tamfar ba a kasar nan aka yi sayayyar ba.

Ta bangaren gidanmu ma babu laifi ga kuma alherin da na samu wurin mutane, Momin Hindu ma ta yi wa Abulkhairi sayayya ma kyau.

Zaman da nake yi da Yaya ba karamin dadi yake yi mun ba, don kuwa ‘tuni na manta da irin zaman Kadaicin da na ke yi da Ishak.
Duk da dai yanzu shima ya daina yin dare Sannan duk da jarirantakar Baba tunda shi abinda yake kiranshi kenan, yana daukanshi ya kwanta da shi a dakinshi.

Ko kuma idan ya ji shi yana kuka ko wani rikici za ka ga yana zaryar tambayar abinda ke damunshi ko da dai ba dani yake yi ba, hakan yana yi mun dadi a raina.

Da sassafe Yaya take juye mun ruwan wanka wanda nake yi da tawul kafin na gama na fito kuwa ta yi wa Abulkhairi.

Muna gama karyawa zata fara shirin dora mana abincin rana idan kuwa ta gama aikace-aikacenta to zama muke yi muna kallon mu muna kuma hira.

Ga ta da kirki da raha da kuma saukin kai, abin ya kan daure mun kai har nake tunanin a raina tamfar ba ciki daya suka fito da Ishak ba.
Shi ma idan ya dawo don kuwa yanzu baya dadewa saboda yana zama hira da Yayarshi, to sai ya kai karfe goma basu kwanta ba suna hirar yan uwa da kumna wasu al’amuransu can. Zaman jegon da nayi mai cike da nutsuwa da kwanciyar hankali shi ne yasa kafin muyi kwanaki arba’in mun yi bumbum gwanin sha’awa.

Babu abinda a yanzu nake tunawa hankalina ya tashi irin na tuna watarana dole Yaya ta tafi, hakan ne yasa muna hira nayi nufin gwada yi mata tayin zama.

Ta kalle ni tayi murmushi ta ce, “Haba Hauwa’u, koda ba ni da miji ai akwai harkoki da nake yi a can na sana’o’i, ga kuma yara.”
Na ce, Yaya ai sun girma. Ta ce, Eh to sun girma amma Rukayya fa? Na ce wacece Rukayya? Ta ce, “A’a ba ki san Rukayyar ba kuma yau? Yarinyar Isiyaku mana.

Abin kawai sai ya dibibice mun har na rasa waye ma Isiyaku. Ita kuwa maganarta ta ci gaba da yi wacce ko fahimta bana yi saboda ganewan da nayi Ishak take nufi.

Ai tun da uwarta ta dawo da ita tana shan nono watanninta goma ta ajiyeta tare da dan uwanta sai kawai naje na debo su na zo nake rike da su.

Ba karamar dauriya nayi ba lokacin da na cewa Yaya, “To amma Yaya ita me yasa tayi hakan?”

Ta ce, “To halin su na yara mana daga ita har shi din wanda rashin hakuri yasa suka yi rabuwar da bata dace ba. Ai shi Isiyaku ma naga ya canza gaba daya yanzu kamar ba shi ba, duk wasu abubuwan da yake yi a da can ya daina su.

Don ko matar da ya sake aura bayan uwar su Rukayya ai bata zauna ba don ita kam ma ai bata haihu da shi ba. Ke dai kiyi hakuri da abin da za ki gani wanda ba zai yi miki dadi ba, don shi aure ba ka samun shi yadda kayi zaton shi.
Maganar da Yaya tayi ya haifar mun da wani abu a cikin raina mai ciwon gaske.

Bai taba gaya mun zancen auren da yayi har guda biyu ba da kuma ‘ya’ya. Menene nufinshi nayin hakan? Yana tunanin wataran ba zan sani ba ne ko kuwa nima bal shirya zama da ni zuwa ranar da zan sani ba ne?

Abinda ya tsaya mun a rai kenan. Babu wata mata da zata iya zama da Ishak idan har ba hakurinta ne ya kai inda ya kai ba.

Mace maras hakuri kuwa to babu inda aurenta zai kai da Ishak. Babu ko tantama abubuwan da yake yi ne sura ga ba za su lamunta ba. Kenan halin shi ne ba kuma zai daina ba.Tunda ai an ce hali zanen dutse.

Taimako daya zan yiwa kaina shine na tsaya tsayin daka na ga na koma makaranta kamar yadda tun farko ya alkawarta.

Gaba daya hirar ta daina mun dadi don haka sallama nayi wa Yaya na shiga daki na kwanta ba don nayi barci ba. Don kuwa wane ni! Ina jin dawowarshi ko motsawa ban yi ba ballantana naje yi mishi sannu. Yau sun kai sha daya suna hirarsu ina jinsu.

Sai a yanzu ne na gane ai dama can idan suna irin wadannan hirarrakin suna yawan ambaton sunan Rukayya da Anas da alama shi ne babban. Ban san lokacin da barci ya dauke ni ba.

Da safe kuwa da na tashi bin Ishak da kallo na rinka yi ina kara jinjina hali irin nashi.

Shiri sosai muka wayi gari yau muna yi saboda gobe ne zamu yi fitan arba’in.

Yaya ce da kanta ta bada lissafin abinda za a siyo mata na yin sadaka. Tayi funkasau da fanke. Ta bi makwabta gaba daya ta rarraba nima ta bayar da na gidanmu aka kai.

Washegari kuwa ta kama Asabar. Kwalliya sosai nayi ta burgewa da nufin Zuwa gidanmu sai Yaya ta ce a’a ba haka ake yi ba nabi makwabtana mu gaisa saboda hidimar da suka yi suma suji dadi.

Ina kallon Ishak in ba don ban taba jin yayi musu da Yaya na tabbata da ya hana, don kuwa tana fada naga yanayin fuskarshi ta canza.

Yana zaune rike da Abulkhairi a hannunshi wanda ya zama tamfar dan wata uku ba shi da niyyar miko mun shi, ni kuma ban ce ba ni shi ba, na gaji da jira na kama hanyar fita tare da yi ma Yaya sai na dawo.

Ta ce,Yau ji mun yarinya za ki tafi ne ki bar yaron a gida ki kai musu kanki? Na dawo da baya ta kalle shi.

“To kai kuma bata shi mana. Ya miko mun yaron na kara gyara mishi ruhuwa na juya zan fita ya ce ke zo nan. Na dawo na ce, “Ga ni.”
“Tafi ki cire gyalen nan ki dauko hijab na ce, “To”. Har da na dauko hijabin ma abin bai yi mishi ba sai da ya ce na goya yaron duk kuwa da shi ma yasan a iyakar unguwarmu zan tsaya, ban ki ba nayi yadda yace.

Gidansu Hindu na fara shiga muma sosai Momi tayi yadda dama can take yi mun. Tasa hannu ta karbi Abulkhairi tana rike dashi tana yaba yaron.

Ni dai duk kunyar Momi ta baibaye m, ko nuna mun alamar ta san abin da Ishak ya yi musu bata yi.

Na ce, :Momi ina Hindu? Ta ce, Tana wanka yanzu zata fito. Muna zaune kuwa sai gata, tsalle tayi ta rungume ni Maman Abulkhairi!:
Na ture ta na ce, Ban son wulakanci, Momi ta ce, A to gaya mata dai mara kunya. Ta karbi yaron ta zuba mishi ido can ta ce, Gaskiya Momi mu ma ta karo mana baby dubi yaron nan kamar na sace. Hindu ce ta ce, na jirata ta shirya ta raka ni gidajen da za ni, har cikin raina hakan yayi mun dadi, don kuwa wasu da yawa ban ma san su ba.

Muka fito daga dakin Momi ta miko mun leda mai shake da turaruka na dakin da na jiki da kuma magunguna ta ce Hindu ta rike mun.
Godiya sosai nayi mata muka fito, mun fito kofar gida kenan sai kawai muka yi ido hudu da Ishak yana tsaye a kofar gidanmu ya zuba hannayea aljihun wandon jeans din da yake sanye da shi.

Kamar yadda na dake haka Hindu ma muka wuce muka shiga wani gidan. Alheri sosai ‘yan unguwar mu suka yi mun na kuma kudura a raina ba zan sake zama ba na mu’amalla da su ba.

A kofar gida Hindu ta tsaya ta miko mun Abulkhairi alamar ba za ta shiga gidanmu ba.
Ni ma ban ce ta shiga ba, nayi mata godiya na kawo alheri cikin wanda na samu na bata ta ki karba nayi rantsuwa na ce ai sai ta karba, hakan ne yasa ta karba.

Na shigo gida Ishak yana zaune a kan kujera one sitter Yaya bata dakin alamar tana kicin ko ta shiga bandaki.

Ban ce mishi komai ba nayi wucewata daki. Na ajiye kayan da ke hannuna na kwance goyon Abulkhairi na ajiye shi a kan gado kenan na juyo na ganshi tsaye a kaina.

Yanayin shi yasa ni ja da baya. “Ban ce miki bana so kina mu’amalla da wadannan mutanen ba iye? Keta dokata da ki ka yi, bata ishe ki ba shi ne ki ka je ki ka bata dana tana goyawa?”

Bude baki nayi da nufin yin magana kawai Ishak ya dauke ni da marin da sai da na kifa a kan dressing mirrow. Ihuna da Yaya taji ne yasa ta tahowa da sauri. Ta kama salati ganin da tayi har bakina ya fashe, kuka nake yi sosai itama Yayan haka tana cewa.

“Ashe baka bari ba Isiyaku, to yaushe kuma? lye na ce maka sai yaushe kenan?

Wannan yarınya menene aibunta’? Ya tsaya zai fara yi mata bayani ta dakatar dashi ta ce, Bana son ji. Na kuma fahimci zamana a gidanka ne ya isheka dama kuma nayi abinda ya kawo ni magana ta kare.

Wucewa Ishak ya yi ya fita ni kuma naje na wanke bakina da ke ta fitar da jini saboda buguwar da nayi kan madubi
hakan har idona na gefen d na fadi ya tara
jini.

<< Mai Daki 8Mai Daki 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×