Rashin Sani
Rashin sani ya fi dare duhu
Kano, Nigeria
"Ya ya aka yi kika fada karuwanci?"
Tambayar da Almustapha ya wullo wa Rukky kenen a bazata. Tana rike da wani donut a hannunta ta sa baki ta gatsa kenen sai ta ji tambayar, tayi sauri ta hadiye tana mai kallon inda ta gatsa. Ba ta ba shi amsa ba ta ce
"A ina ka sayi donut din nan? Dadin ba magana!"
Karasowa yayi yana daura agogon hannunsa ya zauna a daidai inda take zaune kan 2 sitter. Ya kai bakinsa inda. . .