Sharri
Ai sharri kare ne, mai shi yakan bi!
Kano, Nigeria
Shekaru kadan da suka wuce.
Harabar La mirage cike take da manyan motoci na masu fada a ji, wadanda shedan ya buga musu ganga suke taka rawa. Ranar ta kama asabar yawan-yawan ma'aikata da suke Abuja da kaduna sun shigo hutun karshen sati. Mafi yawansu kan rashe a wannan waje domin nishadi, suna taba dan shaye-shaye da caca.
Wannan karin wani mawakin Hausa suka dauka mai suna "dan mudubi". Sukan yi hakan idan sun so nishadi ko su. . .