Kawai durkushewa Habu yayi a wajen yana hawaye
"Na shiga uku Hindatu! Kin ga yadda Allah ya mayar da ni ..kin gani ko? Hakkinki ne! Hindatu ki yafe ni"
Abba ne kuma fuskarsa ta mamaye da mamaki. So yake ya san waye. Mahaifiyarsa ya ga fuskarta gabadaya ta canja, wani irin bacin rai da bai taba ganinta a ciki ba. Ta nuna wanda take kira da Habu da danyatsa a fusace ta ce
"Fice min daga gaban gidan kafin na sa yansanda su fice min da kai!
Jikin Habu har rawa yake zai kamo ta a rikice ta hankada shi. . .