Bayan Shekara Uku
Ita kadai tasan cikin kalar fargaba da tashin hankalin da take a shekarun nan. Yanda duk taso ta nisanta kanta da Hajiya Dije ko dan gudun suje inda za’a binciko mata abinda zai daga mata hankali sai ta kasa, Rayyan na bata tsoro, yanda yake manne da Layla duk idan ya dawo makaranta yana karya mata zuciya. Musamman yanzun da take ganin suna kara girma, yaranta na wani irin girma da har mamakin shi takeyi. Ita ce harta aurar da Khalifa da Zubaida. Kuma duk lokacin da zata sami Ahmadi da maganar takan ga gajiyawa a fuskar shi, kamar ya gaji da yanda ta kasa daukar ido ta saka akan Rayyan din da Layla kamar yanda yayi
“Ya kike so inyi? Ko akan dukan da yakeyi mata nayi magana tsini ne kawai bakina baiyi ba. Kinsan halin Rayyan, abinda ya ga dama shi yakeyi”
Ahmadin yace mata wani lokacin, ita ko dukan bata so, batason wani abu na hada danta da Layla. Batason ganin shi a bangaren Mami sam-sam. Rayyan din ya kara mata tsanar matar kamar zata hadiyi zuciya haka takeji duk idan taga giccinta. Yau da kanta ta shiga kitchen, har Rukayya na mata tsegumi.
“Ayya saboda su Hamma zasu dawo shisa kika ce ke zakiyi girki…”
Dariya kawai tayi, wannan karin sun dade, watansu na hudu kenan rabon su da gida. Duk da ta wani fannin dadewar tayi mata dadi bana wasa ba. Hakan na nufin aikin da Malam Ma’azu kwano kamar yanda Hajiya Dije ta kira shi yaci. Daman tace a borno yayo karatun allo, a haka idan ka ganshi zaka raina shi, sai dai aiki yake kamar babu gobe. Tashin farko dubu goma Ayya ta ajiye mishi na bugun kasa, inda yace ta saka tafin hannunta kan wani rairayi da yake cikin falankin katako. Batayi musu ba ta saka, duk da tasan zancen gizo ba zai wuce na koki ba, ba nan bane wajen farko da sukaje da Hajiya Dije, kuma duk maganar shige dayace, Layla na rike da kurwar Rayyan, danma yana da dakakkiyar zuciya da sai abinda tace ne zaiyi.
Wannan ma suna shiga ta fara labarta mishi matsalarta akan Rayyan din, kafin yace yasan kasa zata nuna mishi komai, ta saka hannunta akan yashin, suna zaune suna kallon yanda yake rubutu yana sharewa yana sakeyin wani, kafin yayi numfashi mai nauyi yana dago kai ya kalli Ayya.
“Yaron ki zai zama shahararren mai kudi, akwai nasarori da suke biye da shi. Shisa abokiyar zamanki ta kasa zaune da tsaye a kan shi. Saboda taje an duba mata yanda kaf gidan ba za’ayi mai arziqin shi ba. Yarinyar da kike magana da ita aka, idan baki tashi tsaye ba duk abinda zai samo a kansu zai kare, ke kanki ga katanga nan naga ana ginawa tsakanin ku.”
Wani irin numfashi Ayya taja, tana duban Hajiya Dije, zuciyarta na wata irin dokawa.
“Yaushe Maryama zata kyaleni in huta?”
Murmushin “Na fada miki ai” Hajiya Dije tayi mata
“Da nace miki ki dinga nemar wa yaranki ko da tsarine ca kikayi kamar Maryama ba zata iya cutar da su ba. Kin daiji da kunnuwan ki yanzun ai”
Kai Ayya ta jinjina mata, taji kam, ba waje daya ba biyu ba, kuma ta gasgata tunda zuwan karshe da Rayyan din yayi, saboda ta mishi magana akan Layla yasa shi daina shiga bangaren ta gabaki daya har suka koma. Sosai abin ya bata tsoro, ashe katanga ake mata da dan data tsugunna ta haifa, dan daya fito daga cikinta. Rashin imani irin na Maryama ba zai misaltu ba. Aiki Malam Muazu yace za ayi sosai akan Rayyan din.
“Gaskiya kudin ki zaiyi yawa, saboda za’a yanka raguna baki da fari guda daya, da zuciyar su za’ayi aikin, sai an hada guda biyu za’a musanya su da ta danki da take rike a wajen su… Aikine babba, zan kuma baki garin maganin da nake so ki tabbata ko yayane shi yaron yaci dan ya karya katangar da take tsakanin ku.”
Hakan kuwa akayi, kudaden duk daya bukata ta bashi su. Daman yace zata ga canji, ba karamin dadi take ji ba ganin yanda Rayyan din ya zauna a makaranta har tsayin wata hudu,mutumin da baya iya hada satika hudu batare da yazo Kano kona kwana daya ba. Shisa take shirya girkin nan da kanta. Duka zata hade abincin ta barbade, har Bilal ma yaci dan shima yana bukatar duk wata kariya da zata ba Rayyan. Dan ma shi tana kula da yanda yake janye jikin shi daga bangaren Maryama, ya rage shiga kamar da, hakan ba karamin dadi yake mata ba.
Gabaki daya cikin nishadi take a duka ranar. Saima da taji sallamar Bilal, da murmushi dauke a fuskar shi. Su Rukayya kance basa bambance muryar Bilal da ta Rayyan musamman yanzun da suka zama Samari, sannan idan a fisge ka kalle su zaka iya dauka Bilal ne, sai ya shigo sosai zaka ga Rayyan ne. Kamannin su har Abbu suke ba mamaki, yana kara jinjina karfin dangantaka ta jini, duk da mutane da yawa kan iya yin kamanceceniya batare da alaka ta komai ta hadasu ba.
Sai dai Rayyan yafi Bilal din haske, kuma yanzun ya dan fishi tsayi duk da su duka dogaye ne, Ayya kan cewa Abbu itama ai doguwar ce duk idan yace tsayin shine yaran suka biyo. Yanzun kuma Bilal na tara suma a kan shi, Rayyan kuma yana asketa kasa sosai sosai, kuma ya tara kasumba a fuskar da ta saka shi wani kwarjini na daban, Bilal gemu ne da samarin yanzun suke ajiyewa da har dariya yake baiwa Ayya. Wani lokacin ma fayau zakaga fuskar shi, ya aske komai.
“Ayya…”
Bilal ya furta yana fadada murmushin shi, kafin ya karasa cikin dakin yana zama kan kujera hadi da sauke numfashi.
“Yan Zaria”
Ayya ta fadi tana saka Bilal din yin dariya, yayi kewarta matuka.
“Harma mun zama yan Zaria kenan Ayya… Ina kowa? Wallahi nayi kewarki da yawa…”
Sosai Ayya take murmushi, tasan yayi kewarta, tunda yana iya kiranta sau biyar ma a rana. Itama idan ta cika awa hudu bata ga kiran shi ba sai ta neme shi. Rayyan ne ma harta saba, a cikin watannin nan hudune da take tunanin aikin Malam ne ya kirata sau biyu, daga gaisuwa yayi shiru, sai tace ta dinga tambayar shi makaranta da lafiyar shi da ya dinga amsa ta dai-dai.
“Ayya gaisuwa ce kawai.”
Ya fadi a hankali, da yasan yanda taji dadin gaisuwar da ko sau dayane a wata ya kirata. Tunda yai wayar hannu sai a wajen Bilal ta sami lambar shi saboda yanda bai taba gwada kiranta ba. Idan sunyi magana to Bilal ya bashi wayar shi ya gaisheta, shima daga yanayin yanda zai magana tasan a kunne kawai Bilal ya saka mishi wayar batare daya shirya ba.
“Duk idanuwanka yayi zuru-zuru.”
Dariya mai sauti Bilal yayi
“Jarabawa ce Ayya… Sai kinga Hamma, gara nima tunda komai na samu ina ci.”
Numfashi ta sauke, ai baizo ba ballantana ta gan shi. Da kanta ta mike tare da fadin,
“Allah yasa an rubuta a sa’a, bari in dauko maka abincin ku…”
Kitchen ta wuce ta dauko mishi kuloli guda biyu da cokula, mikewa Bilal yayi ya amsa yana ficewa daga dakin zuwa dakin su, tunda ya karya kwana ya hango Layla a tsaye, jikinta sanye da wandon jeans ruwan bula da riga ja a jikinta, sai hula, tayi mishi kyau tun ta gefen ta daya hango, yana jin zuciyar shi ta matse a kirjin shi, cikin shekarun nan ya fahimci muhimmanci da Layla take da shi a rayuwar shi. A cikin shekarun ne kuma yayi kokarin janye jikin shi saboda yanda kusancinta da Rayyan yake wahalar da shi.
Suna zaune su biyu zata zo waje, daga nesa zaka ga yanda idanuwanta suke kafe kan Rayyan, lokutta da yawa in ba kuka Rayyan din ya sata ba, sam bata kula da yana waje. Idan Rayyan yana nan idanuwanta a rufe suke daga sauran abubuwan da bashi ba. Ranar da Rayyan ya riko hannunta ji yayi wani abu na budewa a kirjin shi, shisa yanzun yake tashi yana basu waje, yafi mishi kwanciyar hankali, abinda bai gani ba bazai bata mishi rai ba sam.
Wani lokacin idan Rayyan ya kai mata wani dukan har a zuciyar shi yake jin zafin, amman daya kirata zata sake dawowa. Zaka rantse da Allah rashin kirkin da Rayyan yake mata take so. Bashi da inda yake jin sauki-sauki sai wajen Aisha. Yanzun ma daya huta yayi la’asar wajenta zai tafi ko zuciyar shi zatayi sanyi-sanyi. Da ba kulolin abinci bane a hannun shi sam ba zai karasa inda suke ba, ya koyawa kan shi nisanta da Layla, musamman in tana tare da Rayyan haka. Numfashi yaja yana fitarwa, duk wani karfin hali da zai iya ya tattaro yana takawa har inda take tsaye a bakin kofa, kafin yaga Rayyan da yake tattaro shara.
“Hamma Bilal…”
Layla ta fadi cikin sigar gaisuwa batare da ta kalle shi ba.
“Layla…”
Ya amsa a sanyaye, yana shirin karawa da tambayar lafiyarta Rayyan ya dago, da bayan hannun shi ya kai ma Layla wani duka da yasa Bilal runtsa idanuwan shi kamar a kan shi hannun zai sauka, ya bude su a hankali yana ganin Layla da ta kauce tana kara turo baki.
“Nace bai sharu ba kika tsaya gardama dani… Uban meye wannan?”
Ya karasa maganar yana nuna mata wata kasa da batasan daga inda ya sharota ba, saboda har karkashin gadon dakin nasu sai da ta share, kujerar shi da teburi kuwa daga su tayi ta ajiye a gefe, sif din kayan su har samanta sai da ta taka kujera ta share, haka ta sake takawa ta gogo daga saman zuwan jiki, tasan halin shi, dan yatsa zaisa ya dangwalo yaga ko da kura babu.
“Wallahi shara hudu nayi Hamma.”
Ta furta a gajiye, Rayyan din najan wani tsaki.
“Ba abinda kika iya sai shirme…”
Ya fadi yana saka abin kwashe shara ya tattare kasar ya mika mata, karba tayi tana juyawa, shima cikin dakin ya shiga. Inda Bilal ya rufa mishi baya yana samarwa kulolin da suke hannun shi mazauni a tsakar dakin. Rayyan links din jikin rigar shi yake cirewa, dan manyan kayane a jikin shi, wani yadi ruwan kwai da ya sake fito da hasken fatar shi.
“Ayya na tambayar ka.”
Bilal ya fadi badan ya tsammaci amsa daga wajen Rayyan din ba, bai bashi amsar ba kuwa ya wuce yana nufar bandaki, dan ruwa kawai yake son watsawa. Tun da safe kafin su taho yace Layla ta bude dakin ta share musu. Yana saka kafar shi yaji kamar ya taka kasa. Wayarta da ta saukaka mishi komai yanzun ya kira.
“Baki share dakin nan ba Layla.”
Ya furta bayan ta daga, kafin ta amsa shi ya dora da
“Ki zo yanzun.”
Gardamar da ta tsaya mishi da rantse-rantse yasa shi cewa ta dauko mishi tsintsiya. Sanda ta kira shi take fada mishi taci jarabawar aji shidda wato WAEC mamaki ya dingayi yanda rayuwar take wani irin sauri.
“Wayar waye wannan din?”
Shine tambayar da yayi mata a madadin tayata murnar cin jarabawar da ta fada mishi tayi.
“Wayata ce, Abbu ya bani saboda naci exams dina.”
Yanayin muryarta yasa shi gane ta turo bakinta ne take mishi magana
“Saina fasa bakin ki kina mun magana haka.”
Shiru tayi, ya kashe wayar daga bangaren shi, kusan kullum sai ta kira shi, yana dagawa kuma gaisuwar shi itace
“Lafiya? Ko maitar ce ta motsa? Me yasa kike kirana?”
Amman ranar duk da bata kira shi ba, haka zai saka wayar a gaba yai ta kallo, ko yana aji wayar na silent, rabin hankalin shi yana kan darasin da ake musu, rabin hankalin shi na kan wayar. Ranar kuma saiya nemi dalilin da zai kirata, ko yace ta duba dakin su taga ko wani takalman shi ruwan kasa suna nan, ko kuma wata takarda da yasan babu ita sam-sam. Kawai yana dai son yaji muryarta ne. Yana fitowa daga wanka ya samu har filattai Bilal ya kawo, sai da ya samu riga da wando marassa nauyi ya saka a jikin shi ya feshe da turare kamar zai fita wani waje. Sai daya zauna yake jin gajiya sosai.
Filattan ya mika hannu ya dauka yana tashi tsaye. Inda ruwan leda yake jingine ya karasa ya fasa yana daukar guda daya. Bandaki ya shiga ya kara dauraye filattan ya dawo ya dauki cokulla suma ya dauraye. Bilal na kallon shi harya gama, da kan shi ya bude kulolin, wake da shinkafa ne, sai miyar kaji da kamshinta ya cika dakin.
“In zuba maka ko saika yi wanka?”
Rayyan ya bukata yana kallon Bilal
“Ka zuba mun.”
Kai Rayyan ya girgiza
“Jikin ka baya maka danqo?”
Wani irin kallo Bilal yayi mishi
“Da ruwan sikari nayi wanka da safe? Ko motar sikari muka shigo?”
Murmushi Rayyan yayi da yake wahala kagani a fuskar shi. Amman sam jikin shi baya mishi dadi rana ta fito ta fadi bai cakar da Bilal din ba, bai ga hawaye a fuskar Layla ba, ko basa tare yana son yaji muryarta ta canza ta cikin waya alamar ta kwade shi a cikin tunaninta yafi a kirga.
“Daga tambaya?”
Ya fadi yana mayar da hankalin shi kan abincin da yake zubawa a filet
“Akan me jikina zaiyi danqo to?”
Shiru Rayyan din yayi yana kyale shi, yana gama zuba abincin ya mayar da kulolin ya rufe, nashi filet din ya dauka yana gyara zaman shi kan kujera saboda yunwa yakeji ta fitar hankali, ko karin safe baiyi ba. Biscuit ne leda daya a cikin shi duk ranar. Bilal ya riga shi gama cin abincin, yana kallon shi ya wuce bandaki yayo wanka ya fito. Shadda ya saka a jikin shi harda hula, kafin wani lokaci ya fito das da shi. Wata leda Rayyan din yaga Bilal ya bude jakar shi ya zaro .
“Na fita…”
Ya furta a hankali yana wucewa ya zira takalman daya fito dasu. Bangaren Ayya ya shiga yana samunta a zaune.
“Sai ina haka? Anata baza kamshi.”
Dariya yayi a kunyace
“Zan dan fita ne Ayya… Amman kafin Magriba in shaa Allah zan dawo, idan ba inda zakije da motar ki…”
Kafin ya karasa maganar ta katse shi da fadin,
“Kaje ka dauki mukullin yana kan gado…”
Murmushin godiya yayi mata yana cire takalman shi ya wuce har can cikin dakin nata ya dauko, ya fito ne tace,
“Ka gaishe ta.”
Cike da kunya yace
“Ayya…”
Dariya tayi sosai, shima dariyar yayi yana wucewa har wajen motar Ayyar daya bude ya shiga. Saboda ita ya koyi tuqi tunda ta siyi motar da shiya fara sanin zata siyeta dan tare ma sukaje. Sai da ya tsaya yayi la’asar a hanya kafin ya nufi Kinkinau inda gidansu Aisha yake, har harabar gidan aka bude mishi ya shigar da motar yana fitowa, tsaye yayi a wajen ya kira wayarta. Daga inda yake tsaye yana hango ta tana saka hijabinta a bakin kofar da zata hadaka da cikin gidansu, kamar ta kasa jira ta saka daga cikin gida saboda zumudin da takeyi na son ganin shi.
“Allah ji nake kamar na dade banganka ba.”
Ta furta bayan sun gaisa, dariyar shi yayi, yana kallon yanda sosai kominta yake mishi kamar Layla, har shigen yanda take magana, yanzun girma yasa yana ganin banbanci sosai a tsakanin su. Saboda tunda yake da Aisha zai kirga ranakun da ya taba ganin kalar kayanta, saboda hijabai take sakawa, hijabanta kuma masu hannune dogaye sosai har suna share titi, inba ranakun da ta saka abaya ba, ya hangi kala kalar kayan nata ta kasa. Layla kuwa hijabi wahala take mata, ranaku dai-daine zaka ganta da hijabi, ko in zataje islamiyya ko kuma tana idar da sallah ta fito daga daki kafin ta cire.
Yana son kalar shigar Aisha, saboda tattare take da mutunci na gaske, yanda Layla take saka kananun kaya ko skirt din da take tafiya dakyar a cikin shi yakan mishi tsaye a rai. Musamman idan yaga fita zatayi a hakan, zaita tunanin tarin mazan da zasu ganta da wannan shigar. Sai yaga har wani haske ke gilmawa ta cikin idanuwan shi saboda kishin da yakan taso mishi. Amman ita ko a jikinta, hannuwa Aisha ta tafa a saitin fuskar shi, tana saka shi ware mata idanuwan shi da sukafi komai yi mata kyau a tattarr da shi.
“Tunanin me kakeyi?”
Kafadu yadan daga mata yanayin murmushi.
“Kinyi kyau.”
Ya furta a madadin tambayar da tayi mishi, kanta ta saddar kasa cikin jin kunyar shi.
“Kaima kayi kyau ai.”
Kai ya girgiza mata.
“Idan banyi kyau bama ke ba zaki gani ba.”
Dariya tayi sosai, akwai gaskiya a al’amarin shi, kullum kyau yake mata, tun bata da hankali har yanzun da tayi, soyayyar da take mishi mai girma ce, ba zata taba barinta taga wani aibu a tattare da shi ba. Yau ko da wani ne zai kawo mata zance marar kyau akan Bilal tana da yakinin zuciyarta ba zata taba aminta ba, ita bata ma yarda da yanda Ummi yayarta take cewa Rayyan yafi Bilal dinta kyau. Rayyan da ko fara’a bayayi, Bilal kuwa ko hada idanuwa kukayi zai maka murmushi. Ko kamar da ake cewa sunyi ita bata gani, nesa ba kusa ba Bilal yafi mata Rayyan kyau.
“Son da kike maine Allah. Amman Rayyan yana mun kyau tun muna makaranta.”
Ummi ta fadi, haushima taji ta tashi tabar mata wajen. Da aji daya Ummi ta wuce ta, ita tun waccen shekarar ta zana jarabawa, jamb ce bataci ba, kuma ta nace sai ABU zataje. Ita Aisha bata taba tunanin zuwa wata ABU ba, dan duk kawayenta BUK suka nema. Saboda Bilal, dan ta samu damar ganin shi kullum ta biyewa Ummi suka nemi gurbin karatu a ABU din wannan shekarar tunda ita tayi sa’ar cinye jarabawar ta jamb.
“Sanda zan bar Zaria fa lokacin zaki shiga aji uku, haka ni zan dawo gida ki barni da kewar ki.”
Cewar Bilal da ta fada mishi inda ta cike.
“Zaka gane yanda nake ji duk idan kazo zaka koma.”
Dariya yayi sosai.
“Ramawa kike sonyi shisa kika zabi Zaria kenan ko?”
Ya tambaya yana sata dariya itama. Yanzun ma hira sukeyi, Aisha ce kawai take rike shi da hira haka har baya sanin lokaci yaja. Mamakin jin kiran magriba da akeyi suka yi.
“Aisha kingani ko? Nace ma Ayya kafin Magriba zan koma.”
Yanayin yanda yai maganar ya sata yin dariya.
“Laifina ne kenan?”
Kai ya daga mata. Dakyar sukayi sallama bayan ya mata alkawarin zai dawo gobe. Sai lokacin ya mika mata ledar da take hannun shi. Wasu takalma ne da yar ajinsu take siyarwa yayi mishi kyau, taki biyu ya sai mata kala daban-daban. Duk da batasan ko meye ba taji dadi har ranta, Bilal na da kyauta, lokutta da yawa inta juya cikin dakinta taga wani karamin abu da Bilal ya siya mata sai taji ya dan saukaka mata kewar shi. Anan masallacin unguwar su Aisha yayi sallar Magriba, sannan ya wuce gida.
*****
Babu abinda Layla ta dauki gyaran da Mami take yawan yi mata kan kayan da take sakawa banda takura da rashin wayewa irin ta Mami. Ita ta kasa gane yanda duniya take tafiya da zamani yanzun sam. Lokutta da dama Mami na sakata jin daman ace ta fito a kasashen turawa ne, da yanzun ta kai shekarun da zata iya zabarwa kanta duk abinda take so, idan ma gidan zata bari tayi zaman kanta zata iya yin hakan.
Ko facebook data bude, yawancin shafukan da take bi na fina-finan kasashen waje ne, sai kuma na jaruman su. Musamman ma su Kim Kardashian, sai kuma mawaka irin su Rihanna, Drake, Chris Brown da sauran su, dan tafi son wakokin wrap. Takan ji wakokin kasashen sudan, yanayin al’adarsu na burgeta matuka. Lokutta da dama ita kadai a daki tana amfani da mp3 dinta tun kafin tayi waya ta saka earpiece tana gwada kalar raye-rayen da takan gani a fina-finai. Sosai zakayi zaton ta koyi rawa idan kaga yanda take karya gabobin jikinta.
Yanzun kuwa da tayi waya abin ba kama hannun yaro, videos ne da ita kaca-kaca, a jikinta take jin da ace tazo a kasar jamus ko amurka babu abinda zai hanata zuwa makarantar koyon rawa. Ana zuwa gasar da takan gani a fina-finai. Sosai abin yake mata kyau idan ta hasaso, musamman idan ta cire fuskar jaruman ta dora musu ta Rayyan. Wani lokaci abin na bata dariya matuka
“Hamma da rawa.”
Takan fadi ita kadai, sai dai ko baiyi ba ita a kanta rawar tayi mishi kyau, musamman ace ita da shi a tare.
“Perfect…”
Layla take tsintar kanta da fadi idan ta hango ta da Rayyan din, tun kafin ta gane ma’anar soyayya take kallonta a fina-finai, shisa sam bata sha wahalar gane me take ji akan Rayyan din ba, tunma kafin tasan da gaske son shi takeyi. Duk da wani lokaci yana fita daga ranta na yan dakika, wasu ranakun harna yini daya.
“Mayya…”
Kalmar na bakanta mata rai sosai, kuma da gaske ne, akan shi ita din mayyar ce, kome zai mata zuciyarta har tsalle takeyi idan tagan shi, kuma bata fasa daga waya ta kira shi sai dai idan bata da kati. Ko da ace shi da Bilal basa ABU ita kam batajin zata zauna karatu a garin Kano, saboda babu yanda za’ayi abarta ta zauna hostel idan dai a BUK ko Polytechnic take. Shisa bata fadawa kowa ba sanda zata yanki jamb, zabinta na farko ABU din ta saka, tana son samun abinda ake kira “full high institution experience” a Turance.
Batason sa idon Mami, rayuwar jami’a take son barjewa yanda ya kamata. Ta kuma yi sa’ar samun 181 a jamb din, ta tsallake dakyar. Tasan me take so, fannin turanci ne ta zaba saboda tana son samu aiki da wata babbar jarida ko gidan radio. BBC ne harinta, ko ba komai watakila tana da rabon zuwa kasar waje. Shisa ta gama tsara yanda komai zai fito, bata shiga tashin hankali ba sai lokacin da aka fara saida fam din jarabawar tace daliban da zasu sami gurbin karatu. Saboda gefe Mami ta koma tana fadin,
“Duk makarantun da suke garin Kano? Sai kinje Zaria? Zubaida data gama karatunta kinga tabar gari. Khalifa kan shi cikin garin nan yayi nashi karatun, babu inda zakije, gara ma kiyi magana da Abbunku a sama miki gurbin karatu ko a legal ne idan BUK din ba zata samu ba.”
Kuka tayi ranar kamar idanuwanta zasu tsiyaye, dan kiri kiri taga Mami na neman ruguza mata tarin burin da take da shi, a tsayin zamanta da Mami bata taba jin maraici ba sai ranar, watakila inda iyayenta suna raye zasu taimaka mata wajen ganin ta cika burinta ba suyi kokarin zame mata katanga a tsakaninta da abinda take son zama ba. Da Abbu yasa aka kirata ma kuka ta fashe mishi da shi.
“Abbu dan ina mace bazan iya tafiya wani waje karatu ba? Dan ina mace bani da ‘yan cin zabi? Me yasa Mami ba take son hanani? Karatu ne fa ba wani abu marar kyau ba. Ita ya kamata ta karfafa mun gwiwa in cika burina.”
Ta karasa tana wani irin kuka, sosai yake kula da duka yaran. A duk gidan kuma daga Layla sai Jabir ne sukayi wata irin wayewa, rayuwar turawa ita suka saka a gabansu, garama Layla ba sosai takan nuna ba, amman Jabir sai da ya tabbatar har turancin shi ya gyara shi yanda idan yana magana zaka rantse da Allah ba’a kasar najeriya yayi karatu ba, to Layla ma yaji haka take lankwasa harshe.
“Jabir turai”
Shine tsokanar da yakan yiwa dan nashi idan yaji yana magana wani lokacin, ko Layla yakan tsokaneta.
“Ke da Jabir sai kun tauna harshen ku wata rana.”
Kuma da gaskiyar shi, Jabir shine ya fara sakata son gyara turancin ta, haka suke zama kullum tsayin shekara uku suna wannan wahalar, Mami idan tagan su takan ce,
“Ikon Allah, lallai sa kai wanda yafi bauta ciwo, da Qur’ani ne kukewa wannan nacin, ba’a kasar Kano ba, har zagayen Najeriya sai an san da zaman ku.”
Dariya kawai sukanyi dan a ganin su ita ba zata taba ganewa ba. Ko Jabir din “Languages” yake karanta a BUK, kuma yanzun da yake shekara ta biyu, a tarihin department din ba’a taba samun dalibi mai kokarin shi ba. Abbu ma kance.
“Da alama Jabir zaka samu gwamnati ta dauki dawainiyar karatun ka zuwa kasar waje in har kaci gaba da tafiya a haka.”
Itama Layla wannan burin take da shi, amman Mami na neman hanata. Shiru Abbu yayi dan baisan me ya kamata yace ma Layla din ba. Har ran shi yana son su da karatu, a matsayinta na ‘ya mace musulunci yayi mata wata daraja mai girma, suma kuma ya basu ‘yancin kareta da dukkan karfin su. Ya fahimci Mami tunda sunyi zancen tun kafin yasa ta turo mishi Layla.
“Kana kallon yanda nake fama da Layla kan wannan rayuwar turawan data dorawa kanta… Ina ga ta bar inda babu idanuwan kowa?”
Mami din ta fadi muryarta na karyewa, har ranta tana tsoron barin Layla Kano. Karatu duk inda kake zakayi. Shima kuma ya aminta da abinda tace din, amman yanda Layla take kuka a gabanshi ya karyar mishi da zuciya.
“Abbu idan kaima ka hana zaku sakani yin wani tunani daban.”
Layla ta furta tana tashi tabar shi anan zaune. Ya jima shiru, maganganunta sun jefa shi wani tunani daban, harga Allah yafi basu kulawa ita da Bilal sai Haris da yanayin shine son kulawar. Amman ita da Bilal na minti daya bayason suji rashin iyayen su, yasan zafin maraici duk da yayi wayon sanin nashi iyayen, su da basuyi wannan wayan ba baisan abinda sukeji ba, yana kokarin ganin basuji komai ba. Bayason Layla taji kamar dan bata fito daga jikinsu bane suke son zama katanga tsakaninta da burinta.
Yana ganin tayi yarinta ta fahimci cewa basa nufin komai a kanta sai alkhairi, komai da zasuyi dan su kareta ne badan komai ba. Abin ya dame shi, kwana yayi yana juyi, washegari kam yana tashi daga aiki saida ya biya wajen abokin shi Nasiru dan ya nemi shawarar shi, bai boye mishi komai ba.
“Ina tsoron tafiyar ta karatu wani gari, har raina ina tsoron hakan saboda ita macece.”
Murmushi Nasiru yayi.
“Kai kasan indan tani ne yara mata ba zasu wuce matakin sakandire ba, Allah yasan Nabila tayi karatune saboda miji bai fito ba sanda ta gama, Zainabu fa? Ita da kanta ta zabi auren da miji ya fito, sakandiren ma bata samu gamawa ba.”
Kai Abbu ya jinjina mishi, duka shine shaida, yanda Nasiru yasan sirrikan shi, haka shima, suna neman shawarar juna a dukkan lamurran su.
“Meye muke gudu Ahmadi? Lalacewar yaran ce abin gudu, gani muke idan suna gaban idanuwan mu zamu fi kare su yanda ya kamata. Ni ma tunanin da nakeyi kenan yasa nake son nisanta matan da zurfin karatun boko…sai dai rayuwa ta koyamun ba dabarar mu a tarbiyar yara… Ka duba Bashari, a gaban idona tarbiyar tashi take ta tabarbarewa, duka, zagi babu wanda bamuyi ba, yanzun ba addu’a muka koma ba? Shine aka fara samun dan cigaba.”
Numfashi Abbu ya sauke.
“Hakane, kana ganin in barta ta tafi?”
Kai Nasiru ya girgiza mishi.
“Ba ina cewa kabarta ta tafi bane kai tsaye, ina fada maka karka labe a bayan gudun lalacewar tarbiyya wajen hanata zuwan. A gaban idanuwanka abinda kake gudu zai iya faruwa, kai dai kayi iya yinka wajen tarbiyar, ka kuma roki Allah ya kare abinda idanuwanka ba zasu gani ba…”
Maganganun Nasirun sun kara daure mishi kai, duk yanda yaso ya furta da bakin shi cewa yabar Layla ta tafi Zaria yaki, shawarar shi duka akwai kofar zabi daya barma Ahmadin. Haka Yaya Ayuba da ya same shi da zancen.
“Ba gari ba, kaga Nadiya Madina tayo karatunta, duk kuwa da tarin surutun da akai tayi a kai. Gata ta kammala ta dawo lafiya tana dakin mijinta. Kamar yanda kace Nasiru ya fada maka ne, tarbiya iya yinka zakayi, sauran da yafi karfin ka ka hada da addu’a. Karka barta ta tafi sai kana da yakinin duka zuciyarka ta amince maka da tafiyar, idan baka aminta ba hakurin zaifi zama alkhairi. Idan bata fahimce ka ba yau, wata rana zata fahimce ka.”
Akan shawarwarin nasu yaita tunani har kwana biyu kafin ya natsu da barin Layla ta tafi, ranar har tsakar dare ya tashi yayi sallah yana rokon Allah daya kare mishi yaran shi, ya rabasu da abokai gurbatattu. Dakyar ya shawo kan Mami.
“Shikenan, Allah yasa hakan ya zama alkhairi.”
Shine maganarta da wani irin sanyin murya daya taba shi. Layla tayi murna kamar zata goya Abbu. Neman hutun kwana daya yayi a wajen aiki da lokacin jarabawar nata yazo, da kanshi ya dauketa suka tafi har garin Zaria, kwana daya sukayi ta zana jarabawar suka dawo. Ya fadawa Ayya zaije Zaria, dalilin ne bai sanar da ita ba, saboda bai jima da sukayi rikici akan karar Rayyan da Layla ba, idan taji zataje Zaria karatu wani sabon tashin hankalin da bai shirya ba za’ayi a gidan.
Cikin ikon Allah Layla ta ci jarabawar inda ta sami gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello. Ba ta da kalaman da zata dora farin cikinta a kai ranar, Abbu da kanshi yaje Zaria ya amso mata admission letter dinta, kuma a hankali ita da Mami suke shirin tafiyar tata, tana kokarin ganin duka ranakun batayi wani abu da zai bata ran Mamin ba, kananun kaya ma ta daga musu, dogayen riguna take ta fama dasu.
Abbu kuwa aikawa yayi aka kira mishi Bilal ranar daya amso admission letter din Layla. Yana shigowa bayan sun gaisa ya zauna, Abbu ya mika mishi takardar, amsa Bilal yayi yana dubawa, duk kuwa da Layla ta fada mishi, yayi mata murna sosai da sosai.
“Nagani Abbu, ta fadamun…”
Dan lokacin da ta gaya mishi inda ta cika a jamb dinta ta dora da
“Babu wanda na fadawa fa, kai kadaj na gayawa.”
Cikin idanuwa ya kalleta.
“Me yasa?”
Ya tambaya cikin son sani, dan daga mishi kafadu tayi, kawai saboda shi dinne, saboda tasan zai goyi bayanta, zai tayata son abinda take so, zai karfafa mata gwiwa
“Saboda kawai kaine.”
Ta karasa maganar tana saka shi furta
“Hmmm”
Cikin rashin sanin abinda ya kamata yace, lokutta irin haka sai ta saka yaji kamar yana da wani muhimmanci mai girma a rayuwarta. Sai ya ganta tare da Rayyan take karyata mishi hakan. Sai da Abbu ya gyara murya tukunna yace
“Layla kanwa ce a wajen ka, ko bance ka kula da ita ba zakayi. Amman ina so da bakina in roki alfarmar nan, Bilal ka kula da ita, dan Allah ka kula da ita, kudin amana ne a wajena, akan Layla ina so in raba amanar da kai.”
Wani irin nauyi Bilal yaji kalaman Abbu sunyi mishi, nauyi sosai
“Ka kula da ita kamar yanda kake tunanin zan kula da ita, a zaman da zatayi a Zaria ka kareta daga dukkan abinda zaka iya kamar yanda kake tunanin ina kare ku, alfarma ce nake nema a wajen ka.”
Wannan karin dakyar Bilal yake fitar da numfashi saboda nauyin da kalaman Abbu sukayi mishi, abinda yake roko a wajen shi abune mai girma, amana yake bashi, ya kuma san daraja da hukunci hakan a matakin addini.
“In shaa Allah Abbu zanyi kokari.”
Ya furta muryar shi can kasan makoshi, kai kawai Abbu ya jinjina, dakyar Bilal din ya iya tashi dan duk gabban jikin shi a sanyaye yake jinsu, har yakai kofa Abbu yace,
“Bilal…”
Juyowa yayi.
“Ka kula da Rayyan, ka kula da Hamman ka.”
Ya karashe maganar cike da roko a idanuwan shi, bai taba cewa Bilal din ya kula da Rayyan ba, saboda yana ganin yanda yake wannan kokarin a duk rana, ya kuma sha jin Ayya nawa Bilal din wannan rokon, yau din Abbu wani irin rauni yake ji naban mamaki, shisa kalaman suka subuce mishi, kai kawai Bilal ya iya daga mishi, da nauyin zuciya ya fice daga dakin Abbu yana nufar bangaren su, inda ya hango Layla ta dora hannunta akan kafadar Rayyan da alama akwai abinda take fada mishi, tureta yayi yana fadin kalaman da Bilal baiji ba, yana kallo Layla ta juya, Rayyan din na kamo hannunta ya dawo da ita.
Lumshe idanuwan shi yayi zuciyar shi na wani irin dokawa, ta ina zai fara? Wanne alkawari ne ya dauka mai girma haka? Ya daukar wa Abbu alkawarin zai kula da Layla kamar yanda Abbun zai kula da ita, idan tana matsayin yar shi, idan tana matsayin kanwar shi bayason tana rungumar namijin da ba muharraminta ba kamar hakan ba komai bane ba, bayason ta kusa da Rayyan, Abbu yace ya kareta daga dukkan abinda zai iya. Abbu ya kara da fadin ya kula da Rayyan, akwai tarin ma’anoni da yake tattare da kalmar “kulawa.”
Ta ina zai fara kare Layla daga dukkan abinda zai iya?
Ta ina zai fara idan abin farko da yake son kareta daga shi Rayyan ne?
Ta ina zai fara kula da Rayyan idan bai hana shi daukar ma kan shi zunuban da suke tattare da wannan rungume-rungumen da sukeyi ba?
Ta ina zai fara hana shi abinda ya shafi Layla?
Ta ina zai fara kula da su idan matakin farko ya hada da rabasu da junan su?
Kaddarar su mai girma ce. Kaddarar su ta fara tun kafin sanin su.