Kwance Bilal yake yana nazarin wani lissafi, saboda har an fara test tun satin daya gabata, jarabawa nata karatowa. Amman Rayyan zaune yake yana zane, wani lokacin zaka rantse da Allah hutu Rayyan yake zuwa yi Zaria ba karatu ba, saima lokacin jarabawa, idan baka gan shi yana zane ba, to zaka iya ganin shi yana kwance shiru, tunda shi dai baya hada hanya da wata kafar sada zumunta, har dan whatsapp din da akeyi ma bayayi. Asalima wayar shi da screen din ya fashe yar karamar Nokia ya siya ya saka sim din shi a ciki.
Idan wani abu na makaranta ne daya kama sai an duba yanar gizo, da kwamfuta din shi kirar laptop yakanyi amfani. Kuma yana daya daga cikin mutane hudun da suke jagorantar ajin su ta fannin karatu, inda Rayyan dinne na biyu, idan da zai maida hankali ma tsaf zai zama gwarzo a ajin.
“Wai ba test kace kuna da shi ba?”
Bilal ya bukata, kai Rayyan ya jinjina mishi.
“Ba zakayi karatu ba?”
Raba idanuwan shi da takarda Rayyan yayi ya kalli Bilal din, kallon da yake fassara “Da ni kake?” Kafin ya mayar da hankalin shi kan zanen da yakeyi.
“Lokutta irin haka kana sakani inajin kamar bani da kokari”
Dan numfashi Rayyan ya fitar
“Kana da kokarin ne? Tun dazun kake kallon takarda daya.”
Bude baki Bilal yayi, kafin ya mike zaune.
“Kasan wanne lissafine? Kake kira takarda daya kamar wani abu marar wahala”
Fensirin hannun shi Rayyan ya ajiye, ya dan juya zaman shi yana mika hannu ya fisge takardar da take hannun Bilal, duba tambayar yayi, batare daya dago ba yace,
“Ina misalin? Wanda akayi?”
Tashi Bilal yayi ya dauko jakar shi yana fito da littafi ya dubo wani misalin yana mikawa Rayyan daya karba, sosai ya nutsar da hankalin shi yana ganin yanda aka fitar da abin. Kafin ya fara duba wanda Bilal yake nazari, a idanuwan shi yaga yanda komai zai kasance, juyawa yayi ya ajiye akan tebir, cikin mintina kasa da sha biyar ya gama fitar da shi yana jefawa Bilal din.
“Ba zaka maida hankali sanda ake maka abu a aji ba, kana can kana wasu tunane-tunane…”
Rayyan din ya fadi a fadace, dauka Bilal yayi yana duddubawa, murmushi yayi
“Bayani zakayi mun dalla-dalla…”
Hararar shi Rayyan yayi yana sake hade fuska, dariya Bilal yayi mai sauti wannan karin yana tashi ya janyo kujera ya zauna gefen Rayyan din daya ke watsa mishi wani kallo
“Ni kyaleni”
Ya fadi saboda surutu Bilal zai sa shi yayi, watakila sai yayi mishi bayani sau biyu ko fiye da haka, amman sai ya zaqulo wata tambayar yayi mishi. Haka kuwa akayi, har saida ya kule daya fahimci Bilal din ya gane, surutun kawai yake so ya saka shi. Ganin yayi Rayyan din yayi banza ya kyale shi yasa Bilal komawa kan gado abin shi, so yake ya sake fitar da lissafin a wata takarda daban dan yaga koya fahimta, shekarar shi ta farko ya fadi jarabawa guda daya. Rayyan yaita mishi fada kamar zai mare shi, wani lokacin ko bai niyyar karatu ba yakan dauko yayi saboda masifar Rayyan da ba karewa takeyi ba.
Ranar ne karo na farko da yaji kamar yayi dissapointing din Rayyan din, yanayine da baya so ya kara faruwa. Duk da kwakwalwar su ta bambanta, yana iya kokarin shi. Rayyan zanen shi yaci gaba dayi, amman baya tafiya yanda yake so, saboda yau ya kasa rufe gabaki daya tunanin shi kamar yanda yakanyi a lokutta irin haka. Layla ce manne a ran shi, tun jiya bai ganta ba, har wayarta ya kira amman a kashe. Yanzun ma wayar da take ajiye kan tebir ya dauka ya duba ko ta turo mishi sako, amman shiru, sake gwada kiranta yayi yana jin bata shiga ba, kamar matsalar network tunda ba’a ce mishi a kashe take ba
Wajen mintina sha biyar tsakani, batare daya kalli Bilal ba yace,”Ka ga Layla?”
Kai Bilal din ya jinjina mishi, kullum sai yaga Layla, in ya fita kafin ya wuce aji saiya biya ya kirata ta sauko yaga ya ta kwana, ko tana da wata matsala sannan ya wuce, amanar ta Abbu ya bashi, babu yanda za’ayi ba zai dubata a duk rana ba.
“Ni ban ganta ba”
Cewar Rayyan da wani yanayi a muryar shi da yasa Bilal dagowa
“Ba tazo aji ba, bata jin dadine tun jiya da dare”
Mikewa tsaye Rayyan yayi zuciyar shi na wata irin dokawa
“Me yasa baka fada mun ba?”
Kallon shi Bilal yayi yanda ya hargitse lokaci daya kamar yace mishi wani babban abune ya samu Layla, shi yasan lokacin al’adarta ne, badan ta gaya mishi ba, sai dan ya kula da duk wata haka take fama. Wancen watan da ciwon da komai ta zo wajen Rayyan, yana ganin yanda har fuskarta Rayyan din ya taba ko zaiji zazzabi bayan ya tambayeta me ya sameta tace mishi bakomai. Bai fada mishi ba saboda yasan idan akan Layla ne Rayyan zai dauki abin ya saka a ran shi. Amman can kasan zuciyar shi yana jin kamar akwai wani dalili bayan nan, dalilin da bayaso yasan shi saboda yana da yakinin zai saka shi yaji kamar bai kyauta ba.
Jacket din shi da take can gefen gado Rayyan ya dauka yana sakawa akan kayan jikin shi da riga da wando ne, ya dauki wayar shi yana kama hanyar kofa
“Ina zaka je? Takwas da rabi fa”
Ko amsa bai samu ba, numfashi kawai ya iya saukewa yana bin Rayyan din da kallo harya fice daga dakin. Wani irin sauri yake ya karasa titi ya samu machine zuwa gate din makaranta, kawai so yake ya fara hango hostel din su Layla, bai daina gwada kiran lambarta ba, har lokacin bai samu ba, ya kusan mintina goma a tsaye bakin kofar hostel din kafin yayi nasarar samun wayarta
“Ki daga dan Allah”
Ya furta a hankali, ya kasa tsaida bugun zuciyar shi waje daya. Yankewa tayi, ya sake kira, sai gashi ta daga, muryata can kasa tace
“Hamma?”
Kamar tana son tabbatar da cewa shi dinne ya kirata.
“Layla me ya sameki? Me yasa baki fadamun baki da lafiya ba? Ina wajen hostel dinku, ki sauko in ganki”
Ya karasa yana kokarin tuna ranar karshe da yayi magana cikin sauri kuma da yawa a lokaci daya irin haka.
“Ni ba zan iya fitowa ba”
Layla ta fadi daga dayan bangaren, tana saka zuciyar shi kara dokawa, shi fa sam bayason yaji bata da lafiya. Kuma gashi tana fada mishi ba zata iya fitowa ba, wacce irin rashin lafiya ce haka?
“Ki fito ba wasa nake ba, Allah ina jira”
Ya karasa yana kashe wayar, duk wata addu’a da tazo bakin shi ita yake karantawa, ya kafa idanuwan shi a kofar hostel din, har ya hango ta, dakyar take tafiya yana gani, yana kuma ji har cikin ran shi. Ta tsaya yafi sau biyar kafin ta iso inda yake tana tsugunnawa da alamar ciwon da take ji. Ta kwana biyu batayi ciwon mara irin na yau ba. Sunje clinic da Anisa an kuma bata magani, ta sha, sai taji kamar ya kara mata ciwon da take jine. Dakyar ta sauko yanzun ma.
“Layla”
Rayyan ya kira yana tsugunnawa shima, idanuwanta da suka sauya kala zuwa wani launi da baisan ya zai fassara ba ta dago tana saukewa cikin nashi da dole ya rissina su saboda yanda ta kara ma bugun zuciyar shi gudu.
“Ta shi muje asibiti…”
Ya furta a hankali, kai ta girgiza mishi.
“Munje tun jiya, na sha magani”
Shima kan yake girgiza mata.
“Baki da lafiya har yanzun”
Da kyar ta iya fadin, “Zai tafi nan da kwana hudu”
Da rashin fahimta yake kallon ta.
“Ya akayi kika sani?”
Kwanciya kawai Layla take son yi saboda cikinta kamar ana shara a ciki. Kilan Allah ya taimaketa tayi bacci
“Hamma…”
Ta fadi a gajiye, ganin kallon da yake mata ya sata cewa
“Period ne…”
A hankali tana mayar da kanta ta saddar, ya dauki wasu dakika kafin ya fahimci ma’anar kalamanta. Tsintar kan shi yayi da mikewa yana kama hannunta ya taimaka mata ta mike, jin shi yayi da dumi fiye da kowanne lokaci, hakan ya saka shi taba fuskarta, zazzabine ruf a jikinta. Idan yace ya tafi gida hankalin shi ba zai taba kwanciya ba, bayan yasan babu wanda zai kula da ita idan yabarta nan hostel din
“Muje gida, in kinji sauki sai ki dawo”
Yanda yai maganar babu wajen gardama, kallon shi Layla takeyi, bama zata iya gardama ba a halin da take ciki, kwanciya kawai take son yi.
“Zan dauko abu, kuma idan na koma ba zan iya sake saukowa ba Allah… Hamma kabarni anan, zuwa gobe ma zai fara sauki in shaa Allah”
Kai ya ke girgizawa tunda ta fara magana, sai yanzun ya kula duk tayi zuru-zuru. Idan dawowar ne gobe ta dawo, amman yau kam ba zai iya barinta ba, tunani zai mishi yawa.
“Layla tare zamu tafi, karki mun gardama.”
Yanda ya karasa maganar da wani irin sanyin murya da bata taba jiba yasa ta cewa,
“Ka aramun wayarka in kira Anisa to.”
Mika mata wayar yayi, sai da ta dan matsa sannan tayi kiran, kallonta yake duk da baya iya jin me take fadi harta gama ta dawo tana sake tsugunnawa, sun kai mintina goma da wani abu kafin Anisa ta sauko, da fara’a take kallon Rayyan
“Ina wuni…”
Yanayin yanda ta rage muryarta yasa Layla mikewa tsaye tana mata wani kallo
“Sannun ki”
Shine amsar da ta samu daga wajen Rayyan din, kyau yake yi mata tun ranar farko data fara ganin shi, amman tambayar duniya da tayiwa Layla akan shi sai ta hade rai
“Bana so Anisa, bana so Allah”
Takan fadi cike da kishin daya tabbatarwa da Anisa ba ciki daya Layla suka fito da Rayyan ba. Hakan dai bai hana yaci gaba da burgeta ba. Ledar da take hannun Anisa ta karba tana fadin,”Nagode…”
Kafin ta kalli Rayyan da alamar su tafi, ledar hannunta shikuma ya karba, yana kama hannun nata suka wuce cikin yanayin da ya burge Anisa matuqa. Ita daman saboda Anisa ne ta mike, saboda bataso ma Rayyan ya kalleta, ciwo bai hana wani irin kishi rufe ta ba. Yanda ta damqi hannun Rayyan yasan ciwo take ji, ba zaice ga yanda ciwon da take ji yake ba, amman ya san shi a karance. Shisa yanzun yaji har kasan ran shi, tsayawa yayi yana kallon yanda take runtsa idanuwanta
“Sannu…”
Ya furta yanajin kamar ya dauke mata ciwon da take ji, amman babu halin hakan, ganin tana shirin tsugunnawa yasa shi kama hannunta yana hanata. Juyawa yayi ya dan tsugunna, cikin tashin hankali Layla tace
“Hamma…”
Saboda taga yawancin mutane sun fara kallon su
“Zaki hau ko saina watsa miki mari?”
Rayyan ya furta, gara ya dauketa zuwa gate, watakila su sami abin hawa, tunda yaga tafiyar wahala takeyi mata. Bata taba hango kwatankwacin abinda yake faruwa yanzun ba. Rayyan ne, tana hango abubuwa da yawa da zasuyi tare, fiye da rabin abubuwan da tasan a tunaninta kawai zasu tsaya saboda shine, amman abinda yake shirin faruwa yanzun abune da bata taba hangowa ba ko a tunanin nata. Dogon wandone a jikinta da riga, da zata fito sai ta dauki hijabin da Mami ta dinka mata, dogone kusan har kasa, sallah take yi da shi. Yanzun ma shi hannunta ya fara tabawa bayan ya kirata, shisa ta saka.
Ta fara tunanin yi mishi gardama, sai taga dama ce ta samu da bata san ranar kara samunta ba
“Sai ka kara tsugunnawa”
Ta fadi, sai da yadan juya yana harararta, murmushi take dannewa, saboda yanda yayi din kamar dole aka saka shi bashi yasa kan shi ba. Sosai ya tsugunna wannan karin tana hawa bayan shi, ta zagaya hannuwanta ta riko mishi wuya, mikewa yayi kamar bai daga komai ba
“Kasheni kike son yine halan?”
Ya fadi dakyar saboda yanda ta shake mishi wuya
“Ba zaki sakar mun wuya ba”
Ya sake maganar yana karbar ledar hannunta, sassauta rikon tayi, amman sai takejin kamar zata fado, musamman daya fara tafiya
“Allah Hamma zan fado”
Shiru Rayyan yayi yana kyaleta, ya zabi ya maida hankalin shi kan yanda zuciyar shi take bugawa akan Layla da take kwance a bayan shi
“Da gaske nakeyi zan fado… Allah Hamma”
Saboda duk tafiya idan yayi sai taji kamar ta kara sumbulowa, sosai take mamakin yanda yara suke nacewa goyo, babu wani abu mai dadi a cikin shi, ita kam har jiri-jiri take gani. Ciwon daya murda matane ma yasa ta kara saka kanta cikin wuyan shi tana makale shi sosai. Tsaye Rayyan yayi yana runtsa idanuwan shi ya sake bude su
“Na kusan yaddaki kasa idan ba zaki daina motsi ba”
Dago da kanta tayi
“Ya zan daina motsi? Ko yara idan aka goya su baka ga suna motsi ba?”
Hannuwanta Rayyan ya kama yana shirin banbaro su daga wuyan shi, ta saki kara tana dariya
“Yi hakuri… Allah ya baka hakuri, na daina”
Qwafa yayi yana rike hannuwanta saboda bayason zagaya su ta baya ya tallafeta.
“Hamma…”
Ta fara ya katseta da
“Har surutu idan baki daina ba yaddoki zanyi”
Shiru Layla tayi tana jin idanuwan mutane a kan su, amman ko a jikin Rayyan, tafiya kawai yakeyi kamar gabaki daya filin makarantar su kadaine a cikin shi har suka fara hango gate.
“Bansan me kike ci da kike da nauyi haka ba”
Dakuna fuska tayi
“Ni ce nake da nauyin?”
Ta tambaya,”In kika kara magana saina jefar dake”
Shirun ta sakeyi, daman shine yayi mata magana, tunda ai tayi shiru. A gate ma ta tsammaci ko a cikin security din wani zai musu magana. Amman meye basu saba ji ba, idan ma sun tare su ko da ba kanwar shi bace da yace musu kanwar shice zance ya kare. Sai da suka fita kofar makarantar sannan ya sauketa yana mayar da numfashi. Da gaske yayi mamakin nauyin da take da shi, wuyan shi duk ya gaji, haka bayan shi ma. Napep ya tare musu suka shiga, kusan rabin jikin Layla akan shi yake
“Layla jikina zaiyi ciwo”
Rayyan ya furta yana kamata ya kara gyara mata zama yanda zata kwanta a jikin shi kamar bai gama mitar zaiyi ciwo ba. A haka har suka karasa kofar gidansu. Shiya kamata ta fito ya sallami mai napep din tukunna suka shiga cikin gidan. Kana jin hayaniyar mutane, amman kowa na daki, kan shi tsaye dakin su ya wuce yana daga labulen hadi dayin sallama. Bilal da yake kwance daga shi sai singlet ya mike babu shiri ganin Layla. Riga ya dauka da sauri yana kokarin sakawa, itama Layla sadda kanta kasa tayi. Yana karasa saka rigar ya tsayar da idanuwan shi cikin na Rayyan.
“Zazzabine a jikin ta, ba zan iya barin ta ba”
Rayyan ya fadi, saboda ya ga tarin tambayoyin da suke cikin idanuwan Bilal din tun kafin yayi su. Har lokacin kuma kallon shi Bilal yakeyi, saboda na farko, abinda yake damun Layla din bawai na asibiti bane ba, na biyu, a hostel din tana cikin yan uwanta mata da zasu fi fahimtar matsalarta, na uku, baiga dalili kwara daya da zaisa Rayyan ya dauko ta ya taho da ita ba. Na biyu ina yake so ta kwana, gidan maza ne, idan kaga mace to wani cikin kabilun da suke hayane ya kawota, tunda ko yanzun ma akwai budurwar wani Joseph da yake gidan, kusan sati daya kenan da tazo. Amman babu wani hankali a cikin abinda Rayyan yayi tunda basu da inda zasu ajiye Layla, kuma hauka yakeyi idan yayi tunanin zasu kwana a daki daya su duka ukkun.
Ko da ace ciki daya suka fito gabaki daya abune da zai zama zabin su na karshe a matsayin su na baligan musulmi, kuma hausawa. Shisa ya zabi yace
“Allah ya kara sauki”
Ya juya ya dauki wayar shi, takardun da yake nazari yana karasawa ya zira takalman shi da suke gefe ya daga labule ya fice daga dakin. Irin halayyar nan na daya daga cikin halayen Bilal da bayaso. Layla takalma ta cire tana karasawa kan gado ta kwanta, dan bata da lokacin ganin jin dadi ko akasin haka a fuskar Bilal. Rayyan ledar hannun shi ya ajiye, yana bin bayan Bilal din
“Bilal…”
Ya kira ganin harya kusan karasawa dakin su Shehu. Juyowa Bilal yayi amman ya tsaya a wajen, sai Rayyan dinne ya taka ya same shi
“Idan kana da abinda zaka fada mun ka fadamun, bana son ka dinga bani attitude…”
Ya karasa da gajiya a muryar shi, cikin idanuwa yake kallon Bilal din
“Me yasa zaka dauko ta? Meye zakayi mata anan da ba za ayi mata a hostel ba?”
Da sauri Rayyan ya amsa da
“Kulawa, zan kula da ita anan”
Numfashi Bilal yake fitarwa, ran shine bayaso ya baci sam
“Ka manta gidan maza ne nan Hamma? Ina dacewa ta kwana a cikin gidan nan? Me yasa baka tauna abinda zuciyarka ta raya maka kafin ka aikata? A hostel zata kwana da wasu a daki, idan tana bukatar taimako zasu fi saurin bata, anan fa? Ita kadai zata kwana…”
Kai Rayyan ya girgizawa Bilal, duka a cikin abinda yayi baiga na fada ba, yaje ya dubata yaga tana zazzabi, idan ya dawo hankalin shi ba zai kwanta ba shisa ya daukota ya taho da ita. Baisan yanda zaiwa Bilal bayani ya fahimce shi ba
“Zan kwana da ita”
Yanda Rayyan din yai maganar yasa Bilal jinjina kan shi da ya fara alamar ciwo
“Kai da ita? A daki daya?”
Kai Rayyan ya daga mishi
“Ni ba bacci zanyi ba, ina zane. Kuma zan duba abu haka. In tana bukatar wani abu zan sani”
Idan ya tsaya zai iya fadar abinda zaizo ya dame shi, ko kadan Rayyan ba rashin dacewar su kwana daki daya da Layla yake gani ba. Tunanin shi ya tsaya a iya kula da ita ne, baisan ta yanda zai nuna mishi illar hakan ba, musamman wani abu daya tokare mishi kirji ya hana mishi tunanin komai
“Sai da safe”
Ya iya furtawa muryar shi na fitowa a shaqe, kai Rayyan ya jinjina, yana bin Bilal da kallo harya shiga dakin su Shehu, sannan ya koma. Layla ya samu in ta juya nan ta juya can
“Kin ci abinci?”
Ya bukata, kai ta girgiza mishi
“In hada miki tea?”
Da kai ta sake amsa shi, Bilal ya dauko musu wani flask daga gida, yakan dafa tea saiya saka musu a ciki. Yanzun ma cike yake, hada ma Layla kawai yayi yana mika mata kofin ta tashi zaune. Ya hada mata shi da kauri sanin bata ci komai ba, a hankali take kurba tana kallon shi ya natsu kan zanen da yakeyi, zaka iya rantsewa kamar baisan tana dakin ba, sanda ta gama shanye ta danji sauki-sauki. Kawai saita tsinci kanta da son ganin me yake zanawa. Dan haka ta mike tana zuwa ta gefen shi ta leqa, dago kai yayi
“Bana son gulma, ki tashi daga saman kaina”
Turo baki tayi
“Ba aljanu ne da kai ba balle kace na tsaya a kanka zasu ta shi”
Ganin ya motsa yasa ta yin tsalle daya tana matsawa, dariya takeyi ganin yanda yake kallon ta, ta san da lafiyarta kalau saiya masgeta. Shisa ta rufa ma kanta asiri ta koma ta kwanta
“Meye kake zanawa Hamma?”
Ta tambaya, banza yayi ya kyaleta. Kawai dan ta dame shi ne yasa ta dinga mishi tambayoyi, towel din da yake kan kofa na Bilal ya janyo ya ajiye a gefen shi, surutunta har tsakiyar kwakwalwar shi yake ji
“Kaji Hamma…”
Layla ta fadi, ko kadan bata ga dago towel din ba sai da ya shauda mata shi
“Mayya ce ke?”
Towel din ta janye tana ajiyewa gefe, juya kwanciya tayi. Ya furta kalmar daya san zata bakanta mata rai hankalin shi ya kwanta. Zanen shi yaci gaba dayi har sai da yaji shirunta yayi mishi yawa, dubawa yayi yaga tana bacci. Net din da tunda Bilal ya daura musu shi suke fada a kai ya saki yana gyara mata sosai. Kuma kawai dan ya cakar da Bilal din ne yasa shi fadin
“Ni fa ba zan shiga net kamar kifi ba…”
Dan murmushi ne ya kwace mishi yanzun daya tuna mitar da Bilal yai tayi har washegari. Yakan yi tunanin ko bakin Bilal na mishi ciwo wani lokacin saboda mitar tsiya. A haka su Ayya suke cewa Bilal salihi, Bilal baya magana. Bayan har tsegumi yakeyi, shi kadai kuma yake yiwa, baisan ko Aisha naganin wannan bangaren na Bilal ba. Komawa yayi ya zauna, haka kawai wannan karin saiya kasa samun natsuwa, lokaci zuwa lokaci yake tsintar kan shi da kallon Layla da take bacci. Mikewa yayi ya karasa wajen kofa yana kama labulen dakin ya daga shi sama. Fankar dakin ya kurewa gudu duk da an dan fara alamar sanyi. Ya karasa ya bude net din Layla yana rufa mata bargo.
Duk da haka ya kasa samun sukuni, bai daina jin zufar rashin dalili ba duk kuwa da fankar dakin daya kure
“Me yake damuna ne haka?”
Ya furta a hankali. Kwayoyin shi ya tashi ya dauko ya sha yana mayar dasu ya adana. Amman har wajen awa biyu tsakani bai samu natsuwar da yake nema ba. Wata takardar ya dauka ya dora akan ta zanen da yakeyi yana rufa babban towel din daya siya domin hakan kawai ya dora kan shi akan tebir yana kwanciya. Kallon Layla yake da take bacci hankalinta a kwance, ba zai ce ga asalin abinda yake tunani ba, amman rabon da bacci ya dauke shi sha biyu saura ko da taimakon kwayoyi an dade, yau bacci mai nauyine ya dauke shi.
Karfe wajen biyu da rabi hankalin Bilal ya kasa kwanciya, duk yanda yaso yayi bacci saiya kasa, kalaman Abbu na danne shi. Yana jin kamar ya kamata ace ya fadawa Rayyan bai kamata su kwana daki daya da Layla ba, amman sai yayi shiru ya bar shi. Abin kuma ya dame shi sosai da sosai. Tashi yayi ya fita. Hango fitilar dakin su yayi a kunne, kwanakin nan da wuta suke kwana. Yana mamakin yanda labulen dakin yake a dage. Yasan Rayyan, ko shara Bilal din zaiyi ya daga labule sai yaita masifa, quda zai shigo musu daki.
Ya rasa hadin Rayyan da qudaje, ko kwara daya yaga gaccin shi a daki sai ya fitar dashi, ko ya kashe shi hankalin shi yake kwanciya. Balle kuma sauraye, ko jiya dariya Bilal yayi kamar zai shaqe jin Rayyan din na ma sauro masifa
“Dan ubanka idan sha zakayi ba zaka sha ka wuce ba, sai kana mun ihu a kunne”
Yanzun ma dariya ya tsinci kan shi dayi. Yana karasawa dakin. Bacci Rayyan yakeyi akan tebir, ko tunanin ciwon wuya bayayi. Cikin dakin sosai ya shiga, ya dauki maganin sauro na fesawa yana dan fesa musu saboda Rayyan din. Hannu ya saka cikin net din yana janyo dayan pillow din, ya mayar ya gyara. Dan bubbuga Rayyan din yayi daya bude idanuwan shi da suke cike da bacci
“Ka sa pillow hamma, wuyanka zaiyi ciwo”
Karbar pillow din Rayyan yayi yana ajiyewa ya mayar da kan shi ya dora, idanuwan shi ya lumshe saboda baccin da yake cikin su, sai yakejin kamar yayi kwanaki baiyi bacci ba. Wani irin numfashi Bilal ya sauke yana jinjina al’amarin su. Kafin ya fice, dan shima hamma yakeyi, idanuwan shi cike suke da bacci, hankalin shine ba’a kwance ba sai yanzun.
*****
Zai iya cewa tunda safe yake tashi yayi wanka, wajen karfe hudu na safe wasu lokuttan. Yau ma da kan shi ya dora ruwa a kettle yaje ya sirka ya tashi Layla da ta dinga turo mishi baki kamar zatayi kuka. Duk da yasan babu mai fitowa sai da ya tsaya ta wajen hanyar bandakin har tayi wanka ta fito. Lokacin na shi ruwan yayi zafi, da duka kayan shi har wanda zai sake ya shiga bandakin. Yana fitowa ya tsoma wanda ya cire a wani bokitin yana zuwa ya wanke su. Alwala ya daura, saida ya kwankwasa dakin ganin Layla ta saki labulen, muryarta da alamar bacci ta amsa shi.
Hakan yasa shi ya shiga, ya sake komawa ta kudundune cikin bargo. Kai kawai Rayyan ya girgiza. Bayason jikin shi ya bushe shisa ya shafa mai, turaruka ya fesa, yana jin shi a dai-dai. Har wani shiru yake ji cikin kan shi babu wata hayaniya saboda baccin daya dan samu. Share dakin ya karayi yaji kamar ya taka kasa. Zuwa lokacin har anyi kiran sallar farko, masallaci ya fita, kafin a tashi sallah zai samu yayi raka’a biyun da yake sunna mai karfi kafin asuba. Ko da aka idar da sallar asuba ya dade a zaune cikin masallacin, ba lazumi yakeyi ba ko wani abu, kawai lokutta da dama yakan samu natsuwa a cikin masallaci.
Wani lokacin kuma kamar ana mintsinin shi haka yake so ya idar da sallah ya fita, shisa baya wasa da ranaku irin na yau. Sai da ya gaji da zaman sannan ya tashi ya fita. Dakin su ya koma, karfe takwas da rabi yake da darasi, yana nan zaune yana dan dudduba wasu abubuwan da bai fahimta ba har takwas saura, yana da biskit, da shayi ya hada yana cikin shane Layla ta bude ido, tafi mintina biyar kafin tace
“Hamma…ina kwana”
Sai da ya ajiye kofin da yake hannun shi sannan ya amsa da
“Ya jikin ki?
Taji sauki sosai, daman kwana biyun farko sunfi wahalar da ita
“Naji sauki…”
Ta furta a hankali, cigaba da shan shayin shi yayi harya gama
“Ina da lecture da safen nan”
Tashi zaune Layla tayi
“Nima haka… Karfe tara, sai mu wuce tare”
Kai Rayyan ya jinjina
“Zaki iya zuwa?”
Nade net din tayi tana sauko da kafafuwanta daga kan katifar
“Eh mana…”
Bai mata maganar taci wani abu ba, tunda yasan daga ita har Bilal basa iya cin abinci da safe haka. Shikam ko da asuba ne zaici, sai dai in bayajin yunwa. Iya abinda zai tafi dashi na ranar ya harhada ya dauko jakar shi yana kara shiryata ya saka a ciki. Ta riga da ta sake kayanta sanda ta fito, ta mayar da wancen cikin ledar da tazo da ita. Mayafin da ta ajiye akan gado ta janyo, doguwar rigace ta atamfa, mikewa Layla tayi tana duba ledar ta dauko dankwalin rigar ta ajiye. Ta karasa ta dauki ledar ruwa, fuskarta da bakinta take son daurayewa. Anan bakin kofa ta tsaya, tana jin idanuwan wani da batasan waye ba a cikin gidan yana kallonta, ko daga kai batayi ba harta karasa ta koma dakin.
Dankwalin ta daura tana rataya mayafin a kafadarta
“Muje?”
Ta cewa Rayyan, ba kwalliya bace a fuskarta, har lokacin idanuwanta da alamar bacci, amman zuciyar shi dokawa take kamar zata fito waje. Sam ya rasa yanda zaiyi da abinda yake ji akan Layla yanzun, bayason yanda take birkita mishi lissafi haka. Tare suka fito, jan dakin kawai yayi, idan Bilal ya fito ya rufe, yana da mukulli a jakar shi. Baibi takan wasu cikin yan gidan da suke ta binsu da kallo ba har suka fice daga gidan
“Hamma kana sauri”
Layla ta fadi, juyawa Rayyan din yayi, ya kamo hannunta, suka taka zuwa titi, saboda ita yau zai hau abin hawa da safe zuwa makaranta, saboda kuma bata da lafiya.