Su Rayyan ne suke makaranta, sune da karatu amman Ayya ce take ramewa saboda tunani. Duk yanda Bilal yake jaddada mata cewa lafiyar su Rayyan din kalau hankalin ta ya kasa kwanciya. Asalin abinda take son ji Bilal ba zaj fada mata, balle kuma tunda suka tafin basu dawo ba sai yanzun da akayi hutun karshen zango. Da kanta ta nemi Hajiya Dije saboda ta samu a shiga tsakanin Rayyan da Layla, harma da Bilal din. Bata da natsuwar binta wani waje ma, tace taje mata ne, tashin farko dubu sittin Ayya ta tura ma Hajiya Dije. Abinda bata sani. . .