Kwance take a cikin hostel a kan gado, ta lumshe idanuwanta, ba dan gadon yafi nata na gida ba, amman wani irin nishadi take ji yana shigar ta, nishadin da bata da kalaman misalta shi. Ta dauka ita da Zaria sai a mafarki, yanda Mami ta dauki fushi da ita har kasan ranta ta hakura da karatu a Zaria. Ta jigata, ta sha wahala, akan gwiwoyin ta da hawaye cike taf da idanuwanta ta tsugunna tana baiwa Mamin hakuri saboda bata ga abinda tayi mai zafin da zaisa Mami ta daina mata magana ba.
“Ban san sau nawa zan jaddada miki MARTABAR MU a matsayin ‘ya’ya mata ba kafin ki fara kare taki.”
Mami ta fadi tana dorawa da,
“Bance ki dubani ba, ki duba kanki da maraicin ki, yanzun mutunci ne ace kuna wannan rike junan ke da Rayyan?”
Hawayen da suka tsiyayowa Layla ta goge da hannu.
“Ni dai Mami dan Allah kiyi hakuri, nace ba zan kara ba, na daina, dan Allah kiyi hakuri.”
Numfashi Mamin ta sauke,
“In zakiyi hankali dai kiyi, dan an Abbun ku ya tambayi Rayyan din yace ba son ki yake ba…”
Duk wani abu da Mami ta fada bayan nan bai karasa kunnuwa Layla da suka toshe da kalaman Mamin na karshe ba, har kuma ta baro gidan bata samu wani nishadi ba sai yanzun da take a kwance. Kwananta hudu da wani irin zazzabi da ya wajigata. Mami bata taba mata karya ba tun tasowarta, amman kiri-kiri ranar ta tsinci kanta da karyata Mamin, saboda karta komawa Rayyan shisa tayi mata karyar da bakin shi yace wa Abbu baya sonta. Bata tsammaci ya sota ba, batama san da gaske ta daga burinta akan shi ba sai da Mami ta fada mata kalaman da taji kirjinta kamar an kunna wuta a ciki.
Kwana tayi tana kuka, da safe fuskarta kamar kwabin alkubus saboda yanda ta kumbura, Mami bata ce mata komai ba, ko wanke-wanke tanayi tana kuka haka ta karasa shi ranar. Kuma yanzun ma da ta tuno kalaman sai da taji wani irin daci ya taso mata yayi tsaye a karkashin makoshin ta.
“Mami sai dai kiyi hakuri, amman ni ba zan rabu da Hamma ba, ko ya rabu dani ni ba zan rabu da shi ba. Mayya ce, amman mayyar shi.”
Ta furta a hankali, kalmomin, “Mayyar shi,” din na zauna mata. Abin ya hade yayi mata yawa, saboda har suka bar gidan Rayyan baya mata magana, baya kiranta ya saka tayi mishi wani abu. Idan daga nesa ya hangota zai kalli wani wajen, ita kuma tsoron Mami yasa ko a waya ta kasa kiran shi. Ranar da zata koma makaranta babu kalar wa’azi da nasihar da Mami bata yi mata ba, duk da batasan me Abbu ya fadawa Mami ta yarda tabarta komawa Zaria ba. Amman tana da yakinin yana da alaka da yanda watanni shidda ne kacal suka ragewa Rayyan din ya kammala karatun shi gabaki daya.
A mota wannan karin gidan gaba ya zauna, daga ita har Bilal bai musu magana ba, Aisha ma da suka biya suka dauketa, da ta gaishe da shi Layla bata ga yayi alamar yaji ba ballantana ya amsa, muryar shi take son ji da dukkan zuciyarta, amman yayi shiru, cikin kujera ma ya shige yanda ko wuya ta dan leka ba zata iya ganin shi ba har suka sauka. Bata gaji ba dan da ta sauka ta zagaya ta bangaren shi tace,
“Hamma…”
Gilashin murfin motar ya daga yana jan shi sama ya jingina kai a jiki yanda ko fuskar shi ma ba zata gani ba. Za kuwa tayi karya idan tace abin bai mata zafi ba. Da kyar ta danne hawayen da taji suna shirin zubo mata, duk da kwakwalwar ta na son ta tirsasawa zuciyarta tuno maganar Mami, ta tauna taga ko da gaskiya a ciki taki yarda, hakan zai iya barazana da zaman lafiyarta fiye da yanda take ciki yanzun. Ko Rayyan baya son ta bai fadawa Abbu ba, bai fada ba, tana da sauran buri akan zai kalleta da fuskar soyayya wata rana, idan ma baiyi ba ya aminta da tarin soyayyar da ita takeyi mishi, ya ishe su.
Wayarta ta dauka da take ajiye a gefe jin sakonnin da suke ta shigowa. Tun a hanya an mayar da ita group daman, duk yanda taso ta daina karance-karance da takeyi sai ta tsinci kanta da kasawa, duk idan Nanaa ta turo mata sai ta karanta. Da kanta tace a mayar da ita tun tana mota, duk da wani abu a kasan zuciyar ta na son nuna mata tarin kuskuren da yake cikin hakan, yanayin da take jine ya rinjayi wancen kashedin. Gara taji da abu daya, duk da kome ta karanta din sai ta dinga hasaso Rayyan a tare da ita, cikin yanayin koma meye yake faruwa a abinda take karantawar.
Mafarkai takeyi a kwanakin nan da suka kara addabarta, kallo daya zakayi mata kaga tsantsar ramar da tayi, sai idanuwan. Amman wuyanta duk kasusuwan sun kara fitowa. Sosai taji dadin shigowa Anisa da suka rungume juna kamar sun shekara basa tare,
“Nayi kewar ki.”
Cewar Anisa tana kara rungume Layla din, sai kace tunda akayi hutu basa manne a waya da chatting.
“Nima haka Allah…tun dazun nake duba hanya.”
Layla ta karasa tana sakin Anisa, suka karasa suna zama.
“Yunwa nake ji, su Yaya zasu kawoni suka tafiyar su yawo…”
Cewar Anisa, Layla ma najin yunwa ta taso mata, tunawa tayi ko abinci bata ci ba itama, ba yanda Mami bata yi ba taki saboda tana zumudin barin gidan.
“Ko mu dafa indomie? Sai mu siyo kwai?”
Dan shiru Anisa tayi tana nazari kafin ta jinjina kai, Indomie din zatafi musu sauri akan duk wani abu da zasuyi tunani. Sai su dora a risho daya, dayan kuma su soya kwai a kai. Layla ta fita siyo musu kwan, Anisa kuma ta dora indomie din.
*****
Sosai yake mamaki idan yaji mutane na hirar wani abu da ya saka su nishadi, ko suna hirar ranakun farin cikin su. Baisan ko farin ciki shine lokuttan da Bilal kan fadi wani abu da zai saka shi dariya ba, ko kuma lokuttan da Layla zata kalle shi kamar duniyar ta babu wani abu da take gani banda shi, ko da ya bata mata raine. Akwai wani yanayi mabanbanta da zuciyar shi take shiga a duka lokuttan, amman yanda ake labarin farin ciki yana saka shi tunani sosai. Watakila shi har yanzun bai san wannan yanayin ba, kullum duniyar a cunkushe yake jinta.
Ko da yaushe akwai wani duhu a cikin kan shi, akwai wani kunci da ya zame mishi abokin zama. Akwai ranakun da yakan samu saukin kuncin idan yana tare da Bilal, yakan samu saukin shi sosai duk idan yana tare da Layla, musamman idan hannun shi yana cikin nata. A kwanakin nan ko zanen da yakan dan samu ya rage mishi cunkoson cikin kan shi ya kasa samun natsuwar yi. Ba karamin kokari yayi ba nakin neman Layla. Ba dan Abbu ko Mami ba, sai dan ita din da kanta, ba zai iya jure ganin Mami ta dake ta saboda shi ba.
Har yanzun idan ya rufe idanuwan shi yakan ga marin da Mami tayi mata, zuciyar shi kuma na zafi sosai da hakan. Saboda Layla ne yayi nisa da ita badan wani ba, in dan Abbu ne babu wani abu da maganganun shi suka kara mishi banda tunzura shi ya kusanci Layla din, a lokaci daya kuma wasu daga cikin maganganun suna nisanta shi da ita. Yanayine da shi kan shi ya saka shi a cikin rudani marar misaltuwa. Ba bacci yake samu ba, shisa tsakanin safiya zuwa wata safiyar yake yi mishi nisa matuka. Idan ya ga Bilal ya yi bacci sai ya kwanta akan bayan shi ya kalli ceiling din dakin yana tunanin da ba zai iya cewa takaimaimai na mene ne ba.
A kwanakin ko sallar daya kan tashi yayi sai jikin shi yayi matukar nauyi. Bilal dai bai fasa mishi hira ba idan ya tashi, duk da baya iya ce mishi komai. Yana dai jin dadin hirar, fiye da yanda zai iya fada. Saboda ita kadai ce yake ji ta zame mishi katanga tsakanin shi da tabin hankali. Tun sanda ta shigo cikin motar yau da zasu dawo yake jinta a wajaje fiye da zuciyar shi, sai yake jin inda maganganun Abbu suka dauke ta suka jefa yana budewa. Zai rantse yana jin idanuwanta na yawan neman fuskar shi kamar zasu huda kujerar da yake a kai su leko shi. Bayan sun sauka ma haka, yana jin yanda take kokarin yi mishi magana.
Sai take kara mishi wahalar da yake ciki, saboda tana yi kamar ita ka dai take azabtuwa da nisan da suka yi da junan su. Duk yanda yake daurewa sai da tayi mishi magana
“Hamma…”
Kawai ta furta sai da tsikar jikin shi gabaki daya ta mike, komai yana neman kwance mishi, shisa ya daga gilashin motar. Jikin shi har bari yake yi da son fita daga motar ya riketa a jikin shi, so yake ya zagaya hannuwan shi ya riketa dam, yaji duminta ko zai nutsar da hayaniyar da take cikin kan shi. Amman babu wannan damar, zai yi duk kokarin da zai iya na ganin damar bata samu ba. Sanda suka karasa gida har wani numfashin wahala ya ke saukewa. Kayan su ma Bilal ne ya shigar musu da shi.
Basu huta ba suka fara share share, har wankin su labule sai da Rayyan din yayi. Yanajin Bilal na fadin,
“Kabari a bayar a wanke mana.”
Bai saurare shi ba, saboda yana son yin wani abu da zai rage mishi tunani. Sanda ya gama duk wani aiki da zai iya takalowa kan shi har azahar ta kusa, yanayin wanka ya fita yayi sallah ya dawo. Bilal ya sai musu biredi a hanya saiya dafa musu shayi, shi Bilal din yana zaune kan gado ya bude laptop din shi, Rayyan kuma yana zaune akan kujera da kofin shayin da ya yi mishi zafi a hannu yana hurawa a hankali da iskar bakin shi cikin son ya huce.
Wani series film ne Bilal din yake kallo tun suna gida mai suna “Suits”. Shi kallo ba damun shi ya yi ba, idan Bilal ya saka wata rana sunayi tare, tunda ya fara sukan kalli wasu episodes din tare. Duk dai inda ya samu Bilal din na kallo shima dorawa yakeyi. Yanzun ma idanuwan shi ya natsa kan screen din laptop din suna kallon.
“Trevor din nan ba abokin Mike bane wai?”
Rayyan ya tambaya yana kurbar shayin shi, juyawa Bilal yayi saboda yana son tabbatar da cewa Rayyan din magana yayi bayan satikan daya dauka yana azumin yin maganar.
“Abokin shi din nan da suke daki daya”
Rayyan ya sake fadi ganin kamar Bilal bai gane tambayar shi ba, idanuwa Bilal ya runtsa yana bude su akan Rayyan. Baisan yana rike da wani numfashi ba sai yanzun daya sauke shi. Sosai abinda duk yake damun Rayyan din yake ci mishi zuciya. Yayi tambayar duniya Rayyan yayi banza ya kyale shi, har fushi yayi ya gaji ya sauka da kan shi. Yakan dauki kwanaki biyu batare da yace komai ba, amman bai taba daukar wannan kwanakin shiru haka ba.
“Dan Allah Hamma karka sake tsoratani haka… Ko ba zan iya taimaka maka ba, ko banda maganin damuwar ka idan ka fadamun zan saurara. Wasu lokuttan kana bukatar wanda zai saurari matsalarka ne saika sami saukin ta…”
Idanuwan Rayyan din na kan laptop har lokacin yana kuma shan shayin shi a nutse, yaji duk wani abu da Bilal ya fadi.
“Shine, abokin shin nan ne.”
Ya fadi maimakon amsa Bilal din, kai Bilal ya jinjina mishi, sanin in dai ba wannan hirar da Rayyan ya fara ba, sam ba zai saurari wata daban ba.
“Shi ne fa…”
Ya tabbatar ma Rayyan da ya girgiza kai.
“Yasa bana son mutane, har kasan raina zan yafe komai banda cin amanar mutanen dana yadda dasu.”
Dariya Bilal ya yi.
“To a duniya waye zaici amanar ka Hamma? Da wa ka yarda?”
Dan jim Rayyan ya yi, akwai tarin abubuwa da mutane suke da su da bayaso sam shisa yake zabar kadaici akan tarayya da su.
“Kuma idan wani yaji kana maganar mutane saiya dauka ba daga jinsi daya kuka fito…”
Kafadu Rayyan ya dan daga.
“Kai…”
Ya furta yana sa Bilal kallon shi
“Na yarda da kai da Layla…”
Rayyan ya yi maganar muryar shi can kasa yana dorawa da,
“Sai Abbu da Ayya.”
Duk yanda bayajin kusanci da su, yana jin ya yarda dasu, basu taba cutar da shi ba, basu taba mishi karya ba. Shisa ya yarda dasu, baya son karya da dukkan zuciyar shi, ba kuma ya son cin amana kamar yanda ya fadi. Yanzun bashi Trevor yaci amana ba, amman har ran shi yake jin abin, mu’amala da mutane babu komai a cikinta sai wahala.
“Mu din kenan ba za’a yafe mana ba?”
Bilal ya tambaya yana murmushi, kai Rayyan ya girgiza mishi, yana saka idanuwan shi a cikin na Bilal din.
“Ba zai yafu bane…”
Yanayin da yayi maganar na saka wani abu tsirgawa Bilal din. Shiru ne ya ziyarci dakin suna maida hankalin su kan film din da suke kallo, wannan karin kowa da abinda yake tunani a cikin kan shi.
*****
“Hamma…”
Layla ta fadi cike da farin ciki tana zagaya hannuwanta a bayan shi ta rike shi. Idanuwan shi Rayyan ya lumshe yana jin wani irin yanayi da ba zai misaltu ba, sosai a watanni shiddan sa suka wuce mishi a hankali yaso nisanta da Layla, amman ya kasa. Yana bukatar ta a kusa da shi in har zai sami natsuwar kammala jarabawar zangon. Satin farko da suka dawo makaranta ta zo wajen shi, inda ya saba zama. A gefe ta zauna ba tare da tace mishi komai ba. Sun kai mintina arba’in a zaune kawai. Shiru ne da yake cike da ma’anonin da basa bukatar kalamai. Shiru ne daya samar mishi da natsuwar da bai yi zato ba.
Da zata tafi, jakar shi ya bude ya zaro jacket yana mika mata, babu musu ta amsa ta saka a jikinta. Ita kanta ta samu natsuwa, da gangan a ranar ta saka doguwar rigar. Tana son ko yaya ne ta ga wani kusanci da yake a tsakanin su tunda baya mata magana. Haka taci gaba da zuwa su zauna shiru kawai, a ranakun da tasan yana azumi takan kai mishi abinci har gida. Sau biyu yana hanata zama, tana ajiye kwandon da ta jera kuloli Rayyan yake mikewa alamar su tafi. Shisa ta daina sallamar mai napep ko mashin din daya kawota, tana ajiyewa itama take tafiya ba saiya koreta ba.
Ranar da taji kamar zata mutu idan batayi magana da shi bane ta dauki waya ta kira shi, yana dagawa wani irin kuka ne ya kwace mata da yasa Rayyan din lumshe idanuwan shi, yanajin wani abu na budewa a zuciyar shi
“Layla…”
Ya kira da wani irin yanayi daya kara tunzura kukan da takeyi.
“Ban san ya zanyi ba… Ban sani ba wallahi.”
Ya fadi yana sauraren sautin kukanta da yake kara mishi hayaniya a cikin kan shi. Kamar katinta ne ya kare wayar ta yanke, kira ya kai biyar yayi bata dauka ba, yaso ya share, har kwanciya yayi, sai ya kasa. Idan kuka yake so tayi zai bata dalili, baya son wannan kukan nata. Mikewa ya tsinci kan shi dayi yana saka takalma, gani yake idan ya taka ba zai isa inda take da wuri ba shisa ya hau mashin. Sanda ya karasa bakin hostel din, ya mata kira yafi goma kafin ta daga tana fadin
“Hello…”
Muryarta na fitowa daga can kasan makoshi.
“Layla…”
Rayyan ya furta yana lumshe idanuwan shi, abinda yake ji yaso yayi kokawa da shi ya kasa.
“Ki fito… Ki fito in ganki.”
Ya karasa hadi da sauke wayar daga kunnen shi. Sanda ta fito hula ce kawai a kanta, bai san ya zai kira abayar jikinta ba, ta dai mishi kyau saboda farar hular da ta saka. Baya son hada ido da ita bai gama karewa fuskarta kallo ba, ji yake kamar ya dade bai ganta ba, wata irin kewarta ke danne shi.
“Hamma…”
Layla ta kira sunan shi daga kasan zuciyar ta, hannu Rayyan din ya mika mata, da sauri take takawa ta karasa tana kama hannun na shi, ta sa kafa ya hankade kashedin Mami da rokonta da yake shirin yi mata katanga da Rayyan din. Shi kam babu abinda yake ganewa, babu abinda yake gani a duk fadin wajen banda ita, babu abinda yake ji banda son hada jikin shi da nata, a hankali yake jan hannun nata da yake rike da shi harya hadata da kirjin shi inda yake jin kamar ya jima a cikin dokar daji, yanzun daya riketa ne ya iso gida.
Bai taba furtawa kan shi yanda ko ina bako bane a rayuwar shi banda wannan yanayin, har Bilal wani lokacin yakan ji kamar bako ne a wajen shi, amman banda Layla, tun ranar farko daya fara hada idanuwa da ita suka firgita shi yasan ita din ba bakuwa bace a yar karamar duniyar shi da take cike da tarin hargitsi, ta jima a tare da shi, tun kafin ya santa kaddara ta hada hanyar su, tun kafin ya ganta yaga halitta mai kalar idanuwanta.
“Hamma.”
Layla tayi maganar da alamar kuka da wani shauki a muryarta tana kara shigewa jikin shi. Ita kanta abinda take ji ba zai misaltu ba, kalar duk soyayyar da take gani daban take da wadda takewa Rayyan. A jikin shi kawai taji ta yanzun, amman launin duniyar gaba ki daya ya sauya mata. Idanuwanta a lumshe take, bata taba ganin kyawun duhun da yakan baibaye kwayar idanuwanta bayan ta rufe shi ba sai yanzun, saboda a cikin duhu take yawo harta isa wani waje da ya haska mata Rayyan a tsaye, tana kallon shi da zuciyarta da take cike taf da soyayyar shi
“Shhh…”
Rayyan ya fadi yana kara riketa a jikin shi, su duka kamar sun gaji da yawon neman juna har sun fitar da rai kafin su hadu haka suke ji. Da kyar ya iya dagota daga jikin shi yana kallon fuskarta batare da ya hada idanuwa da ita ba, duk da yau tana son ganin kwayar idabuwan na shi, ko dan taga idan yanajin wannan yanayin da take ji, a karo na farko ya sumbaci goshin ta.
“Na yi duk kokarin da zan iya. Ban san ya zanyi nisa da ke ba.”
Rayyan ya yi maganar ba tare da yasan ko ta fahimce shi ko itama tana jinta cikin kalar rudanin da yake ji ba.
“Kar kayi mun nisa, dan Allah Hamma ka daina kokarin yi mun nisa.”
Numfashi Rayyan yaja yana fitarwa. Tare suka taka rike da hannun juna, har suka samu inda suka zauna. Sun fi awa a haka, hannunta yana cikin na shi, har sai da yaga dare na karayi tukunna. Daya rakata kuwa da kyar ya bar wajen, kamar ta bashi hannun ya tafi da shi, bai karasa gida ba ranar natsuwar daya dan samu a tare da ita na kwacewa komai yana dawo mishi sabo. Daga ranar ya sake budewa kan shi kofar da ya sha matukar wahala kafin ya kulleta. Bayan nan Bilal yayi mishi magana, yayi da lallami, yayi da fada, ya yi da tashin hankali kamar zai cinye shi akan rike Layla ya rasa yanda zai ya bari.
Itama Layla a nata bangaren hakane, in da tasan yanda zata daina taba shi da tayi, ko dan yanda taga hankalin Mami ya tashi, amman bata sani ba, Mami take roko da ta yafe mata, ta fahimci ba laifinta bane, soyayya ce take rinjaye akanta a kowanne lokaci, zuciyarta take riritawa fiye da martabar ta da Mami take yawan kira mata a duk wayar da zasuyi. Ta dai ji tsoro na fitar hankali randa Bilal ya sameta har hostel bayan ya kirata yana fada mata magana yake so suyi, bata kawo komai a ranta ba sai bayan sun sami wajen zama ya fara da cewa.
“Ban san ta ina zan fara ba, na dai san tuntuni ya kamata in miki magana, in muku magana, sai na zabi in yiwa Hamma duk da na yi a kurarren lokaci, nayi kokarin gyara kuskuren yaki…”
Sai lokacin zuciyarta ta fara bugawa sosai da sosai, musamman da Bilal yaci gaba da fadin,
“Abbu ya bani amanar ki, Abbu yace in kula da ke, na kuma mishi wannan alkawarin. Gashi na kasa cikawa, ranar farko da na ga kin rike Rayyan ya kamata in tsawatar miki, banyi ba. Kin san illar hakan, kin san rashin kyautuwar hakan Layla…ban san ya zan miki fada ba, amman zan rokeki, idan ina da wata daraja a idanuwan ki za ki bari, zaki jini tunda shi yaki jina.”
Lokacin idanuwanta sun cika taf da hawaye, sai da ta saka su cikin na Bilal kafin hawayen nata su zubo.
“Ina son shi.. Hamma Bilal ina son shi.”
Ta fadi da dukkan gaskiyarta, a karo na farko tana furtawa wani soyayyar da takeyiwa Rayyan din. Cikin sonyin amfani da ita dan ta zame mata hujjar da zata isa ta bata damar rike shi, tana kallon yanda Bilal din yake fitar da numfashi a hankali kamar yana cikin tashin hankali, sai dai itama a cikin shi take.
“Shi sa zaki daina, saboda kina son shi. Ba zaki so ya ci gaba da tarawa kan shi zunubi ba.”
Bilal ya fadi cike da son ta fahimce shi, kai girgiza tana mikewa kawai tabar mishi wajen. Kuka tayi sosai ranar, da wayarta tayi kara ko bata kira ba sai gabanta ya fadi, sai tayi tunanin ko Bilal din ya kai karar su gida ne. Bata san me kuma zata cewa Mami bayan karyar da ta shirga mata na cewa Rayyan din baya kulata ba. Kuma da alama Mami ta yadda, bata dai fasa jaddada mata muhimmanci kare martabar ta ba. Kamar yanda itama bata gaji da amsa ta da,
“In shaa Allah.”
Ba, bata san ya suke so tayi ba, daga Bilal din har Mami, da alama basu san yanda soyayya take ba, basu san yanda duk lokacin da wanda ka ke so yake a kusa da kai baka muradin komai banda kaji ka rike shi koyaya ne, ka kara hada kusancin da kake ji. Musamman idan wanda kake so din Rayyan ne, Hammanta da emotions sukewa wahalar nunawa, Hammanta da bata da tabbacin zai furta mata wasu kalamai da suka danganci soyayya. Amman idan yana jinta a jikin shi sai take ganin a hankali zata raunana zuciyar shi, zata saka kalaman da take son ji su kubce mishi.
Balle takan karanta girman tasirin mace a wajen namiji, ko sarki ne akan ce a gaban mace shi din bakomai bane. Zuwa yanzun kuma tasan kalar halittar jiki da Allah yayi mata, maza da yawa a makarantar idanuwan su a kanta suke. Bata da wani makami akan Rayyan banda jikin da shima duk baudadden halin shi taga yana so, ko hannun shi ta rike tana kallon yanda yake sauri ya dumtse shi cikin na shi kamar yana tsoron karta subuce mishi. Bilal da Mami ba zasu gane wannan bace kawai hanya daya da zata iya mallaka mata Rayyan.
Tana ganin yanda Bilal ya kalleta bayan kwana biyu da rokon shi, yanda ta hada ido da shi cikin ban hakuri kafin ta rike Rayyan din. Sai mikewa yayi yana bar musu wajen,
“Hamma Bilal zai fadinma Abbu bamu daina ba.”
Layla ta furta muryarta na rawa tana dorawa da.
“Ya mun magana, yace in daina rike ka, Hamma ban san ya zan fada mishi ya gane ba. Dan Allah kayi mishi magana karya fada a gida. Saboda Mami.”
Sake riketa Rayyan yayi a jikin shi, shima din baisan ya zai fadawa Bilal ya fahimta ba, shisa bai taba amsa shi ba. In da zai iya daina rike Layla din daya bari ko dan yanda Bilal yake mishi tashin hankali a kai. Amman bai sani ba, sam baisan yanda zai fara bari ba. Hakan zaiyi dai-dai da nisa da yar natsuwar da ya samu. Yana bukatar wannan natsuwar, tana daya daga cikin katangar da take tsakanin shi da tabin hankalin da yakan ji a kurkusa wasu lokuttan. Haka suka rarrafa sukayi watanni shiddan daya kawo su inda suke tsaye yanzun.
Dan Layla tafi awa biyu a tsaye gaban ajin su tana jiran Rayyan din ya rubuta jarabawar shi ta karshe a ranar ya fito. Kuma da alama bai tsammace ta ba, tana rike da shi din tace,
“Congratulations…”
Dan murmushi yaji yana shirin kwace mishi, lokacin daya kama hannunta yana zagayo da ita, kewar shi take ji tana tunanin yanda makarantar zata yi mata fadi idan baya ciki, amman zata danne komai yau ta taya shi murnar kammala makarantar shi lafiya. Wani dan ajin su ta gani yazo wucewa da rigar da daliban da suka kammala karatun su kan saka dan a dauke su hoto, kuma ya kalleta har da dan murmushin shi.
“Ko zan iya aron rigar hannun ka na yan mintina dan Allah?”
Murmushin shi ya fadada, yana mikawa Layla da take mishi kallo cike da godiya, tana saka Rayyan kama dayan hannunta ya rike yana ma saurayin wani irin kallo.
“Na san yarinyar ka ce.”
Saurayin ya fadi yana wuce su. Duk wanda yake a ajin su Rayyan din, koma department din yasan shi da Layla, wanda suke burgewa da yawa, wanda kuma suke zagin su ma haka. Wasu na musu kallon masu dace a soyayya, wasu na musu kallon tantiran marassa kunya. Duk da haka rayuwa take tafiya, mutane basa taba rasa abinda zasu fada a kanka. Balle kuma Rayyan da Layla da suka basu abin magana a kai, a gaban kowa suke rike juna kamar su ka daine a filin wajen, kamar ba yaran Hausawa tarbiyyar musulunci ba.
“Ni fa ba zan saka ba.”
Rayyan ya fadi yana kallon rigar hannun Layla din.
“Dan Allah Hamma… Dan Allah.”
Take furtawa tana jan hannun shi da nata yake ciki, bai musa ba yake binta, basu kai da barin wajen ba Bilal ya karaso, hannun Layla da yake cikin na Rayyan din yabi da kallo, shima a watanni shiddan nan duk yayi zuru-zuru. Abinda wasu zasu alakanta da karatu, kusan harda karatu, amman baifi kaso ashirin ba, tamanin da doriya Layla da Rayyan ne. In da zai iya bude bakin shi ya fadawa Abbu a tsawatar musu zaiyi, amman wata murya na fada mishi kishi ne yake saka shi wannan tunanin ba girman amanar da Abbu ya bashi ba.
Sanda duk zai ga Rayyan da Layla a tare, tana mishi murmushin nan kamar zata iya tsayar da duniyar kacokan domin Rayyan idan tana da damar haka sai wani abu ya bude a kirjin shi. Amman ranar da yaji kamar kirjin na shi ya rabe gida biyu shine ranar fa ta saka idanuwan ta cikin nashi tana fada mishi yanda take son Rayyan, tana maganar kamar shine dalilinta na rike shi, dalilinta na komai. Har jiri yake ji sanda ya karasa gida, daren ranar salloli ya kusan kwana yanayi, bai san da gaske soyayyar Layla a zuciyar shi mai girma bace sai da yaga digar hawaye a cikin sujjadar shi yana neman sauki a wajen wanda ya halitta mishi zuciyar har ya darsa bugunta da soyayyar Layla.
Banda wajen Aisha babu inda yake samun sauki, kamar kaddara ta san zai shiga wani halin da zai bukaci taimakon Aisha a cikin shi shi yasa ta hada hanyar su.
“Hamma kace ya saka rigar nan ayi mishi hoto dan Allah.”
Layla ta cewa Bilal din tana katse mishi tunanin da yake yi.
“Ka saka ko dan tarihi, kayi abu daya yau da zai nuna da gaske kayi makarantar nan ba siyen takardun kayi ba.”
Bilal ya karashe cike da tsokanar da yaso ta dan washe mishi kishin daya taso mishi, amman hakan bai faru ba. Rayyan din dai ya yarda ya saka rigar. Sun danyi hotuna, kafin suka tafi gida dan Rayyan na kiran kan shi na ciwo. Layla hostel suka rakata tukunna. Bilal na kula da kalar kallon da take yiwa Rayyan, kamar tana son daukar iya hotunan shi da zata iya a cikin makarantar kafin ya tafi, sai ya ji kamar ya sama mata sauki ta hanyar fada mata plan din Rayyan din.
“Ni in dai zan samu bautar kasar da zanyi anan Zaria ko Kaduna nake so.”
Ya fadi kamar daga sama kwanaki yana saka shi tambayar.
“Saboda me?”
Kafadu Rayyan din ya dan daga mishi, duk da a idanuwan shi yake ganin Layla ce baya son yayi nisa da ita. Addu’a yake da dukkan zuciyar shi kar Rayyan din ya sami abinda yake so, ya kamata ya yi nisa da Layla, ya taimaka mishi yayi nisa da ita ko zai saukaka mishi jin amanar Abbu da bai rike ba, ko zai daina ganin yanda yake raba zunubin duk wani abu da zasu yi shi da Layla din.