A Zaria yai zaman shi, babu yanda Bilal bai yi da shi ba.
“Ka zo mu tafi gida. Idan muka yi sati daya sai mu dawo. Ko dan Ayya…”
Kai Rayyan ya girgiza mishi. “Sai sun ganni zan musu laifi. Ka barni Bilal, ka cikani da surutu.”
Shine amsar daya bashi, duk wata magana da Bilal din yayi bayan nan bai ko kalle shi ba ballantana ya amsa. Yana kokarin kare Layla ne iya yanda zai iya. Idanuwan Mami ko Abbu ba zasu hana shi riketa ba idan ya tashi. Ko dan Abbu ya nuna baya so, akwai abinda zai tunzura shi ya rike Layla a gaban Abbu, abinda har yanzun ya kasa gane kan shi, yana fahimtar yanayin mutane tun kafin ya karanci fannin, shisa baya son su. Amman ya kasa fahimtar kan shi, ya kasa gane abinda yake damun shi.
Ya sha cin karo da abinda ake kira “Depression” a turance, yanzun haka yana kan magungunan shine da basayi mishi aikin komai banda kara mishi kuncin da yake ciki. Zuwa yanzun ya hakura, ya saduda da cewa akwai wani likita da zai mishi maganin matsalar shi, ko zaima fahimceta. Ya dai san katangar da take tsakanin shi da tabin hankali bata da kauri. Shisa ya zabi zama a Zaria, shi zai dauki duk wani surutu da za’ayi. Layla ba zata dauka ba, baya son kukanta, baya son ganin hawayen da bashi bane dalilin su a idanuwanta.
Sam ba zai iya zama a cikin gida daya da ita yayi mata nisa ba. Zaman shi a Zaria shine saukin su dukan su. Kuma ya ma tsaya ya karasa project din shi a satika shiddan da aka bayar ya tattara ya basu yasan ya gama. Su yake jira, ya tafi bautar kasa abin shi. Duk da Ayya ta kira shi a satin farko, sallamar da tayi ya amsa yana yin shiru.
“Shine baka zo ba ko Rayyan? Yaushe rabon da in gan ka? Baka tunanin idan kai baka kewata ni zanyi taka?”
Akwai wani yanayi a muryarta a ranar da yasa shi fadin,
“Ina abune haka Ayya…”
Yanda ta ce,
“Hmm…”
Sai da yaji wani iri, kafin ta dora da,
“Allah ya taimaka ya tsare.”
Bai iya amsawa ba harta kashe wayar, daya sauke daga kunnen shi bin wayar ya yi da kallo, lokutta da dama yakan nemi kusancin daya kamata ace ya kasance a tsakanin mahaifiya da danta a tsakanin shi da Ayya ya rasa. Sosai yake so yaji wannan kusancin, yakan ga Bilal na binta da kallo kamar babu macen da zata zamana da muhimmanci, kima da daraja a idanuwan shi kamarta, zai rantse murmushin da Bilal kan yiwa Ayya bai taba yi mishi irin shi ba. Akan fuskar shi zaka ga tsantsar kaunar da yake yi mata a shimfide. Ko a waya ta kira shi, kafin ya daga Rayyan ya san ita ce, saboda yanda fuskar shi take canzawa gabaki daya.
Ko ran Bilal a bace yake idan Ayya ta kira shi sai yayi murmushi, karshen bacin ran kenan a wasu ranakun. A tare da Bilal yake ganin kaunar daya kamata ta kasance a tsakanin shi da mahaifiyar shi. Zai karya idan yace abin baya mishi wani iri, sosai abin yake ci mishi rai, bambancin da yake tsakanin shi da sauran mutane mai girma ne. A tsayin satikan su kanyi magana da Layla, rannan ma tace mishi,
“Dan Allah Hamma ka siya babbar waya.”
Tun kafin ta karasa maganar ma yake girgiza kan shi.
“Um um.”
Ya furta.
“Dan Allah, za muna chatting fa.”
Numfashi ya sauke yana sake furta,
“Um um.”
Jin ta fara cika mishi kunne yasa shi fadin,
“Idan kika dameni zan kashe wannan in ajiye.”
Sallama tayi mishi da sauri tana katse kiran, sai da yayi murmushin da bai bayyana akan labban shi ba, a cikin kan shi kawai ya tsaya.
“Mayya… Mayya ta.”
Ya tsinci kan shi da furtawa. Ranar da suka dawo kuwa bata yarda Bilal ya kaita hostel ba, da yake wannan karin daga ita sai shi suka dawo. Aisha bata samu dawowa a satin ba, Mamanta tana asibiti, tafi so taga jikin ya kara warwarewa tukunna ta samu natsuwar dawowa makaranta. Bacci ma ta sha a mota har suka isa Zaria din. Shisa ta ga saurin tafiyar, kewar Rayyan take yi har cikin kasusuwan jikinta. Ko da wasa a satikan da tayi a gida batayi maganar shi ba, Mami ta tambayeta ya yake sau daya ta amsa da,
“Ban sani ba Mami, Hamma Bilal zaki tambaya…”
Kuma da gaske a lokacin bata sani din ba tunda kwana biyu jujun ya motsa baya daga wayarta. Kuma da alama Mamin ta karanci gaskiyarta shisa tayi shiru. Tun daga soron gidan take kiran.
“Hammaaa!”
Harta karasa ciki inda ta ga Rayyan tsaye a bakin kofa yana kallon ta, sai ta ga kamar gashin fuskar shi ya kara cika yana kara mishi wani kwarjini da taji har a zuciyarta.
“Hamma.”
Ta kira wannan karin da tarin kaunar shi a muryarta tana takawa ta karasa inda Rayyan yake tsaye ko motsi baiyi ba. Kallon ta yake yi, sai ya ga kamar ta kara girma, ko kuma yanayin rashin makaranta ne, zai iya yiwuwa dadewa da yayi bai sakata a idanuwan shi bane kuma. Amman wani irin abu ne yake motsa mishi da ganinta. Ba zaiyi karya ba yayi kewarta sosai. Duk wani zane da yayi a satikan abune daya dangance ta, idan ba fuskarta ba, wani abu nata, wata jaka da zai iya tunawa, wani takalmi nata daya gani, ko duk wani abu da zai tuna mishi ita.
Hannun shi ya mika mata da ta kama yana karasa jan ta kusa da shi, ya saka dayan yana rankwashin ta,
“Wayyo Hamma, me nayi maka?”
Ta furta tana turo labbanta hadi da murza wajen daya rankwasa din,
“Kira goma saboda mayya ce ke. Ina sallah waya namun ihu a kunne.”
Dariya Layla tayi.
“Ina ta kewar ka shisa.”
Wani rankwashin zai sake kai mata ta kauce tana dariya. Kai kawai Rayyan ya girgiza.
“Ina ta so in gan ka na roki Hamma ya kawoni.”
Kai ya jinjina yana saka takalma a kafafuwan shi.
“Naji muje.”
Ya furta yana jan hannunta. Saboda ba karamin kokari yake ba, ba iya hannunta kawai yake son rikewa ba.
“Ba kai kadai zunubin yake tararwa ba Hamma, har da ita…idan kai ka roki yafiyar Allah wanne tabbaci kake da shi tana wannan tunanin?”
Sosai kalaman Bilal din sukayi mishi tsaye, suka kuma tsorata wani abu a tare da shi. Bayason wani abu ya sami Layla saboda shi. Babu kalar fadan da baiwa kan shi ba a satikan nan. Amman yana ganinta komai ya kwance mishi sai da yaji hannunta cikin na shi sannan ya dan nutsu. To a kirjin shi yake son jinta, idan tana tsaye kuma yaci gaba da ganinta abinda zai faru kenan. Shisa ya kama hannunta, gara Bilal ya mayar da ita a hostel. A soron gidan yai tsaye yana sakin hannunta
“Tam. Bye”
Ya fadi yana shirin juyawa. Ta gefe Layla ta rike shi a jikinta, sai da ya sauke wata siririyar ajiyar zuciya, kafin ya tureta yana fadin,
“Mayya…”
Murmushi tayi kawai, a hankali ya korar mata ciwon da sunan yake yi mata. Ta gama yarda akan shi din da gaske mayya ce ita. Babu wani abu da zaiyi wanda zai rabata da shi kuma. Juyawa yayi, sai da ya bace ma ganinta sannan ta fice itama, inda tabar Bilal zaune a mota nan ta same shi, ta bude ta shiga ya juya yana kaita hostel.
*****
Baisan me Bilal ya fadawa Abbu ba, bayan sunan shi ya fito a Bauchi, Wailo NYSC orientation camp din da yake a karamar hukumar Ganjuwa. Ana gobe zai tafi ne yace mishi
“Ga lambar da Abbu ya turo, ka kira shi idan kaje, yasan wajen da zaka biya kudin…da duk yanda za a sauya maka waje zuwa inda kake so.”
Bilal din ya karasa yana daukar wayar shi ya saka lambar a ciki. Saving yayi zuwa Bappa, kamar yanda ya fada mishi sunan. Sanin halin Rayyan ya saka Bilal kiran Bappa da tashi lambar sukayi magana. Rasa yanda zaiwa Bappa bayani ya gane yayi, a daburce yace,
“Zan turo maka da lambar dan uwan nawa. Dan Allah sai kayi hakuri da halin shi, wani irin baudadden mutum ne.”
Dariya Bappa yayi sosai.
“Karka damu, ba matsala in shaa Allah.”
Bilal yaji dadin yanda daga yanayin muryar Bappa ya gane cewa yana da kirki. Duk da zai wahala Rayyan bai kure hakurin Bappan ba.
“Dan Allah kana shiga Bauchi ka kira shi. Ka ga da ka iya tuki sai ka tafi da mota.”
Harya gama duk surutun shi in da yake Rayyan bai kalla ba. Shi babu motar da zai dauka ko da ya iya tuki. Balle bai iya ba, ba yanda Bilal baiyi ba ya koya mishi, amman yaki mayar da hankali. Ran daren da zai tafi har cikin makaranta ya shiga wajen Layla ya ganta.
“Yaushe zan kara ganin ka?”
Ta tambaya da wani yanayi a muryarta da yasa ka shi fadin,
“Idan kika mun kuka ba zan dawo ba.”
Runtsa idanuwanta tayi tana kokarin mayar da hawayen da suke shirin zubo mata.
“Zanyi kewar ka da yawa…”
Shiru Rayyan yayi suna cigaba da tafiya, ganin ya fara hango gate kuma sanin ita kadai zata koma yasa shi cewa,
“Ki koma haka.”
Kai ta girgiza mishi tana kasa Magana.
“Zan kira ki, zamuyi waya.”
Ya fadi, idanuwanta ta sauke cikin na Rayyan tana saka zuciyar shi wani irin dokawa, da sauri ya cire na shi yana tsayar dasu akan fuskarta.
“Ba zaka kirani ba, haka kake cewa ko da yaushe, ni na san ba zaka kira ba.”
Ta karasa muryarta na karyewa.
“Zan kira ki.”
Ya maimaita daga zuciyar shi wannan karin. Ba kiran nata bane baya sonyi wasu lokuttan, baisan abinda zaice mata bane, har yanzun bai fassara alaqar da take tsakanin su ba, bai shirya bata suna ba, yana da tarin abubuwan da yake son ya dai-daita tukunna yayi wannan tunanin. Ba yanzun ba, zuwa nan gaba.
“Ki wuce kafin in watsa miki mari Layla.”
Rayyan ya fadi yana cire hannunta daga cikin shi. Kamar ya bata damar da zata rungume shi, matse shi tayi a kirjinta kamar tana son dibar duk wani dumi na shi da zata iya ta adana tana daukowa a lokuttan da baya nan. Hannun shi daya ya zagaya ya dan dafa bayanta. Wani abu yake ji yana kwancewa a zuciyar shi da baisan mene ne ba, sun kusan mintina uku, kafafuwan shi da yaji kamar suna neman yin sanyi ya saka shi dagota daga jikin na shi.
“Dan Allah ka kirani.”
Kanta ya mangare yana sata murza wajen da hannu.
“Ki wuce Layla.”
Ya fadi, labbanta ta turo gaba cikin yanayin da ya tsirga mishi yana saka shi dauke idanuwan shi daga kan fuskarta kafin yayi abinda zai dade yana juyi a kai. Juyawa Layla tayi, sai da ta dan bada taku hudu a tsakanin su, wata irin bugawa zuciyar ta takeyi kamar zata fito daga kirjin ta saboda hukuncin da taji zuciyarta ta yanke mata lokaci daya, tukunna tace
“Ina son ka, karka so kowa Hamma… Ni nake son ka, na riga kowa farawa, na riga kowa fadi.”
Wani irin numfashi take saukewa tana dariya ganin yanayin da yake kan fuskar Rayyan din, wayarta ta daga da sauri tana shiga Camera ta dalle mishi fuska, ya dago hannu, kafin ya kare ta dauke shi, tana kara daukar wasu sun kai kala biyar da sauri.
“Layla…”
Rayyan ya fadi tana takawa cikin kokarin hade space din da yake tsakanin su
“Ina son ka Hamma Rayyan… Ina son ka da yawa.”
Ta fadi cike da wani irin nishadi da baisan lokacin da murmushi ya kwace mishi ba, da gudu Layla ta juya tana dariya.
“Mayya.”
Ya furta a hankali zuciyar shi na tsalle kamar zata rabo da kirjin shi, ga wani dumi da gabaki daya jikin shi ya dauka da kalamanta.
“Mayya… Mayya ta.”
Ya sake fadi wannan karin yana dora hannun shi akan kirjin shi. Sai da ya daina ganin Layla tukunna ya juya. Murmushi yake har kumatun shi sun fara amsawa da rashin sabawa. Bai san mene ne asalin farin ciki ba, amman idan aka tambaye shi ko ya taba jin shi, tabbas zai ce eh, idan bai gajiya da surutun ba zai bada labarin wannan yanayin da yake ji yanzun. Zai bada labarin ranar da yaji zuciyar shi ta kumbura taf ta cika kirjin shi, ranar da murmushin shi ya fito daga wani bangare na zuciyar shi.
Har yaje gida kalamanta na amsawa a cikin kunnuwan shi. Ko dan babu wanda ya taba cewa yana son shi, ko da wasa kuwa, ya sha jin ana fadawa Bilal, ba kuma Aisha ba, har su Rukayya idan suna waya ya saka a speaker yakan ji tace,
“Ina son ka Hamma na.”
Wasu lokuttan Bilal kan amsa da,
“Fada mun me kike so kawai Ruky.”
Amman ko da tana son wani abu ne da gaske take nufin kalamanta. Yaune karo na farko da yaji an ambaci “So” kuma an hada da sunan shi a ciki, sai yaji ya natsar da wani abu a cikin kirjin shi, har haske yaji a tarin duhun da yake cikin kan shi.
“Na gode… Na gode Layla.”
Ya furta a hanyar shi, har yaje gida yana jin shi sama-sama. Bilal yayi bacci sanda ya karasa, shi sai da ya watsa ruwa tukunna ya fito robar ruwan da Bilal ya shigo da ita, ko fasawa baiyi ba, shi ya fasa ya sha rabi ya kulle ya ajiye, dauka ya yi, kwayoyin shi ya dibo, ya ga alama idan ya zuba su a lemo ko ruwa sunfi saka hayaniyar da yake ji yin shiru. Ya jefa a ciki ya mayar yana kullewa. Da yake ba wani sake dandanon ruwan sukeyi ba, da wahala kaji su akan harshen ka, da robar a hannun shi ya karasa ya daga net ya shiga. Ajiyeta yayi a kasa ya gyara net din yana kwanciya. Babu abinda yake dawo mishi banda kalaman Layla, baima sha ba bacci mai nauyin gaske yana dauke shi, baccin daya manta rabon da ya same shi ta dadin rai.
Yayi wanka kafin su tafi masallaci daman, sanda suka dawo yawanci duk an tashi ana ta hada-hadar shirin tafiya makaranta, masu lakcar safe da masu shirin wani dan test da za’ayi, ko suna son shiga makaranta da wuri dan su kwafi assignment duk anata sauri. Bilal bai samu ya yi wanka da wuri ba.
“Da na sauke ka tasha sai in dawo”
Bilal din ya fadi ganin kamar yana batawa Rayyan din lokaci shi da yake da tafiya a ranar. Shikuma yafi son Bilal din ya shirya gabaki daya, idan ya sauke shi tasha daga can makaranta zai koma kai tsaye ba saiya wani dawo gida ya fara wani shirin ba, idan shine ba zai iya wannan ba. Wani irin sama-sama yake jin shi, ko dan hutun daya samu ne daga bacci, yana bude ido kalaman Layla ne suka dawo mishi suna saka zuciyar shi cigaba da dokawa, har zuwa yanzun kamar ana kara mata gudu, yanayi ne da bai taba jin irin shi ba, har sai da yai tunanin anya lafiya, kamar bugun da zuciyar shi takeyi ya wuce iya kalaman Layla, kamar tana son sanar da shi wani abu mai girma da yake shirin faruwa da shi. Lokaci zuwa lokaci yakan sauke ajiyar zuciya a hankali.
Aikam sanda Bilal din ya gama shiryawa har karfe bakwai da kusan kwata. Rigace fara ya saka sai wandon jeans bula, hutun da aka dawo na karshen nan ya tara kasumba irin ta Rayyan, kalar gyaran fuskar shi da askin yayi, ya rage sumar shi kasa sosai sosai shima. Ranar da ya shiga dakin Ayya kuwa sai da tace,
“Oh Allah na Bilal.”
Dariya yayi sosai.
“Kema karkice kin dauka Hamma ne, yanzun Huda tace mun a waje, wai dana wuce ta dauka shine ya dawo.”
Murmushi Ayya tayi, to a cikin gidan nasu ma mutane da yawa sun mishi magana, daga nesa za’a dauka Rayyan ne, saiya matso kusa yanayin haske da Rayyan ya fishi da tsayi kan banbanta su, sannan shi Bilal yana fara’a. Amman tabbas idan ba farin sani kayi musu ba, ka kuma jima baka ga daya daga cikin su ba, da wahala ka gane. Baiji wani iri ba sai da suka hadu da Layla, yanda ta dafe kirji tana wani irin mayar da numfashi kafin dissapointment ya lullube fuskarta ya taba zuciyar shi.
“Me yasa kayi irin askin Hamma?”
Ta bukata tana dorawa da,
“Na dauka shine, wallahi na dauka shine.”
Ko amsar shi bata jira ba ta wuce. Zai karya idan yace abin bai mishi ciwo ba, shisa ya yanke hukunci ba zai kara tara suma ba, irin yanda Rayyan din yakeyi zaici gaba, gashi a fuska damun shi yake shisa baya ajiyewa daman, yanzun kam harya fara sabawa, yana kuma kallon yanda Layla ta kan bishi da ido kamar yayi wani abu da bai kamata ba.
“Ka gama? Mu tafi?”
Cewar Bilal yana daukar wayar shi ya saka a aljihu. Mikewa Rayyan yayi yana daukar jakar shi suka fice, kofar kawai Bilal yaja bai damu daya kulle ba. Mota suka shiga, ko yar jakar shi Rayyan bai saka a baya ba, anan kan cinyar shi ya ajiyeta, ya juya motar suka fice daga layin.
Da mashin Layla ta hawo da ta ga motar su, amman napep ta samu, dan harta fara takowa da kafarta tunda skirt dinta ba zai hau mashin bama. Sai ga nepep ta samu, kuma kanta na kan wayar da take dannawa. Da mafarkin Rayyan ta kwana, mafarkai cikin yanayin da take fatan yin tsayin rai dan ta gani.
Ji tayi tana son ganin shi kafin ya tafi, tana sauka daga cikin napep din zuciyarta tai wata irin dokawa da sai da ta lumshe idanuwanta tana budewa. Dari biyu ce ta baiwa mai napep din tana furta,
“Ka je kawai.”
Ko godiyar da yake mata bata amsa ba, zuciyarta ke bugawa kamar zata fito waje. A irin yanayin daya kamata ace tayi addu’a, harshen ta ne yayi nauyi na gaske. Wata murya ke bata shawarar ta juya, amman ta kasa, kamar wadda akewa dole haka ta taka tana shiga cikin gidan. Makoshinta harya bushe saboda bugun da zuciyarta takeyi, dakin su Rayyan ta wuce kanta tsaye tana turawa ta shiga hadi da sake tura kyauren duk da bai rufe duka ba, dakin ya mata duhu da yake kwan a kashe yake, idan akwai wutar lantarki bata kula ba, balle tayi tunanin kunna kwan. Da fitilar wayarta ta haska, robar ruwa ta gani a kasa ta karasa ta dauka ta kwance, ta sha fiye da rabi tana dorawa kan tebir din Rayyan.
Gefen gadon ta zauna tana maida numfashi.
“Hamma tafiya kayi.”
Ta furta da wani yanayi a muryarta, watakila Rayyan din daya tafine yasa zuciyarta bugawa haka. Sosai ta so ganin shi, gashi tasan magana da sassafe wahala takeyi mishi fiye da kowanne lokaci, idan ta kirama ba dauka zaiyi ba shisa bata kwatanta ba. Haka kawai sai taji kanta ya fara mata nauyi, kamar wadda rashin lafiya ke son kamawa, takalmanta da ta shiga dasu cikin dakin sosai ta cire tana turawa gefe wajen tebir din. Kwanciya tayi sosai, a hankali ta zame dan mayafinta ta ajiye a gefenta. Wani irin yanayine daya hade mata da wanda ta shigo da shi da karatun wani labari a group ya taso mata da shi harya darsa mata son ko da ganin Rayyan ne.
Tunda take a duniya bata taba jinta a irin yanayin nan ba, kamar wadda take yawo a wata duniya ta daban, kamar tana cikin mafarkin da idanuwanta suke a bude haka take ji, shisa ta lumshe idanuwanta tana tunanin yanda akayi su Bilal din suka saka gado a maimakon katifa kawai a dakin nasu. Tana kuma tunanin yanda suka kyauta saboda taji dadin kwanciyar sosai. Kamar a cikin mafarki haka taji shigowar Bilal da harya kusa makaranta aka kira shi aka fada mishi Malamin ba zai sami damar zuwa ba, yaji dadin hakan saboda bashi da natsuwar daukar darasin ko da anyi.
Hankalin shi baya tare da shi sam, har sanda ya shiga dakin, ya kuma mayar da shi ya tura kamar babu kowa a ciki, shisa ko kadan bai hangi Layla da take kwance can karshen gadon su ba, ga kuma net da ya tattare ya kai can karshen, ga duhun dakin dan ma sun saba, kamar ta mirgina ne tana nade kanta da shi, da wahala kayi zaton akwai mutum a wajen. Balle kuma Bilal din da hankalin shi na tare da kalaman Rayyan din da suke ta fadar mishi da gaba tunda ya fade su, lafiya kalau ya sauke shi ta sha, sai dai yanata kallon shi, kallo da yake cike da tarin ma’anoni har saida ya saka shi tambayar,
“Hamma… Lafiya kuwa?”
Da alamun damuwa da Bilal din zaice bai taba ganin kalarta ba a fuskar Rayyan din yace,
“Zuciyata namun wani irin Bilal.”
Tsoro Bilal yaji ya baibaye ta shi zuciyar, Rayyan bai cika fadar abubuwa irin hakan ba.
“Ko dai zaka hakura da tafiyar ne? Idan zuciyar ka bata natsu ba ka hakura.”
Kai Rayyan ya girgiza mishi.
“Bana jin ni ne.”
Cike da rashin fahimta da kuma son karin bayani Bilal din yake kallon Rayyan, cikin idanuwa Rayyan din ya kalle shi wannan Karin.
“Ka kula da Layla, ka kula mun da Layla kaji Bilal, zuciyata na mun wani iri.”
Kai ya daga mishi, saboda yanayin shi yasa ko kishin daya sabaji sam bai taso mishi ba.
“Ta ce tana so na, jiya tace tana sona kamar bata san nasani ba tuntuni.”
Cewar Rayyan, saboda saida suna kan hanya yake tunanin babu wani bakon abu a cikin kalaman Layla, abu ne daya riga ya sani tuntuni, ya riga yasan tana son shi, a cikin duk wani riko da zatayi mishi yasan hakan. A yanda take dawowa wajen shi bayan ya koreta ya karanci hakan, tana son shi duk tarin duhun da yake baibaye da shi bai hana zuciyarta doka mishi ba. Da sanyin murya Bilal yace,
“Ni ma ta fadamun…”
Ganin kallon tashin hankalin da Rayyan yai mishi yasa shi yin murmushin da yakejin ya fito daga wani waje daya tsage a zuciyar shi yana dorawa da
“Tana son ka, ta fadamun tana son ka.”
Kai Rayyan ya jinjina, damuwar da tabar fuskar shi tana dawowa sabuwa.
“Shi sa zaka kula mun da ita, ban san meye nake ji ba, dan Allah Bilal.”
A tsorace Bilal yace,
“Zan kula da ita Hamma, kai dai ka kula da kan ka dan Allah. Ni duk ka tsoratani…”
Numfashi Rayyan ya sauke yana juyawa kawai. Maganganun shine suka yawaita a lokaci daya yau. Shisa suka tsorata Bilal din, sai juyawa su yake a ran shi. Yana jin kamar wani abu mai girma na shirin faruwa da su yau din nan. Shima ta shi zuciyar bugawa takeyi, ruwan daya gani a roba shiya dauka ya kwance yana kafa kai ya shanye, na karshen na sauka bakin shi da wani dandano daya kasa ganewa. Anan ya tsaya yana mayar da numfashi, wayar shi ya zaro daga aljihu ya ajiye akan tebir din, wani irin sama-sama yake jin shi, banda yanayin Rayyan babu abinda yake gani.
“Allah ya sauke ka lafiya Hamma”
Ya furta jin zuciyar shi bata daina rawa ba. Agogon hannun shi ya kwance, kamar zazzabi yake son yi, da wahalar gaske gabaki dayan yau ya iya zuwa makaranta. Kayan jikin shi ya rage yana barin gajeran wando, shima wandon anan ya cire shi yana zare kafafuwan shi ya tsallake tunda Rayyan din da zai fada ya ajiye wando a kasa baya nan. Ya kama riga ya cire yaji kamar jiri zai dibe shi, babu shiri ya zauna a gefen gadon batare daya juya ba balle yaga Layla, kan shi ya dafe cikin hannuwan shi biyu. Da gaske duniyar shi ce take wasan kura da shi. Ya gwada mikewa yafi sau biyar yana kasawa saboda yanda jiri yake dibar shi, babu shiri ya kwanta ko zai samu sauki. Daga nan ba zai ce ga iya lokacin daya dauka baisan abinda yake faruwa a duniyar ba.
Kamar a mafarki haka Layla ta bude idanuwanta tana ganin komai na rabe mata biyu.
“Hamma…”
Ta kira a cikin kanta ganin Bilal din a kwance a gefenta, sai taga tazarar da take tsakanin su tayi mata nisa, ga yanda jikinta duka yai nauyi sanda taja shi tana matsawa sosai kusa da shi.
“Hamma”
Ta sake kira tana jin ashe gara da tazo, ashe Rayyan bai tafi ba, watakila kuma daya daga cikin mafarkan da ta sabane na shi, saboda yanayin ta ya nuna haka, tana jinta kamar tana yawo a gajimare, hannunta ta dago tana dorawa akan fuskar shi, fuskar da take mata kyau a kowanne yanayi, duk da duhun dakin ya hana mata ganin shi sosai, sai tarin kasumbar da yake fuskar shi. Kamar yanda take jinta a mafarki hakama ya kasance a wajen Bilal, dumi yaji ta inda bai taba zato ba, dumi yake ji akan kirjin shi da wasu sassa na jikin shi inda Layla ta kwanto, sai kan fuskar shi da sam baisan meye a kai ba, har saida ya kai na shi hannun yana kama nata cikin na shi.
Ya sha ganin hannuwanta, ya sha hasaso yanda zasu kasance a cikin na shi, amman yau daya jisu a cikin nashin, a duniyar da yake suna dayane yazo mishi.
“Aisha”
Ya furta iya kan shi yana kara rikota a jikin shi, yanajin yanda bugun zuciyar shi ya karu har cikin idanuwan shi da suke a rufe, yanda ta biye shi na kara tabbatar da mafarkin da yakeyi. A cikin su babu wanda ya dawo hayyacin shi har sai da Layla taji abinda yake faruwa ya girmi duniyar da take tunani ta mafarki ce, ya kuma girmi duniyar da take ciki gabaki dayanta, a dai-dai lokacin da Bilal ya rabata da Martabar da bata san haka take ba a duk lokuttan da Mami take kira mata ita sai yau da tashin hankalin rabuwa da ita ya wujijjigata yana fisgota daga duniyar da ta fada zuwa ta mutane, lokacin da ta bude idanuwanta tana son saka duk wani karfi da zata iya tattarowa ta ture Bilal din.
Tashin hankali yayi kadan a yanayin da take ciki, saboda taji muryar shi a kunnenta da wani irin yanayi yana furta.
“Aisha… Aisha”
Muryar da yanayin bai hanata gane waye ba, sunan daya kira na sake tabbatar da firgicinta, azabar da take ratsa ruhinta ta girmi mafarki tabbas da ta fassara abinda yake faruwa din da mummunar mafarki, kuka da ihu take son tattarowa daga wani loko da tashin hankalinta yake faruwa, da kyar ta samu ta iya furta.
“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”
A matukar wahalce tana jan numfashin da ta fitar da sauran natsuwar daya rage mata kafin azaba da tashin hankali su sake rabata da hankalinta.