May 1985, Kano
Da gaskiyar iyaye da kance kukan yaro yafi komai daga hankali, har kasan ranta take jin kukan Rayyan, a gaggauce ta karasa wankan, sabonta ne sai ta saka hijabi idan ta daura zani sannan take fitowa daga wanka, kamar yanda takan shiga da ita. Amman yanzun kam haka ta fito, hijabin ma a bandakin ta baro ta. Ganin ta lallaba Rayyan din yayi bacci shisa ta lallaba tadan watsa ruwan ta fito, ashe ba nisa baccin yayi ba. Tana daga labulen gabanta nayin wata irin mummunar faduwa ganin Maryama data mika hannu tana shirin daukar. . .
Masha Allah. Allah ya ƙara basira. Fatan alheri. #haimanraees