Lokaci zuwa lokaci wanda yake kujerar kusa da shi a cikin jirgin yakan ja karamin tsaki saboda yanda Rayyan din yake bubbuga kafar shi a kasa cikin kosawa. Gani yake kamar jirgin baya sauri, baisan mene ne a nannade tare da harshen Bappa da kalaman shi ba, amman sunyi tasirin da suka saka shi daukar shawarar shi na tsayawa ya yi abinda ya kaishi Bauchi ya wuce wajen, sai su duba idan akwai jirgin da zai tashi daga Bauchi zuwa Zaria, da yake a yar jakar shi duka katikan shaidar shi suna ciki, na makaranta, katin zabe da kuma katin. . .