"Layla ta dawo ko?"
Naadir ya tambaya yana shigowa dakin, murmushi Mami tayi,
"Bata dawo ba."
Ta amsa shi, kallon ta yakeyi da murmushi a tashi fuskar kafin ya wuce kitchen, bude-bude ya fara yana ganin wake da shinkafa, sai sauce din manja da ta sha kifi, yana zubawa yake fadin,
"Layla ta dawo Allah Mami...ni na sani."
Dariya tayi wannan karin, da yake nan BUK Naadir din yake yi, kuma duk a cikin yaranta shine makaranta take wahalar wa, saboda kokarin shi bai kai nasu ba, yana cikin gari amman ba kullum yake kwana a gida ba. . .