Can nesa Layla take jin duk wata magana da sukeyi, ba zata ce ga abinda ya dinga faruwa ba, daga asibiti, zuwan Abbu, dawowar su gida, banda sautin kukan Mami babu abinda take ji, dan yanzun haka da suke a tsakar gidan ta samu wajene ta zauna a kasa, gefen Mami da ta kasa shiga daki ta durkushe a wajen. Kuka takeyi kamar ranta zai fita, dan har yanzun ta rasa ta inda zata fara yiwa Abbu bayani, sanda yazo asibitin ta farfado, dan haka suka dawo gida, ita da shi a mota daya, sai Jabir daya kama hannun Layla. . .