Maganganun Ayya ne suke mishi yawo, kafin ya zare hannun shi daga cikin nata, yana kallon Layla da jin an kira sunan shi ya sakata bude fuskarta, idanuwanta har sun kumbura saboda kukan da takeyi. Tana jin su, bata san kalar tunanin da ya kamata tayi ba, duniyar duka take ji ta hade mata waje daya. Ta rasa da wanne zata fara, tashin hankalin abinda yake faruwa da ita karon kanta, halin da su Mami suke ciki, Abbu da take ganin ba zuciyar shi kawai ta taba ba, harda Martabar shi, ko kuwa Rayyan da take ji suna lakabama laifin. . .
Thanks for all