Skip to content
Part 27 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Ko sallamar Abbu daya dawo daga masallaci kan shi tsaye ya nufo bangaren ta bataji ba. Zuciyar shi na wata irin dokawa ganin ta rike da Rayyan din.

“Rayyan…”

Ya kira muryar shi na fitowa yar karama saboda tsoron da yake ciki.

“Me ya same shi? Me ya faru?”

Saboda ya ga fitar Rayyan din daga dakin shi, kuma lafiya kalau ya gan shi. Baisan me yake a kwance haka kamar gawa ba. Ayya da sai lokacin hawaye masu zafin gaske suka zubo mata ta dago tana kallon Abbu, bakinta take so ta bude tayi magana amman ta kasa, saboda zafin da zuciyarta takeyi. Ta dauka raba soyayyar Abbu shine abu mafi daci da zata dandana a zaman duniyarta gabaki daya. Saboda Abbu ne komai nata, sai yanzun da take tunanin inda Bilal ya nufa a cikin duniyar da babu aminci, a rayuwar da naka ma da wahala ya taimaka maka balle wanda baka sani ba.

Kafafuwan Abbu har rawa yake sanda ya kara bandaki ya dibo ruwa ya dawo. Da kan shi ya tsugunna yana dibar ruwan a hannun shi ya shafama Rayyan a fuskar shi, sai da yayi hakan kusan sau biyar sannan Rayyan din yaja wani irin numfashi mai nauyi yana mikewa gabaki daya.

“Bilal”

Ya kira daga lungun zuciyar shi yana kallon Abbu.

“Abbu tafiya yayi… Bilal tafiya yayi.”

Cike da rashin fahimta Abbu yake kallon Rayyan din, kafin ya maida duban shi kan Ayya da ta saka fuskarta cikin tafukan hannunta tana wani irin kuka marar sauti, bayani yake so wani yayi mishi yanda zai fahimta. Dube-dube Rayyan yayi yana dauko takardar da Bilal ya bar mishi da take can gefe ya mikawa Abbu, sai da ya karanta babu adadi kafin kalaman su zauna mishi. Baiyi magana ba ya mike tsaye, aljihun shi ya laluba yana zaro wayar shi da sabo ya saka shi daukarta ya zira bayan yayi alwala zai fita masallaci.

Jikin shi babu inda baya bari, dakyar ya iya saka lambobin sirri ya bude wayar. Sakkoni ya gani da hannun shi ya dangwalo batare da yayi niyya ba. Ganin sakon Bilal a sama ya saka shi saurin budewa,

“Kayi hakuri Abbu, ka yafe mun dan Allah, watakila zan samu sauki a duk inda rayuwa zata jefani. Ka yafe mun ban rike amanar da ka bani ba, ban kula da Layla yanda nai maka alkawari ba. Nagode da karbata da kayi, nagode da yanda ban taba jin maraici a karkashin kulawar ka ba. Ina fatan nisan da zanyi ya saukaka muku komai.”

Sosai Abbu yake jin kan shi na sarawa.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Ya furta yana saka Rayyan saurin fadin,

“Mene ne Abbu? Ya fada maka inda yaje?”

Ya karasa yana mika hannu ya karbi wayar da Abbu ya miko mishi, karanta sakon yakeyi wani abu na tattarowa yayi mishi tsaye a kirjin shi, dago idanuwa yayi yana kallon Abbu cike da wani yanayi.

“Amana ka bashi Abbu? Me yasa?”

Saboda bai ga dalilin da zai sa Abbu yace ya bashi amanar Layla ba, sun san yanda Bilal yake, su dukan su kowa yasan raunin Bilal, yanda bashi da wani aiki sai kula da kowa, furta kalaman ba zaiyi komai ba sai dora ma Bilal din wani nauyi da Rayyan bayajin Abbu ya fahimta.

“Abbu ko bakace ba, ko baka furta da bakin ka ba Bilal zai kula da ita da duka zuciyar shi, me yasa ka dora mishi nauyin nan? Kaga ya tafi, saboda yana tunanin ya kasa sauke nauyin amanar daka bashi ya tafi… Kasa ya barni.”

Yanda Rayyan din yake magana kamar ba a cikin hayyacin shi yake ba, wanda zai dora ma alhakin tafiyar Bilal yake nema, bai sami kowa ba sai Abbu a yanzun. Dube-dube yakeyi ganin Abbu ya sadda kan shi kasa ya kasa cewa komai, har saida ya hango wayar Ayya sannan.

Idan Bilal ya turoma Abbu sako, tabbas itama yasan ya tura mata, watakila ya fada mata inda zashi ita. Yana dauka yaga ko password babu ita, dan haka kanshi tsaye wajen sakkoni ya shiga, ya kuwa ga Bilal din ya turo mata itama:

“Ki yafe mun Ayya, zanyi kewar ki da yawa.”

Dariya Rayyan yayi da bata da alaka da nishadi, saboda ko shi zai fita duk yanda magana mai tsayi bata hadasu da Ayya, iya abinda zai tura mata kenan. Bai taba sanin Bilal bashi da hankali ba sai yau. Wayar ya ajiye gefe yana samu ya mike.

“Ina zaka je?”

Abbu ya bukata, amman Rayyan din bai kula shi ba ya wuce. Tsintar kafafuwan shi yayi da bin Rayyan din, kafin shima ya tafi, jin takun Abbu a bayan shi ya saka shi juyawa.

“Abbu ba inda zanje, ka koma dan Allah… Ba inda zani.”

Ba don ya yarda da kalaman Rayyan din ba, ya dai yi tsaye ne har sai da ya daina ganin Rayyan din da ya nufi dakin su. Kayan da Bilal ya baza ya fara harhadawa, watakila yabar wani abu da ko yane zai nuna alamar inda ya nufa, amman harya gama hadasu baiga komai ba. Gefen gadon ya zauna yana rasa kalar tunanin da ya kamata yayi, kafin wani abu cikin kan shi ya fada mishi baiyi sallar asuba ba. Alwala kam dan sabo ne shisa ya cikata dai-dai. Lokacin daya idar da sallah, bai san ta inda zai fara addu’a ba ko abinda zai roka, kawai yana rokon Allah Ya duba halin da yake ciki ya karbi sallar da yasan bashi da wadatacciyar nutsuwa a lokacin daya gabatar da ita.

Baisan iya lokacin daya dauka a zaune ba, rurin da wayar shi takeyi ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da yakeyi. A hargitse ya mike yana rasa inda zai gano wayar, har ta yanke tana sake daukar ruri.

“Dan Allah ina dubawa ne Bilal, nasani, ni nasan babu inda zaka tafi ka barni.”

Rayyan yake fadi yana cigaba da neman wayar kafin ya juyo ihunta cikin jakar shi da ko budeta baiyi ba. Lalubo wayar yayi, kafin ya daga ta sake yankewa, budewa yayi yana kallon lambar hadi da nazarin inda ya taba ganin ta, ko ma a ina ne yasan lambar, kafin a sake kira, bai tsaya jira ba ya daga wayar yana karawa a kunnen shi.

“Hamma…”

Muryar Aisha ta daki kunnen shi tana saka zuciyar shi matsewa a cikin kirjin shi, kafin ya amsa ta dora da fadin,

“Hamma ina Nawan? Sakon shi nagani yanzun, bansan ko ya yarda wayar bane, saboda na kasa fahimtar duka zantukan da yake yi.”

Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi, akwai wani yanayi tattare da muryar Aisha da yake kara bude bangarori da dama a cikin zuciyar shi.

“Dan Allah ka fadamun…kai mun Magana.”

Sai da ya bude idanuwan shi sannan ya iya cewa

“Ina kike tunanin idan Bilal ya bar gida zai je?”

Ta kusan mintina uku kafin ta amsa shi, muryarta na fitowa a karye.

“A watan nan yana yawan maganar kasancewa a wajen da kowa bai san shi ba, yana fadin Lagos ne kawai zakaje ka bace bat… Ban sani ba, ban san me yake faruwa ba, me yake faruwa Hamma? Me yasa zai tafi?”

Ta karasa maganar ne da alamar kukan da ya kwace mata, ba shi da amsar da zai bata, ba kuma shi da wasu kalamai da zai tausheta dasu, shima yana bukatar lallashine.

“Ina zai tafi ya barni? Ta ina zan fara?”

Wani irin numfashi take saukewa kamar wadda aka shake.

“Zan kiraki”

Rayyan ya fadi yana sauke wayar daga kunnen shi, dan yaji alamar zata kara hargitsa mishi lissafi ne. Yana da abubuwa da yawa a gaban shi. Mikewa yayi yana saka wayar a aljihun shi, sai da ya karasa bakin kofa sannan yayi tunanin saka takalma a kafafuwan shi, tashin hankali bai barshi yaji kasar da yake ta takawa ba yau. Yana fitowa daga daki yaci karo da Abbu.

“Abbu zan duba a tasha, ina motocin Lagos suke lodi? Aisha tace Bilal yana maganar zuwa can ne.”

Kai Abbu yake jinjina ma Rayyan, gabaki daya ya rasa abinda zaiyi tunani. Duniyar ta birkice mishi, yaran da yake tunanin yana duk wani kokari da yake karkashin ikon shi dan kare sune yake kallo yau kaddara na aikinta a kan su babu abinda zai iya. Bilal ne ya dauki kafar shi yabar gida yau, Bilal da gabaki daya rayuwar shi zagaye take da tasu, shine yau ya nufi inda baisan kowa ba, ya ture komai ya tafi saboda yana tunanin yayi musu wani laifi. Wani irin tsoro Abbu yake ji yana shigar shi, Rayyan yake kallo, yana tuna kalaman da yayi mishi jiya na yabar gida.

“Ko da zan taba ce maka kabar mun gidana, karka tafi ko ina, kalaman ba zasu taba fitowa daga zuciyata ba.”

Abbu ya fadi yana dorawa da,

“Bari in dauko mukullin mota sai mu tafi.”

Anan inda yabar Rayyan ya dawo ya same shi, sun karasa wajen motar ne Yaya Ayuba ya shigo, ko gaisawa ba suyi ba ya fara da tambayar,

“Lafiya? Ina zaku je da sanyin safiyar nan?”

Abbu na bude murfin mota ya amsa shi.

“Bilal ne ya bar gida, Rayyan yace kamar Lagos ya nufa. Shine zamu duba a tasha mugani.”

Karasawa Yaya Ayuba yayi yana karbar mukullan motar daga hannun Abbu batare da yace komai ba. Shiga sukayi, Rayyan na bude gidan baya ya shiga. Da yake Yaya Ayuba yasan duk tashoshin da motocin Lagos suke lodi. Tunda kafin ya samu budin hawa jirgi idan tafiya kudu ta kama shi motar hayar yake bi. Rayyan ba tuqi ya iya ba, amman gani yake kamar Yaya Ayuba baya taka motar da sauri, saboda so yake kawai su karasa yaga Bilal din yaji dalilin da zai sa ya fara tunanin barin su.

Kudi Kawu Ayuba ya bama cikin yan kamasho na tashar, kafin kace wani abu an dauko musu wani babban littafi da jerin sunayen mutanen da suka hau motocin Lagos daga daren jiya zuwa wayewar gari, motocin safe. Amman ko daya babu sunan Bilal a ciki, duk da Rayyan yaki aminta, wanda ba shi ya duba ba da kan shi sai da ya karba ya sake dubawa, tashoshi suka dinga bi har wajen karfe tara na safe, saboda duk inda sukaje sai sun tsaya an duba list sannan suke barin wajen. Suna hanyar nufar wata tashar da akayi musu kwatance, wayar Rayyan ta fara ihu, bai bi ta kanta ba harta yanke, saboda wani abu na fada mishi ba Bilal bane ba.

Sake kira akayi, ko waye ma bai hakura ba a karo na biyu, ya sake kiran a karo na uku.

“Rayyan ba wayar ka bace take kara?”

Yaya Ayuba da yake tuki ya tambaya, Rayyan din bai amsa shi ba, dan daga jikin shi yayi yana zaro wayar daga aljihun shi, dubawa yayi yaga ko Aisha ce, dan bashi da wata magana da zai fada mata, da akwai daya kirata kamar yanda yai mata alkawari. Wata lamba ce yagani daban, karamin tsaki yayi yana shirin saka wayar a silent kar a dame shi aka sake kira, dagawa yayi ya kara a kunnen shi yana fadin,

“Waye?”

A hasale, ta dayan bangaren aka furta,

“Daga tashar Mass ne, mun dauki lambar cikin lambobin da daya daga cikin fasinjan da motar su ta tashi karfe hudu na safiyar yau daga nan Kano zuwa Lagos ne mai suna Bilal Abdullahi Dikko…”

Zaman shi Rayyan ya kara gyarawa yana kai hannu yana wuyan rigar shi da haka kawai yaji kamar ya shake shi.

“Ni ne, ina Bilal din?”

Ya furta a kagauce, dan jim yaji anyi cikin yanayin da ya saka shi fadin

“Hello, ina Bilal din? Wacce unguwa tashar taku take?”

Yana kallon Abbu ya juyo da jikin shi gabaki daya daga gaban motar yana fuskantar shi.

“Bilal ne ya bada lambata a tashar shine suka kira ni.”

Ya tsinci kan shi da fadama Abbu daya sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba, Rayyan kuwa hankalin shi ya mayar kan wayar jin har lokacin ba’a kara cewa komai ba, ya bude baki zai magana yaji muryar mutumin ta daki kunnen shi da wata iska mai karfin gaske.

“Sun sami hatsari ne…”

Cikin wata irin murya da Rayyan baisan daga inda ta fito ba ko yanda akayi ya iya motsa labban shi yace,

“Hatsari? A ina? A ina? Suna ina yanzun?”

Wannan karin iskar yake ji tana kadawa a ko ina na jikin shi da yayi wani irin sanyi na ban mamaki, baya tunanin ya fahimci abinda aka fada din, saboda kunnen shi yaji daga wajen.

“…Babu wanda ya fita a motar, da tankar mai suka hade…”

Abinda aka fada kafin nan da bayan nan duk bai jisu ba, iya inda yaji din ma bai fahimta ba shisa ya mikawa Abbu wayar,

“Ban gane me yake fada ba Abbu, kaji me yace.”

Abinda mutumin ya fadama Bilal shi ya sake maimaitawa Abbu da wayar ta subuce daga hannun shi yana furta.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Yana sake maimaitawa ko ina na jikin shi na bari, duniyar gabaki daya tana hargitse mishi.

“Mene ne? Me ya faru?”

Yaya Ayuba yake tambaya saboda yanayin Abbu din duk ya hargitsa shi, shisa ya sauka daga kan titi yana yin parking din motar, wayar Rayyan da take jikin Abbu ya dauka, kiran ya yanke. Bai bi takan su Abbu ba ya sake duba lambar da yake itace kan kiran karshe da ya shigo, sau hudu yana kira duk ana ce mishi busy alamar ana kira da layin, sai ana biyar tukunna ta shiga.

“Ina kira akan Bilal Abdullahi Dikko ne, bamu fahimci me kake cewa ba.”

A nutse yayiwa kawu bayanin hatsarin da motar ta samu a hanyar Zaria, hatsarin da aka dade ba’a ga irin shi ba, saboda doguwar motar gabaki daya babu wanda aka fitar a ciki, wasu ma sun zama toka, iya gawarwakin da aka samu fitarwa basu fi goma ba idan aka hada jimillarsu, suma wasu duk sun hade da yan uwan su, yanayin da bai bar ma mutanen da suka kawo musu dauki wani zabi daya wuce hade su gabaki daya aka yayyafa musu ruwa aka sallace su hadi da haqa kabari daya aka hade su ba. Shi kan shi kawu babu inda jikin shi baya kyarma, saboda a tunanin shi ma ya kasa hasaso yanda lamarin ya kasance

“Bilal ya rasu.”

Ya furta a hankali yana dorawa da.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Abbu ma abinda yake fadi kenan yana maimaitawa, baya son bama kwakwalwar shi wani space nayin tunanin komai. Sun kai mintina goma a wajen kafin ya iya samun karfin jan motar suna nufar gida. Da suka karasa ma aka bude musu ya shiga yayi parking, duka yan gidan babu wanda bai tashi ba. Sun zo harabar da ake ajiye motocin sunyi tsaitsaye ne kamar suna jiran dawowar su Abbu din. Shi kan shi Yaya Ayuba da ya fito yana ganin su tsaitsaye yaji kamar ya koma cikin motar, amman daga Abbu har Rayyan babu wanda ya iya ko motsawa balle yayi tunanin ko zasu fito.

Ayya ce ta karaso wajen da sauri, kallo daya zakayi mata kaga yanda idanuwanta suka kankance suka sake launi saboda kukan da tayi, kukan da yanzun ne zata soma shi.

“Kun gan shi?”

Ta tambaya, Yaya Ayuba na girgiza mata kai hadi da dauke idanuwan shi daga kanta. Ya daiyi mamakin ganin harsu Khalifa a cikin gidan. Suna hada idanuwa da Khalifa ya tako ya karaso inda Yaya Ayuba da yaji shi gefe yake.

“Khalifa ya rasu… Bilal ya rasu.”

Yaya Ayuba ya furta girman kalaman na dukan shi, cikin tashin hankali Khalifa yake kallon shi, da hankalin shi, a tsayin rayuwar shi baisan wani abu rashi ba, wani daya taba shakuwa da shi bai taba rasuwa ba, yaune rana ta farko da aka fara sanar da shi labarin mutuwar da ya saka gwiwoyin kafafuwan shi yin sanyi gabaki daya, da Yaya Ayuba bai riko shi ba sai yakai kasa

“Subhanallahi, Khalifa.”

Yaya Ayuba ya fadi, a zaton shi tunda Khalifan ne Babba a gidan, zaifi sauki shiya fara sani kafin a san yanda za’a sanar da Ayya da ta karaso wajen tana kallon Yaya Ayuba.

“Me ya faru? Me akayi?”

Kan shi Khalifa ya dafe yana saki, numfashi yake fitarwa ta baki ko zai samu saukin abinda yake ji, amman komai kara hade mishi waje daya yake. Gurin motar Ayya ta karasa tana bude bangaren da Abbu yake, kan shi taga ya hade da gaban motar, a tsorace ta dafa shi, ya kasa dagowa.

“Ahmadi.”

Ta kira, amman bai ko motsa ba, mantawa tayi da yaranta na wajen, mantawa tayi akwai kowa banda ita da shi, ta saka hannuwanta tana dago da shi.

“Ahmadi…”

Ta sake kira, idanuwan shi Abbu ya saka cikin nata, kafin ya dago nashi hannuwan ya kama nata da yake jikin shi, kamar yana so ta taimaka mishi ya fito daga motar, hakan kuwa tayi, duk da yana fitowa sai ya kasa yin komai banda jingina bayan shi da motar yana zamewa a hankali ya zauna, har lokacin yana rike da hannuwan Ayya shisa itama ta bishi kasan tana tsugunnawa, da wani yanayin tashin hankali yake kallonta.

“Ya rasu Maimuna… Bilal ya rasu.”

Ba wannan bace mutuwa ta farko da aka fada mata, ance baka san daci na mutuwa ba sai ranar daka rasa mahaifa, miji ko da. Ta dandani mutuwa kala-kala, bata san ciwon rashin da daban yake ba sai yau, dan wani abune ya tsirga mata daga dan yatsan kafarta zuwa tsakiyar kanta, kafin komai ya tattaro ya dawo yana tokare mata kahon zuciya, kukan kowa da wani yanayi yake isa kunnuwanta, musamman Rukayya da ta karaso inda take tana jijjigata.

“Ayya me suke cewa? Ayya kice mun karya ne, ki ce mun Hamma Bilal bai rasu ba.”

Bata ko iya juyawa ba, hannuwa Abbu da yake rike da nata ne kawai abinda tasan yana rike da sauran hankalin da take tare da shi, haka Rukayya ta dinga bin duk wanda ta samu tana jijjiga shi, har ta karasa inda Mami take tsaye hawaye na zubar mata, wani nabin wani. Tun jiya Ayya ta fada musu abinda yake faruwa, tun jiyan kuma Rukayya take tunanin rayuwa da yanda komai zai iya canzawa cikin kankanin lokaci. Tun da ta taso Ayya ke fadin laifukan Mami, duk da sanda ta fara hankali ta gane rabin mitar Ayya din na tare da kishin da yake dawainiya da ita.

Mami bata taba ko da mata kallon banza ba, gaisuwar mutunci tana hadasu, wasu lokuttan ma har su danyi hira. Duk yanda Ayya taso ta ga laifin Mami bata taba gani ba, sai yau da ta karasa tana kama hannun Mami.

“Kingani ko Mami? Muna zaman mu ki dauko mana Layla, da bata shigo rayuwar mu ba da yanzun bamu san tashin hankalin nan ba, da Hamma bai bar gida ba, da labarin mutuwar shi baizo mana ba… Wallahi ba zan yafe miki ba, Mami ba zan yafe miki ba…”

Rukayya take fadi tana durkushewa wani irin gunjin kuka na kwace mata. Duk abinda akeyi Rayyan na cikin motar, ba jinsu bane bayayi, kan shi yake ji kamar a wata duniya ta daban. Komai ne yake karasawa cikin kunnuwan shi kamar saukar ruwan saman da babu hadari, yana zaune ciki yaji muryar Haris na fadin,

“Bilal ya rasu? Yaushe? Garin yaya?”

Kafin ya dora da,

“Ina Rayyan?”

Baiji wani ya amsa shi ba, ya dai ji lokacin da Haris din ya bude murfin motar a bangaren da yake. Ya kuma ji hannun Haris ya kama na shi yana janyo shi ya fito da shi daga motar.

“Rayyan… Rayyan.”

Haris yake kira, amman baya ganin komai, ba shi da kalma ta hausa da zai misalta ganin shi da ita, abinda bature ke kira da “Blank” shine abinda yake faruwa da ganin shi. Yasan akwai mutane a zagaye da shi, amman baya ganin su, jin su kawai yakeyi. Da duk dakika kara jinsu yake, kukan su da maganganun su da yake tabbatar mishi da kalaman da yaji dai-dai ne, Bilal ya rasu, Bilal ya bar shi, ya mishi nisan da bashi da tabbas akan ranar da zai kamo shi.

“Rayyan…”

Ya sake jin muryar Haris wannan karin yana jijjiga shi, iska yake nema, ko yayane ya samu ta isa cikin kwakwalwar shi, watakila ganin shi ya dawo, watakila ya daina jin duniyar na katantanwa da shi. Idanuwan shi ya lumshe yana jin wani shiru a cikin kunnuwan shi, kafin tunanin shi ya dauke gabaki daya.

Bayan Kwana Uku

Hannun shi yake ji kamar a daure, yayi kokarin motsa shi amman bayajin karfi ko kadan a jikin shi balle ya iya motsawa, idanuwan shi ma ya dauki wasu dakika yana kokarin motsa su cikin son ya bude su kafin ya samu nasarar yin hakan, wani haske da yaji yayi mishi yawa na saka shi mayar da su ya rufe gam saboda kan shi da ya fara sarawa, sake gwada bude idanuwan na shi yayi, yanayin dakin ya fara karewa kallo, yana kokarin fahimtar inda yake, kafin yabi hannun shi da kallo, karin ruwa ne a jiki.

“Rayyan…”

Yaji wata murya da bai taba sanin ta ba ta kira shi, a hankali ya juya kan shi yana kallon mutumin da kayan jikin shi yasa shi gane likita ne, kafin ya tabbatar da a asibiti yake, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su da tunanin me yake yi a asibiti, sake runtsa idanuwan shi yayi, komai na dawo mishi kamar shirin film kafin ya bude su yana wata irin mikewa, likitan ya dafa shi.

“Akwai karin ruwa a jikin ka, kabi a hankali.”

Hannun likitan da yake kafadarshi ya ture, yana jin makoshin shi kamar sahara ce a ciki saboda bushewa, karin ruwan da yake jikin shi ya fisge yana sauko da kafafuwan shi kasa, maganar da ta daina karasawa kunnuwan shi ita likitan yakeyi, da ya saka kafafuwan na shi a kasa ya taka sai yaji kamar sunyi mishi sanyi, kamar yayi kwanaki bai taka su ba, shigowar Haris da ya fita siyo wata allura ya saka shi daga kai ya kalli Haris din da yaga kamar ya rame,

“Hamma mu tafi gida.”

Da alamun gajiya a tattare da Haris din yace,

“Yanzun ka tashi Rayyyan, dan Allah kayi hakuri ka kara warwarewa tukunna, kaji…”

Kai Rayyan yake girgizawa tunda Haris ya fara magana, ba zai zauna ba shi kam, yana son ya ga Ayya, yana son ganin Abbu, da dukkan zuciyar shi yake jin son ganin iyayen na shi kafin ya bude zuciyar shi da koma mene ne yake ji.

“Dan Allah Hamma, rokon ka nakeyi, ka kaini wajen Ayya.”

Kai Haris ya jinjina mishi, bashi da karfin yin gardama da Rayyan. A kwanakin nan ukku shi kadai yasan kalar tashin hankalin da ya gani.

“Ka zauna in zo to.”

Wannan karin Rayyan baiyi musu ba ya koma ya zauna kan gadon. Da ido Haris yayi wa likitan nuni da su dan fita. Dakyar ya samu ya yarda su tafi da Rayyan din, dan likitan na tsoron yanda jinin Rayyan din ya hau, idan ya sake faduwa zai samu babbar matsala. Sai da Haris yayi ma likitan alkawarin zasu dawo sannan. Duk yanda Rayyan yaso yin musu da Haris ya kama hannun shi yana dorawa a kafadar shi saiya kasa, bashi da karfi ko kadan.  Suna fita daga dakin Haris ya cire takalman kafar shi yana sa kafar shi daya ya tura su saitin Rayyan din da yaji wani abu ya tsaya mishi a wuya.

Saka takalman yayi, shi Haris din na takawa a haka har suka fita daga asibitin zuwa inda motar shi take, sai da ya taimakawa Rayyan ya shiga sannan ya zagaya ya shiga shima. Gida suka nufa, wannan karin ma sai da Haris ya taimaka mishi suka fita daga motar. Sai Rayyan din yake ganin kamar gidan ya canza, saboda akwai mutane a harabar gidan, an kafa rumfuna, ganin su na kara gudun bugun zuciyar shi. Yana jin Haris yayi musu sallama wasu na furta.

“Ya karin hakuri?”

Yana amsa su da,

“Mun gode Allah.”

Ya ja Rayyan din suka wuce, har dakin Ayya, nan ma akwai mutane, bai damu da su ba, idanuwan shi Ayya suke nema, harya hangota a zaune da hijabi a jikinta, zame jikin shi yayi daga na Haris da yake rike da shi.

“Rayyan…”

Batare da ya kalli Haris ba yace,

“Zan iya.”

Tsaye Haris din yayi yana kallon Rayyan ya taka ya karasa inda Ayya take zaune yana tsugunnawa a gabanta.

“Ayya.”

Ya kira, sai lokacin ta kalle shi, idanuwanta duk sun kankance.

“Rayyan…”

Ta furta, yanda muryarta ta karye na tabbatar mishi da abinda yake son ji, da kyar ya dafa kasa yana mikewa, batayi kokarin hana shi ba harya bar dakin. Wuce Haris daya bi bayan shi yayi, bango yake dafawa yana tafiya saboda rashin karfin da yake ji, dakin su ya nufa yana kama kofar ya bude ya shiga, jin Haris a bayan shi ya saka shi juyawa.

“Dan Allah Hamma, ina son zama ni ka dai ne… Dan Allah.”

Sai da Haris ya sauke numfashi tukunna ya dan daga kai, su duk sunyi kukan su, ciwon bai fara rage musu ba, amman sun yarda da cewa Allah da ya basu Bilal ya karbi abin shi, Rayyan na bukatar lokaci yaji mutuwar shima, ya yarda da sun rasa Bilal, ya rasa Bilal. Shisa ya juya, anan inda yake tsaye Rayyan ya durkushe yana zama da gwiyoyin shi a kasa, zafin kirjin shi yakeyi, kamar an tura mishi wani abu a ciki haka yake ji, idanuwan shi ya lumshe.

“Ya rasu Maimuna… Bilal ya rasu.”

Kalaman Abbu suka dawo mishi, wani irin numfashi yake fisga kamar rayuwar duka na barin shi, sunan Allah yake son kira ko zai samu sauki amman ya kasa motsa labban shi, hade kan shi yayi da jikin shi saboda kirjin shi da yake zafi, kafin yaji an dago shi.

“Rayyan”

Yaji muryar Abbu da ta saka shi dora kan shi a jikin Abbun.

“Kayi hakuri Rayyan, hakuri zamuyi, bamu da wani zabi daya wuce duk muyi hakuri.”

Kai Rayyan yake girgizawa Abbu, kalaman Abbu din na saka wasu irin hawaye masu zafin gaske zubo mishi. Da komai na jikin shi yake son yarda da mutuwar Bilal.

“Kun ga gawar? Kun binne shi Abbu?”

Ya bukata wasu hawayen na zubo mishi, yana jin hannuwan Abbu a jikin shi kamar wata fanka da take fifita mishi ciwukan da ke mishi azabar ciwo.

“Bamu gani ba, baya nufin bai rasu ba, naga motar, munje ni da Yaya Ayuba, babu wanda ya fita a motar Rayyan… Kuma Bilal ita ya shiga… Kayi hakuri dan Allah, kayi hakuri.”

Wani irin gunjin kuka ya kwace ma Rayyan, kuka yake yi kamar yaro dan shekara biyu, kukan da idan wani yace zaiyi irin shi koma meye zai faru da shi kuwa zai karyata. Amman yau kara shigewa jikin Abbu yake yana kuka kamar ran shi zai fita, baiga ta inda zai fara yarda ya rasa Bilal bayan ko gawar shi baigani ba, akwai wani abu a kasan zuciyar shi da yake fada mishi bai rasa Bilal ba, koya ne da yaji a jikin shi, da yaji cewa yana gab ko kuma ya rasa Bilal din gabaki daya.

“Ab.. Abbu zuciyata… Kirjina Abbu.”

Rayyan yake fadi yana jin kamar shima yabi Bilal din koma ina yake ko zai samu sauki. Kara gyara zaman shi Abbu yayi yana sake riko Rayyan, rabon daya rike shi a jikin shi haka tun yana dan karami, bai taba zaton zai sake samun dama irin haka ba, sai dai yanayin ba mai dadi bane balle yace zaiyi wannan tunanin. Rike yake da Rayyan da sai rashin Bilal yasa shi kasancewa karkashin inuwa daya haka da shi. Da dukkan zuciyar shi yake jinjina kokarin iyayen da suka taba binne yaron su. A gefen zuciyar shi addu’ar samun saukin karbar rashin Bilal yake yiwa Rayyan da har lokacin kuka yake a jikin Abbu kamar ba zai taba dainawa ba.

<< Martabarmu 26Martabarmu 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×