Kwance take, da kyar take iya daga idanuwanta. Haris ne ma ya kirata a waya yana tambayar ta ko tana son cin wani abu, tace mishi yoghurt. Da yawa ya siyo ya kai mata daya har daki, sauran yace ya saka mata a fridge. Shima ko rabi bata sha ba ya fita daga ranta, kusan aman shi tayi. Hannun ta dafe yake da cikinta da ta fara ganin alamar ya dan taso, saboda bata da tumbi da can. Lumshe idanuwanta tayi tana jin suna mata wani radadi saboda kukan da takeyi, ko hasken waya bata so a cikin idanuwan nata. Bata taba tunanin zata kwana ta yini ta sake kwana ta yini tana kuka ba sai da labarin rasuwar Bilal ya daki kunnenta.
Ita safiyar ranar da akayi rasuwar bacci ta dan samu, saboda ta kwana tana kuka, ta kwana cikin tashin hankalin rabuwa da Rayyan, ta kira shi yafi sau hamsin bai daga ba, ko ya daina son ta tana son ya saurareta, tana son ta fada mishi batasan yanda akayi abinda ya faru din ya faru ba. Tana son ta bashi uzurin da kowa ya kasa yi mata, ta kare kanta kamar yanda Ayya ta kare Bilal, yanda ta kira abinda ya faru da su da sunan kuskure. Saboda idan Rayyan da kan shi ya barta ina zata je? Wa zai karbeta? Waye ba zai dora alhakin komai a kanta ba?
Kuskurenta ne daukar kafafuwanta taje gidan su, ta rigada ta san wannan, bata tsaya ba har dakin su. Amman batajin tana da laifi a cikin jirin da ya fara dibarta cikin yan mintina kadan da zamanta. Ta zauna ne ta dan huta, ta maida numfashi, bama zata ce ga dalili kwara daya da yasa ta zauna ba, tunda ko Rayyan yana nan ba ko yaushe take zama ba, baya bari, da ta shigo yake mikewa. Da taji maganar shi kamar yanda ya hana mata zama a dakin, da gidan ma gabaki daya ko da suna nan, balle kuma basa nan, watakila da bata zo in da take ba yanzun.
Da tarin burin da take da shi na auren Rayyan bai ruguje ba. Da bata ga tsanarta a cikin idanuwan shi ba. Abbu ya kara hargitsata da furucin shi, saboda idan duniya duka zata hade da ita a waje daya bata hango yanda zata fara zaman aure da Bilal ba. Ko na minti daya zuciyarta bata taba doka mishi ta wannan fannin ba, yanda zata fara kwanciya ta tashi da shi karkashin inuwar aure da sanin ya rabata da komai da take takama da shi, banda Martabar ta harda Rayyan, harda Hamman ta. Ba laifi take kokarin dora mishi ba, amman zata iya farawa idan suka kasance inuwa daya.
Tashin hankali ne shimfide take hangoma rayuwarta da ta birkice cikin kankanin lokaci. Da tunani kala-kala a ranta har gari ya waye, da tayi alwalar asuba ma sai da ta koma ta dan kwanta saboda sanyin da ta dinga ji da yake akwai zazzabi a jikinta. Ta samu bacci ne ba jimawa, dan ji tayi kamar tana bude idanuwanta ta mayar da su ta rufe ne taji kamar an fasa kuka, yanayin da ya sakata bude idanuwa babu shiri, ba kuma karya kunnuwanta sukayi mata ba, kuka ne, da kyar ta iya saukowa daga kan gadon, da yake window din dakinta ta wajen harabar motocin gidan ne, zagayawa tayi ta leka ta hango kusan kowa na gidan a wajen. Kafin kunnuwanta su tsinto mata.
“Bilal ya rasu.”
Cikin muryar da bata san ko waye bama, bangon wajen ta dafa tana runtsa idanuwanta, duniyar na wulwula mata kafin wani abu ya tsirga mata a ciki yana saka bayanta amsawa. Babu shiri ta durkusa saboda azabar da ta dirar mata ga kidimar mutuwar Bilal da take mata kamar almara, sunan Allah duk wanda yazo bakinta shi take kira, tana dafe cikinta da kamar ana tsinka wani abu a ciki, kafin wasu irin hawaye kamar an kwance wani abu a cikinta su fara zubo mata. Sai a cikin kwanakin mutuwar washegari ta fara jero neman gafarar Allah saboda sabon da tasan ta dinga yi na yanda za’ayi Bilal ya rasu.
Kafin wani matsanancin tsoro ya tsirga mata na yanda zai fara amsa tambayoyin shi a kabari, tunanin ko abinda ya gifta a tsakanin su zai rushe tarin ayyukan shi. Ranar bata iya runtsawa ba, gani take kamar da ta rufe idanuwanta itama mutuwa zatayi gaba da ita. Kuma tana jin daudar da take da ita tafi ta Bilal, duk laifukan shi ba zasu wuce abinda ya gifta a tsakanin su ba. Amman ita kam duk wani karami da babban laifi haka ya dinga gifta mata a rai yana kara hautsina mata lissafi.
A cikin sujjadar duk sallolin ta na farilla a kwanakin nan yafiya take rokawa Bilal, ko da basu da bayanin da zasuyi akan abinda ya faru, zunubin daya ne dana wanda suke da bayanin yi. Amman Allah Mai Rahma ne, tana kuma da yakini mai girma akan hakan. Yau kwana biyar, amman ko motsi taji sai ta dauka shine zai shigo, sai taji kamar wani ne a cikin gidan ya zo ya karyata labarin mutuwar. Zuciyarta tayi wani irin nauyi na ban mamaki, ga zazzabin da take kwana tana yini da shi. Yau ne ma ta balli Panadol ta sha.
Ita kadai take kukanta, Mami bata mata magana balle tasa ran zata lallasheta, ko ta gaisheta sama-sama take amsata. Haka zata sha kukanta ta kuma bama kanta hakuri, ta daina kokarin kiran Rayyan tunda baya dagawa, ta dai fada mishi duk wani abu da yazo kanta ta text. Tun tana duba wayarta ko zai amsa harta daina ma. Wani irin kadaici take fama da shi na ban mamaki, sai dai inta rage volume din wayarta sai ta saka karatun Qur’ani, takan ji nauyin da kirjinta yayi mata yayi sauki lokutta da dama, ko yau da ta tashi ta gwada shiga wajen hotunan wayarta ta ga na Bilal, amman yanda zuciyarta take dokawa sai ta kasa.
Sai dai rashin ganin hoton bai rage mata zafin rashin Bilal ba, bai kuma hana mata ganin shi a cikin idanuwanta ba, ko suna rufe ko suna bude. Yanzun ma hannunta ta dora saman cikinta tana shafawa a hankali. Tudun shi na tabbatar mata da yana nan, da dane yake girma a cikinta, abinda har yanzun ya kasa samun wajen zama a kwakwalwarta. Gyara kwanciyar ta tayi, tana jin hawayen da ta saba dasu yanzun suna silalowa ta gefen idanuwanta zuwa kan filon da take kwance a kai. Akwai tarin abubuwa da har yanzun basu gama zauna mata ba, taji ciwon su harta san yanda zata fara jinyar ciwukan balle kuma ta fara hango ranar warkewar su.
Tunanin Rayyan ne ya kara dirar mata, yana saka hawayenta cigaba da gudu. Rayyan da ya samu da kyar ya raba jikin shi da gado ya fito yana nufar bangaren Ayya dan ya dauko ruwa, babu wanda yayiwa magana ya wuce Kitchen ya dauki ruwan ya sake ficewa. Ayya ma da take zaune kan kujera bin shi tayi da kallo. Rukayya take ce mata ruwan saura leda biyu ajiye a kasa, na cikin fridge din kuma wasu duk sunyi kankara, batama iya amsa Rukayya ba, wayarta da take gefe ta janyo da nufin ta kira Bilal tace mishi ya kira yan gidan ruwan kai tsaye yaji idan zasu shigo yau suna so. Da yake nan makotan su ta gefe matar na siyar da ruwa, zobo da kunan Aya.
Harta dauki wayar ta cire daga key zuciyarta tayi wata irin dokawa, komai na dawo mata. Tana tunanin yanda zata fara rayuwa babu Bilal a ciki, babu yaronta. Saboda bata hango ranar da komai zai dawo mata dai-dai ba. A rayuwar ta gabaki daya ko a mugun mafarki batayi hasashen daya daga cikin yaranta zasu barta ba, duk yanda takan hango rayuwa mai karewa ce, ita take ganin zata mutu tabar su, kamar yanda nata iyayen suka mutu suka barta. Sai dai mutuwa ba zabe takeyi ba, lokaci me kawai abinda take dubawa, babu ruwanta da yanda makusantan wanda ta dauka zasu kasance cikin jimami da radadin rashi.
Da mutuwa na duba wannan da tabar mata yaron ta. Yanzun ta dandani zafin rashi na daban, ta san yanda kakeji idan ka rasa danka. Sai dai bakowa bane zai fahimci yanda kakeji idan kayiwa dan da aka fada maka ka rasa batare da kaga gawar shi ba kuka. Saboda bata jin har abada wani bangare na zuciyarta zai aminta da ta rasa Bilal, zataci gaba da kallon kofa, da tsammanin shigowar kowa a matsayin danta, saboda bata ga gawar shi ba, bata kalle shi a shimfide a gabanta ba. Shisa mutuwar shi take mata wahalar dauka.
Jiya ma Abbu sai da ya fara mata wani wa’azi da bata fahimta, tace mishi
“Ahmadi ba ganewa zanyi ba wallahi, ka kyaleni inyi kuka ko zuciyata zatayi mun sauki…”
Kyaleta din yayi kuwa. Yanzun ma hannu ta saka tana goge hawayen da suka tarar mata a gefen idanuwanta. Hakuri ya zame musu dole ta sani, amman yanzun zatayi kuka, zataji ciwo, hakurin zai biyo bayan su. Wayar da ta ajiye ce ta dauki ruri, ta dan kalleta, ganin Hajiya Dije rubuce a jiki ya sakata daukar wayar, cikin sanyin murya tayi mata sallamar da ko amsawa batayi ba.
“Ya karin hakuri Maimuna?”
Numfashi Ayya ta sauke, kiran na tuna mata da sau daya Hajiya Dije din tazo mata gaisuwa. Abin na kara bata mamaki duk kusancin su.
“Alhamdulillah”
Ayya ta sake amsawa har lokacin muryarta a sanyaye.
“Ina ta so in shigo dan mu samu mu zauna. Ranar naga ga mutane ga shi kuma rasuwa na tabaki.”
Shiru Ayya tayi tana jin Hajiya Dije ta cigaba da fadin,
“Wallahi sai kin tashi tsaye sosai. Kinga me nake fada miki ko? Haka ake so a kada miki kan yaran duk su cimma ajalin su. Kudi zaki turo inje miki wajen Sharu dana samo kwanaki.”
Dan dafe kai Ayya tayi, tana mamakin hali irin na Hajiya Dije da yanda akayi bata ga kuskuren da yake tare da duka shawarwarin da take bata a baya ba. Danta ya mutu ba zata ko barta taji da abinda yake damunta ba, tana son nuna mata cewa mutuwar Bilal din ma ba daga Allah bane ba. Bata ce babu sihiri ba, amman duk abinta tasan abubuwa da yawa daga Allah ne. Da Malaman na da amfani da sun hana ma Mami aure mata miji, sun taimaka mata ta fitar da ita daga gidan. Amman da yake abin duk bigene ga Mami nan zaune daram a cikin. Ita da suna wani aiki duk bugun kasar da sukayi mata da sun hango mata kaddarar Layla da Bilal.
“Ba wannan bane a gabana Hajiya Dije. Banda duk wannan lokacin yanzun.”
Ayya ta furta wani abu na tokare mata makoshi.
“Bangane baki da wannan lokacin ba? Kar dai an saka miki shashatau ni Dije…”
Dan karamin tsaki Ayya taja a cikin ranta.
“Wai ke babu wani abu da zai faru da ba asiri bane ba? Idan ma shine na bar mutum da Allah. Dan Allah ki kyaleni inji da abu daya.”
Bata ma jira Hajiya Dije ta amsata ba ta katse kiran. Tana jan tsaki a fili, kawai sai taji ranta na baci da abinda Hajiya Dijen tayi mata. A lokaci daya hawaye masu zafi na zubo mata. Bilal da zai mata hirar shi sai ya ga tayi dariya ma baya nan. Mikewa tayi ta shige daki, ta dan fito ne ko zata sami saukin abinda take ji daman.
*****
Ruwan ya ajiye a gefe, tun jiya da dare ya kare mishi. Haka ya dinga juyi a gado, ya tashi yaje ya dauko abin na mishi wani iri. Guda daya ya fasa ledar ya dauka, anan tsayen ya shanye, yana jin muryar Bilal kamar yana dakin,
“Ba kyau shan ruwa a tsaye, ka samu waje ka zauna, ka juye a kofi.”
Da dafe kan shi yayi, kirjin shi na daukar zafi. Karasawa yayi kan gadon ya koma ya kwanta. Gobe ne ya saka ranar da zai koma Kaduna. Saboda sati daya suka bashi, har gida Bappa yazo musu gaisuwa shi da Baba da yayi ma Rayyan din nasiha mai shiga jiki ganin yanda ya rame yayi duhu. Nasihar da bata kai mishi daren ranar ba ya nemeta ya rasa. Kusan kullum ma kuka yake yanzun, daren jiya wando zai dauka ya ga rigar Bilal, kawai yaji idanuwan shi sun cika da hawaye. Yanzun ya yarda da maganar Bilal da suna kallon wani film yana mamakin yanda hawayen jaruman mazan suke a kusa.
“Kuka fa shi yake yin kan shi Hamma, karka yi mamakin ganin kana hawaye kamar karamin yaro.”
Kai kawai ya girgiza, saboda yasan suna da bambanci mai nisa da turawan da suke kallo, yanayin rayuwar su, da komai daban ne. Sosai ranar ya dinga tunanin a duniya abinda zai saka hawayen shi zuba. Sai gasu yanzun, kila duk wanda suka taru ne shekara da shekaru suke fitowa gabaki dayan su yanzun. Wayar shi ya mika hannu yana dauka. Da yake ya kashe karar gabaki daya, baima bi ta kan tarin kiran da aka dinga yi mishi ba. Ya san ba zai wuce Layla ba. Bai ganta ba tun rasuwar, baya so ya ganta saboda yayi waje a kasan zuciyar shi ya dannata. Mutuwar Bilal ce a gaban shi, baya son tunanin komai.
Haka kawai ya tsinci kan shi da bude bangaren sakon shi, yana cin karo dana Layla sun fi guda arba’in. Can kasa yayi yana cigaba da dubawa, na MTN ya dinga goge su, saina banki ma duk yabi ya goge. Zuciyar shi nayin tsalle zuwa makoshin shi, jikin shi har bari yake lokacin da yaga sakon Bilal. Da sauri ya bude yana soma karanta na farkon,
“Ban san me zance ba Hamma, na ce ba zan roki ka yafe mun ba saboda ina jin ban cancanci hakan ba. Amman na kasa, rokon yafiyar ka na daga cikin abu na farko da nake son yi. Ka yafe mun, dan Allah ka samu waje a cikin zuciyarka ka yafe mun.”
Numfashi yake fitarwa a hankali lokacin da ya sake bude wani sakon.
“Kana cikin rudani kamar yanda nake ciki daga randa abin ya faru zuwa yau. Baka tambayeni ba, nayi kokarin maka bayani iya yanda zan iya kaki saurarena, dan Allah ka karanta abinda zan fadi, bance ka fahimce ni ba, ni kaina ban fahimci komai ba. Amman ka karanta.”
Jikin shi Rayyan yake ji ya dauki dumi kamar ana hura mishi wuta, da kyar ya iya samun karfin motsa yatsan shi ya latsa wayar yana samu ya shiga wani sako da alamu ya nuna mishi dogo ne,
“Na kaika ta sha ranar na koma gida, laifina ne da ban kunna fitilar dakin ba, amman mun saba Hamma, sai muyi shiga nawa da duhun dakin, ban san tana ciki ba, wallahi ban kawo ma raina Layla na ciki ba, watakila daga baya ta shigo, shima ban san shigowar ta ba. Ruwa kawai na dauka akan tebir na sha, sai kaina ya fara nauyi na kwanta. Ban san me ya faru ba, ban san ya akayi abinda ya faru ya faru ba, ba ina kokarin wanke laifina bane. Ina so ka sani ne kawai, kaji nawa bangaren Hamma, wallahi ban san ya akayi ba. Ka yafe mun, ka yafe mata itama, karka bari kuskurena ya shiga tsakanin tarin kaunar da take yi maka.”
Rayyan bai ma duba dayan sakon Bilal din ba, saboda zuwa lokacin ya tashi zaune, da sauri yake shiga sakonnin Layla yana son tabbatar da abinda tunanin shi yake kawo mishi .
“Dan Allah Hamma, wallahi ban nufin in kwanta bakwa nan ba, ruwa kawai na sha sai in dan huta in tafi, jikina yai mun nauyi, naji bani da lafiya lokaci daya. Shine na dan kwanta in nutsu…”
Bai karasa karantawa ba saboda yanda komai yake hautsina mishi. Numfashi yake kokarin fitarwa cike da tashin hankali, baisan lokacin daya danna lambar Layla ba ya kara a kunnen shi, baima ji tayi ringing ba sai dai muryarta da yaji cikin kunnen shi.
“Hamma… Hamma na.”
Ta furta tana saka wani abu ya tsirga mishi, da kyar ya iya lalubo yawu ya jika harshen shi da yake ji a bude kafin ya bude bakin shi.
“Ruwan da kika sha… Layla ruwan da kika sha a roba ne?”
Harya bude bakin shi zai sake tambayar ta ta amsa,
“Eh…”
Wani nannauyan numfashi yaja kirjin shi kamar an kulle.
“Zaki tuna a ina kika dauka? A cikin dakin mu a ina?”
Wani shirun ta sakeyi da yake ji har bayan zuciyar shi.
“Na zauna a gefen gado, anan nagan shi, an sha ne an ajiye kamar, me ya faru?”
Wayar ya sauke daga kunnen shi, baima kashe ba ya mike yana dora hannuwan shi saman gwiwoyin shi ya dan rankwafa kamar mai shirin yin raku’u kafin ya sake mikewa yana furzar da iska ta cikin bakin shi. Ruwan da ya ajiyene suka dauka, daga ita har Bilal ruwan da ya durama kwayoyi ne suka dauka suka sha. Laifin da yake fadama Bilal ba zai yafe mishi ba, laifin da ya ke son taba zuciyar Layla kamar yanda ta taba tashi a kai ne yayi yawo ya zagayo ya shake mishi wuya yana girgiza gabaki daya rayuwar shi. Dakin yake gani kamar yana kara zurfi, ko kuma shine yake shigewa cikin wani irin rami da baisan akwai a dakin ba ya rasa.
Sai da tafukan kafar shi suka taka kasa ya gane sun dauke shi zuwa wajen dakin, sun kuma ja shi zuwa bangaren Ayya. Kamar su suke da iko da shi, yanajin dai zuciyar shi take iko da gabaki dayan su, saboda ita ce take son kallon idanuwan Ayya ta fada mata yanda shine sanadin rayuwar Bilal, dan da tafi shakuwa da shi sama da su. Da bai zuba kwayoyin a ruwa ba, da ya zuba din daya shanye abin shi, ko ya fitar da shi. Da ba su dauka ba, Bilal da Layla da basu gani ba sun sha har sunzo in da suke yanzun. Da suna zaman su lafiya, suna rayuwar su cikin walwala. Duka laifin na shi ne, ko da bai ganta a falo ba dakin baccin ta ya karasa yana kwankwasawa, sai da yaji ta bashi izinin shiga sannan ya tura kofar ya shiga yana mayarwa ya rufe.
“Ayya laifina ne, ni na kashe Bilal…”
Murmushi Ayya tayi mai ciwo, idan aka tsaya zakule-zakule tana da tabbacin laifin zai rarrabu, kuma daga Mami har Abbu ba zasu fita ba. Mami ta dauko musu Layla kamar yanda Rukayya ta fadi, Mami kuma tabarta zuwa Zaria da yardar Abbu. Duk da wani abu a kasan zuciyarta yana fada mata kaddarar da tabi Layla da Bilal Zaria zata iya samun su a cikin gida. Amman kuma ba zata ji kamar laifin na su Mami bane ba, idan har kaddarar ta biyo su Bilal har gida, ba zataji duk wannan abin da take ji ba.
“Ka bar fadin haka Rayyan, mutuwar sabuwa ce shisa. Kowa ma idan ya zurfafa tunani zai iya ganin kamar laifin shine.”
Saboda itama tanajin akwai nata laifin, da ta duba Bilal din da dare, bayan yabar dakin Abbu da taje tayi magana da shi. Da ta canza mishi tunani da cewar tafiyar ba mafita bace ba, tafiyar kuma ba zata kawo sauki a zukatan su ba. Amman batayi ba, laifin nan zai zauna da ita na lokaci mai tsayi. Kai Rayyan ya girgiza mata, sosai take kallon shi, zuciyarta na matsewa a cikin kirjinta, duhun da yayi a kwanakin sai kamanin shi da Bilal suka kara fitowa, sai dai Bilal kullum baka raba fuskar shi da fara’a.
“Laifina ne Ayya… Ni na zuba abu a ruwa ya sha, duka laifin nawa ne.”
Cike da rashin fahimta Ayya take kallon Rayyan din, Haris yace sai ta dinga mishi addu’a saboda yanda mutuwar Bilal ta dake shi, karya samu matsala. Bata dauki abin da muhimmanci ba saboda itama mutuwar ta dake ta. Sai yanzun da yake mata wasu zantuka da bata ganewa. Numfashi yaja yana kokarin bude kafofin shigi da ficen iskar shi da suka toshe, ba zai manta wayar Bappa da Baba ba, kuma Bappa yace mishi.
“Sihiri gaskiya ne Rayyan, mutane ba su da kirki wani lokacin, Baba bai gayamun kai tsaye ba, amman ciwon ka na da alaka da hakan.”
Bai amsa Bappa ba, saboda bashi da abinda zaice, baiga dalilin da wani zai yi mishi sihiri ba, idan anayi din kenan. Kuma ace tunda karancin shekarun da yasan bai isa daukar hakkin kowa ba balle aji haushin shi, ko a yanzun da girman shi bashida wani abu da zai tsarewa wani komai. Kuma sihirin ace an hana kusancin shi da iyayen shi? Abin da wahalar dauka, sai dai a halin da yake ciki yanzun zantukan dawo mishi sukeyi, ko zai samu wanda zasu raba laifin da yake ji tare, dan nauyin laifin yana gab da danne shi idan har bai raba da wani ba.
Yau daya zaice da ba’ayi mishi sihiri ba da bai fada depression din da yaja mishi shan kwayoyin da ya zuba a ruwa harsu Bilal suka dauka ba, yana son ya kalli idon ko waye yayi sanadin zuwan su inda suke yanzun ko zai samu sauki.
“Sihiri akayi mun, ba laifina bane ba nima.”
Ya tsinci kan shi da furtawa.
“Baba ne ya fada, kuma yayi mun addu’a na samu sauki yanzun, koma mene ne Bappa yace naci ne ko na sha a cikina shisa bana son zama waje daya da ku, da Abbu, bana son duk abinda Abbu yake so, Ayya wani marar imani zai raba da iyayen shi? Ribar meye zai samu?”
Da farko ta dauka matsala Rayyan ya samu, sai da kalaman shi suka daskarar da ita a inda take zaune suna saka wani irin sanyi ziyartar ta kamar tana cikin fridge. Shi kan shi baisan me yake fadi ba, kawai so yake yau duk abinda zai iya amayarwa ya amayar ko zai daina jin nauyin abinda ya yi.
“Baku sani ba, Bilal bai sani ba amman ina shan kwayoyi, sune na zuba a ruwa har ya samu ya sha, har suka sha da Layla… Laifina ne Ayya… Ina jin laifina ne. Amman idan da gaske sihiri akayi mun, ni wa zan daurawa laifi? Wa zance ya kawo mu inda muke yanzun ko zan samu sauki. Ayya ina zan kai laifin nan?”
Rayyan ya tambaya yana kallon cikin idanuwanta.
“Ya zan fara rayuwa a duk rana da sanin nayi sanadin mutuwar Bilal?”
Ya karasa maganar wasu hawaye na cika misji idanuwa. Numfashi me nauyi ya sauke yana sake kallon Ayya da ta sadda kanta kasa, bata son ganin shi, ya kashe mata yaro dole taki son ganin shi, shima baya son ganin kan shi yanzun nan. Juyawa yayi yana ficewa daga dakin, sai dai baisan inda ya kamata ya nufa ba, bakin kofar dakin su ya tsaya yana tsintar kan shi da kasa shiga. Abu daya zai gani na Bilal abinda yake ji yana gab da ballewa a tare da shi zai balle, tsaye yake yana maida numfashi yana kuma son ganin hawayen da suke cikin idanuwan shi basu zuba ba. Kirjin shi ya dan dafe yana murza inda yake ciwo kamar zai rabe biyu.
“Hamma…”
Yaji muryar Layla da ta saka shi juyawa, kamar tsayuwar wahala take mata shisa ta dafa bango. Ta dade bakin kofa ko zata ga giccin Mami kafin ta samu ta fito, tana jin numfashin da Rayyan din yake fitarwa ta cikin wayar cikin yanayin daya daga mata hankali, gashi tanata magana shiru kafin kiran ya yanke. Zuciyarta ta kasa hakuri, wata irin soyayyar shi ce take dawainiya da ita, tunanin halin da yake ciki, tsantsar ciwon zuciyar da taji a cikin muryar shi ya hade yana sakata kasa hakuri sai ta gan shi, ko na dakika biyu ne ta leka taga yana nan dai zata samu sauki. Sai da ta fara takowa taji kamar tana yawo saman iska.
Shikuma kallonta yakeyi, idanuwanta na saka shi jin wani iri, amman ya kasa daina kallon su, saboda a cikin su yake ganin tarin rudani a shimfide, kafin ya samu ya kalli duka fuskarta da har zanen kashin kuncinta ya fito kamar wadda ta dade tana jinya, tayi zuru zuru ta fita hayyacinta. Tana cikin firgicin da yake jin duka shine silar shi.
“Layla”
Ya kira da wani yanayi mai wahala.
Idanuwanta cike taf da hawaye tana jan numfashin da ta fitar da shi tare da hawayen ta da suka zuba, dayan hannunta ta saka ta share su, tana kallon yanda fuskar shi take cike da gashi, kayan jikin shi sunyi daudar da bata taba ganin shi da ita ba, shi kan shi ya mata wani irin cuku-cuku. Ko takalma babu a kafafuwan shi, Rayyan da ko a daki baya yawo babu takalmi ko safa, Rayyan da ta san zai iya wanka hudu a rana, shine yau a firgice haka. Hannunta ta kai tana dafe cikinta da taji kamar ya kulle, yanayin da ya saka Rayyan bin cikin nata da kallo.
Akwai yaron Bilal a cikin nata, a jikinta yana rayuwa, kwai daya da Bilal yake da rabon samu a duniya. Kwan da zaizo ta hanyar da kowa yake gudu saboda shi.
“Ki yafe mun Layla.”
Yayi maganar yana sadda kan shi kasa, wasu hawayen ne masu zafi suka zubo mata, bata san me yasa yake rokon ta yafe mishi ba. Bayan ita din ya kamata ta roki ya yafe mata. Jin tayi shiru ya saka shi sauke idanuwan shi cikin nata, yana jin yanda bata kyauta mishi ba.
“Ban hana ki zama a gidan mu idan bana nan ba? Me yasa kika zauna?”
Kafadu ta dan daga mishi, bata da bakin magana bata da wani bayanin da zatayi mishi.
“Baki kyauta mun ba, kin sani ko?”
Da ta taimaka mishi bata zauna ba, da ya gujema abubuwa da yawa. Duk da kukanta na kara mishi zafin da zuciyar shi takeyi. Amman yana bukatar raba laifin da wani. Numfashi ya sauke ya juya da nufin shiga daki.
“Hamma…”
Ta kira shi, juyowa Rayyan yayi, kuka yake so yayi har sai inda hawayen shi suka tsaya. Amman baya son yi a gabanta. Baya son kowa ya lallashe shi. Idan ya gama duk zai roke su da su yafe mishi, sai ya kara yawaita addu’o’in shi akan Bilal ko zasu isa wanke girman abinda yayi mishi idan suka tsaya a gaban Allah.
“Idan na kira ka daga, dan Allah kayi mun kowanne hukunci karka rabani da kai, abubuwan da suka rage mun basu da yawa.”
Kai kawai ya iya daga mata yana shigewa daki. Wani irin numfashi ta sauke mai nauyin gaske tana samu ta koma bangaren su tana wucewa daki. Wannan karin waje ta samu ta zauna, kafafuwanta taja ta hade su da kirjinta, sai taji bata iya fitar da numfashi sosai, kamar ta matse cikin nata da yawa, babu shiri ta sauke kafafuwan nata, kafin wani irin tashin hankali ya dirar mata, cikine a jikinta da gaske, da duk ranar da zata wuce da yanda cikin zai cigaba da fitowa. A hankali take jin yanda ba rabuwa da Rayyan bane matsalarta ta farko, yanda zata fara rayuwa da cikin da in ya tako duniya bata da amsar bashi, cikin da Bilal baya nan ballantana ya tayata yi mishi bayani.
“Na shiga uku.”
Ta furta a hankali tana fashewa da kuka, komai nata ya canza, rayuwarta, makaranta, watakila tabarta kenan har abada, idan haihuwa tayi ta ina zata fara yawo da yaro cikin mutane, me zata ce musu idan sun tambayeta? Ya Mami zata fara shiga dangi, wacce tambaya kowa zai jefe ta da ita? Watakila kowa ya fara tunanin Mami bata riketa da kyau ba, su Abbu basu riketa da kyau ba saboda ita din ba yarsu bace ba. Duk yanzun ne ta samu damar yin wannan tunanin da yake kara daga hankalinta, kasa ta kwanta kan tayal din dakin da sanyin shi ke kara mata zazzabin da ya sake saukar mata, kuka takeyi marar sauti, kukan da bata hango ranar da zata daina shi ba.