1986, Kano
Yaron da yake rike a hannunta take kallo, yaran da duka satin shi biyar a duniya, wasu hawaye masu dumi na tarar mata cikin idanuwa. Amman zuwa yau tasan cewa kukan nan babu wani amfani da zai musu, kukan ba zai dawo mata da kaninta ba, ba zai canza kaddarar yaron da yake hannunta ta Maraici a satika biyu bayan haihuwar shi ba. Ba zatace tashin hankali bakonta bane ba, tasan shi a lokacin da ta raya Yayya, ta kuma san shi a lokacin da Ahmadi ya hadata da Maryama da ta zame mata Karfen kafa. . .