Skip to content
Part 30 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Dan ware idanuwa Bappa yayi, yana sake kallon farantin da yake gaban Rayyan a ajiye,

“Meye wannan Rayyan?”

Ya bukata, Rayyan din na dan juya idanuwan shi, yasan sarai Bappa ya gane plantain ce, tunda suka kwaso ta da dankalin turawa, sau biyu yaga Bappa ya soya. Abin a ido kamar ba zai wahala ba, sai da yazo tun daga yankawar ya gane aikin ba karami bane ba, da yake man yayi zafi sosai sanda ya zuba kafin ya juya wata, wata ta kusan konewa, gabaki daya sunyi baki, har cikin makoshin shi yana jin daci-dacin da sukayi. Sai dai yunwa yake ji da yake ranar ta zo musu a karshen mako, Bappa din kuma ya fita, yana jin kwiyar zuwa ya siyo wani abu.

“Da me yayi maka kama?”

Rayyan ya amsa tambayar Bappa din da wata tambayar, yana sake saka cokali mai yatsu ya caki guda biyu ya saka a bakin shi yana taunawa kamar babu dacin da Bappa yasan zatayi, dariya Bappa yayi.

“Ka tashi mu fita, nima ba abinda naci”

Kafada Rayyan ya makale, bayajin zuwa ko ina.

“Me yasa bakayo mana take away ba? Dole sai ka dawo ka fitar da ni.”

Tunanin ne bai zo ma Bappa ba sam, saboda yasan halin Rayyan din, bakomai na waje yake ci ba, idan suka fita tare saiya zaba da kan shi, ba’a cika yi mishi gwaninta ba.

“Ka tashi dan Allah, ba kana maganar waya ba? Sai mu biya ka duba.”

Dan jim Rayyan din yayi, da gaske yana son siyan babbar waya. Saboda yanzun sukanyi kwanaki har biyu ko fiye da hakan ma tunda ya dawo basuyi waya da Layla ba. Sukan yi musayar text dai, ta cikin su yakan fahimci kamar yanzun tana rasa abinda zatace mishi, idan suka gaisa sai ya jima yana kallon wayar yana jiran yaga amsarta, sai yake tsintar kan shi da tunanin ko tana lafiya ko akasin hakan. Idan ya kira ma wasu lokuttan bata dagawa, ba ko yaushe take biyo kiran ba sai dai idan ya sake gajiya ya kara kiranta.

Yasan zai iya zuwa gida idan yana so, Bappa da wahala yayi kwana biyar bai shiga Kano ba, yawon shi har mamaki yake bama Rayyan din, gidane bayason zuwa, tunanin ya shiga dakinsu babu Bilal yana mishi wani iri. Duk da akwai damuwar da ta daga a kirjin shi baya nufin baya kewar Bilal din, ba kuma ya nufin tafiyar da Bilal yayi bata mishi ciwo, yana dannewa ne.

“Zaiyi sauki, In shaa Allah komai zaiyi sauki.”

Bappa kan yawaita fada mishi haka kawai idan yaga yayi shiru yana kallon bango. Baya amsawa, baya tunanin Bappa nayin maganar ne dan yana jiran ya amsa mishi. Kawai yanayine saboda yasa shi yaji kamar wani ya damu, kamar yana kula da yanayin shi. Kuma yanaji din, har cikin zuciyar shi yanajin kulawar Bappa da baiyi tunanin wani bayan Bilal da Layla zasu gwada mishi ita ba. Su Ayya iyayene, bayajin akwai zabi a tasu kulawar, kamar da haihuwar shi da yanda kula da shi ya zame musu tilas ko da basa son hakan, ko da ta takaitaccen lokaci ce.

Watakila Bilal na kula da shi saboda su din yan uwane, Layla kuma dan tana son shi. Kusan suma zaice basu da zabi, amman Bappa na da zabi, sai ya zabi kula da shi, ya zabi yi mishi karamci duk da shi din bashida wani abu da zai iya mayarwa Bappa da shi.

“Zama da kai ba abu bane mai sauki Hamma.”

Bilal ya taba fada mishi da sukayi wani rikici, kuma yasan gaskiya ya fada. Amman Bappa na zaune da shi kamar hakan abune mai sauki. Bappa ya bashi abinda bai taba tunanin zai samu ba a rayuwar shi, ya bashi abota. Satin su biyu da dawowa Kaduna aka koma makaranta, da yake akwai kanin Bappa a ABU din shisa ma Rayyan yasan an koma. Rana daya ya tambaya a wajen da suke serving aka kuma bashi, da yacewa Bappa zaije Zaria da mamaki ya kalle shi.

“Me yasa yau? Ka bari sai weekend mana mu shiga tare.”

Kai Rayyan ya girgiza mishi.

“Akwai abinda zanyi yau din shisa.”

Yana jin dadin da bakomai Bappa yake tsaurara tambaya a kai ba. Fatan alkhairi kawai yayi mishi dana Allah ya tsare hanya. Dan da yace ya kai shi tasha yace zai hau mashin. Abinda duk yake bukata yana cikin yar jakar shi daya goya a baya yana ficewa daga gidan zuwa ta sha. Saura mutum biyu motar ta cika sanda ya shiga, aikam yana zama ana kara samun wani, sosai yaga saurin saukar su, ko dan tunanin da yakeyi ne. Kan shi tsaye makaranta ya wuce, abinda bai taba tunanin zaiyi ba shi yayi, har Office din wasu cikin Malaman shi dan ya tambayi abinda yake bukata din.

Sun kuma karbeshi a mutunce haka amsar duk tarin tambayoyin da yayi. Kananun kayane a jikin shi, rigar mai dogon hannu, shigar da baka raba Bilal da ita. Bai taba tsintar kan shi a yanayin da yake ji ba yau, musamman da ya kasa tuna wanne kalar passport ne Bilal ya manna a jikin takardun su, ko kamannin su sun fito ko basu fito ba. Sauran semester daya Bilal ya kammala karatun shi, yana ji a jikin shi zai dawo, yana kuma fata da addu’ar dawowar ta zamana a kusa, ya iya kalar signature din Bilal, dan ya ko shi Bilal yakan yi mamaki.

“Dan dai kana zane ne, shisa bai maka wahala ba.”

Cewar Bilal wani lokaci can baya, bai sha wahalar tsayar ma da Bilal karatun ba, yayi amfani da uzurin rashin lafiya ne. Kusan rabin rana yana abu daya, dan akwai kudin da ake biya kafin a iya. Wajen uku saura ya samu ya kammala komai, saiya tsinci kan shi da samun wata natsuwa da baisan daga inda ta fito ba. Baisan kafafuwan shi na daukar shi zuwa gidan su ba sai da ya gan shi a kofar gida, akwai mukullin daki a jakar shi, dan haka bai sha wata wahala ba daya shiga, ya daiyi mamakin yanda jikin shi ya dinga bari wajen budewa.

Yaji dadi sosai da bai samu kowa daya sani ba harya shiga. Dakin zaka rantse anyi watanni ba’a shiga ba saboda kurar da yayi. Sai yaji zuciyar shi ta matse a kirjin shi, tsaye yayi a tsakar dakin yana ganin rayuwar da sukayi a cikin shi kamar an kunna film, yana ganin Bilal a ko ina na cikin daki, yana jin shi a ko ina na zuciyar shi da take wani irin ciwo da baiyi tsammani ba. Ba zaice ga lokacin daya dauka a tsaye a wajen ba, wayar shi da ta fara ihu a aljihun shi ce ta katse mishi tunanin da yayi zurfi a ciki, ko dubawa baiyi ba bayan ya dauka ya daga kiran, karawa yayi a kunnen shi.

“Hello…”

Ya fadi muryar shi na fitowa daga can kasan makoshi.

“Rayyan”

Yaji muryar Haris cikin kunnen shi da ta saka shi yin gyaran murya saboda yanayin da yake ji.

“Hamma”

Ya iya fada, muryar shi na fitowa a shake.

“Kana ina? Me ya faru?”

Haris ya tambaya cike da kulawa, yanzun da ya dawo kamar kowa yake jin yanda bai cancanci tarin kaunar da yan uwan shi sukeyi mishi ba, saboda sam bai tuna wani lokaci daya nuna musu ko da kadan a cikin kalar kaunar da sukeyi mishi ba. Amman yana tuna yanda duk ture sun da yayi bai hana su kokarin kusantar shi ba. Kaunar su daban take, kaunar su na da alaka da jinin shi da yake yawo a nasu.

“Rayyan kayi mun magana dan Allah.”

Numfashi ya sauke,

“Zaria, ina Zaria Hamma.”

Haris ya dan jima kafin yace,

“Zan kwashe kayan, munyi maganar da Ayya, ka bar shi karshen makon nan da yardar Allah zan shigo Zaria din.”

Numfashin Rayyan ya sake saukewa,

“Kar ka bayar da komai, duka komai da komai.”

Duk da baya gani yasan kai Haris din yake daga mishi.

“Babu abinda zan bayar, duka zaka zo gida ka samu kayan. Ka dai fito daga gidan idan kana can, kana jina, ka fito ka tafi…zaka iya ai ko?”

Dan murmushi ya kwacewa Rayyan.

“Ba yaro bane ni Hamma…”

Yanajin dariyar Haris din, bai jira yace wani abu ba ya sauke wayar daga kunnen shi yana katse kiran kafin ya mayar da ita aljihun shi. Da gaske kirjin shi zafi yakeyi, kasancewa a cikin dakin ya dawo mishi da abubuwan daya dauka ya rabu da su. Kasancewar shi a dakin ta saka mishi wasi-wasin da bayason zurfafa tunanin shi a kai sam. Shisa ya dauki shawarar Haris din ya fice daga dakin ya mayar da shi ya kulle yana fita daga gidan. Ko daya karasa ya shiga motar da ta mayar da shi Kaduna bai daina jin kirjin shi na zafi ba.

“Magana fa nake tayi maka.”

Muryar Bappa ta daki kunnen shi tana dawo da shi daga tunanin daya zurfafa ciki. Mikewa yayi yana fadin.

“Dole dai saika fitar da ni…”

Bappa bai kula shi ba ya juya, shima bayan Bappa yabi har suka fita daga gidan zuwa inda motar Bappan take suna shiga.

*****

Ba zatace duka duniyar ta daina yi mata dadi ba, saboda yanzun duniyarta ta tattaru ta dawo cikin dakinta. Anan take gudanar da rayuwarta ta yau da kullum, ko da safe ba kullum take samun karfin zuwa su gaisa da Mami din ba. Sai dai ita ta shigo ta dubata, saboda cikinta daya fara fitowa sosai, bata son Mami na ganinta, kowa ma na gidan bataso yana ganinta. Sai taga kamar basa ganin komai a tare da ita, kamar hatta da sunanta ya bace, banda cikinta babu wani abu da kowa yake gani a tattare da ita yanzun. Jafar ne kadai yakan fito da ita falo wasu lokuttan.

“Malama fito kiga wani abu.”

Yakan ce, duk iya kokarin shi na ganin bai nuna cikin jikinta ya dame shi ba, a muryar shi takan ji canjin da ya faru da rayuwar su gabaki daya. Ta kan biye Jafar din suyi kallo tare har su danyi hirar film din, amman gabaki daya babu wani abu da take jin dadin shi. Ba dai ta iya cin wani abu sai mai manja, in dai ba girkinta ita kadai Mami takeyi mata ba to duka dakin su an koma cin abinci ne da manja. Shima kawai wasu lokuttan takan ji idan bataci ba kamar zata mutu, sai kuma yoghurt da baya yanke musu a cikin fridge.

Lokutta kamar irin yau da take zaune dafe da cikinta, hawaye ne masu ciwo suke zubar mata, tun tana daukar zasu kare har ta daina yanzun. Takan yi kukan halin da take ciki, takan kuma yi kukan rashin Bilal ba kadan ba, a hankali a hankali mutuwar ta dinga tabata kamar ciwonta ba zaiyi mata sauki ba. Anisa kuwa yanzun ba sosai suke magana ba, tunda Layla ta fada mata anwa Abbu transfer ne zuwa kudu, shine suka koma gabaki dayan su, sukan gaisa lokaci zuwa lokaci ne. Zuwa yanzun makaranta ce karshen abinda yake ranta, ta rigada ta cire karatun daga zuciyarta.

Rayyan na kokarin kiranta, shima batasan me zatace mishi ba a yanzun. Ko wanka ta shiga bata tsayawa kallon kanta, saboda bata son ganin yanda gabaki daya jikinta ya canza. Jiya ma sai taga kamar har fuskarta ta canza, bata san ko dan ta jima bata kallo mudubi bane ba. Yau ma sam batayi marmarin kallo ba, da ta sau wata doguwar riga ta zira a jikinta sai ta koma kan gadonta. Idan har bata son ganin kanta, tana da yakinin Rayyan ma ba zaiso ganinta ba, ita da kanta ba zataso yaga canjin da yake tare da ita ba.

Zatayi karya idan tace zuciyarta bata mata zafi, amman a cikin abubuwan da ta nisanta zuciyarta da su, samun Rayyan na daya daga cikin su. Ba abu bane mai sauki, amman da duk ranar da zata wayi gari da yanda take kokarin yin wani tunani na daban, tana hasaso dirowar abin da yake cikinta. Tana kuma tunanin yanda rayuwa zata kasance mata bayan hakan, duk ta yanda ta hasaso abin ba mai sauki bane, tsoro da zullumi sun bata taimako wajen danne Rayyan can kasan zuciyarta.

Alamun shigowar sako take ta ji, hawayenta ta share tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta dauki wayar tana budewa ta duba. Sai da taji zuciyarta tayo wani tsalle kamar zata baro kirjinta, mamaki na dirar mata ganin Rayyan ne yayi mata magana a manhajar whatsapp.

“Layla.”

Sakon shi na farko kenan.

“Na siya waya.”

Ta sake karantawa.

“Ba kya magana dani kwana biyu ko?”

Murmushi tayi me ciwo, ta fara rubutu yafi a kirga tana gogewa cikin rashin sanin abinda ya kamata tace, kafin ta yanke hukuncin fadin gaskiya, abubuwan da suka rage mata basu da yawa, ba zata bari gaskiyarta ta kwace mata ba, musamman ma a wajen shi.

“Komai ne baya mun dadi Hamma, duniyar duka ta tsaya mun waje daya.”

Kallon shi tayi yanata rubutu.

“Zai wuce wata rana, ki daure.”

Kai ta jinjina kawai, har zata ajiye wayar saboda bata san me zatace mishi ba ya sake fadin.

“Ki turomun duka hotunan mu.”

Bata san me yasa taji cewa harda na Bilal yake nufi ba, duk da bai ambaci suna ba. Jikinta har bari yakeyi lokacin da ta shiga gallery din, tana binciko hotunan da ta kasa dubawa duk yanda taso yin hakan. Idanuwanta cike taf da hawayen da batayi kokarin hanasu zubowa ba ta fara tura mishi duk wani hoto na Bilal da taci karo da shi, kafin ta tura mishi nashi da take da shi, sai na shi shida Bilal wanda idan Bilal ya saka takan ce ya tura mata. Kuka takeyi sosai lokacin da ta gama tura mishi dan harda hotunan Aisha da Bilal din da yawan gaske a wayarta. Hotunan da suka sakata tunanin Aisha da halin da take ciki a yanzun.

Bataji shigowar Mami da ta juya a hankali ba, dan Abbu yace ta dinga barin Layla tanayin kukan, dan akwai sauki a cikin shi. Yana nufin tana fito da abinda yake damunta bata barshi a cikinta ba. Amman da wahala, batasan ba cikin Layla bane kawai jarabawa harda damuwar da take gani shimfide a fuskarta a duk rana. Shi kadai yakan jijjiga zuciyarta. Amman ta bar komai a hannun Allah, shi daya kadarta musu ya san yanda zaiyi dasu. Sharar da take kitchen ta dauka dan ta fita da ita can harabar gidan ta zuba a babban wajen da suke zubawa sai a fita da ita duk sati.

Ta dawo ne taci karo da Ayya, zasu iya haduwa irin wannan fiye da goma basu cewa juna komai ba, shisa abin yayi mata wani iri yau da taji tace,

“Maryama.”

Mamakine bayyane a fuskar Mami sanda ta juya, saboda yanayin da taji a muryar Ayya bana tashin hankali bane ba.

“Ya Layla?”

Ayya ta tambaya tana kallon Mami din, ba abinda taso fadi bane ba, a kwanakin nan da suka wuce mata da wani irin yanayi, baccin kirki bata samu. Saboda tana tunanin makomarta, tana kuma tunanin abinda zata cewa Allah idan mutuwa ta risketa da hakkin mutane da yawa a kanta. Idan ana maganar lahira bata tunanin wani girman kai na da amfani, ta sha fitowa da nufin samun Mami har cikin daki ta roki gafararta amman sai ta tsinci kanta da kasawa. Yau dinma na zatace ga abinda ya fito da ita ba, kuma sai ta hadu da Mami din, ta dauki hakan a matsayin wata ishara ta samun sauki, ba saita taka kafarata zuwa dakinta ba.

“Tana lafiya. Alhamdulillah.”

Mami ta fadi tana shirin raba Ayya ta wuce.

“Maryama…”

Ayya ta sake kira tana saka Mami tsayawa a karo na biyu.

“Ban san ta ina zan fara ba.”

Cewar Ayya da muryarta take rawa.

“Cutar da nayi miki wanda kika sani da wanda baki sani ba…”

Kafin ta karasa Mami ta katseta da fadin.

“Dan Allah Maimuna… Idan kin taba cutar dani ko kokarin hakan Allah ya zama shaida yau na yafe miki. A zaman mu ba zance ko a tunani ban soki da abinki ba, ki yafe mun nima.”

Numfashi mai nauyin gaske Ayya ta sauke tana jin kamar an dauke mata dutse a kirjinta.

“Na gode… Ba zan miki karya ba, hakan baya nufin ba zan neme ki da rigima ko ba zanyi tashin hankali ba.”

Murmushi Mami tayi, murmushin da ta kwana biyu batayi kalar shi ba. Batace komai ba ta raba Ayya ta wuce, in dai wannan ne ta saba da shi, mai hali baya barin halin shi akace. Kishi da rigima halayen Ayya ne, batajin kuma wani abu zai taba canza hakan, bata tsammaci maganar da sukayi yanzun ta saka su zauna kamar aminan juna ba, ko su fara hira da mutuncin da basayi a da. Idan akwai abinda ya fara sakawa take ganin girman Ayya shine matar bata iya munafunci ba, abinda yake ranta ne zata nuna maka, idan kaji haushi ma bai dame ka ba.

Ko da wasa bata taba nuna tana sonta ba tun shigowarta, tana kula da yanda taso ta ture har yaranta, sai Haris yayi nasara a kanta, duk da batajin tana son sauran kamar Haris. Da zama da munafiki da zai nuna yana sonka a gabanka a bayanka ba haka ba, gara ka zauna da wanda zai kalli fuskarka ya fada maka baya yinka, hakan ba zaisa ka daga burinka a zaman ku ba. Rigimar Ayya ta jima da sabawa da ita, kamar yanzun yanda take jin wata rana zata zo da zasu saba da wannan yanayin da suke ciki, ranar da komai zaiyi musu sauki. Ayya ma dakinta ta wuce tana jin wani sauki ya saukar mata, tana jin yanda ta rage kadan daga cikin hakkin mutanen da take ji ya shake mata wuya.

*****

Sosai yaji dadin yanda duk watannin daya dauka ko Ayya bata ce mishi yaushe zaije gida ba. Suna waya kullum, yana kiranta sau hudu har fiye da haka a rana, ba hira sukeyi ba, dan yakan ce,

“Zan sake duba kine daman.”

Kamar yanda yakan ji Bilal yace mata wasu lokuttan, so yake ya rage mata kewar Bilal da yasan tanayi a lokaci daya kuma bayason ya fama mata ciwon da baisan koya fara warke mata ba. Tun biyan farko da akayi musu Bappa yace mishi anayin wani adashi, yayi bayanin amman badan Rayyan ya gane ba, shi din bamai yawan siye-siye bane ba, badan abinda yake turawa account din Bilal ba, kusan fiye da rabin kudin haka suke zama account din shi. Ko lokacin da suke makaranta sai kudin Bilal ya kare na shi akwai dan saura.

“Duk yanda kake ciro dubu dai-dai ga kudin nan ya kare.”

Ya kan fada idan yaji Bilal na maganar kudin shi sun kare shi.

“Koyon ajiye kudi yana da amfani, ko badan ka siya wani abu ba, tsaron lalura ne. Idan baka saba ware wasu ka ajiye ba tun kana kai kadai, zai maka wahala idan ka fara tara iyali.”

Bappa ya fada mishi, ya sha dauka yana abubuwan shi a tsare sai yanzun daya hadu da Bappa, sosai yana koyon abubuwa a wajen shi, watakila mu’amala da mutane bashi da aibun da yake tunani. Tunda yanayin Bappa din yanzun yana koyar da shi abubuwa da dama.

“Ace shekaru kusan talatin amman kaga mutum baya tunanin abinda zaiyi da rayuwar shi, kudin duk da zasu shigo mishi ko bashi da abin siya saiya kirkira.”

Lokutta da dama zantukan Bappa kan saka shi yayi murmushi, idan kaga yanda yake magana ko tsare-tsare sai kayi tunanin yanada yara fiye da goma da suke karkashin kulawar shi. Amman Bappa ya saka shi tunanin da gaske yana bukatar adana kudade, musamman da haka kawai Bappa din yace mishi.

“Idan na koma karatu inajin idan ba nawa auren ba nakane zai dawo dani kasar nan.”

Yana tuna mishi da cewa zai koma, duk da yanajin kamar babu nisan da zai yanke zumuncin da yake tsakanin su. A lokaci daya yana saka shi tunani akan abubuwa da yawa, tunani akan shi da Layla, baisan me take so ba a yanzun, amman shi ya kwana biyu da sanin abinda yake so. Da tunanin yake kwana yana tashi a satin, shisa ya yanke hukunci bin Bappa yau su tafi Kano tare, duk da baice komai ba yaga jin dadin hakan, tunda ya dade yana fama da shi da ko na rana daya ya bishi suje sai su dawo yana ki.

Ko bakomai ma yana son ganin Layla, kewarta yake ji har a kasusuwan jikin shi. Yaji dadin yanda Bappa ya sai da ya shiga ya gaishe da Ayya sannan ya wuce da nufin zai dawo da dare su fita da Rayyan din. Ayya ma taji dadin ganin shi, sai da yaje dakin su ya rage kayan jikin shi ya share dakin tas sannan ya shiga yayi wanka ya sake wasu kayan yana dawowa dakin Ayya. Anan ya zauna yaci abincin da ta zubo mishi, sai da ya gama ya dauke kwanonin ya kai kitchen sannan ya dawo ya zauna. Har yanzun bai saba magana da ita har haka ba.

Tauna abinda zai fada yakeyi, dagowa yayi yana kallon fuskarta,

“Ayya ina so muyi magana ne daman.”

Bata san me yake so ya fada ba, ta dai bashi dukkan hakalinta tun kafin yayi maganar.

“Ina sauraren ka Rayyan.”

Gyara zaman shi ya yi.

“Zan auri Layla, idan ta haihu zan aureta. Ina tara kudi Ayya, ban san ko zasu isa ba saboda gasu kama gida da su kayan lefe.”

Bata san ya taji maganar ba, tunani daya ne yake mata yawo kawai.

“Babu wanda ya isa ya canza kaddara.”

Ta kuma gani yanzun, duka kudadenta da ya kamata ace tayi wani abu muhimmi da shi ta kwashe ta baiwa Hajiya Dije da sunan a raba Layla da Rayyan, a raba harda Bilal da take gani a kusa da ita. Ga shi yanzun kaddarar da take zagaye da su ta hada su ukkun duka a gaban idanuwanta kuma da yake bata da iko a kai ba abinda zatayi.

“Ayya…”

Rayyan ya kira saboda baisan me shirunta yake nufi ba, ya fara fada mata ne saboda yasan bata son Layla a kusa da shi, bata kuma son Mami, gara taji daga wajen shi. Rayuwar shi duka yayi ta ne cikin rashin daukar duk wani abu da zatace da muhimmanci, shisa yanzun zai fara, ya rigada ya yanke hukunci auren Layla, amman baya nufin zaiyi shi bada yardarta ba.

“Kiyi mun magana Ayya, ni din ban saba jin maganar ki ba, ina so in aureta, idan hakan na nufin in jira sai kin amince zan jira in dai bata da matsala da hakan itama, amman kice wani abu dan Allah.”

Haka kawai taji zantukan shi sun karya mata zuciya. Kai ta jinjina kawai, muryarta na rawa tace,

“Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya kaimu lokacin.”

Numfashin da baisan yana rike da shi ba ya saki. Ya dan kara jimawa batare da sun cewa juna komai ba sannan ya mike ya fice, sai da yayo sallar azahar ya dawo sannan ya shiga bangaren Mami, itama suna gaisawa kan shi a kasa yace,

“Layla fa? Ina so inyi magana da ita Mami.”

Dan jim Mami tayi kafin ta mike, dakin Layla ta nufa tana Kwankwasawa kafin ta tura, tana zaune a kasa da alamar sallah tayi itama, dan ko hijabi bata cire ba.

“Ga Rayyan a falo yana so yayi magana dake.”

Mami ta fadi tana juyawa batare da ta jira amsar Layla din ba, dakinta ta koma. Zuciyar Layla har cikin tafukan hannayenta take jin su. Ta ga kiran shi amman bata daga ba, saboda yace mata zaizo bata bashi amsa ba, tunda safe da taga sakon shi take kuka. Yanzun ma idanuwan ta taji cike taf da hawaye, watakila idan yaga bata fita ba ya hakura ya kyaleta, batajin zata iya bari ya ganta a yanda take din nan. Cikinta ya fito sosai tunda ya shiga cikin wata na biyar, har awo na farko tayi, yanzun takan ji motsin abinda yake ciki, har bacci yakan tasheta idan yayi wannan kwakkwaran motsin.

Text taji a wayarta, ta mika hannu tana daukowa ta duba, Rayyan ne,

“Ba zakici gaba da shareni ba, ba zan barki kici gaba da shareni ba. Idan baki fito ba zan shigo.”

Hawayen da suka zubo mata ta share tana dafa gadon ta mike da da kyar. Cikin yasa tana kallon Mami da wata daraja ta daban yanzun. Ko juyi zatayi a bacci saita tashi zaune idanuwanta tar sannan take juya, ga wani irin ciwon jiki da take fama da shi naban mamaki. A kasan zuciyarta haka kawai take jin kamar kafarta daya a duniya take daya kuma a wani waje da bata da sunan da zata bashi har yanzun. Tana tallafe da cikinta ta fito daga dakinta, bata ga fuskar Rayyan ba, bayan kan shi kawai tagani, amman ya isa ya karyata mata duk wani tunani da tayi na binne mafarkin samun shi.

Saboda wata irin soyayyar shi ce ta taso mata tana saka har abinda yake cikinta yayi wani irin motsi daya sakata kiran sunan Allah cikin yanayin da ya saka Rayyan juyawa ya sauke idanuwan shi cikin na Layla da ta bude. Sai taji ta daburce, juyawa take shirin yi ta ruga, wani waje take son kasancewa da baya nan.

“Layla… Dan Allah… Karki boye mun.”

Rayyan din ya fadi cike da wani irin tsoro a muryar shi da yayi mata tasiri. Ganin ta tsaya tana juyowa yasa shi mikewa ya zagaya zuwa inda take yana fuskantarta. Jikin shi bari yakeyi daga ciki, hatta da zuciyar shi rawa takeyi mishi. Baice yanayinta bai taba shi ba, bai kuma yi kokarin boye hakan dan karta gani ba. A duk rana tun bayan daya sani da cikin jikinta yake kwana yana tashi. Amman hakan baisa yaji saukin ganinta dauke da shi ba, ganin shi ya fito sosai haka.

“Hamma”

Layla ta kira da wani yanayi a muryarta, tana saka har dayan hannunta ta kare cikinta kamar tana son boye shi saboda irin kallon da Rayyan din yake mata.

“Kaima ka daina ganina ko? Ka daina ganina sai cikin da yake jikina.”

Ta karasa maganar tana jin wani daci a zuciyarta da hawayen da suka zubo mata. Kai Rayyan yake girgiza mata, amman ya kasa hada idanuwa da ita har lokacin, cikin kuka tace,

“Na sani, kowa baya gani sai cikin nan, kamar ba a jikina yake ba haka nakeji, ina jin kamar tare da cikin ni na bace, shisa kowa baya gani na.”

Sai lokacin ya iya kallon idanuwanta da suke cike taf da hawaye yana furzar da numfashi ta bakin shi, bayajin akwai wasu kalamai na lallashi da zai fada mata.

“Ina ganin ki, ina ganin ku duka ba zan miki karya ba. Amman ina ganin ki.”

Cewar Rayyan yana dorawa da,

“Na san na fadi abubuwa da yawa. Zan sake fadin wani yanzun. Zan aure ki, ba dan abinda ya faru ba, dan ina son ki, zan aure ki in har yanzun kina jin zaki iya rayuwa da ni.”

Sai da ta dafa kujerar da take gefenta sannan ta iya tsugunnawa saboda yanda kalaman shi suka daketa. Numfashi take fitarwa wani irin kuka na kwace mata. Tsugunnawa yayi shima, idan zai fada mata sau dari ba zai gaji ba, saboda bayason wannan kadaicin da yake gani a cikin idanuwanta, bayason yanda take jin kamar ita kadai ta rage a duniyarta, kamar babu wanda zai taba fahimtar halin da take ciki, wannan yanayin shi yake kaika fadawa depression, abinda zaiyi komai da yake karkashin ikon shi na ganin bai bari Layla ta dandana wannan duhun ba.

“Na fadama Ayya, ta mana fatan alkhairi. Bake kadai bace ba, ba zan fahimta ba nasani. Amman ina tare dake, koma menene ni da ke muna tare.”

Kamar maganganun shi na kara tunzurata, kuka takeyi sosai, bai hanata ba, bai dai daina gaya mata yana tare da ita ba cikin wata murya da take kara karya mata gabban jikinta. Ba zatace ga iya lokacin da suka dauka a haka ba, ta dai tuna yanda ta samu da kyar tana mikewa.

“Ina tare da ke.”

Da Rayyan ya fadi ce ta rakata dakinta, ya kai mintina biyar kafin shima ya iya mikewa. Idan ma bata yarda ba zaici gaba da fada mata daga nan har lokacin da zata yarda da shi. Saboda wannan zaman da sukayi kawai ya kara tabbatar mishi da ana halittar wani dan wani, dan yanajin zuciyar shi an halitta mishi itane kawai dan ta dokawa Layla ita kadai, ita din tashi ce kamar yanda yake fadi a ko da yaushe.

“Aure zanyi Bilal, har yanzun ba zaka dawo ba ko? Da gaske wannan karin ba zan yafe maka ba.”

Shine abinda ya fadi bayan ya shiga daki da dukkan zuciyar shi yana fatan Bilal din zaiji shi ko ta wanne haline. Saboda kwanakin sun fara mishi tsayi.

<< Martabarmu 29Martabarmu 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×