“Abbu ka yafe mun, dan Allah Abbu ka yafe mun, duk ku yafe mun…”
Shine kalaman da sukewa Abbu amsa kuwwa a cikin kunnuwan shi harma da kai. Muryar Layla na zauna mishi da wani yanayi, yanda tayi maganar kamar tana saka ran fitar duk abinda yake cikinta zaizo ne da ajalinta. Da kan shi shekaranjiya bayan sun sake kwasowa zuwa asibiti cikin dare ya samu likitan yace,
“Wai ba zakuyi mata aiki ku ciro abinda yake cikin nata bane? Tun da satin nan ya kama yarinyar nan take cikin wahala, dan Allah ku duba lamarin.”
Murmushin karfafa gwiwa likitan yayi mishi yana kuma bashi tabbacin babu wata matsala dan wasu matan nayin haka. Ba zai manta ba, ko Mami takan yi doguwar nakuda, ta Layla din ce dai take tsaya mishi a rai fiye da duk wadanda yagani a baya. Nakudar ce saita taho mata gabaki daya sunzo asibiti sai kuma ta lafa ace ba haihuwar bace su sake kwasa su koma, yau ne karo na hudu a sati daya. Ita take ciwon amman zai iya rantsewa rashin natsuwa ya saka sunyi zuru-zuru gabaki dayan su. Yau kam ko da sunce ba haihuwar bace shikam zaice a barta a asibitin ne kawai.
Bai san akwai tsoron da zai danne na ganin jikan da zai diro ahalin su da gurbataccen asalin da bashi da masaniya a kai ba sai yau. Ko da yake zaice akan cikin Layla ya fahimci ba mata kadai ke da gulma ba, ba kuma su kadai tsegumi ya tattara ya zaunawa ba. Tun bai gane kallon da akeyi mishi a masallaci ba, da yanda har wani dan jinjina kai wasu a cikin mutanen unguwar sukeyi kamar alamun tausaya mishi duk idan sun hada idanuwa, ciki harda mutanen da gaisuwar musulunci ce kawai take giftawa a tsakanin su.
A cikin irin mutanen ne wani ya iya samun karfin gwiwar tarar shi sun fito daga masallaci yana fadin,
“Alhaji ashe kuma haka wannan lamari ya faru da yar wajen ka? Allah ya kiyaye na gaba, kasan yarane yanzun ka haife su baka haifi halin su ba, kana iya kokarin ka akan tarbiyar su suna dauko maka magana. Allah dai yasa an dauki hukunci mai karfi akan yaron da ya yi ta’asar.”
Tunda ya fara magana kallon shi kawai Abbu yakeyi, shi da kan shi sai da ya tsargu ya fara kame-kame yana barin wajen. Amman tabbas zantukan shi sun rigada sun isar da sakon da yake son su isar a zuciyar Abbu, mutane sunyi gaskiya, zancen duniya baya boyuwa, ba kuma komai bane idan ka binne yake kwanciya lafiya, wasu hawaye yaji masu zafin gaske sun taru a cikin idanuwan shi. Da girman shi da komai, ashe kallon tausayin da kowa yake mishi kenan a cikin unguwar, kallon yanda martabar gidan shi da ahalin shi ta tabu. A ranar sai da ya kasa hakuri yake labartawa Mami abinda ya faru, sai dai murmushi tayi mai cike da karayar zuciya.
Don dai batason kara daga mishi hankali shisa bata fada mishi ya taushi zuciyar shi ba, ba zatace ga lokacin da maganar cikin Layla ta bullu a cikin dangin su ba, ko ta hanyar da hakan ya faru. Duk da tana son dora alhakin akan Anty Uwani, dan itace ta zo gidan tayi sa’ar ganin giccin Layla, duk da a lokacin akwai hijabi a jikin Layla, kuma cikin duka bai shige watanni ukku ba. Da farko bata kawo komai a ranta ba akan yawan ziyarar da yan uwa na jiki da na nesa suke kawo mata ba, sai da suka fara tambayar inda Layla take da yanda suka kwana biyu basu ganta ba, suna yin tambayar idanuwan su na yawo a cikin gidan kamar zasu iya hangota ta cikin daya daga bangwayen da suke zagaye da dakin.
“Tana lafiya. Alhamdulillah.”
Shine amsar da suke samu, sai ko murmushi mai ciwon gaske daga wajen Mami din, tana so tace musu Layla tana makaranta ko dan gujema tarin tambayoyin su, shisa a irin lokuttan take zabar ta mike ta kawo musu abin sha ko ta kawo wani zancen da zai sa su kyaleta, amman sai sun san yanda sukayi suka dawo da zancen akan Layla. Tun tana kuka bayan tafiyar kowanne a cikin su har zuciyarta ta bushe. Duk zuwan bai musu ba sai da suka dinga turo yaran su ‘yan matan suna kusan yini a gidan. Haka makota ma da suka fara mata zarya, har mutanen da bata taba sanin da zaman su a cikin unguwar ba.
A lokacin ma cikin Layla ya shiga wata na bakwai, sun fita kenan zasuje awo, ita da Layla da Jabir da zai kaisu, basu karasa fita kwalta ba Layla ta zage gilashin bangarenta tana zura kanta saboda amai daya taso mata. Hakan yasa dole Jabir din yayi parking a gefe ta fito, wahala ma tasha dan batayi aman ba. Sai ruwa da Jabir ya dauko mata na roba ta kuskure bakinta tana kuma wanke fuskarta. Mami ma hankalinta yana kan Layla da ta jigata, tun da rabonta da wasu amai tun cikin na karami, taji Jabir yace
“Da kin karaso ai saiki fi ganin mu da kyau.”
Hakan ya sata daga kai ta sauke shi kan matar da bata ga fuskarta ba sai bayanta saboda ta wuce da sauri har tana tuntube, kai kawai Mami ta jinjina suka shiga mota suna tafiya. Har suka kai Jabir na kwashewa matar albarka.
“Aikin banza, shisa rayuwar turawa tayi wallahi, babu wanda ya damu da kai ballantana.”
Ita dai batace mishi komai ba saboda jikinta da yake a sanyaye. Haka mutane suka dinga shigiwa gidan, wasu da uzurin an kwana biyu ba’a gaisa ba, ko zasu wuce shine suka biyo. Murmushi Mami takanyi, tasan gulmace da tsegumi kawai ya shigo da su, idan basu ga Layla ba ta boye tana daki, lokaci zaizo da zasu shigo gidan kukan duk abinda zata haifa in dai ya taka duniya zai tabbatar da zargin su idan tantama sukeyi. Ta jima da daina gujema kaddarar da ta same su, idan tana boyewa babu abinda zai karawa Layla sai tarin damuwa fiye da wadda take ciki.
Ga duk zuwa awon da zasuyi sai likita ya kara musu kashedi kan kwantar mata da hankali saboda jininta da ya hau, abinda ba’a so a tare da mai ciki. Yan uwanta ma gulmar sukeyi, dan wasu yan unguwa sunyi bata ga laifin su ba, masu dalilin da zasuyi mata uzuri ma basuyi ba, kowa dan yatsa ya daga ma kaddarar da ta same su kamar su din sunfi karfin hakan, kamar su din suna da dabarun kaucewa abinda ya sameta. Dan akwai matar da tana shigowa gidan sun gaisa ta zauna sai ga Jabir shima ya shigo ya gaishe da matar yana wucewa kitchen.
Kallon sani Mami takeyi mata, amman ta rasa inda tasan ta.
“Nasan baki gane ni ba ko? Matar Balarabe ce da muka zauna nan baya.”
Kai Mami ta jinjina, shekaru wajen tara ba wasa bane ba, kuma ko da can din da suka zauna anan unguwar tasu in ba jaje ko barka ba, babu abinda yake hadasu.
“Allah Sarki, shekarun ne da yawa shisa, duk ina yaran, ya wajen Salamatu.”
Wata yar dariya matar tayi.
“Kowa lafiya, na shigo unguwar ne nake jin rasuwar Bilal, nace aikam zan shigo in muku gaisuwa. Allah ya yi mishi Rahma.”
Bayan Mami ta amsa tana shirin mikewa kenan dan ta kawo mata ruwa tace,
“Allah dai ya kara karemu, ashe haka abubuwa duk suka faru, ga yar wajen ki din nan da akace kina riko ya take da suna ita kuma ta dauko magana, abin ya bani mamaki kwarai…”
Kallonta Mami takeyi, kafin ta iya yin wani tunani Jabir ya fito yana fadin.
“Mene ne abin mamaki?”
Ko ina na jikin shi bari yake da bacin rai, sosai yanzun mutane suke bashi mamaki, yana kuma sake jinjina ma Rayyan da tun da wuri ya gane halayen mutane ya nisanta kan shi da su. Shima abinda yakeyi kenan yanzun, saboda su din basa gajiya da yin abubuwan da zakayi komai dan ka gujewa zama jinsun su.
“Jabir”
Mami ta kira, kai ya girgiza mata yana fadin,
“Layla! Layla!!”
Yana kallon matar da take ta kifkif da idanuwa cike da tarin rashin gaskiya.
“Layla!”
Jabir ya sake kira lokacin da yayi dai-dai da fitowar Layla da take rike da bayanta, idanuwanta na fara sauka akan Jabir da yake takawa ya karasa inda take yana kamo hannunta, bin shi take cikin rashin fahimta harya zo da ita tsakiyar falon yana tsayar da ita a gaban matar.
“Ki daina mamaki yanzun, ki gani da idanuwan ki, saiki fita ki sake tabbatar musu idan akwai mai sauran mamaki ya bari, idan suma zasu shigone su ganta su shigo.”
Kanta Mami ta sadda kasa tana kai yatsanta a hankali ta share kwallan daya taru a cikin idanuwanta, zuciyarta na wata irin kuna, mikewa matar tayi babu ko sallama ta raba Layla ta wuce. Har lokacin jikin Jabir bari yakeyi. Sakin hannun Layla yayi yana wucewa dakinta da kan shi ya dauko hijabi ya mika mata.
“Hamma…”
Ta fadi muryarta na rawa, idanuwanta cike da hawaye, kai Jabir ya girgiza. Zuciyar shi sam ba zata iya dauka ba. Baice abinda Layla tayi bashi da muni ba, amman tsakaninta ne da Ubangiji, a cikin duk tarin mutanen da suke mata surutu, suke nunata da yatsa babu wanda za’a binne su a tare, sanda za’a kaita a rufo a barta da ayyukanta ba lallai su sani ba, addu’ar neman Rahma ma ba lallai bane su bita da ita. Baisan inda tarin mutanen suka shiga ba a lokacin da ta samu makaranta, lokacin da tayi saukar Al’Qur’ani mai girma, duka bai gansu sun shigo tayata murna ko jinjina ma su Mami kan kokarin su ba.
Sai yanzun da kowa yake tunanin sunyi kuskure a rikon Layla, sai yanzun da ita kanta Layla din wani abu mai muni ya sameta, tarin mutanen da basu da masaniya akan kominta sune a gaba wajen yanke mata hukuncin da basuda hurumin yin haka. Yana gab da fara sakawa mutane hannu idan yana gidan suka shigo, baisan me yasa Mami bata binsu da tabarya ba, shi bashida wannan hakurin sam.
“Ba zaki kare duka rayuwarki a cikin bango hudu na dakin ki ba Layla, idan baki fita da cikin nan ba zaki fita da yaro ko yarinya. Mutane suna magana yanzun, ba zasu daina magana ba, karki barsu, karki bari su takura ki fiye da yanda kike a takure.”
Jabir ya karasa maganar da wani irin yanayi a muryar shi da yasa hawayen da ke cikin idanuwan ta zuba.
“Jabir ka kyaleta, me yasa baka da hankaline kai?”
Mami tayi maganar tana kokarin tarbe kukan da yake barazanar kwace mata, hijabin Layla ta karba tana sakawa a jikinta. Zuciyarta na wata irin dokawa kamar zata baro kirjinta. Mami bata hana su ba, tana kallo Jabir ya koma ya daukowa Layla takalmanta, fitar sukayi, daga farkon layin har titi, Layla tana jinta kamar babu kaya a jikinta saboda kallon da mutane suke binta da shi, kamar yanda Jabir ya fadane, ba zata cigaba da boyewa ba har abada, zancen ya rigada ya bazu, gara ta fara koyan yanda zatayi rayuwa da tabon da yake jikinta.
Sanda suka koma numfashi ma da kyar take fitar da shi, har bakin kofar dakinta Jabir ya rakata sannan ya tsaya yana fadin.
“Babu hakkin mutane a kanki. Ba zan miki karya ba kin sani, duka rayuwar ki ta duniya ce ta samu tangarda, ba zancen zancen ki ba zai wuce a baku nan mutane ba, amman duk sanda zaki gifta zaki tuna musu abinda yake adane a zukatan sune, bansan al’adun mu na Hausawa basawa mata adalci ba sai yanzun Layla, sai da rashin adalcin ya biyo ta cikin gidan mu…”
Wani irin numfashi Jabir yaja, bayason hawayen shi su zuba a gabanta, zai kara karya mata zuciya.
“Ba zaki iya gyara tsakanin ki da mutane ba, ki gyara abinda kike da tabbas akan shi, ki gyara tsakanin ki da Allah, sai Ya tausaya miki ya gyara duniyar ki, karki bar su, karki bari su takura ki fiye da yanda kike a takure, kina jina.”
Kai ta daga mishi tana goge hawayenta. Sai da yaga ta shiga daki sannan ya juya yana komawa wajen Mami ma da tun da suka fita tana zaune tana wani irin kuka mai cin rai.
“Dan Allah ki rage sanyin halin nan Mami, ki daina barin mutane suna bi takan ki akan abinda baya karkashin ikon ki, idan ba zaki iya korar su ba Mami ki daina sauraren me zasu ce suna bata miki rai, dan Allah. Wallahi zuciyata zafi takeyi mun, sosai da sosai.”
Cewar Jabir yana ficewa daga dakin saboda bayason ganin kukan da Mami takeyi. Har Abbu ya samu da daren ranar, dan Abbu ba zai manta yanda Jabir ya shiga dakin babu ko sallama ba.
“Yaushe abin nan zai wuce mana Abbu? Me yasa mutane ba zasu kyale mu ba? Ina ruwan su da rayuwar mu?”
Hannu Abbu ya dan bubbuga a gefen shi yanawa Jabir din alamu daya je ya zauna, bai musa ba kuwa ya karasa yana zama inda Abbu ya nuna mishi, idanuwan shi sun kada sunyi ja, watakila da yayi kuka zai samu sauki.
“Nagaji da ganin Mami na kuka kullum, ina jina so helpless…”
Dan murmushi Abbu yayi.
“Ka kalleni Jabir, ban san inda nake samun karfin bude idanuwa ba a duk safiya, saboda wannan ne karo na farko da ko kalaman lallashi bani da su, damuwar ku gabaki daya ta tarar mun, ni ya kake tunanin ina ji? Um Jabir? Dan Allah ka dan kara daurewa, komai zaiyi sauki In shaa Allah.”
Jabir ya dade zaune a dakin ya hade kan shi da gwiwa yana neman sauki koyaya ne. Kamar yanda shima Abbu yake tsaye a wajen yana neman sauki a yanzun, daga shi, Ayya sai kuma Mami a asibitin, da yake dare ya farayi sanda suka fito din, wajen sha daya. Addu’ar duk da tazo bakin Abbu ita yakeyi, kafin wayar shi da take aljihun shi ta fara ringing, yana fito da ita yaga Rayyan ne, yana dagawa ya saka a kunnen shi muryar Rayyan din ta daki kunnen shi.
“Ina ta kiran Ayya bata daga ba, Mami ma haka, Layla fa? Nakudar ce ta sake dawowa ko Abbu? Ina magana da ita naji shiru, sai kira nakeyi itama bata dagawa.”
Dan siririn numfashi Abbu ya sauke,
“Gamu nan a asibiti m…”
Rayyan bai bari Abbu ya karasa ba yace,
“Me suka ce? Ga shi dare yayi ni ba zan iya tahowa ba yanzun.”
Duk da halin da Abbu yake ciki sai da yayi dan murmushi.
“Ka kwantar da hankalin ka. Babu abinda zai faru sai alkhairi da yardar Allah, zan dinga kiran ka ina fada maka yanda ake ciki, kayi mata addu’a kai dai kaji.”
Sai da ya amsa sannan sukayi sallama, su Mami ya kalla.
“Rayyan ne”
Kai Mami ta jinjina, ko lokacin da ake maganar soyayya a dangin su, zancen baya wuce.
“Anya akwai matar da tayi sa’a irin Maimunan Ahmadi?”
Ko da ta aure shi ta sabajin yanda ake fadin.
“Maimunan Ahmadi.”
Shisa sam bata jin kishin haka, zata so a yanzun na minti daya idanuwa da hankulan kowa su dauke daga cikin Layla su koma kan ita da Rayyan, tana da tabbacin tsantsar kaunar da take tsakanin su zai saka su fara sabon mamaki, ba kowanne namiji bane zaiyi abinda Rayyan din yayi. Ko ita maganar ta daketa da tajita daga farko, sai ta dinga ganin kamar mafarkine, duk da tasan da yawa zasu ce tayi azarbabi, kamar ta jira taga yanda zaman Rayyan da Layla zai kasance a karkashin inuwar aure kafin ta yanke hukunci akan tarin kaunar da suke yiwa juna. Sai dai ta kasa, tana da yakini mai girma akan kaunar Layla da take gani tattare da Rayyan din.
Watakila kuma idanuwanta ne suka rufe saboda nauyin da Rayyan din ya dauke mata na tunanin wanda zai zamo miji a wajen Layla, wanda zai kauda kai daga tabon da yake tare da ita harya ganta din, da tarin kalubalen da zata iya fuskanta daga wajen dangin shi idan har ta samu din ma. Duka rayuwar ‘ya mace zagaye take da martabar da tabuwarta yake dai-dai da nakasun da zai taba gabaki daya ahalinta. Kuskure daya tak zai iya canza komai ta fannin da gyaruwar shi zatayi wahala. Dukan su a tsaye suke duk kuwa da kujerun da suke a wajen, babu mai natsuwar zama, kowa da abinda yake sakawa yana kwancewa a cikin zuciyar shi.
*****
Motar farko ya samu daga Kaduna zuwa Kano, asuba ma a tasha yayita. Da yake Bappa ya kai shi, amman gani yakeyi kamar motar bata sauri, yau ne ya sake jin takaicin rashin iya tuki, da yana da mota a hannun shi iya gudun da yake so zaiyi. Abbu ma da safen nan kira biyu yayi mishi bai daga ba, ga shi yanzun sun fara shiga wajajen da babu network me karfi, ko shi tun yana gwada kira harya hakura ma, ko baccin kirki bai samu ba, lokaci zuwa lokaci yake kira yaji ko ta haihu.
“Har yanzun dai, da ta sauka din zan kiraka In shaa Allah.”
Shine amsar da yake samu wajen Abbu. Ba dan baisan yawan yan gidan su gabaki daya ba, amman a daren sai da ya tsinci kan shi da kirgasu, saboda yana son yaga sau nawa Abbu ya jure tashin hankali irin wanda yake jin shi a ciki. Yama fi jinjinawa matan, dan yana da yakinin idan shine a matsayin su babu abinda zai hada shi da ciki. Yara ne ya ga na yan uwa sun ishe shi, amman da yake Allah yayi wa mata wata irin jarumar zuciya, sai ka sha wahalar nan kuma gobe ma ka sake maya wata. Babu kalar tunanin da baiyi ba, ciki harda na yanda da yasan cewar kaso kusan casa’in cikin matsalar shi bata da alaka da asibiti, da saiya tafi fannin mata wato Gynecology ko dan rana irin wannan.
Sanda ya sauka garin Kano, daga tasha kan shi tsaye asibitin da Layla take wanda na kudine ya tari mashin yana nufa. Tun bai karasa sauka ba yake kiran Abbu da ayi mishi kwatancen inda suke din, shisa sanda ya karasa Abbu din ma ya fito bakin kofar asibitin yana jiran shi.
“Da ka zauna ai Rayyan.”
Abbu yace bayan sun gaisa, kai Rayyan din ya girgiza mishi.
“Hankalina ba zai kwanta ba Abbu. Gara ina nan din dai.”
Da gaske yakeyi, dan duk abinda suke fada mishi jinsu kawai yake, yafi so yana gani da idanuwan shi. Sauran duk da tayi ba’a dadewa haka ake ce mishi ta samu bacci ba haihuwar bace da ta tashi zasu tafi gida, ko kuma gasu a hanya zasu koma. Amman yau har yanzun da suke takawa suna shiga cikin asibitin babu wani labari.
“Ayya…”
Cewar Rayyan cikin sigar gaisuwa, ita da Mami suka juya a tare, kafin su amsa shi daya daga cikin Nurses din ta fito da murmushi a fuskarta.
“Ta sauka lafiya.”
Ta fadi tana saka su tattara hankulan su zuwa kanta gabaki daya. Lumshe idanuwan shi Rayyan yayi yana sauke wani numfashi da baisan yana rike da shi ba. Duk wani abu da suke fadi baya karasawa kunnuwan shi sam. Ba zaice ga asalin abinda yake ji ba, kafafuwan shi ne sukayi wani irin sanyi, baisan lokacin daya tsugunna ba, banda numfashi kamar wanda ya sha gudu babu abinda yakeyi, baisan lokacin daya dauka a wajen ba sai da yaji Abbu ya dafa kafadar shi.
“Ka zo ka fara karbar ta.”
Kalmar “ta” na fada mishi ‘ya mace ce Layla ta haifa, zuciyar shi yake ji cikin tafukan kafafuwan shi a lokacin daya mike yana bin bayan Abbu zuwa dakin da aka dawo da Layla din da akanwa lakabi dana hutu. Amman baya ganin komai, idanuwan shi kafe suke kan yarinyar da take hannun wata Nurse da taketa murmushi ta karaso tana mikowa Rayyan yarinyar, hannuwan shi duka rawa suke lokacin da ta saka mishi yarinyar, yana mamakin rashin nauyinta, dan ji yake kamar zata subuce mishi idan yayi wasa. Yawu yake nema a cikin bakin shi da yayi wata irin bushewa lokacin da ya kafa yarinyar da take ta mutsilniya a cikin farin towel din da take nade ciki har wuyanta.
Kafafuwan shi yake ji suna son karayin sanyi, da kyar ya iya dan rankwafawa da kan shi saitin kunnenta yana mata kiran sallah a ciki kafin yayi mata hudu da.
“Maimunatu”
Kamar yanda yasan burin Bilal kenan, maganar shi kenan, zancen shi akan yara baya wuce farawa da samun ‘ya mace da zai sakawa sunan Ayya, yana dagowa ya sake kallon yarinyar yana jin yanda a duniyar shi bai taba sauke idanuwa akan halitta mai kyawunta ba, bai taba ganin wankakke abu da babu dauda a jikin shi ba sai ita, kafin yaji wani abu ya tsirga mishi yana saka shi tallafeta a kirjinta kamar yana son kareta daga tunanin shi, yana son kareta daga furucin mutane akan laifin da bata da alaka da shi.
“Idan baka dawo danni ba, dan Ayya, ka dawo dan ita Bilal, dan Allah ka dawo haka.”
Ya furta a cikin kan shi yana jin wani irin radadi na ratsa duk wata gaba ta jikin shi, ko da su Ayya suka shigo da kyar suka iya raba Rayyan da yarinyar daya fara kira.
“Nur”
Saboda da gaske ita ce hasken daya gani a cikin yan watannin da rayuwar su gabaki daya tayi wani irin sauyi. Ko da taje hannun Ayya, bata san lokacin da hawaye suka fara zubar mata ba, Mami ta mikawa ita tana ficewa daga dakin gabaki daya, waje ta samu ta zauna a bakin kofa, kuka takeyi da ta kwana biyu batayi irin shi ba. Kuka takeyi na abubuwa kala-kala, kuka take musamman akan rashin danta, kuka takeyi na hakkin Rayyan da har yanzun ta kasa samun karfin gwiwar kallon idanuwan shi ta fada mishi balle ya yafe mata. Anan bakin kofa ta samu kujera tayi zamanta, Mami ma tayi kuka ba kadan ba, jikar tace ta farko ta rike, jikar da tazo mata ta wani fanni mai wahalar gaske.
“Ina nemar kariyar Allah a kanki daga dukkan wani abu mai muni, daga saukin shafar da kaddarar iyayenki zatayi miki”
Shine addu’ar farko da tayi bayan ta karbi yarinyar. Abbu ma tunda ya karbeta yayi mata addu’a ya basu ita, saboda shine yake da karfin zuwa yaji ko akwai sauran kudaden da zasu biya. Da yake Layla din ba wata matsala ta samu ba, sai jigata da tayi, wajen azahar aka sallame su gabaki daya suka dunguma zuwa gida. Rayyan bai samu sunyi wata magana da Layla ba, ko idanuwa ta kasa hadawa da shi har suka sauka gida, yana gani Mami ta jata suna shigewa bangaren su, har daki ta kaita, sannan ta koma dan ta hada ruwan wanka, zaune Layla take inda Mami ta barta, sai Nur a gefe da take bacci kamar bata da wata damuwa a fadin duniya.
Sai lokacin hawayen da suke cike da idanuwan Layla suka zubo. Nur take kallo, wasu hawayen suna kara zubo mata, bata dauka zata haifota batare da ta rasa tata rayuwar ba, ta sallama da lamarin duniya gabaki daya, saboda duk wani ciwo da ta taba tunanin taji nafila ne akan zafin nakuda, jikinta babu wata gaba da bata amsa da ciwon ba, ta sha wahalar da bata taba hangowa ba, wahalar da take fatan ta zame mata kaffara saboda tana kokarin ganin ta cika duka sharuddan tuba, tana kuma da yakinin Allah mai Rahma ne
“Ga kaddarar mu Hamma, kaddarar da mu duka bamu hango ba. Allah ya yafe maka, Allah ya yafe mana”
Ta furta a hankali, tana kai hannu ta share siririyar kwallar da ta zubo mata. Babu wani abu da yake da sauki a cikin rayuwa banda bautar Allah, ita ce zakayi ka samu natsuwa, ita ce kuma zakayi a kyauta. Amman yanzun take ganin kacokan wahala ce a cikin zaman duniya, a da tunanin yanda zata bada labarin kaddarar da ta gifta tsakanin ta da Bilal ne, kafin fuskantar su Mami, sannan kuma rayuwa da cikin da kowa yake nunawa ‘yatsa. Tunanij ta gabaki daya ya sauya lokacin da kukan Nur ya dira a kunnenta a karo na farko, ta sake gane komai ba komai bane in dai ba zai taba yarinyarta ba lokacin da aka saka mata ita a cikin hannunta.
Yanzun gabaki daya babu wani tunani a cikin kanta banda na kare Nur daga duk wani abu da zata iya, a lokaci daya darajar su Abbu na kara daguwa a idanuwanta, ashe haka iyaye suke ji, ashe haka ‘da yake, cikin awanni kalilan ta dandani fargabar da take cikin kula da amana mai girma har haka.