1993, Kano
Zata iya cewa tunda Ahmadi yabarta tafiyar nan take shiri, kusan sati daya kenan. Sau daya ta taba tafiya mai nisan awa biyu. Wani lokaci ko da irin hakane, Ahmadi baya barinta
“Tsoro ya miki yawa Maryama… Shisa banason kina nisa ke kadai.”
Yakan ce, kuma da gaskene, har tsiya akeyi mata a gida wasu lokuttan, ace da tazo a karkara ba zatayi kyawun gani ba. Dariya kawai takanyi ta kyale su, sau daya kafafuwanta suka taka kauyen Kankia da yake a jihar Katsina, shima rasuwa Mannira ce, matar Yayanta Deeni. Zata tuna yanda aka kai ruwa rana kafin a barshi auren Mannira, na daya bata kasance daga danginsu kamar yanda suka saba ba, duk da yanzun wasu na bijirewa auren dangin. Amman rabon tilar yarinyar su Laila ne kawai ya saka shi kafewa da watsi da maganganun da kowa yakeyi na yaren Mannira.
“Ka rasa wa zaka jajibo kana zaune lafiya da matarka sai banufiya, salon duk tazo yanda ta lashe maka kurwa ta lashe kurwar sauran yaran ko?”
Maryama ta tuna maganganun Mahaifiyar su lokacin da yazo mata da zancen auren Mannirar, kowa a dangi da abinda yake fadi, mahaifin sune kawai ya bashi goyon baya, sosai ya dinga fada.
“Nayi bincike, iyayen yarinyar nan mutanen kirkine, suna zaune da kowa lafiya. Ita ma nagartacciya ce, addinin musulunci dai shi muke bi, kuma a sharuddan da aka kafa mana na neman aure, bamuda wani dalili na hana shi aurenta.”
Hakan yasa dole kowa ya hakura, amman badan anaso ba, yanda yan uwa suka daga hankalin su akan auren Deeni da Mannira, ko matar shi da zai hada zama da Mannirar bata tunanin ta damu haka, ko ita da suka zauna da Deenie suna zancen ta jinjina al’amarin matuka.
“Ni banki ka kara aure ba Yaya, da ba’a karawa nima da ina gidan wani ba Ahmadi ba, amman banufiya fa, ka dai kara duba lamarin.”
Dan yanda sukayi kaurin suna wajen shaidar da akeyi musu ta maita da tsafi na sanyaya jikinta
“Duk musuluncin banufe sai yayi tsafi.”
Haka takanji ana fadi, tana kaunar Deeni har ranta, bata son abinda zaizo ya cutar dashi sam.
“Ke dai kiyimun fatan alkhairi kawai.”
Deeni ya fadi yana dariya, sai gashi daga baya kowa na yabon kirkinta. Cikin kankanin lokaci ta shiga zukatan jama’a. Maryama da kowa sun alakanta hakan bayan rasuwar Mannira mintina kadan bayan haihuwar ‘yarta mace. Mutuwar ta daki Deeni ba kadan ba, har akayi jana’iza baisan inda kan shi yake ba. Kowa ya budi baki ca yakeyi rabone kawai ya hada kaddarar Mannira da Deeni, shisa duk yanda akaso hana shi aurenta yaki ji, ashe ma zaman nasu bamai tsayi bane, tunda duka watannin su sha hudu. To lokacin ne tafiyar da tayi mai tsayi, shekaru kusan biyu kenan da suka wuce.
Lokaci zuwa lokaci takan yi tunanin yarinyar, saboda tun a wajen rasuwa kowa ya kalleta sai yayi magana kan kalar idanuwanta. Tasan ba kasafai ake samun irin idanuwan a cikin mutane ba, musamman anan yankin Najeriya. Amman sai take ganin gara idanuwan yarinyar da taci suna Layla akan na wani bawan Allah data taba gani, har gobe ko ita kadai ta tuna sai tsikar jikinta ta tashi, saboda sak kalar idanuwan miciji, sai da tayi zaton ko tayi gamo ne. Ahmadi yaita mata dariya, yake cewa a wajen aikin su akwai wani bature nashi idanuwan kalar ganye, koraye ne sosai. To ita kam gara mata bature, wannan ba abin mamaki bane, amman a jikin bakar fata, dole abin ya girgizata.
Shisa da taga Layla ta kara jinjina ma Ikon Allah, dan Shi ya banbanta halitta a tsakanin mutane, bata da kalar da zata misalta idanuwan Layla dashi, ko kyanwa kowacce da kalar nata idanuwan. Amman tabbas ta wata kyanwa kawai ta taba gani da kalar idanuwan yarinyar. Kalar surutun da akeyi tun a wajen rasuwar Mannira, sam Maryama ba zaci za’ayi bakwai yarinyar bata bi mahaifiyarta ba. Tun tana tsammanin bayan dawowar su labarin rasuwar Layla zai iso musu harta daina.
Yau dinma har tasha Ahmadi ya rakata, da yake kwana biyu zatayi, daga ita sai Marwan ta taho. Sauran yaran tabar su wajen Maimuna da fuskarta babu yabo babu fallasa tace mata.
“Allah ya tsare, ki gaida su.”
Da tayi mata sallama, babu wani abu da zatayi da Maimuna zata zauna lafiya da ita. Shisa yanzun inta gaya mata maganar da taji ba zata iya dauka ba, ramawa takeyi. Yaranta ne kawai ta kula Maimuna na budewa hakora, kishinta sai yazowa Maryama da sauki tunda bata saka yaran a cikin rashin jituwar su. Hankalinta kwance tabarsu a gida, suma basu damu ba tunda ko unguwa zata fita a gida takan barsu. Ranta kal tanata kallon gari har suka isa kankia.
Furaira uwargidan Deeni ta karbeta hannu bibbiyu, ta sauketa kamar yanda ta saba taryar su, shisa kowa a danginsu baya gajiya da fadar alkhairinta. Sai dai ta girgiza matuka da ganin dan uwan nata, damuwar da take shimfide akan fuskar shi mai yawa ce, duk da murmushin da yake mata da suke gaisawa, tana ganin yanda bai kai cikin idanuwan shi ba. Tunda ta isa ta jima bata ga giccin Layla ba, kafin daga baya yarinyar da take bacci ta taso ta fito. Farat daya Maryama tajita har cikin ranta, sai bayan Furaira ta basu waje da Deeni ne ta samu damar tambayar shi me yake faruwa, murmushin da yayi mai ciwone matuka.
“Bana jin dadin tsangwamar da Layla take fuskanta daga wajen mutanen kauyen nan. Ko unguwa Furaira ta rage fita sai dole, tana iya kokarinta, amman ko taro ta shiga da Layla sai iyaye su fara janye yaran su, babu wanda ta taba cutarwa, bansan me yasa suke alakantata da maita ba. Dan Allah ya banbanta kalar idanuwanta da nasu sai suke dora alhakin hakan akan Mannira, suna zantukan da bana son maimaitawa….”
Deeni ya karasa maganar yana sauke ajiyar zuciya.
“Wallahi a kwanakin nan ina tunanin mayar da ita hannun Inna….”
Kai Maryama ta jinjina mishi, zancen na taba zuciyarta fiye da tunani.
“Allah ya kyauta ya rufa asiri, rashin ilimi cuta ce babba a tsakanin al’umma. Zan tafi da ita idan zan wuce, nasan Ahmadi ba zaiki ta zauna a hannuna ba, amman kaga ba zai yiwu inje mishi da zancen kai tsaye ba.”
Kai Deeni yake girgiza mata tunda ta fara magana.
“Karki dora mishi dawainiya, ga nashi yaran.”
Murmushi Maryama ta yi.
“Babu wata dawainiya, indai zai amince in riketa, ina da sana’ata ko ka manta? Ba wani abu nakeyi da kudadena ba. In shaa Allah rike Layla ba zaimun wahala ba. Amincewar ka itace komai na.”
Numfashi Deeni ya fitar mai nauyi.
“Ni dai ina so ta tashi inda babu tsangwama, inda wani ba zai lakaba mata maitar da batada ita ba…”
Kusan har karfe dayan dare suna shan hirar yaushe rabo da Deeni. Taji dadin damuwar da taga ta ragu a idanuwan shi kafin ta baro garin Kankia tare da Layla, wannan karin da tunani fal a zuciyarta, har ranta take jin kaunar yarinyar, ko dan Allah bai bata ‘ya mace ba har yanzun, kuma tana so, inda wani zaman kirki suke da Maimuna ba zataki ko Rukayya ko Zubaida wata ta dawo dakinta gabaki daya ba, musamman tunda yanzun Maimuna goyon mace takeyi, yarinyar da aka mayarwa sunan mahaifiyar Maimuna suke kuma kira da Intisar.
Amman abune da tabar shi a zuciyarta, tunda tasan furta shi matsala kawai zai janyo mata. Addu’a takeyi Ahmadi yabarta ta rike Layla. Harta isa gida, inda bata sami kowa ba cikin yaran gidan, tasan babu Islamiyya tunda ranar Alhamis ce, suna gidan Yaya Ayuba, tunda basu da wajen shiga daya wuce nan din. Daki ta wuce kanta tsaye tunda dai tasan Maimuna ba fitowa zatayi dan ta taryeta ba, ga jigatar hanya, saboda daga Marwan har Layla bacci suketa shirga, shi ta goyashi, Layla kuma tana sabe da ita, ga kayan su ga tsarabar da aka hadota da ita.
Banda nishi babu abinda take dirkawa, fitowa tayi tsakar gidan da nufin yin alwala, in tayi sallar la’asar ko da taliya ce sai ta dora musu, tana da dakakken yaji, yunwar da take ji ba zata jira wata miya ba ko da tana da cefane. Ta idar da alwalar kenan ta shiga daki taji sallamar Zubaida.
“Mami sannu da zuwa.”
Zubaida ta fadi tana ajiye mata kular abincin da take rike da ita hadi da dorawa da
“Gashi inji Ayya…”
Kallon Zubaida tayi da wani yanayi daya girmi godiya shimfide a fuskarta. Ko a mafarki bata tsammaci wannan kirkin ba. Batama sakawa ranta ba.
“Ki ce nagode sosai Zubaida.”
Dan murmushi Zubaida tayi tana ficewa daga dakin. Saida ta fara yin sallah tukunna ta gyara zama ta janyo kular gabanta, dambun shinkafa ne sai kamshi yakeyi. Wani numfashi ta sauke tana daukar kular ta mike tsaye. Kitchen ta nufa ta sami filet ta zuba, ta saka mai da yaji ta dawo dakinta. Tas ta cinye ta mayar da ruwa tanayin hamdala, batasan ta gaji ba saida ta kwanta, kuma lokacin Marwan ya zabi ya tashi ya fara damunta da rikicin shi, dole ta kara mikewa tana zuwa ta zuba mishi dambun shima. Kewar su Haris na damunta, amman da yake ba hankali gare su ba ko suzo su duba suga ko ta dawo.
Ko bayan Magriba da ta jiyo hayaniyar su bangaren Maimuna suka wuce, abin sai da yai mata wani iri, kamar ta aika Marwan ya kira su, shima sunata wasa da Layla tun dazun. Ganin Ahmadi ya sanyaya mata zuciya, da murmushin nan nashi ya shigo bangarenta.
“Mutanen Kankia…”
Yai maganar cikin sigar tsokana, dariya tayi tana mishi sannu da zuwa, yana zama idanuwan shi akan Layla suka fara sauka.
“Ina kika samo mana yarinya haka?”
Zuciyar ta taji ta doka, duk da babu alamar komai a muryar Ahmadin
“Yarinyar wajen Margayiya Mannira ce.”
Dan ware idanuwa Ahmadi yayi.
“Allah Sarki… Girman dan mutum ba wahala, rayuwa kenan.”
Ya karasa maganar cike da tausayawa, yasan zafin rashin iyaye, duk da bai taso cikin rashin kulawa ba, musamman ace mahaifiya. Ita kuma Maryama kallon shi takeyi, ko zataji yayi magana kan idanuwan Layla din, amman wata hirar yajata da ita yana tambayarta hanya kuma yanda ta baro mutanen can din. Hira suke kamar sunyi satika basu ga juna ba, kirki irin na Ahmadi yakan bata mamaki duk tsayin shekarun nan da sukayi a tare.
Bai tashi daga bangarenta ba sai da aka kira sallar isha’i. Tasan sai washegari zata karbi girki, dan haka sallama sukayi. Sai kuma lokacin taga su Haris da suke mata sannu da zuwa
“Ba kun manta dani ba Haris?”
Dariya yayi
“A’a Mami, Ayya ce tai mana masa, shine mukace bama so da miya sai ta saka mana sikari, yayi dadi sosai ko Jabir?”
Haris ya fadi, Jabir din ba daga mishi kai, surutun su suka cigaba dayi mata tana biye su dan bata da abokan hirar da suka wuce yaran nata, Haris ne kawai bai tsareta da tambayar inda ta samo Layla ba, su Jabir kuwa sai tambaya sukeyi tace kanwar su ce
“Idon ta wani iri… Me yasa ba kalar namu ba?”
Jabir ya tambaya yana saka Maryama dogon nazari kafin tace,
“Kowa da kalar nashi, kaima idan ka duba naka ba iri daya bane da na Naadir”
Cike da rashin fahimta Jabir din ya leka idanuwan Naadir
“Iri dayane Mami, ki kalla kiga”
Kai ta girgiza mishi
“Ba zaka gani ba sosai yanzun…”
Hakura yayi ba dan yagane ba
“Anan gidan zata zauna? Zamu dinga wasa tare?”
Dan jinjina kai Maryama tayi
“Nima ban sani ba”
Wannan karin su duka suka hada baki harda Haris
“Dan Allah Mami kibarta anan”
Dariya kawai tayi, ba zatai musu wannan alkawarin ba sai ta fara yin magana da Ahmadi tukunna, idan ya amince mata zataji dadi, ita kanta tana son ta rike Laylar, batasan ko tana da rabon samun ‘ya mace ba. Tunda ga maza nan har hudu a gabanta.
*****
“Saboda na kawo Bilal? Shisa itama taje ta dauko yarinya kenan? Ahmadi mayyar zaka bari ta zauna mana a gida? Wannan yarinyar mai idanun mage zaka hada mana a cikin yara?”
A tsayin shekarun nan ya zaice ya saba da rigimar Maimuna, ta karfi ta mayar da shi mafadaci, dan wani lokacin saiya balbaleta da fada yake samun kanta, wani lokacin kuma ficewa yake yabar mata gidan gabaki daya. Bako yaushe take bata mishi rai ba, saboda duk yanda yake jin Maryama, Maimuna daban take a zuciyar shi, ita dince karfin gwiwar shi, har yanzun ko matsala ya kwaso wajenta yake fara nufa, saboda yasan idan bata da shawarar da zata magance mishi matsalar shi zata raba nauyin matsalar tare da shi.
Labarin soyayya kala biyu zai bayar da kan shi a dage, muryar shi dauke da alfahari, shine soyayyar mahaifiyar shi, sai kuma soyayyar da Maimuna take yi mishi, shisa ya fahimci kishinta, tana mishi son da yake da yakinin yanzun a fadin duniyar shi baida na biyun sa. Amman a lokaci irin wannan yana rasa me yake lullube kwakwalwarta haka, me yasa soyayyar shi bata sakata zaben kalaman da zata furta mishi, kishin shi yasa ta daina gudun bacin ran shi sam.
“Ina manta cewa Bilal ba daga jikin mu ya fito ba wallahi, ki daina maganar nan dan Allah…”
Ahmadi ya fara cikin taushin murya, amman kai Maimuna take girgiza mishi, tun jiya da safe da ta fita tsakar gida taga Layla sai da gabanta yai wata irin mummunar faduwa, babu shiri ta koma daki tana karanta duk wata addu’a da zata zo bakinta, gashi yarinyar bata da haske can da zatayi zaton ko daga kasar turawa ta fado musu cikin gida. Babu kalar tunanin da batayi ba a ranta kan yarinyar, ko da Ahmadi ya dawo ta tambaye shi saiya fada mata ko wacece Laylar.
Bata manta lokacin da akaita surutun auren Deeni da Mannira a dangi ba, har Gwaggo bare na fadin,
“Mugun abinsu ne ya fara koma musu, shisa yaje ya kwaso mayya… Watakila ta lashe mana kurwar Karime duk mu huta.”
A lokacin abin dariya yayita bata, sanda labarin mutuwar Mannira ta riske su zatai karya idan bataji wani iri a ranta ba, duk surutun da ta dinga sha, ashe ma ba ta da rabon zama mai nisa a gidan auren, fatan samun Rahma tayi mata. Ta dauka tunda tayiwa Maryama gaisuwa a wancen lokacin ba zata sake jin ko da labarin Mannira bane ba. Sai ga yarta a cikin gidan ta, yar Mannira mai idanuwan aljanu, yarinyar da tun jiya ta kasa samun sukuni a cikin nata gidan saboda su Haris sun shigo mata da ita bangarenta.
Har ranta ta dauka ko Maryama tazo da itane ta kwana biyu ta mayar da ita, sai yanzun da Ahmadi yazo mata da wani bayani da babu abinda ta fahimta a cikin shi sai cewar Layla din zata zauna ne a cikin gidan.
“Ni dai ba zan zauna a gida daya da ita ba, sai kasan yanda zakayi da mu… Haka kawai muna zaman lafiya zata zo ta lashe mun yara.”
Rai a bace Ahmadi yake kallon ta.
“Wani lokaci sai ki dinga magana kamar baki da ilimi. Kina manta babu wani abu maita a addini ne, sai kambun baka… Kuma ita kadai kika fara gani da kalar idanuwa haka? Ko bakiga wanda aka haifa babu idanuwan bane gabaki daya? Kinsan karki fara mun fitinar da bata da karshe, na fada miki Layla zata zauna ne saboda girmamawa, ba wai shawararki nake nema akan hakan ba.”
Wannan karon itace take kallon shi, yanda ya rufe ido yana datsa mata maganganu har yana kiranta da jahila a fakaice saboda wannan dangin mayun.
“Ni kake kira da jahila? Ahmadi ni kake cewa jahila akan nace ba zan zauna gida daya da mayya ba?”
Numfashi ya sauke.
“Kinga irin abin ko? Ni ban kiraki jahila ba, ki daina ce ma yarinyar mutane mayya tunda idan wani ya kira naki yaran da wannan kalmar ba zakiji dadi ba…”
Ido cikin ido take kallon shi.
“Akan me za’a kira nawa yaran da mayu tunda basu hada hanya da maita ba? Ni dai na fada maka ba zan zauna gida daya da ita ba, ko ka kwashe ta da Maryaman kasan inda zaka kaisu, ko kuma ni kasan inda zaka kaini.”
Murmushin takaici Ahmadi yayi yana binta da ido.
“Kiyi duk abinda kike so, Layla kam zataci gaba da zama a gidan nan, in ba aure ko mutuwa ya rabata da shi ba…”
Idanuwan Maimuna cike taf da hawaye take kallon shi, tana son tabbatar da cewa da gaske yakeyi wannan yarinyar da tun jiya take firgitata zai bar mata cikin gida.
“Ahmadi da gaske nakeyi ba zan zauna da ita ba. Dan Allah to ka raba mana gida.”
Ta karasa hawaye na zubo mata.
“Ke kinsan ko ina da hali ba zan raba muku gida ba saboda banason zumuncin yarana ya samu tangarda, balle kuma bani da wannan halin…”
Mikewa Maimuna tayi, hawaye takeyi sosai, ta kowacce fuska Maryama ta zame mata bala’i.
“Ni kam zan bar muku gidan, sai ku zauna. A banza ba za’a zo a lashe mun kurwa ba wallahi.”
Gyara zaman shi Ahmadi yayi baice mata komai ba, rigima take nema sosai. Ya rigada ya gama magana, ba zai biye mata ba. Kamar yanda yace Layla kama zama daram a cikin gidan. In tayi rikicin ta gama taga da gaske yakeyi zata hakura. Yana nan zaune yaga ta fito da jaka ta saka mayafi.
“Ina zakije?”
Sai da ta share kwallar da ta zubo mata sannan tace mishi.
“Gidan mu”
Yasan ba lokacin da ya kamata yayi dariya bane, amman dariyar ce ta kubce mishi, da kuruciyar su ma, duk fadan da takeyi dashi batace zatayi yaji ba sai yanzun da girma yazo musu, dariya yakeyi sosai da ta kara sosa ranta, wato bai damu ba, bai kuma dauki abinda takeyi din da wani girma ba.
“Tunda kaga mahaukaciya dole kayi dariya Ahmadi…”
Ta karasa maganar cikin kuka tana daukar yar jakar da ita kanta batasan me da me ta zuba a ciki ba. Tasan idan akace ta bar gidan Ahmadi da sunan yaji ba zata iya ba, tunda ta aure shi, rasuwar Audu ne tayi kwanaki har bakwai batare da shi ba, kuma ko a cikin jimami na rashi, kewar shi na nukurkusarta. Yanzun ma tayi ne kawai dan ta razana shi, ganin kukan da takeyi yasa Ahmadi tashi, amman har lokacin murmushine a fuskar shi, jakar yake kokarin kwacewa ta janye, ya kama hannunta duk kokarin kwacewa da takeyi ya karbi jakar, da kanshi ya kama mayafinta yana cirewa.
“Ke yanzun da girman ki sai kiyi yaji? Kuma ina zakije ki barni? Ko bakisan Maimuna ce jigon rayuwar Ahmadi bane?”
Wasu hawayen ne suka kara zubo mata, tana tsinewa ranar da Maryama ta dora idanuwanta akan Ahmadi har taji ya kwanta mata, tasata raba wannan soyayyar tashi da ita, shisa bata ga ranar da zata wayi gari da son matar nan ko kankani a zuciyarta ba.
“Ni ba zan zauna da yarinyar nan a gida daya ba, ba zan zauna ba. Kabarni in tafi tunda su ka zaba a kaina. Ka nuna mun yanda banda wani muhimmanci a wajen ka.”
Kamata yayi suka zauna, kalaman da yasan da wahala taki yin laushi yake amfani dasu wajen tausarta, tasan yasan cewa shi dinne rauninta, soyayyar shi ita ce rauninta.
“Idan ta lashe mun yara fa?”
Tayi maganar da wani irin sanyi murya dan gabaki daya ya gama kashe mata jiki.
“Ba zatayi ba, ki yarda dani mana…alfarma nake roko a wajenki Maimuna, ko saina tsugunna…”
Ahmadi ya karasa maganar yana kokarin sauka daga kujerar, da sauri ta riko hannun shi tana girgiza mishi kai, murmushi yayi mata.
“Nagode… Dan Allah karki takali Maryama da maganar nan, alfarma dana roka ta hada da wannan, wallahi badan Bilal ta kawo Layla ba, itama da nata dalilin kamar yanda kike da shi.”
Taji shi, amman ita tasan gasa Maeyama takeyi da ita, tunda ta kawo Bilal gidan take bakin ciki, shine sai da itama ta nemo wannan mayyar ta kawo, kowa na da yara da kuma dan riko kenan a cikin gidan.
“Kinga daman bata da mace ko…”
Ahmadi ya fara, wani irin kallo da Maimuna ta watsa mishi yana saka shi yin dariya yana daga hannuwan shi ya hadesu waje daya cikin sigar ban hakuri.
“Ka tashi ka tafi wajenta idan kewarta ce tasa kake son yimun hirarta a daki…”
Maimuna ta fadi wani irin kishi na taso mata, tashin yayi niyya tunda daman ya jimane haka saboda yana so ya fada mata zancen Layla. Amman maganar da tayi tasa shi yanke hukunci kara zama, yasan ana gab da kiran isha’i, sai yayi amfani da wannan damar ya fice gabaki daya. Maimunar tashi ta zama a lallaba, rikicinta sai shi.
*****
Ba ko yaushe yake zama gidan Yaya Ayuba ba, ko da kuwa duka yaran gidan suna can. Lokutta da dama dawowa yake yai kwanciyar shi a daki, yasan ko Ayya tana tunanin yana can wani lokacin. Haka yakan haramtawa Bilal zaman ko da yana so, shi dai da bakin shi baya ce mishi ya taso su taho tare, idan ya taso din kuma baya hana shi biyo shi. Yau baima kula da ya dawo gida ba, zane yake sonyi, haka kawai tunda ya fara rike fensiri, tun ma kafin Abbu ya saka su makaranta zaiyi zane akan duk wani abu da zai samu. Ganin ko gawayi ya tsinto yana musu zane a jikin bango yasa Abbu din kwaso mishi litattafan da zai dingayi a kai.
Yanzun ma gara yayi zanen shi, ko fada sukeyi idan aka rabasu akan takardun zanen shi yake huce haushin shi har sai yaji zuciyar shi tayi sanyi. Ba kasafai yake ganin kyawun abinda yake zanawa din da baya wuce mutane, dabbobi, kwari, ko duk wani abu da yake so ya zana din, amman sai ayita cewa yayi kyau.
“Allah yayi riko da hannayenka Rayyan, watakila kai kuma abincin ka a zane yake.”
Abbu ya fadi kwanakin baya, baigane asalin ma’anar kalaman ba, ya dai amsa da Amin ne kawai. Ya fara zanen yaji yunwa na naniqar shi, sai ya tuna fada yayi a makaranta bayan sun tashi, daya dawo baibi takan abinci ba. Tashi yayi ya fita daga dakin yana nufar kitchen, yasan inda Ayya take ajiye musu abincin su shida Bilal, nashi ya dauko da cokali, yana dawowa dakin ya samu Layla a ciki, hannunta rike da fensirin zanen shi, dayan rike da takardar da yai kwana biyu yana aiki a kanta, a karo na farko da yaso gwada zana wani a cikin gidan, ya kuma zabi daya fara da Bilal, ta dakuna takardar, tana kuma kokarin kara bi da fensirin a kai.
Kwata-kwata tun ranar daya sauke idanuwan shi kan yarinyar batayi mishi ba, bayason mage, basu da ita a gidan su, akwai a gidan Yaya Ayuba, kuma in dai zai shiga gidan zasu dauke dan ansan tsoron ta yake, a cewar Hajja Mama, matar Baffa kamar yanda suke kiran Yaya Ayuba din, tun yana yaro bayason mage, da ya gani kamar zai shide, shisa bayason Layla, idanuwanta na mishi kama dana jaririn magen gidan Baffa daya gani. Gashi duk inda yayi cikin gidan sai yaga kamar tana bin shine, lokutta da dama Haris ke zuwa yayi sauri yaja hannunta dan kamar shi kadai ya kula da bayason yarinyar na zuwa kusa da shi.
Kuma akan kunnen shi rannan yaji Ayya tace mayya ce, baiyi mamaki ba. Tunda itace mutum ta farko daya taba gani da kalar wannan idanuwan, da gaske mayyar ce, shisa duk inda yabi cikin gidan sai ya ganta. Yar kular abincin ya ajiye a gefe yana karasawa cikin dakin, fensirin ya fara fisgewa daga hannun ta, kafin ya fara kokarin karbar takardar da take rike da ita, bayason yasa karfi ya karba, kamar yanda da dukkan zuciyar shi bayason ko yaya ne jikin shi ya hadu da nata, dan a tsorace yake, kokari yakeyi na ganin bai kalli fuskarta ba.
“Saki mana…”
Ya furta, amman sai ta maqale kafada, ran shi bashida wuyar baci.
“Mtswww, ki saki nace, ta ina ma kika shigo mana.”
Rayyan yake fadi yana sake jan takardar, itama ja tayi ta kuwa rabata gida biyu, cikin tashin hankali Rayyan yake kallon takardar da take hannun shi, kafin ya kalli ta hannun Layla din, wani malolon bakin ciki na mishi tsaye a makoshi, baisan lokacin da ya dauketa da wani irin mari ba, dai-dai shigowar Bilal daya karasa da gudu yana tare hannun Rayyan daya daga zai sake mata wani marin, dayan hannun shi kuma yana ture Layla da ta gigice ko kuka ta kasa saki saboda azaba.
“Hamma… Me tayi maka? Baka ga yarinya bace?”
Bilal yake tambaya cikin tashin hankali yana juyawa ya kalli Layla da sai lokacin ta samu ta fashe da wani irin kuka.
“Ban sani ba, daka shigo baka ga abinda yake hannunta bane ba? Me yasa zata shigo mana daki?”
Hannunta Bilal ya rike yana rasa ta inda zai fara lallashinta.
“Amman ai karama ce, me yasa zaka mareta?”
Bilal ya sake tambaya, dan shi sam baiga dalilin da zaisa duk girman Rayyan ya mari ‘yar yarinya kamar Layla ba. Duk da saurin hannun shi akan kowa yake sauka. Ko jiya yayi mishi magana daya mari Shamsu saboda bai gani ba ya diga mishi ruwa. Yan kananan yaran gidan babu mai zuwa kusa dashi, wani lokacin ko wasa sukayi yayi sallama da gudu zakaga kowa na neman wajen boyewa. Wanda suka girmi Rayyan ma shakkar shi sukeyi, ko Khalifa yakan rabe gefe yaba Rayyan hanya, bamai so wani abu ya hadasu sam.
“Ka fita da ita, wallahi zan kara dukan ta idan taci gaba da kuka.”
Bilal hannun Layla ya kama yana janta suka fice daga dakin. Rayyan din nabin su da wani irin tsaki. Yanajin yanda bai daki wahalar kwanan shi biyu da yayi yana wahala ba sam, da Bilal bai shigo ba ya samu ya jibgeta da ya samu saukin tafasar da ran shi yakeyi yanzun
“Mayya kawai” Ya furta yana jin wata tsanarta a ran shi, a gefe daya kuma Bilal ne yake ta kokarin lallashin Layla daya samu tayi shiru, sai yatsun Rayyan kwance akan fuskarta. Baisan menene maraici ba, duk da yaji idan Ayya tayi baki wata rana suna maganar yanda shi din maraya ne. Itama kuma yaji ance marainiya ce, haka kawai yake jin tausayin yarinyar. Ko ido suka hada saiya tsinci kan shi dayi mata murmushi. Ko kadan basu da masaniya akan yanda kaddara ta bude musu sabon shafi.