Skip to content
Part 6 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

“Abbu…Sannu da zuwa.”

Huda da take zaune a cikin falon ta fadi cike da farin cikin ganin shi, idan kaga yanayin autar ta Ayya zaka rantse tayi satika bata ga Abbun ba, a maimakon kwanaki hudu.

“Huda”

Cewar Ahmadi yana dorawa da

“Ke kadai? Duk ina kowa? Ina Ayyar ku?”

Da murmushi a fuskar Huda har lokacin tace

“Kowa yana daki, Ayya tana sallar isha’i.”

Numfashi Ahmadi ya sauke, a gajiye yake jin shi, ko dan tun da suka isa Abuja bawai sun zauna waje daya bane ba, hidimar da ta kaisu kawai sukeyi.

“Ma shaa Allah, Ke kinyi sallar dai ko?”

Kai ta jinjina mishi.

“Tun dazun ma… Hamma Bilal ne daya shigo sai yace inje inyi.”

Wannan karin Ahmadi ne yayi murmushi.

“Madallah da Hamma Bilal…bari inzo kafin ta idar.”

Ya karasa maganar yana ficewa daga dakin. Kan shi tsaye bangaren Maryama ya nufa, ita da Jabir ya samu zaune a falon suna cin abinci. Jabir suna gaisawa ya dauki filet din shi yana ficewa.

“Sannu da dawowa…kayi zuru-zuru.”

Maryama tai maganar cike da kulawa, yar dariya Ahmadi yayi.

“Yanzun nan? Ko dan ba zama mukayi waje daya ba, kinsan ni da nayi zirga-zirga sai fuskata ta nuna.”

Murmushi tayi

“Hutu ne yai maka yawa.”

Ta karasa maganar da sigar tsokana tana mikewa, tana jin dariyar da yakeyi. Ruwa taje ta kawo mishi, bata ma gwada mishi tayin abinci ba tunda girkin Maimuna ne, tasan ko yana so ba zai taba ci ba. Wani lokacin ita kadai takan yi tunanin ko duka maza haka suke da adalci irin Ahmadi, sosai yake duk wani kokarin shi na ganin yayi adalci a tsakanin ta da Maimunar.

“Ya kuke? Fatan dai kowa lafiyar shi kalau… Na shiga in duba yaran a daku nan su dana shigo, ina jin basu dawo daga sallar isha’i ba.”

Kallon shi takeyi.

“Anya kuwa? An idar da sallah, sai dai ko in sun tsaya wajen abokai ana hira. Duka lafiyar su kalau. Alhamdulillah.”

Kai ya jinjina

“Alhamdulillah, ina Layla?”

Murmushin ta Maryama ta fadada.

“Fushi take mun dan na mata fada kan saka kananun kaya.”

Dariya yayi

“Layla manya… Yaran ne basajin magana, ni da ina yaro abinda za ayi mun magana ma bana farawa, idan akayi sau daya kam bazan bari a maimaita ba…”

Numfashi Maryama ta sauke, zata ce duk wani abu da ta saka Layla tanayi, bangaren aiki kuwa in ba tana makarantar boko ko ta islamiyya ba cokali bata bari ta daga. Girki tun tana koya mata har yanzun babu wani abu da bata iya girkawa ba. Tana da rigima, sosai tana da rikici, amman idan ba tabata kayi ba babu ruwanta da kai, ga fadanta baya rabuwa da wuri saboda mita da take da ita, kusan Maryama zatace duka yaranta sun biyo sanyin hali irin nata, kau da kai da sanin ya kamata irin na baban su. Jabir ne ma bashi da hakuri idan ka tabo shi.

Sai Layla tayi wani abin sannan take tuna cewa ba daga jikinta yarinyar ta fito ba. Matsalar da suka cika samu da Layla bai wuce yanda a rayuwarta take bala’in son kananun kaya ba, idan zata wuni da dogon wando da yar riga yafi mata dadi, gara ma ranakun asabar da Ahmadi ya ware yana zama a gida. Shine zaka ga tana yini yawo da hijabi, kamar duk gidan shi kadai ne take jin nauyi ko shakka kar yai mata magana. Amman da yan shekarunta ko atamfa ce skirt din sai tace a sha mata shi, ga kirar jiki da Allah yayi mata, wasu lokuttan Maryama kan jinjina kalar jikin da Layla take da shi, shisa take tsoron shigar da takeyi.

Bataso, amman da duk rana da take kokarin ganin ta rabata da kananun kaya, da ta daina sai mata, kudinta duk idan ta tara akwai gidan su Farida, nan cikin unguwa, islamiyyar su daya da Layla din, kuma ajin su daya, sana’ar gwanjo mahaifin Farida yakeyi, dila-dila yake kawowa daga kwatano, hakan yasa matar kan bude itama tana siyarwa cikin gida. Sai dai Maryama taga Layla ta shigo da abinta, duk yawancin kudadenta yanzun a can suke karewa, kuma sukan mata saukin kayan saboda sanayya. Idan ma tayi mata fada sosai, kwana biyu tana saka atamfa haka zakaga dakyar take motsawa saboda matsewar siket din da yake jikinta.

Zatayi karya idan tace abin baya damun ta, sai ta tuna zancen da mutane kanyi na cewar

“Dan riko wahalar sha’ani gare shi”

Wasu ma sukan ce

“Maraya akwai wahalar riko.”

Duka biyun take gani akan Layla wasu lokuttan, amman duk wani abu da zaifi karfinta da addu’a take hada shi, Laylar ma addu’a takeyi mata, saboda girma take karayi, halittarta ta ‘ya mace na kara fitowa, shisa yanzun Maryama ta numfasa kawai tana fadin.

“Allah dai ya shirya mana, yaran yanzun magana har sai bakin ka yayi tsini.”

Mikewa Ahmadi yayi.

“Amin thumma amin. Abinda yafi tsini kam bakin ka zaiyi. Idan sun shigo nasan zangan su…”

Ya fadi yana dorawa da yi mata sallama, daman lafiyarta da ta yaran ya shiga dubawa kamar yanda ya saba ko aiki ya dawo, balle kuma tafiyar kwanaki hudu. Yayi kewar su ba kadan ba. Yana fita dakin Maimuna ya wuce, inda ya sameta ta fito falon tana zaune, yanayin fuskarta yake kallo, girma bai hana shi gane rigimar da take shimfide a kan fuskar ba.

“Uwargidan Ahmadi…”

Kallon shi tayi tana kauda kai, tunda ta fito daga daki Huda ta fada mata ya shigo ya fita take kallon agogo, mintina sha ukun sai take ganin su kamar awanni sha ukku dan tasan yana wajen Maryama ne. Wani irin tuquqin kishi da shekaru basuyi komai wajen rage mata ba take jin yana taso mata.

“Magana fa nake yi…”

Sake kallon shi tayi

“Ai na dauka a can zaka kwana.”

Yanayin yanda tayi maganar ne yasa shi dariya.

“Hmm…”

Ta furta, ba yau ya saba mayar da ita mahaukaciya ba daman.

“Yi hakuri… Na shigo kina sallah, shine nace bari inje mu gaisa kafin ki idar.”

Cike da rigima take kallon shi.

“Ko dawafi nakeyi ai kasan na idar tun dazun dai. Sai kayi zaman ka kunata labari, kuma tunda girkina ne, kwana hudu bangan ka ba, ya kamata ace ka bari na fara sakaka a idanuwana tukunna kaje duk inda zakaje.”

Murmushi Ahmadi yakeyi, zuwa yanzun indai rikicinta ya saba da shi.

“Ba za’a kara ba Uwargida. Kiyi hakuri…”

Numfashi ta sauke

“An dawo lafiya?”

Ta fadi ciki-ciki har lokacin, sai da ya tabbatar ya jata da hira ta daina amsa shi dai-dai tukunna ya mike.

“Da kaci abinci dai sai kayi wankan.”

Kai ya girgiza mata

“Bari dai in watsa ruwan, kafin in fito kin hadamun abincin…”

Ahmadi ya karasa maganar yana soma tafiya. Mikewa tayi itama, so yayi ya wuce bangaren shi, amman yana son ganin su Rayyan, haka kawai ya kasa hakura, musamman da yasan in ba a hanya ya hadu da Rayyan din ba, ba zaije yayi mishi sannu da zuwa ba. Kowa zaije amman banda shi, yaso ya tambayi lafiyar yaran daya bayan daya, amman yana gudun jin ance Rayyan din yayi wani abu bayan tafiyar shi, Allah ne shaida da shi yake kwana a ran shi, da shi yake kuma tashi. Ko waya tayi kara sai gaban shi ya fadi, sai yayi zaton ko Rayyan ne ya dauko wata maganar da yayi nisa da gida.

Akan Rayyan ne yasan cewa zai yiwu ka haifi da ka dinga jin zuciyarka na rawa duk sanda zaka gan shi, yanzun da yake nufar dakin su Rayyan din sai yaga kamar yayi mishi nisa.

“Oh Allah…”

Ahmadi ya furta jin yanda zuciyar shi ke rawa.

“Allah idan jarabta ce ka kadarta mu ta fado akan Rayyan, Allah ka bani karfin zuciyar daukar ta. Allah na yafe mishi duk wani laifi daya taba mun, wanda na tuna da wanda na manta. Rabbi ka shiryamun yarona, Kai ka bani amanar shi, kai ka sakamun kaunar shi, Allah karka sa ya zama rauni na.”

Shine addu’ar da ya tsinci kan shi da yi, duk da ya kasa samun natsuwa, musamman daya tinkari dakin yaji wani irin wari da tashin hankali bai barshi fahimtar ko na meye ba farat daya, sai da ya kara kusantar dakin sannan ya gane warin sigari ne, badan cutarwar da takeyi ba, cutarwar da yagani da idanuwan shi akan abokin aikin su da bature ne dan kasar amurka, haka da wahala ka ganshi batare da sigari ba, kullum cikin buka ma cikin shi hayaqi yake, lokaci daya ya fara wani irin tari daya kwantar da shi, kafin ace kansar huhu ce tayi mishi muguwar illa a sanadin taba.

Ko sanda sukaje asibiti duba shi kafin a mayar da shi kasar shi inda ya mutu a can, yanda yake kokawa da numfashin shi Ahmadi zaiso duk wani mashayin sigari ace yana dakin asibitin dan yaga tashin hankali da illar da sigari takeyi ko zai yarda ya daina cutar da kan shi. Shi ko warin ma idan yaji sai zuciyar shi ta dinga tashi, tana daya daga cikin abubuwan da yaki jinni.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ya furta a fili yana kasa kwankwasa kofar dakin jin warin sigarin da zuciyar shi taki taya kwakwalwar shi karyata cewa ba daga cikin dakin su Rayyan warin sigarin yake kara fitowa ba. Wani irin bacin raine da yake shirin danne firgicin da yake ciki ya saka shi tura dakin batare da sallama ba, haske ne gauraye da dakin saboda akwai wutar lantarki. Rayyan na zaune akan kujera ya dora hannayen shi kan teburin da yake gaban shi, Bilal na tsaye, inda ya juyo saboda turo kofar da su duka suka ji anyi.

“Abbu…”

Bilal ya kira da wani irin yanayi da yafi tashin hankali a muryar shi, Ahmadi kuwa kallon su yake, dan yanzun ya kara tabbatar da cewa daga dakin su warin sigarin yake fitowa. Tunda gashi nan cike da shi.

“Sigari, Rayyan sigari kake sha yanzun kuma?”

Cewar Ahmadi da wani irin bacin rai da disappointment na gaske tattare da muryar shi, yanayin da ya saka Bilal fadin.

“Ba shi bane Abbu, ba Hamma bane.”

Da wani yanayi Ahmadi yake kallon Bilal, Rayyan kuwa yana zaune inda yake, ko motsi baiyi ba balle wani yai tunanin zai tanka, asalima idan ka shigo dakin zaka rantse da Allah abinda yake faruwa bai shafe shi ba, wani ma zai iya cewa bai taba sanin Bilal din da Ahmadi ba ballantana yabi takan abinda suke tattunawa.

“Kar kaimun karya Bilal, warin sigari tun daga wajen dakin nan anaji, karka ce mun daga kofar gida ya taso ya zabi ya tattaru cikin dakin ku.”

Kai Bilal ya girgiza

“Ba ina nufin ba’a sha sigari bane, ina nufin ba Hamma ya sha ba.”

Duk da alamu sun nuna Ahmadi bai gama yarda da zantukan Bilal din ba, amman akwai wani hope daya cika idanuwan shi, da gaske so yake ko yane a karyata mishi zargin shi. Abin zai mishi yawa idan ya zamana Rayyan dinne.

“Bilal…”

Ahmadi ya kira cike da kashedi, sauran karshen sigarin daya rage Bilal ya dago hannun shi yana nunawa Ahmadi da fadin.

“Ba shi bane Abbu, ni ne”

Ya karasa maganar muryar shi na fitowa can kasan makoshi.

“Bilal”

Wannan karin da mamaki Ahmadi yai maganar, badan baya ganin samari sa’annin su Bilal da wanda ma basu kaisu ba da shan abinda yafi sigari, sai dan haline da ko a mugun mafarki bai hango Bilal din dayi ba

“Sigari Bilal? Ina kuke so in saka raina, kamar Rayyan bai ishi sakani juyi duk dare ba, sai ka fara kaima ko? Hawan jini kuke son ganin na samu? Kun kyauta mun kenan yanzun? Um? Bilal ka kyauta mun?”

Kan shi Bilal ya sadda kasa, yanajin wani abu na taso mishi tun daga dan yatsan kafar shi har zuwa kirjin shi inda yai mishi karan tsaye a zuciyar shi.

“Allah ya kyauta.”

Ahmadi ya fadi yana juyawa ya fice daga dakin, zuciyar shi zafi takeyi, duk da wani bangare na zuciyar shi da yake jin kamar bai kyauta mishi ba wajen jin dadi da ba Rayyan bane ya sha sigarin, a lokaci daya wani abu da baiyi tunani bane yaji ya karya a zuciyar shi, kamar Bilal ya karya yardar da yayi mishi ne. Saboda ko a cikin mutane yakan yi alfahari da halayen Haris da Bilal, yakan ce zai shaidi yaran nashi su biyu akan komai. Idan shima yace zai fara rashin jin nan baisan inda zai saka kan shi ba.

Da yawan mutanen da suke zagaye da shi kanyi zaton hakurin da yake da shine raunin shi, yana mamaki yanda mutane suke daukar hakuri a matsayin rauni. Sam hakuri ko da yayi yawa baya taba zama rauni, idan baka da karfin zuciya ba zaka iya hakuri akan lamurra da yawa ba, sai juriyarka ta kai wani mataki ne zaka iya kauda kai akan wasu abubuwan. Hakurin shi ne karfin zuciyar shi, yaran shi sune raunin shi, yaran shi sune cikon farin cikin shi, tunda ya same su duk inda zai juya da tunanin su manne da zuciyar shi.

Kaddara ce ta bashi Layla da Bilal, duk da jinin shi na yawo cikin nasu, amman basu da gadon shi, shisa a duk cikin yaran Bilal ne kadai ya taba siyan fili da sunan shi, takardun na ajiye ko Maimuna bata san da shi ba, yana jin yaran inda yake jin su Haris. Da gaske yake wani abu ya karye a zuciyar shi, baisan wani zazzabin tashin hankali ya rufe shi ba saida ya watsa ma jikin shi ruwa yaji tsikar jikin nashi na mimmiqewa da alamun wani sanyi da yake ratsa shi.

Ko da Maimuna ta shigo yayi duk wani kokarin shi na ganin bata karanci damuwar da yake tattare da ita ba, abincin da ta kawo haka ya dinga saka shi a baki yana taunawa yana hadiyewa, lomar da yaji ta kakare a makoshin shi sai ya bita da ruwa. Da tayi magana kan canjin yanayin shi ca yayi mata.

“A gajiye nake jina Maimuna, kamar gajiya ke son saka mun zazzabi.”

Da ta bashi maganin zazzabi bai musa mata ba ya karba yana hadiya tunda da gaske yanajin zazzabin. Sai dai barawon bacci ma kasa samu yayi duk da ya raya daren ne da salloli yana rokama yaran nashi karin shirya, addu’ar tashi na yawaita akan Bilal, Rayyan da kuma Layla. Saboda yanda yake jin kamar duk wata kaddara da zata same shi ta bangaren yaran da wahala ta wuce kan su ukkun, tunda su kadai ne suke caja mishi kai har haka.

***** *****

Tunda Ahmadi ya fice daga dakin babu wanda ya motsa a cikin su har lokacin, Bilal jin shi yake kamar iskar da yake shaka bata kaiwa cikin shi, kamar iskar dakin gabaki dayanta tayi mishi kadan, hakan ne yasa shi takawa yaje inda makunnin fankar dakin take yana kure gudunta gabaki daya. Tsaye yayi a wajen yana sauke numfashi cikin son yaji ya koma mishi yanda yake da kafin maganganun Abbu. Sai dai me, yana juyawa yaji komai ya jagule mishi, ganin Rayyan ya dauko zaro kwalin sigarin shi daga cikin aljihu yana zaro lighter din shi, ya bude kwalin ya zaro kara daya ya saka a bakin shi yana riketa a tsakanin labban shi, kafin yayi ma karshen sigarin rumfa da hannun shi ya kunna wutar lighter din gudun kar iskar fankar ta hure mishi

“Hamma…”

Bilal ya kira da duk wani bacin rai da zai iya dorawa a kan muryar shi. Satika ukku da suka wuce yana kwance Rayyan din ya shigo dakin, sai da gaban shi ya fadin jin warin sigarin da yake yi.

“Hamma warin sigari kakeyi, daga ina kake?”

Shine tambayar da yayi wa Rayyan din yana mikewa zaune babu shiri, da wani yanayi a fuskar Rayyan din yace

“Da gaske? Warin kaji a jikina?”

Kai Bilal ya daga mishi yana tabbatar mishi, baice komai ba ya taka inda suke ajiye turarukan su ya dauki daya yana fesa ma jikin shi, hadi da dan daga hannayen shi yana shakar iskar ko zaiji warin sigarin da Bilal yace yaji yanayi.

“Yanzun fa?”

Ya bukata, yana saka Bilal din binshi da wani irin kallo

“Daga ina kake? Me yasa kake warin sigari?”

Kujera Rayyan yaja ya zauna batare da yace komai ba, hakan yakan yi duk idan Bilal yayi mishi tambayar da yasan idan ya amsa mishi ita zai sake bude mishi kofar jifan shi da wasu sababbin tambayoyin ne. Daga waje yake, kuma yana warin sigari ne saboda ya sha, idan ya amsa Bilal zai fara tambayar shi dalilin da ya saka shi shan sigari, kuma shi da kan shi baisani ba, wucewa yazo yi yaga wasu gungun samari anan kasan layin su sun taru suna ta sha, baisan meye dayan abin ba, sigarin kawai ya iya ganewa, kuma haka kawai yaji a duniya babu wani abu da yake son yi banda ya sha sigari.

Shagon da yaje siye sai da mutumin ya tambaye shi har sau biyu idan sigari yake son siye

“Malam idan babu ne ka fadamun in tafi.”

Rayyan ya fadi maimakon amsa tambayar da mai shagon yayi mishi

“Akwai, wacce iri?”

Cewar mai shagon da wani yanayi a muryar shi

“Ni dai kabani kowacce iri.”

Hakan kuwa ya siyi sigarin da sai bayan an bashi ita da lighter din daya siya yabar shagon tukunna ya duba kwalin yana ganin an rubuta aspen a jiki. Zuqar farko da yayi wani irin tarine ya sarqe shi kamar zai shide, amman yana gama dawowa ya sake gwadawa, har ya sha kara biyu bai gane dalilin da yasa mutane suke sha ba, banda bakin shi, da makoshin shi da yaji suna wani qauri-qauri, kirjin shi a cike yake fal da hayaqi. Daga ranar ne kullum idan ya fita sai ya busa yakai kara biyar, har zuwa yanzun ba zaice ga dadin sigari ba, ba zaice ga dalilin shi na sha ba, abu daya zai iya shaidawa, yanda idan yaji yana son sha din jikin shi har wani iri yake yi mishi.

Ya gane dalilin da yasa ake cewa sigari na da wahalar barin sha, duk sanda zai sha a waje zai saka minti a bakin shi dan ya daina warinta, amman shekaranjiya har Ayya sai da ta ce

“Ni kam bansan inda hancina yake dibomun warin sigari ba.”

Sanda ya shiga ya dauki abinci, hakan yasa shi yana shiga daki ya sake kayan jikin shi yana kuma watsa ruwa. Bilal a satika ukkun bai gaji da tambayar shi ba, shikuma bai daina yi mishi shiru ba, har sai jiya da yaji yana son ya sha, amman bayason fita daga gida kuma, saboda zaune yake yana zane, yanzun daya zana jarabawar shi ta gama sakandire yana zaune jiran sakamako ya fito, yakan tsinci kan shi da jin kadaici na rashin abinyi. Musamman idan Bilal yana makaranta, shisa zanen ne kawai abinda yake debe mishi kewa, ba abokai yake dasu ba ko a cikin unguwa ballantana yace zai fita suyi hira.

Idan yagaji da zama a daki yakan fito ko zai ga giccin Layla, haka zai ta mata aiken rashin dalili har saita kosa ta mayar mishi da magana yaga yasa ta kuka tukunna, to jiyan sam bai ganta ba, sanda ya aika a kirata ance mishi kanta yake ciwo ta sha magani ta kwanta. Zai iya cewa harda son ya ganta da yakeyi, ya duba yaga ya jikinta da kuma kin son ganinta da ya hade mishi waje daya ya kara mishi son busa hayakin, ko ba komai zai kalli yanda ya gwanance yake fitar da samfur samfur na hayakin cikin satika kadan haka.

Ya zuqa sosai yana fito da hayakin Bilal ya shigo, bai ma gama ba ya koma mishi ciki yana saka shi fara tari.

“Hamma…”

Bilal ya fadi da bayanannen tashin hankali yana karasawa inda Rayyan din yake hadi da mika hannu zai karbe sigarin, Rayyan ya janye hannun shi yana fadin.

“Meye haka? Ka daina yi kamar baka san ina sha ba.”

Ya san yana sha, tun ranar farko da yaji warinta a jikin shi, da yana da abokai ne ma sai yayi zargin wani daga cikin sune yake shan sigarin suka zauna waje daya har jikin shi ya dibo warin hayakinta, amman Rayyan ne, bashi da zuciyar hakuri da mutane har suyi sabon zama abokai, koya kaso jurewa shine zaiyi fada da kai ya daina maka magana.

“A waje kake sha, me yasa zaka fara a cikin gida? Me yasa? Idan Ayya ta gani fa? Idan Abbu yagani me zaka ce?”

Sake kai sigarin shi Rayyan yayi a bakin shi yana zuqa hadi da fitar da hayakin.

“Dan Allah, dan girman Allah ka kashe, idan dole ya zame maka sai kasha, kayi a waje, kar kabari Ayya ko Abbu sugani… Ni dai na roke ka.”

Bilal din ya fadi kamar zaiyi kuka, idan har zuciyar shi na zafi akan wannan sabuwar dabi’ar da Rayyan ya kwaso musu, baisan me Ayya da Abbu zasuji ba, maimakon halayen Rayyan din su gyaru, kullum kara watsewa suke kamar ba’a mishi addu’ar shiriya.

“Hamma…”

Bilal ya kira yana kallon yanda Rayyan din yake cigaba da busa tabar shi kamar bada shi yake magana ba. Idan yayi wani abin Layla tace

“Jujun ne ya motsa”

Sai abin yaba Bilal dariya, amman yanzun da gaske ya fara yarda da maganarta, Rayyan ba zai rasa almatsutsai ba, in ba haka ba, kana zaune lafiya ba zaka tattago abinda zai saka ran kowa da yake kusa da kai ya baci ba. Tsaye yayi har sai da ya gama shanye sigarin, dan yasan idan gidan Radio zai bude a wajen saboda surutu Rayyan ba zai kula shi ba. Karshen da ya ajiye kan tebir Bilal ya dauka ya saka a aljihun shi.

“Ka rufa mun asiri, ka boyeta inda wani ba zai gani ba.”

Daukar kwalin Rayyan yayi yana sakawa cikin aljihun wandon shi. Yana sake gyara zama a cikin kujerar da yake zaune, yana kallon Bilal din ya dinga feshe dakin da turaruka. To yau ma da yayi sallar isha’i a waje ya tsaya suna zancen wasan kwallon kafa da matasan unguwa shisa bai shigo gida da wuri ba, ganin lokaci na jira, kuma yasan Ayya na can tana tunanin dalilin da yasa har lokacin bai shiga ya dauki abincin ba yasa shi yi musu sallama ya shigo gida. Yayi niyyar wucewa bangaren Ayya kai tsaye, sai kuma yaji yana son shiga bayi, shisa ya nufi dakin su, inda ya sami Rayyan zaune yana shan sigarin shi kamar yana abin kirki.

Fada yakeyi kamar zai ari baki, ya karasa ya kwace karshen sigarin kenan ya kasheta jikin tebirin da yake ajiye ya sake bude baki zaiyi magana Abbu ya shigo. Tun tasowar su akwai kananun laifuka da Rayyan din zaiyi ya dauke mishi su, zuwa yanzun kuma ko a aiko Rayyan ya kira shi bai fada mishi ba, zai ce ya fada shine ya manta baije kiran ba, irin kananun abubuwa haka da zai iya dauka na laifukan Rayyan duk yanayo. Shisa yau sam karyar cewa shi yake shan sigarin batayi wahalar fitowa daga bakin shi ba sam. Musamman da yaga abinda yake cikin idanuwan Abbu, yanda ya nuna ba zai iya jure wata gurbatacciyar halayya daga bangaren Rayyan din ba.

Sai dai maganganun shi sun daga hankalin Bilal fiye da yanda yayi zato, ya dauka maganganun sun taba zuciyar Rayyan, sai yanzun da yake kallon shi ya sake kunna sigarin shi kamar komai bai faru ba, kamar Abbu bai fadi abinda ya fada ba

“Anya akwai hankali a tattare da kai kuwa Hamma? Ko zuciya ce kai ba’a halliceka da ita ba, da gaske sigarin kake kara kunnawa? Baka ga halin da Abbu ya fita a ciki bane halan? Baka ga me kasa nayi ba?”

Karan sigarin Rayyan ya cire daga bakin shi, saboda baiga dalilin da zaisa Bilal ya tsare shi yana mishi fada kamar kanin shi ba.

“Me nasa kayi?”

Ya bukata yana tsare Bilal din da idanuwa, dariyar takaici mai sauti ce ta kwacewa Bilal din

“Tambayata kakeyi? Hamma tambayata kakeyi?”

Yana kallon yanda kowa a gida yake fadin ba’a batawa Bilal rai, jinsu kawai yake, ko suce Bilal na da hakuri, Bilal baya fada, Bilal baya fushi, suna magana kamar a duniya babu wanda yake da halaye nagartattu kamar Bilal, bayan rana bata fitowa ta fadi baiga kalar rashin hakurin Bilal ba, baya saukewa akan kowane sai shi, yanzun ma ga bacin rai nan bayyane a fuskar shi.

“Ka daina girmamani kana kirana Hamma, kana kuma hadawa da ihu a karshen zancen ka.”

Karasawa Bilal yayi inda Rayyan din yake yasa hannu ya dauki kwalin sigarin da ya ajiye da lighter din, hannu Rayyan ya dago, kallon da Bilal yayi mishi yana saka shi mayar da hannun

“Woo… Allah ya baka hakuri.”

Rayyan ya fadi yana dariya ganin yanda ran Bilal din ya baci da gaske, shikuma a cikin abinda ya faru duka baiga wani abu na bacin rai ba, sigari ce ya fara sha baisan dalili ba, yanzun kuma bashi da wani dalilin dainawa. Shi baice Abbu yaji haushi dan ya sha sigari ba, baice Bilal ya dauki laifin da ba na shi ba, yana kallon shi tun tasowar su yana hakan, so yake yanda bai taba tambayar shi dalili ba, shima ya daina tambayar shi dalili akan abubuwa irin haka. Yana kallo Bilal ya fice daga dakin, mikewa yayi yana shiga wanka abin shi, idan Bilal ya gama fushin ya huce zai neme shi ya sani.

<< Martabarmu 5Martabarmu 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×