Bai fara dana sanin neman gurbin karatu a jami’ar Ahmadu Bello da take garin Zaria ba sai da ya samu. Bai san sa’a bace ko kuma matakan su daya tsallake ko kuma sanayya ta manyan mutane da Abbu yayi ta saka shi samun abinda ya nema. Kawai dai yasan ya fara dana sani ne daga jiya da Haris ya dawo har dakin su ya shigo da sallamar shi yana zaune, maganar shi ta farko bayan sun gaisa ita ce,
“Abbu yake fadamun ka samu gurbin karatu a makarantar mu, shine ko ka kira ka sanar dani. Naji dadi wallahi, saboda duk bangaren lafiya dai ne.”
Tsayawa yayi yana kallon Haris da yake magana kamar ya fada mishi ya zabi karantar fannin daya danganci kwakwalwa da sanin halayyar dan Adam wato Psychology saboda ya kasance waje daya da shi. Ya zabi fannin ne saboda yana son fahimtar wasu daga cikin halayen shi, wasu cikin tarin tambayoyin da yake tunanin bangaren zai amsa mishi akan kan shi, badan wani dalili ba. Kuma ko ba komai kaunar da yake ma uniform zai kasance yana saka farar rigar nan lokaci zuwa lokaci. Saka uniform ne abu daya da yayi kewa bayan gama sakandire din shi. Haka kawai sai yaga duk kayan da zai saka ba zasu kai yanda yake saka uniform yin kyau ba.
Wani lokaci can baya kaunar da yake ma uniform ta saka shi tunanin aikin soja, sai dai har kasan zuciyar shi yaji haka kawai ba zai iya nisa da gida ba, kuma bayason takurar da take tattare da aikin, yana da taurin kan da yake da tabbacin zai wahala a aikin. Zuciyar shi ba tada sanyin da zata lankwasu yayi biyayyar da yaji ana labarin yiwa manya. Shisa bai kara barin tunanin ya dame shi ba, kafin ya yanke hukuncin zabar fannin da ya zaba yanzun, yayi tunani kala-kala, ayyuka barkatai sun zo ran shi. Sai dai zuciyar shi tafi rinjaye akan Psychology din ne.
Haris din kuma yana bangaren lafiyar yara ne wato Pediatric. Ba shiga harkar kowa yake ba a gidan banda Bilal, anso hada su daki daya. Tashin hankalin da ya dinga yine yasa su Abbu suka bar su shida Bilal a daki daya. Lokacin da yaji labarin bangaren da Haris ya samu gurbin karatu da Bilal kawai yayi zancen
“Hamma zaiyi kyau da likitan yara…ko a gidan nan ka kalli yanda su Intisar ke son shi. Ko masallaci muka fito ba zaka rasa ganin shi rike da wani yaron ba”
Murmushi Bilal yayi.
“Duk yaushe ka kula da Haris haka?”
Harar Bilal yayi.
“Dan bana shiga harkar kowa baya nufin bana kula da abinda yake faruwa.”
Jinjina kai Bilal yayi.
“Naga alama ai, ko Ayya zancen da tayi mun kenan. Sanyin halin shi ne yasa yara suke manne da shi, ga kyauta kuma, ba zaka raba aljihun shi da dan biskit ko alawa ba.”
Rayyan kwanciya ya gyara yana yin shiru, surutun Bilal ya cigaba da yi har saida ya kule
“Wai bacci kayi ko wulakanci ne yasa kayi banza ka kyaleni ina ta zuba ni kadai?”
Ba baccin da yakeyi, ya lumshe idanuwan shine, yana jin shi, a duka zancen shi babu wanda zai bada amsa, a wajen shi hirar ta rigada ta kare, ya fadi abinda yake son fada. Duk da yaso hirar tayi tsayi sai Bilal din ya kunna shi da maganar da yayi kan yaushe yake kula da halayen Haris. Yana so ya mayar da shi kamar baisan abinda yakeyi ba. Shisa sam mutanen da yake ji a ran shi basu da wani yawa, saboda halayen su na saurin cakar da shi.
Jiyan ma kallon Haris ya dinga yi, har ya gama surutun da zaiyi. Ganin ba amsa shi zai ba yasa ya tashi ya fita daga dakin. Yanayin fuskar shi ma ya bala’in bata ma Rayyan din rai, saboda haka kawai ba gayyato shi yayi ba, baice ya shigo daki ya same shi ba. Da suka gaisa bai sashi zama ya fara mishi hirar rashin dalili ba, yazo yasa yanajin kamar yayi mishi laifi. A fuska ya nuna baiji dadin shirun da yayi ba.
“Tsalle kake so inyi mu rungume juna saboda zamu kasance a makaranta daya ko me?”
Rayyan din ya furta cikin sigar mita yana karasa maganar da jan tsaki. Yana da dalilai da yawa da yasa baya shiga harkar kowa. To yau ma yana haduwa da Haris din yake tambayar yaushe yake da niyyar zuwa ya fara hada-hadar registration
“Ko zamu tafi tare gobe ne?”
Kai ya girgiza mishi, da alamar kosawa a muryar shi ya ce,
“Zan taho da kaina Hamma…”
Dan jim Haris din yayi, yana son duka yan uwan shi, ba su kadai ba, shi mutum ne na mutane. Wasu lokuttan Rayyan na saka shi son tambayar shi ko ya taba mishi wani abune da bai sani ba shisa yake karayin kicin-kicin da fuskar shi duk idan sun hadu. Shi bayaso ya bata ran kowa sam-sam, ko wani yagani cikin bacin rai yakan yi kokarin ganin yaja shi da raha har saiya murmusa. Tun tasowar su abu kadan Rayyan bai taba duba cewa ya bashi shekaru kusan ukku ba, haka zai kama shi da jibga kamar ganga. Da suka fara hankali kuma baya magana da shi, in zasuyi haduwa goma idan bai mishi magana ba zai rabe gefe kamar bayason wani abu ya hadasu.
Ranakun duk da Rayyan ya fara mishi magana to na farko ba zai manta ba, rashin lafiya yayi harya kwanta asibiti, da sukaje duba shi yayi mishi ya jiki, amman yana iya yin jinya. Rayyan din ya shiga dakinsu da sunan duba shi, bayan sallama zai iya mintina goma a tsaye ya jingina bayan shi da bangon dakin, har sai in shi ya gaji da jin shirun yai yawa yace
“Rayyan…”
Sannan fa zai amsa da
“Ya jikin ka?”
Bayan ya amsa wannan da wahalar gaske ya kara cewa wani abin zai juya ya fita daga dakin. Wani lokacin yana ganin Rayyan din yayiwa sauran mutanen gidan haka. Amman shi Haris wani irin mutum ne mai son kulawa. Bai saba a share shi ba, ko waje ya shiga kirkin shi na sawa kaga mutane zagaye da shi, kowa na son kula shi, kowa na mishi fara’a banda Rayyan. Bai gajiya ba, cikin sanyin murya ya ce,
“Registration din su da dan wahala Rayyan, da mun tafi tare sai in tayaka, kaga ba sanin kan makarantar kayi ba.”
Kallon shi Rayyan din yake yi, gabaki daya surutun ya ishe shi, tsayuwar da yayi ma ya gaji da ita
“Zan taho idan na shirya…”
Yanayin yanda yai maganar yasa Haris din jinjina kai kawai
“Allah ya bada iko ya taimaka…”
Ya fadi, ko amin din a zuci Rayyan ya fadeta ya raba Haris din yana wucewa daki. Ya guji jami’ar bayero saboda Abbu da tarin abokan shi da yake da tabbacin ba za’a rasa a duk wani fanni da zai nemi gurbin karatu ba. Duk da Abbu din yana bangaren lissafine. Amman yana da matsayi a makarantar da ko da mu’amala bata hadaka da shi ba, yasan kasan sunan shi, kasan kuma ko waye shi. Baya bukatar wannan attention din na mutane, da ma ace Abbu zai shiru da bakin shi, yanda yake alfahari dasu ba zai barshi yaki nuna cewa shi din ba nashi bane ba.
Kowa zai dauki ido ya saka mishi, wasu da yawa zasu dinga tsammanin gaisuwa daga wajen shi a duk haduwar da zasuyi. Ba zai iya wannan rayuwar ba. Yanzun ya tsallaka Zaria ma, Haris yasa shi harya fara dana sani. Dadin shi daya kawai, Bilal yace shima nan din zai nema.
“Na dauka Bayero kake so, saboda ka burge Abbu.”
Kai kawai Bilal din ya jinjina yana furta
“Kana da matsala.”
Ya fita ya kyale shi. Har ran shi daman yaso ya roki Bilal din daya zo ABU shima, tunda har ya hango yanda zaiyi rayuwa a makarantar shi kadai. Tunda yana da yakinin ba zaiyi aboki ko daya ba, watakila sai dai iya gaisuwar cikin aji idan ta zama dole. Yana lissafin yanda da wahala ya iya hada satika hudu cikakku bai shigo Kano ba, har kasan zuciyar shi yake jin yanda zai yi kewar Bilal din.
“Har da Layla”
Wani bangare na zuciyar shi ya fadi a lokacin, zai kewar ganin ya sakata kuka. Yana da wannan tabbacin, amman bayajin tana cikin dalilin da zai sashi zarya tsakanin Kano da Zaria duk bayan wasu yan kwanaki. Sai bayan da Bilal yace zaije Zaria. Sai yaji son yazo duk bayan wasu kwanaki sunki fita daga kan shi, ya fadama kan shine zai dinga zuwan ne kafin Bilal ya sami gurbin karatu. Idan ya samu kuwa watakila sai hutun karshen zango na watanni shidda.
Yunwa yake ji, ko abincin rana baici ba, yasan da gangan Bilal yaki shigowa dakin. Saboda sunyi fada da rana, shine dalilin da yasa ma Rayyan ko yunwa baiji ba, ran shine ya baci. Bilal yafi kowa sanin yanda yake da saurin hawa haka yake da saurin sauka, amman sai suyi fada wani lokacin shi ya gama fushin Bilal yana mishi fisge-fisge. Daya shigo zai zubo musu abinci su dukan su, da Ayya na aiko musu da shi, Bilal ya koyi kinibibin zuwa ya zubo. Sai Ayya ta daina turowa a fada musu ta ma gama abinci ko da suna jin yunwa in bata bayar an kawo ba.
Tunda idan aikowa tayi zai saka dan aiken ya karbo mishi. Abinda bai sani ba shine Ayya ta daina ne saboda shi, saboda wannan yunwar ce kawai dalilin da yake saka shi shiga bangaren ta wani lokaci harta gan shi, tana iya aikawa a kira shi a dawo ace mata an kwankwasa dakin shiru, idan Bilal yana nan kuma yace a shiga, an shiga an same shi yana bacci. Idan ya tashi kuma ko an fada mishi ba zuwa yake ba wasu lokuttan, sai ta taka har dakin da kanta ta mishi tas, shima sai dai yaita kallon ta ko ya ce,
“Ni na manta ne Ayya.”
Shisa take kyale su, wanda duk yunwa ta dama yasan inda zaije ya dibi abinci. Tashi yayi yana saka takalman shi da suke bakin kofa ta cikin dakin yana ficewa. Ya karya kwana kenan da nufin shiga bangaren Ayya ya hango Layla. Sai da zuciyar shi ta doka.
“Subhanallah…”
Ya furta kasan makoshin shi, tana karasowa ta zabi ta sauke idanuwanta cikin nashi. Duk fadin wajen sai a cikin nashi idanuwan ne zata nemawa nata masauki.
“Mayya…”
Ya fadi yana kallon yanda ta kara ware mishi idanuwan.
“Me yasa ba zanzo waje ba sai kinsan yanda kikayi kika biyoni?”
Kallon shi takeyi, duk ranar bata saka shi a idanuwanta ba, asalima tun jiya da rana rabonta da shi. Har rigar shi daya bata guga ta shiga taje ta kai mishi baya nan. Islamiyya da zata fitane da kuma kashedin da yayi mata na da yamma zai saka rigar yasa ta bude dakin ta ajiye mishi rigar. Da ta bari ya dawo ta gan shi tukunna. Tana da mukullin dakin su, da hannun shi wata rana ya kama hannunta ya saka a ciki.
“Idan ya bace saina karya ki Layla.”
To wani lokacin yakan sa ta share musu dakin, ko idan ya aiketa yace ta kai mishi daki. Duk da idan tayi shara sai ya maimaita, wata rana ma bayan ta gama zai kai mata duka ya karbi tsintsiyar.
“Kina mace baki iya share waje da kyau ba, fita kafin in kwada miki mari…”
Dalilin ya daketa kawai yakan nema tasani, shisa yake sakata shara, ko son ya wahalar da ita, tunda sai ya maimaita, da wanki ma idan ya bata tana kawowa ya jujjuya zai nade rigar ko wandon ya lafta mata
“Haka ake wanke kaya? Banda maita zuwa duk inda nake me kika iya a rayuwar ki?”
Yakan sata ta dibo ruwa a bokiti ya kara tsoma kayan ya wanke, ya bata ta shanya, wata rana ma tana tsaye tana kukan dukan da yai mata. Yanzun ne ma zata wanke mishi kaya wata ran baya ko duba hannuwan, wuyan rigar da wajen aljihun. Yake karba ya ajiye. Ta dai rasa dalilin da duk wahalar da take sha a hannun Rayyan haka kawai wani lokacin idan ta dauki wasu awanni bata ganshi ba sai taji tana son ganin shi. Da ta ganshin kuma zai fita daga ranta, saboda sai ya fada mata maganar da zataji tayi dana sanin son ganin nashi.
Har lekowa tayi dazun, bata gan shi ba ta koma, sau biyun da aka leko akayi mata magana a daki sai da taji gabanta ya fadi, tana mikewa da sauri zaton ta shine ya aiko a kirata, sai taji wani abu kamar dissapointment a lokutta biyun da kiran ya kasance ba daga shi bane ba. Yanzun ma shanya uniform dinta da ta wanke ta fito yi a igiyar dake bayan bangaren nasu, tana sane ta zagayo ta nan, da fatan ko zata ganshi a ranta, saboda tun dazun take tunanin ko bashi da lafiya, ko wani ya bata mishi rai shisa yayi shiru da yawa haka.
Tana hango shi wani murmushi ya kwace mata, murmushin da tayi kokarin boyewa daga kan fuskarta, murmushin daya dishe gabaki daya bayan kalmar shi ta,
“Mayya…”
Da ya jefeta da ita. Badan bai saba fada ba, itace ta kasa sabawa har yanzun, sosai kalmar take mata zafi, musamman idan daga bakin shi ta fito, tana jin maganar da take son mayar mishi na mata kaikayi akan harshe. Amman sai ta zabi yau da taqi biye mishi. Ta juya kenan yace
“Layla…”
Kowa idan zai kira sunanta sai taji kamar Laila yake fadi da harafin “i” maimakon harafin “y” da take amfani da shi. Rayyan ne kawai yake kiran sunan ta yanda take jin tana furta shi a bakinta. Hatta Mami bata kiran sunanta yanda take so, yana ba harafin “y” din da yake ciki hakkinsa, tun tana mita tana gyarama sauran yan gida da mutane yanda take so a fadi sunanta harta gaji ta kyale su.
“Sam idan kana tare da yan gargajiya ba zasu barka yin gayu yanda ya kamata ba.”
Shine abinda take fadama kanta a ko da yaushe. Ko maganar kananun kaya Mami tayi mata sai wannan tunanin yazo ranta. Ita Mami yar gargajiya ce, tunaninta yaki tafiya da zamani, taki gane cewa yanda sukayi tasu rayuwar daban da yanda ta yanzun take. Zabinta ne taci gaba da gudanar da rayuwa kamar zamanin da, amman ita kam tana jin ya kamata a kyaleta ta tafi a zamanance. Ko kallone ba zaka rabata da fina-finan amurka ba. Saboda yanayin ‘yan cinsu yayi mata. Yanda suke gudanar da rayuwar su tayi mata.
Shisa take da wani irin buri nayin zurfi a karatu, zatayi wayewar da babu wanda zai kuskura ya alakantata da maita, zata zama tana zagaye da wayayyun mutane da idanuwanta ba zasu saka su fadin komai ba sai yanda suke jin daman ace suma sun sami idanuwa irin nata suma. Wayayyu da zasu fuskanci cewa maita bata da wani yare, asalima a musulunci bata da tushe. Ta tambayi duk wani Malami da yake a islamiyyar su ana tabbatar mata da maita bata da tushe a addini, kambun bakane kawai musulunci yai magana a kai.
Ta rasa dalilin da yasa ake hada yaren nufawa na mahaifiyarta ana fadin duk yawancin su mayu ne. Mami kan jaddada mata da cewa mahaifiyar ta ba mayya bace duk idan ta shiga da kuka wani lokacin kan Rayyan ya kirata da mayya. Yanzun kam yanda ya kira sunanta yasa taji zuciyarta ta wani kumbura ta cika kirjinta taf, har murmushi tayi, gabaki daya ya wanke bacin ran da ya sakata yan dakika da suka wuce. Bata juyo bane sai ma tafiya da ta fara yi, hannun taji ya riko yana juyo da ita da karfin da yasa ta fadin
“Hamma hannu na.”
Gyara rikon da yayi ma hannun nata yayi yana murdawa sai da taji idanuwanta sun tara hawaye.
“Dan Allah kayi hakuri.”
Ta furta cikin rawar murya, idanuwanta kan rage bashi tsoro idan suka cika da ruwan hawaye haka, sai yaga sun kara sake mishi launi, sakin hannunta yayi, yana kallon yanda ta yarfe shi tana murzawa. Bude baki yayi zai magana, Maimuna da ta leqo ta gansu a tsaye tana saka shi mayar da bakin shi ya rufe.
“Ina wuni…”
Layla ta furta tana kokarin mayar da hawayen da suke cike da idanuwanta bayan ta, wata irin harara Maimuna ta zabga mata, kamar surutai taji, kuma sai muryar tayi mata kamar ta Rayyan, shisa ta leqo, sanin in dai surutun shi ya yawaita to da Bilal ne. Zaka iya kirga maganar shi, itama a fuska da yanayi zakaji yanda yake yinta kan dole. Yana iya bata maka rai kayi shiru ka kyale shi, sai da gabanta ya fadi da ta gan shi tsaye da Layla, sai taga kamar data fito yana rike da hannun Layla din, daga ranar farko da ta dora idanuwanta kan Layla bata kaunarta ko kadan, kuma ta tabbatar da Layla ta san haka.
Ko tare suka shigo da su Haris sai ta koreta, itama Layla din a nata bangaren hakane, Ayya na daga cikin jerin mutanen da bata kaunar gani, da hankalinta ita ce ta farko da ta kirata da mayya. Gashi ko a hanya suka hadu cikin gidan sai ta bita da harara, tana gaishe da itane saboda Abbu, dan a yanda taki jinin Ayya ko Mami bata isa tasa ta gaisheta ba, darajar Abbu take ci, dan tana jin shi har ranta, batayi wayan sanin iyayenta ba, gara mahaifinta zata iya tuna fuskar shi, sai kuma tsillin hotunan da Mami ta samo mata nashi bayan ya rasu sanadin gajeruwar rashin lafiya.
Na rana daya Abbu da Mami basu taba bari taji maraici ba, komai da take so Abbu yana mata, a fuskar shi ma bai taba nuna cewa ita din ba daga jikin shi ta fito ba. Haka dakin Maimuna banda ita da Rayyan duka suna zaune lafiya da sauran yaran, babu mai nuna mata tsana ko wariya. Gara ma Intisar wasu lokuttan takan mata magana taqi amsata. Shisa bata damu dan bata amsa gaisuwar ba yanzun, juyawa tayi zata tafi abinta, muryar Rayyan ta katse ta da fadin
“Na ce na gama magana da ke?”
Tsaye tayi cak, Ayya da take kallon su da mamaki bayyane a fuskarta ce tayi magana
“Rayyan…”
Ta kira cike da mamaki, idanuwan shi ya dauke daga kan Layla yana mayarwa kan Ayya, jin tayi shiru yasa shi cewa,
“Ayya”
Cike da mamaki har lokacin ta ce,
“Me zatayi maka?”
Dan ita batasan lokacin daya fara magana da Layla haka ba, zata tuna lokacin kuruciya da, har saida ta fara jin wani iri kan yanda Rayyan din ya addabi yar mutane, haduwa goma zasuyi sai ya kwada mata mari, akwai tabon da har yanzun yana gefen goshinta inda Rayyan din ya hankadeta ta fadi, ranar ita kanta Ayya hankalinta ya tashi, dan bayan Maryama ta dauke Layla sai da ta daki Rayyan din. Hakan ba yana nufin taji kaunar Layla ko kadan a ranta bane, yanzun da suka fara tasawa, inba Abbu ya aiko Layla ba, yarinyar bata fara shigo mata daki.
Ta san dai Bilal ne da babu yanda zatayi da shi akan nacin Maryama da yakeyi, bata da matsala da yaran Maryama din, Haris ne daman, kuma shekarun nan sun sa yaran ya shiga ranta, da wahalar gaske ma kayi zaman awa daya da Haris bai shiga ranka ba. Wani lokaci anan falon ta yake cin abinci. Sauran yaran ne in dai tasan abu daga bangaren Maryama ya fito bata bari suci, Bilal ne kawai yake shigo mata da shi har daki kuma ya zauna yaci. Tama gaji da magana tunda dariya yakan yi yace
“Ayya…”
Da yanayin nan nashi da yakan yi duk idan tayi mishi maganar za’a barbada mishi wani abu a abincin. Kamar bai yarda yana iya faruwa ba. To tasan yana magana da Layla, ko tace Laylar ta nace mishi, kwanakin baya har zancen tayi mishi.
“Bilal kaima ka fara koyon taurin kai, idan nayi magana ma ba jina zakayi ba. Banason yarinyar can tana naniqe maka, kafin ta lashe maka kurwa… Ko dan Maryama ta fara lashewa, ragowa ce Layla zata samu, kaga saika hada kayan ka gabaki daya ka koma can, in rasaka hankalin su ya kwanta ita da uwar rikon ta”
Dariya Bilal din yayi kamar a duk ranar babu wanda ya fadi wani abu da ya saka shi nishadi irin maganganunta.
“Dan ubanka sai kaje kayi ai, tunda kaga ka fini tsayi, ka rainani ai.”
Yana dariyar ya ce,
“Yi hakuri, haba Ayyata, ni na isa.”
Harar shi tayi tana wucewa abinta, haka ya bita yana mata hirar shi har saida ta huce. To batajin tana da matsala da Bilal, kowa ma kulawa yakeyi shi, kusan halin shi na mata shige da Haris, bambanci shine zakagani a fuskar Haris idan ka mishi abinda baiso ba, Bilal kam ko kayi tunanin ka bata mishi rai sai dai yayi dariya kawai. Amman Rayyan, zuciyarta rawa takeyi mata, saboda Rayyan daban ne, su Rukayya ma baya magana dasu mai nisan da taji yanayi da Layla din. Yanda ya tsare yarinyar da idanuwa yake yanzun yasa ba zuciyarta ba har kafafuwanta ma rawa taji sunayi.
Tana can tana tsoron Layla karta lashe kurwar Bilal, ashe lallabowa tayi wajen Rayyan, shiru yayi yana kallonta.
“Tambayar ka nake kana jina.”
Yanda yakan yi duk idan bayason yin magana an saka shi yayi dole shi yayi da fuskar shi yanzun ma.
“Ina magana da ita ne Ayya…”
Ya amsa, yana saka kirjinta wani irin lugude, ko ita Rayyan baya tsayawa yayi wata magana da ita. Bilal ma ta kanga yana bin Rayyan din idan yana son magana da shi. Asali yaune rana ta farko tun tasowar shi da taji yace yana magana da wani har ya tsayar dashi dan basu gama ba
“Rayyan…”
Ayya ta kira wannan karin da bayanannen tsoro a muryarta.
“Idan nagama zan shigo.”
Ya fadi yana dauke idanuwan shi daga kan Ayya. Hannun Layla ya kama yana fisgarta cikin yanayin da yasata binshi dole, suna barin Ayya tsaye ta saki baki cike da mamakin abinda ya faru a gaban idanuwanta. Cike da ta’ajjabin da gaske a gabanta Rayyan ya damki hannun Layla batare da tunanin abinda yayi ba dai-dai bane a tafarkin addini idan bai guji bacin ranta ba, idan ma ji yake dan in aka bibiya ta wani bangaren ya hada jini da Layla, kuma sun taso gida, ai hakan baya nufin ita din muharramar shi ce.
Bayan wannan ma, yaushe Rayyan ya fara magana da Layla, yaushe ya sakata cikin jerin mutanen da yake kulawa, harma kusancin su ya kai na ya damqi hannunta ya jata subar waje kamar akwai zancen sirrin da sukeyi da bayaso ita taji. Rayyan fa, Rayyan dinta da take daukar kafafuwanta, ta karya matsayinta na mahaifiyar shi mai cikakke iko da hakki a kan shi ya taso yazo har inda take ya gaisheta, taje dakin su dan kawai ta saka shi a idanuwanta. Shine yau take ganin kusancin da tayi shekaru tana neman ta samu a tare dashi yana nunawa akan Layla, akan mayyar yarinyar da taki jinin ta wayi gari ko a tunaninta tajita, balle kuma ta saka ta a cikin idanuwan ta.
“Bayana kike son gani Maryama… Sakani raba Ahmadi dake bai isa ba? Kassarani kike neman yi shisa kika kawo wannan mayyar…”
Ayya take fadi muryata na rawa, cikin tashin hankali kamar wadda ta samu tabin kwakwalwa. Gabaki daya hankalinta idan yayi dubu kowanne a tashe yake.
“Tafdin… Na rantse da Allah ba’a isa ba…ina tunanin wuta a makera ba zanji tashin ta a bayan gari ba.”
Duk tsoronta akan Rayyan, duk tunaninta akan halayen shi ta alakantasu ne da abinda tayi kuskure ya sha, sanadin da kawancen su da Khadi bai koma kamar da ba, saboda tayi da ita su koma wajen Malam taqi, sai tama dinke mata, sam ta daina labarta matsalolinta da ita. Gwaggo ce a lokacin kafin rasuwarta, idan ta matsa sai tace mata tana karbo taimako a wajen Malamin Khadi. To dan Rayyan ne ta dinga amso karya tambaya, da yana yaro in ta danne shi tana samu ta dura mishi, daga baya ba zai sha ba, banda abinci sai ruwan leda, ko ya tarya a fanfo, ko zobo ta hada Rayyan baya sha sam.
Bata san ba abinda yasha bane yake dawainiya da shi sai yanzun, bata dauka Maryama na bibiyarta da yaranta ba har yanzun sai yau
“Minna, Neja da Bidda ma ubansu yayi kadan wallahi, balle kuma wata yar banufiya da uwar rikon ta…”
Cewar Ayya, bacin rai da tunanin barkatai na maye gurbin tsoronta, tana murna yaronta ya sami gurbin karatu a jami’ar da ake ji da ita a fadin Najeriya, kuma Abbu sai alfahari yake da fannin da zai karanta shine ake neman kassara shi.
“Wallahi da sake…” Ayya ta furta tana samu taja kafafuwanta da sukai mata mugun nauyi tana komawa daki, kanta harya fara sarawa da tashin hankalin da take tunanin ya kunno mata kai.