Skip to content

Martabarmu | Babi Na Ashirin Da Hudu

5
(3)

Karanta Babi Na Ashirin Da Uku.

Can nesa Layla take jin duk wata magana da sukeyi, ba zata ce ga abinda ya dinga faruwa ba, daga asibiti, zuwan Abbu, dawowar su gida, banda sautin kukan Mami babu abinda take ji, dan yanzun haka da suke a tsakar gidan ta samu wajene ta zauna a kasa, gefen Mami da ta kasa shiga daki ta durkushe a wajen. Kuka takeyi kamar ranta zai fita, dan har yanzun ta rasa ta inda zata fara yiwa Abbu bayani, sanda yazo asibitin ta farfado, dan haka suka dawo gida, ita da shi a mota daya, sai Jabir daya kama hannun Layla yana sakata a motar da suka zo suka taho.

“Wai dan Allah wani a cikin ku ya bude baki yayi mun magana, tun dazun na tambaye ku abinda ya faru.”

Abbu yake maganar da wani yanayi a muryar shi, hankalin shi a tashe ya same su asibiti, sai dai lokacin harma sun fito, tun daga can kuma Mami take kuka, sau daya ya tambayeta abinda ya faru, da bata amsa ba sai yayi shiru saboda bayason su fada mishi abinda zai saka shi kasa yin tukin su iso gida.

“Layla me ya faru? Wani abin suka ce ya same ki?”

Ya karasa tambayar yana kallon Layla da ta dago idanuwanta tana saka su cikin na shi, bata san me zata ce mishi ba, saboda har yanzun wani irin shiru take ji cikin kanta. Kafin jikinta gabaki daya ya dauki bari, zuciyarta na soma dokawa, girman abinda yake faruwa da ita yana danneta, so take ta bude bakinta, ba ta dan ta bawa Abbu amsa ba, sai dan ta kira sunan Allah, ta furta Kalmar.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un..”

Ko zata samu sauki, ko Allah zai kawo mata dauki abinda yake faruwa ya zama mafarki, amman ta kasa, Abbu kallon shi ya mayar kan Jabir da karo na farko a duniya yake son kasancewa ko ma ina ne da cikin gidan, banda fuskantar abin nan da yake faruwa da su.

“Abbu karka tambayeni, dan Allah karka sa in fara fada maka.”

Ya karasa maganar muryar shi na karyewa, zuciyar shi zafi takeyi, so yake yabar wajen, amman ya kasa, ba kukan Mami bane baya ci mishi rai, tunanin halin da Abbu zai shiga ne yake hautsina mishi lissafi.

“Ciki gare ta, cikine a jikin Layla… Ahmadi ciki.”

Mami ta karasa tana jin kamar ana zare mata rai, ya kusan mintina biyu maganganunta na yawata mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su, so yake ya ga shin shi kadai ne yake ganin wani duhu-duhu ko kuma garin ne gabaki daya ranar da ake kwallawa ta lumshe, amman da ya bude wannan karin ma duhun ya sake gani, kamar a cikin duhun wani abu na jujjuya mishi. Ba dan Bilal daya fito daga bangaren Ayya da kofi a hannun shi ba, ya hango su ya fara karasowa in da yake ganin kamar Abbu na shirin faduwa, yanayin da ya saka shi yin jifa da kofin zobon da yake rike da shi ya karasa ya tallafe shi yana taimaka mishi ya tsaya kan kafafuwan shi, tabbas da zancen ya bambanta.

“Subhanallah, Abbu…”

Bilal ya kira zuciyar shi na wani tsalle cike da tashin hankali, Abbu kuwa kafadar Bilal ya dafa yana samu ya tsugunna saboda kafafuwan shi da suke rawa, kokawa yake da numfashin shi saboda tashin hankali, baiga ta yanda Mami zata ce mishi Layla na dauke da ciki ba. Kirjin shi na zafi yake kallon Mami.

“Maryama ki fadamun abinda zuciyata zata iya dauka… Dan girman Allah, rokon ki nakeyi.”

Hannu ta saka tana share hawayen da suke sake zubo mata, ta bude bakinta yafi sau biyar tana rasa kalaman fadi, haka kawai Bilal ya tsinci kan shi da shiga tashin hankali, bai san me yake faruwa ba, amman zuciyar shi duk ta gama birkicewa, hannun shi yaji Abbu ya kamo.

“Bilal kaji me tace? Wai Layla ce take dauke da ciki, yata Bilal, yarinyata, amana ta.”

Runtsa idanuwan shi Bilal yayi, ya bude su a cikin na Layla da take kallon shi, duniyar na karasa hautsine musu a lokaci daya. Kai ta girgiza mishi a hankali tana neman hawayen da zasu sama mata sauki ko yayane. Amman ta rasa su, sunki fitowa. Tsaye Bilal yake a waje daya, amman duniyar duka juyawa takeyi da shi, kamar wanda aka dauka ana zagayen cikar shekara haka yake jin shi, so yake wani ya taba shi ko zai daina jujjuyawa haka, kamar an amsa rokon shi yaji hannuwan Ayya akan kafadar shi, hannun da yake da yakinin zai gane shi a cikin dubban hannaye.

Hannun daya kama nashi a lokacin daya rasa kowa, hannun daya taimaka mishi tun kafin ya budi bakin rokon hakan. Ayyar shi, juyawa yayi yana ganin damuwar da take kan fuskarta.

“Ayya”

Ya kira da wani yanayi da ya sata fadin,

“Mene ne? Me akayi maka? Me aka ce kayi?”

Saboda ta san yaranta, tasan Bilal ba zai hargitse haka ba idan ba wani laifin akace yayi ba, ganin yana kallonta kamar duniyar shi na shirin zuwa karshe ya sa Ayya kallon su Abbu sa suma a hargitsen suke, ba zatace ga abinda ya fito da ita ba, zuciyarta ce taki samun natsuwa sam. Ashe yaranta aka saka a gaba haka shisa hankalinta yaki kwanciya.

“Me yayi muku?”

Ta watsa tambayar, tana saka Mami share hawaye kafin ta kalli Ayya.

“Ba shi bane ba, Rayyan ne.”

Ta amsa muryarta na fitowa a dakushe, yanayin da yasa Abbu fadin.

“Maryama!”

Juyawa tayi ta kalle shi.

“Karka ce mun baka san in har cikine a jikin Layla to na Rayyan bane ba…”

Cike da rashin fahimtar in da zancen su ya dosa Ayya take binsu da kallo, saboda maganar ce ta daketa a haggunce.

“Ciki? Laylar ce da ciki? Ciki naji kince Maryama. Kin san me kike fada kuwa?”

Saboda duk yanda ta tsane su, duk yanda bata son ganin su, ciki na daya daga cikin abu na karshe da zata so kowacce yarinyar da bata kasance karkashin inuwar aure ba da shi, ko da bata santa ba, balle Layla da suke cikin gida daya. Yarinyar da ta girma a gaban idanuwanta, bugun zuciyarta da yake kara hauhawa na tabbatar mata da tashin hankalin nan bana Mami bane ita kadai, kafin wani bangare na kwakwalwar ta ya juya kalaman Mami din.

“Mami…”

Wannan karin Layla ce ta kirata, wani irin kuka na kwace mata, kukan da take ta nema tun shigowar su gidan.

“Uban waye? Ki fadamun cikin waye a jikin ki idan bana Rayyan ba Layla? Ki fad…”

Bata karasa zancen ba Ayya ta katse ta.

“Rayyan ya fita daga bakin ki Maryama, nasan kina cikin tashin hankali, wannan karin zan miki uzuri. Amman karki sake alakanta cikin jikin ta da yarona. Wallahi zamuyi tashin hankalin da bamu taba yin irin shi ba.”

Wata dariya Mami tayi duk kuwa da sabon kukan da yake gab da kwace mata.

“Akwai wani tashin hankali da kike tunanin zai girgiza ni bayan wannan da nake ciki? Babu, yau dai kece zaki girgiza saboda ina dai-dai dake.”

Kallon su Abbu yakeyi, tun kafin Mami ta shigo gidan yake fuskantar tashin hankali kan zuwanta a wajen Maryama, tun da tazo duk tsayin shekarun nan da addu’a yake shigowa cikin gidan shi kar yaji wani tashin hankalin.

“Idan har ba zaku iya ajiye haukan nan ku san muna cikin matsalar da ta fishi girma ba ku fitar mun daga gida, dan Allah ku duka ku fitar mun daga gida inji da abu daya.”

Daga zuciyar shi yayi maganar, ba zasu kara daga mishi hankali fiye da wanda yake ciki ba, saboda a duniya baisan akwai irin wannan tashin hankalin ba, duk yanda yake dauka labaran kalar shi na taba shi, bai kai yanzun ba sam, ta ina zai fara? Yar shi da rayuwarta gabaki daya ta sauya? Amanar daya kasa rikewa? Ko kuma Rayyan da Mami take alakantawa da wannan barnar? Dan mutane basu dame shi ba, abinda zasuce bashi bane a gaban shi a yanzun. Yanda zai fara daukar wannan matsalar balle ya nemi mafitarta.

Wasu hawaye masu zafi Mami taji sun zubo mata. Ayya ma ji tayi kafafuwanta sun kasa daukarta, har ranta taji zafin abinda Mami ta fadi akan Rayyan, badan tasan halayen shi ba, amman zuciyarta ba zata taba yarda shi yayi wannan barnar ba. Kallon Layla tayi da ta saka fuskarta cikin hannuwanta tana wani irin kuka. Abinda duka yara suka kasa ganewa kenan, abinda in da yanda zatayi zata bi yara wanda suka kai Layla, wanda basu kaita ba, wanda suka girmeta daya bayan daya ta hasko musu wannan ranar, ta nuna musu tashin hankalin da zai biyo bayan kuskure kwara daya.

Abinda duk suke dauka wayewa aikin banza ce in har ta kasance ba’a karkashin inuwar aure ba. Jin dadin wani lokaci zai iya zama barazana da sauran zaman lafiyar da ya rage musu a duniya. Kuskure daya zai jefa wasu wasi a zukatan mutane kan Martabarsu, da ta duk wani ahali nasu, kuskuren su zasu aikata, amman zunuban zasu raba da duk wani daya damu dasu ne. Sai da tsikar jikin Ayya ta mike gabaki daya da ta hasaso faruwar abin nan akan Rukayya, wani irin tsoro marar misaltuwa na dirar mata. Kafin ta tuna ta kula da Layla, sai taji kamar ba huruminta bane bincike saboda Layla ce, saboda ta tsane ta, ta kuma tsani Mami, ga shi yanzun abin ya samu wajen zama a kirjinta yana sakata jin daukar wani bangare a kason tashin hankalin da suke ciki.

“Ta fadi komai Ahmadi, komai banda dorawa Rayyan laifin nan.”

Ayya tayi maganar cike da roko, kirjinta kamar ana hura wuta. Saboda batasan ya zatayi ba idan akace dan daya fito daga cikinta ne yayi wannan aikin.

“Baki san na gansu rungume da juna ba? Ya zaki ce mun bashi bane ba?”

Mami ta tambaya tana kallon Ayya da take mata wani irin kallo itama.

“Rayyan da Layla kika gani rungume da juna?”

Cewar Ayya, Mami na jinjina mata kai.

“Saboda baki da mafadi ko rashin hankali shine kika sake barin ta kusa da shi? Maryama sai kika barta a kusa dashi in har kin gansu da idanuwan ki kamar yanda kika fada… Baki da hankali ashe? Auren mijin mutane ne kawai abinda kika iya, baki iya kula da tilon yarinyar da kike da ita ba?”

Ayya take maganar yau tana jin da tana kusa da Mami din sai ta dauketa da mari, tana jin yanda komai ya koma gefe sai kalaman Mami din, tana jin yanda har zuciyarta ta shafe mata matsayin Rayyan, so take taji me abinda ya kwance akan Mami tabar Layla ta sake komawa Zaria in har da gaske ta ga Rayyan rungume da ita. Saboda daga ranar da ta ga maganar banza a wayar Rukayya tsakaninta da wani a makaranta, ko duniyar zata hade waje daya tabar makarantar kenan, saboda bata da iko da yaron balle ta hana mishi bibiyar mata yarinya, amman zatayi ikon da Allah ya saka a karkashinta ta nisanta yarinyarta da shi.

“Ya ma za ayi ace tana da ciki baki kula ba? Ki kwana daki daya da ita ki tashi daki daya da ita kice mun baki kula wani abu ya canza a tare da ita ba? Sakarar ina ce ke?”

Daga Mami har Abbu sun kasa cewa komai, maganganunta ne suke shigar su, musamman Mami da take jin Ayya na zakulo kasawarta a matsayinta na uwa, yau matar da take dauka ta tsaneta, bata kaunar ta ganta ce take fada mata gaskiyar da bata da mai gaya mata ita, duk da gaskiyar tazo a kurarren lokaci.

“Kasanta gansu rungume da juna? Ahmadi ka sani?”

Ayya ta tambaya tana kallon Abbu daya kara sadda kan shi kasa, baya son hada ido da ita, so yake dai labban shi su motsa ya roketa da tayi shiru, karta saka zakulo mishi nashi laifin, amman lokaci ya kure musu gabaki daya.

“Ka sani kenan…”

Ayya ta fadi, shirun shi na tabbatar mata da ya sani, mikewa tayi tana wani irin maida numfashi, yau da yaranta ne sai ta hadasu ta zane su gabaki daya.

“Sai kaima kabarta ta koma ko? Saboda ba yarku bace ba.”

Su duka suka kalleta lokaci daya.

“Maimuna…”

Cewar Abbu, kai ta girgiza mishi.

“Baka son ji nasani, amman ka duba zuciyarka Ahmadi, idan Rukayya ce zaka bari ta koma? Me yasa kabar Layla? Ni me yasa baku fadamun kun gan su tare da juna ba?”

Saboda tana da tabbacin zatayi tashin hankalin da ba zasu bar Layla ta koma ba, ko dan ta nisanta yarinyar da Rayyan. Amman sai suka barta, saboda suna ganin ita din marainiya ce, kamar komawar ne gatan da zasuyi mata, barinta da zabinta shine cikar soyayyar su. Juyawa Ayya tayi da nufin barin wajen ta hango Rayyan da jaka a kafadar shi, har ya kama hannun kofar dakin su, hayaniyar da yake ji ta rinjaye shi zuwa cikin gidan saboda muryar Ayya yake jiyowa. Tana ganin shi kuwa ta karasa ta kamo hannun shi.

“Zo ka fada musu Rayyan, suji da kunnuwan su.”

Binta yakeyi, amman idanuwan shi na kafe kan hannunta da yake rike da nashi, so yake yaji yanayin nan da yake ji duk idan tayi kusa da shi haka, amman babu, bayajin komai sai Ayya, sai yanda kusanci da ita bai saka zuciyar shi ciwo ba. Kamar mai yawo a duniyar mafarki haka yake jin shi, lokacin daya dauke idanuwan shi daga nata yana mayarwa kan Abbu da yake zaune.

“Abbu…”

Rayyan ya kira a cikin sauki, a karo na farko a tsayin rayuwar shi. Wani murmushi mai sauti ya kwace mishi, ya sake kallon Abbu yana jiran sanannen yanayin nan ya taso mishi, yaji iskar wajen gabaki daya tayi mishi kadan, amman babu, sam bayajin kamar zai mutu idan ya kalli Abbu, ko sun kasance a waje daya kamar haka, shisa bai ga tashin hankalin da suke ba, yau baya ma ganin komai banda iyayen shi.

Waje daya Bappa ya samar musu inda suke bautar kasar.

“Akwai gidan Uncle dina, Autan su da yake karatune a ciki da abokin shi, daki ukune amman, akwai extra daki da zamu iya rabawa da kai…”

Cikin ido ya kalli Bappa ba zai manta ba.

“Ban tuna na fada maka ina son zama waje daya da kai ba.”

Ya amsa yana saka dariya kwacewa Bappa.

“Allah ya bada sa’ar neman gidan haya a garin Kaduna, zama dani ne saukin ka, kuma ina da mota.”

Wani irin kallo Rayyan yake mishi, banda Bilal bai taba kwana daki daya da wani ba, sai dai Ayya lokacin da yana yaro. Amman da hankalin shi ko na rana daya, sai ranar daya kwana a Bauchi da Bappa din, yanzun kuma ba zai zamana kwana daya ba.

“Nawa ne zamu dinga biya?”

Yayi tambayar saboda har ran shi baya son takurawa Bappa din, bashi kadai ba har sauran mutane.

“Zan iya kiran Uncle dina in tambaye shi, amman ba ma shiri.”

Numfashi Rayyan ya sauke, ya kula Bappa na da son maida magana da yawa wasa, kamar Bilal haka yake wani lokacin.

“Da gaske bana son imposing…”

Kai Bappa ya girgiza mishi.

“Karka damu, babu wata matsala, ka yarda dani shine saukin mu, idan ina da wani wajen ba zan zauna a gidan mutimin nan ba.”

Cewar Bappa, kallon da Rayyan yake mishi yana saka shi karawa da

“Karka ce mun a cikin Uncles dinka babu wanda baka so.”

Kai Rayyan ya girgiza mishi, bawai yasan sauran bane ba, zai iya kirga lokuttan da ya taba ganin su har suka gaisa. Cikin su Yaya Ayuba ne kawai ya sani sosai sosai. Kuma karyane kace akwai wani abu da zaka ki so a halayen shi. Mutum ne mai saukin kai, kusan zai iya cewa duka yan gidan su Abbu ne da sanyin hali, har matan daya gani kuwa.

“No way.”

Bappa yai maganar cikin rashin yarda yana saka murmushi kusan kwacewa Rayyan din, bayason mutane, amman Bappa na da wani abu a tattare da shi da yaja shi hira haka har maganar ta tsawaita.

“Ba kamar kai ba, ni ina son kowa.”

Yayi maganar cikin sigar wasa, sosai Rayyan yayi dariya.

“Karka manta karantar mutane ne fanni na.”

Murmushi Rayyan yayi yana fadin,

“Bana son mutane, ko kadan.”

Kusan zaice ranar ne ya san menene aboki, menene magana da wani da bai hada jini da shi ba. Duk da cikin satin farko na zama da Bappa ya saka shi jin kamar zai dinga tsigar gashin kan shi saboda yanda Bappa yake tura shi bango, kuma dariya yakan yi.

“Bafa zan zauna bana magana bakina yayi tsami ba.”

Tunda sassafe zai fara bashi labari, wani lokaci saiya nemi wani abu ya jefa mishi, saboda sai da safen yake samu yadan runtsa bayan ya gama shiryawa, wajen karfe tara suke fita, amman surutun Bappa ba zai barshi ba.

“Bacci kake yi?”

Zai tambaya, ko yayi shiru ya kyale shi zai fara mishi surutu yana bashi labarai.

“Wai akan me zaka dinga bani labarin da ban tambayeka bane ba Bappa?”

Ya tambaye shi wani lokaci, sai yaci gaba da kurbar shayin shi yana bashi labarin kamar ma baiyi magana ba, juyawa Rayyan yayi yana daukar dayan Pillow din ya rufo daga kunnen shi zuwa fuskar shi, kafin yayi amfani da shi yana jifan Bappa daya addabe shi, ko Layla bata takura mishi yanda Bappa yakeyi a yan kwanakin daya san shi. Sosai yake shigar mishi hanci, musamman ma akan magungunan da baisan me yasa yake sha a gaban shi ba, tunda ko Bilal baisan yana shan su ba.

Ranar da ya saka shi a gaba yana fada mishi illar kwayoyin da bukatar sake ganin likita tunda ba damar ya ga kan shi yana abusing magunguna haka kamar bai sani ba ya tura Rayyan din bango, sosai yake jin ya gaji da yanke mishi hukunci da Bappa yake dan yana shan kalar magungunan da yake sha, duk da ba kullum ba, kuma guda daya yakan sha.

“Me yasa kake tunanin ka sanni ne Bappa? Dan kana shan Anti-depressant baya nufin ka fahimci matsalata.”

Cikin ido Bappa yake kallon shi.

“Ka fahimtar da ni.”

Numfashi Rayyan ya sauke, watakila idan ya fito da abin a fili yayi mishi saukin dauka, watakila idan ya fadama Bappa ya daina damun shi, ba zaice ga dalili daya da ya saka shi bude bakin shi da yake rufe da matsalolin shi duk shekarun nan ba, dan ko likitocin da ya dinga gani bai fada musu ba, har wanda sukayi tunanin bayan depression yana tare da post traumatic disorder wato PTSD, da sauran tarkacen ciwuka da suka shafi mental health.

“Bana son ganin Babana, ko kadan bana son ganin shi, bana son magana da shi, bana son duk wani abu da shi yake so. Koma menene idan ya nuna yana so zuciyata kamar wani na turata ta nisanta da abin… Idan ya matso kusa dani kamar zan mutu nake ji. Bappa babana fa, Abbu, bana son komai yana hadamu kamar ba daga jikin shi na fito ba…”

Rayyan ya karasa yana numfasawa da nauyin da abin yake mishi a zuciya

“Kowa na dariya da shi, suna magana, suna hira. Kowa nayi da baban shi, ni ban samu wannan ba. Ban kuma san dalilin da yasa na kasa samu ba, karka tambayeni. Ina tuna lokuttan da nake zama tare da shi, amman lokuttane masu nisa, bansan me ya faru ba lokaci daya…”

Ganin Bappa yayi shiru yana sauraren shi da dukkan hankalin shi yasa Rayyan cigaba da magana, a wannan bigiren baima jin zai iya yin shiru ko da yaso, duk da abu da yawa da yake damun shi din baisan yanda zai misalta ba. Kirjin shi ya dafa

“Kaman akwai duhu a zuciyata da kaina haka nake ji, duniyar duka bata mun dadin zama, ko karatun Qur’ani da nake samun sauki bana iyayi wata rana, jikina namun nauyi in tashi, ban san ya zan fada ka gane ba, amman bana jin dadi, na zabi Psychology dan in fahimci matsalata, amman babu abinda nagane, nawa ba depression bane ba, ya wuce haka.”

Ya karasa da wata irin karamar murya, kafin shiru ya ziyarci dakin, siririn numfashi Rayyan ya sauke, akwai tarin maganganu da yake sonyi amman ya gaji, ba da surutun ba, da yanda zai hada abinda yake cikin kan shi ya zama kalamai. Gyara zama yayi da nufin ya koma ya kwanta, muryar Bappa ta daki kunnuwan shi

“Mu biyar mukai accident, Mamana, Yayyena guda biyu sai Kanwata, ni ka dai na fita…”

Kallon shi Rayyan ya yi.

“Ban san me yake damun ka ba, ba kuma ina kokarin nuna maka matsalata tafi taka bane ba, ina so ka fahimci komai zaiyi dai-dai, kowacce matsala tana da lokaci… Bana jin taka na da alaka da asibiti. Baba zai zo Kaduna nan da kwana biyu, sai muje mu fada mishi, kila zai iya taimaka maka.”

Kai Rayyan yake girgiza mishi tunda ya fara maganar, shima baisan ya akayi ya fada mishi ba, bayajin bakin shi zai sake budewa a karo na biyu ya fadama Baba kamar yanda Bappa ya kira shi. Kallon Bappa din yake da wani yanayi na daban.

“Allah ya jikan su.”

Ya furta a hankali, kan da Bappa ya jinjina yana amsawa da.

“Amin Ya Rabbi.”

Shi yasa Rayyan sanin yaji me yace, saboda a hankali yaji muryar shi ta fito. Hidimar su sukaci gaba dayi bayan nan kamar kowa baisan ciwon kowa ba. Har kwanaki biyu suka cika, Bappa baice mishi komai ba, bai sake daga mishi maganar zuwa ganin Baba ba, duk da yaji sunyi waya sun gaisa. Jikin shi na mishi wani iri, musamman da ranar tazo asabar, su kadaine a gidan, sauran yaran da suke nan sai da ya gansu duk basu shige sa’annin Layla ba. Gashi suna da hankali, basa wani hayaniya suna damun su, ko falo suka zauna suna kallo da wahala kaji hayaniyar su, kuma zasuyi kasa da maganar TV din.

Har yamma suna gida a zaune, Bappa ya dafa musu taliya, kamar Haris, ya iya dafa abubuwa da yawa. Kuma mai dadi yakeyi musu ba irin girkin Bilal ba. Dan haka babu inda suka fita, yanzun ma yana zaune yana kallon wani film a laptop din Bappa, Chinese ne ma, amman yana mishi dadi, yaga Bappa ya mike, gyara zama yayi yana cigaba da kallon shi, har saida ya dawo yana fadin.

“Ka fito ga Baba nan.”

Bai bashi damar amsawa ba ya sake ficewa, wani irin bugawa Rayyan yaji zuciyar shi nayi, tabbas zai saukema Bappa, saboda ba suyi haka da shi ba, sai ya tsinci kan shi da jin wani irin nauyi, saboda idan har Bappa na mishi kwarjini haka, baisan yanda baban shi zai kasance ba. Tunda yake bai taba sake kayan da suke jikin shi bai kara wanka ba, amman yau manyan kaya ya dauka ya saka, yana nemar hula ya dora a kan shi sannan ya fita. Aikam baiyi mamakin ganin kwarjinin da yake tattare da Sheikh Abdullah ba. A mutunce suka gaisa, Baba na dorawa da,

“Bappa yamun bayanin komai, In shaa Allah babu abinda yafi karfin addu’a. Anjima da daddare sai kuzo ku karbi sako, akwai addu’o’in da zan baka kuma, saika daure ka dingayi kullum da safe muga abinda Allah zaiyi nan da kwana bakwai.”

Kai Rayyan ya jinjina, sai da Baba yayi musu addu’a sannan ya mike, har bakin kofa suka raka shi, Rayyan ya dawo ya jira Bappa anan falon harya raka Baba waje ya dawo.

“Baka da hankali ashe? Me yasa zaka saka Baba yazo?”

Murmushi Bappa ya yi.

“Ba zan iya daukarka ba, balle in sakaka a mota in kaika, shisa. Kuma karka damu Baba bashi da wata matsala bai dauki hakan komai ba.”

Numfashi Rayyan ya sauke, shi ya dauki hakan wani abu, saboda Baba mutum ne Babba, ko bai girmi Abbu ba zasu zo sa’anni. Haka yayita jin wani iri har sanda suka je gidan da Baba ya sauka. Ruwan zam zam ne ya basu roba biyu, daya yace Rayyan din ya samu waje mai tsaf sai ya shafe duka jikin shi, kullum da dare har kwana bakwai, dayan kuma ya dinga zubawa a cikin kofi, ya saka garin habba, sai Ayat as shifa da zai karanta kullum. Sosai ya tsinci kan shi da yiwa Baba godiya, bai barsu sun tafi ba sai da suka ci abincin dare tare da shi, yanda yake ta musu hira na saka Rayyan jin wani iri.

Saboda shine karo na farko da ya zauna da wani babba suna cin abinci. Ko Yaya Ayuba basu taba yin wannan da shi ba, da suka koma gida ma ya kalli Bappa da nufin yi mishi godiyar da baisan ta inda zai fara ba katse shi yayi

“Karka cemun ka gode, get better, shine godiya da zakayi mun, nasan depression Rayyan, na san duhun da yake cikin shi. Kayi kokari dan Allah, sai muje asibiti daga baya kan kwayoyin nan, yanzun ka fito daga duhun da kake ciki.”

Kai ya jinjina, ranar kuwa yayi amfani da duka ruwan zam-zam din biyu kamar yanda Baba yace tunda a hanya suka tsaya suka siyi garin Habba din me kyau. Baiji komai ba saida ya kwanta, kamar ana zare mishi rai haka ya dinga ji, jikin shi ya dauki zafi sai kace yana cikin gidan biredi. Zuwa karfe sha daya na dare ya fara galabaita da tuqar amai da take taso mishi, aman daya dinga kwarawa kamar zai fitar da kayan cikin shi. Haka suka kwana, Bappa yaki yin bacci saboda yanata fama da Rayyan suje asibiti amman yaki. Da safe kasa fita masallaci yayi, sai a gida suka tsaya Bappa yaja musu sallah. Har wajen tara yana jin gabaki daya jikin shi ko karfin kirki babu.

Da Bappa ya taba shi ture mishi hannu ya yi.

“Rayyan kaji jikin ka kuwa? Tsaf zan soya kwai akan goshin ka, ka tashi muje asibiti.”

Banza yayi ya kyale shi, amman halin da yake ciki yasa Bappa ya kira Baba yana fada mishi.

“Alhamdulillah, abinda nake tunani ne ya tabbata, ka barshi, aman shine saukin shi. Yaci gaba da sha, har Allah ya taimaka ya fitar da abinda yayi karfi a jikin shi.”

Cike da tsoro Bappa yace,

“Sihiri ne ko Baba?”

Murmushi kawai Baba yayi ta dayan bangaren.

“Allah ya bashi lafiya. Allah ya kare mana imanin mu ya nisanta mu da dukkan abin ki.”

Numfashi Bappa ya sauke, yana amsawa da,

“Amin.”

Kafin yayiwa Baba sallamar. Kwanakin da suka biyo bayan ranar ba masu sauki bane ba, dan duk yanda Rayyan din yaki saida Bappa ya kira likita cikin gida aka daura mishi karin ruwa. Kamar ana zuko wani abu a cikin jijiyoyin da suke jikin shi suna hade da zuciyar shi haka yake ji. Bai taba ciwo irin wannan ba, cikin kwanaki bakwai kamar bashi ba, duk ya fita hayyacin shi, wajen aiki ma randa yaje ca sukayi ya koma ya kara hutawa na sati daya sannan. Yayi wata irin ramewa. Baba sai da ya kara aiko mishi da wasu robobin biyu, yace karya daina sha saiya sha sau biyu yaga baiyi amai a cikin kwanakin ba tukunna.

Ba abinda ya dinga bama Rayyan mamaki sai baccin da yake kusan kwana ya wuni yanayi, saiya alakanta hakan da rashin karfin da bashi da shi. Amman a cikin sati na biyu ranar ya tashi da safe yaji shi kamar yana lilo saman iska, kan shi wasai, sai kace an kwashe wani datti daya jima yana taruwa a cikin kan nashi haka yake ji. Da sukayi waya da Layla dariya yaga yanayi, zuciyar shi na dokawa da wani bakon yanayi da bai taba sani ba, kwana wajen hudu yana tashi a tsorace, saboda gani yake kamar yanayin ba mai zama bane ba.

Sam baiwa Bappa gaddama ba sukaje asibiti, wasu magungunan aka dora shi a kai. Yana sha kuma, yana samun bacci, ashe haka baccin dare yake tattare da Rahma, duk da ba duka daren bane tunda ya samu sauki, amman zaiyi bacci wajen sha biyu har safe, sai yake jin shi duk wani sakayau. Ga Bappa baya barin shi ya zauna shi kadai, kullum suna yawon zaga gari, har gidan ball yake jan shi suje kallo, duk da yakan dawo da ciwon kai. Yanzun yake sanin halayen shi akwai wanda basu da alaka da komai, sam bayason mutane, wannan halin shine. Baba bai daina aiko mishi da robobin zam zam ba, a cewar Baba har yanzun yana bukatar su.

Saboda hutun rashin lafiya da suka bashi shisa basu zo Kano ba, sai yau, Bappa ya sauke shi ya wuce, yanata sauri shisa bai karaso da shi ba, yace zaiyi zuwa na musamman idan ya tashi. Da wata irin kewar Layla da Bilal din ya sauka garin Kano, da ita kuma ya shigo gidan har yake tsaye inda yake yana juya kasancewa waje daya da Abbu batare da yaji kamar iskar wajen tayi mishi kadan ba. Yana kuma jin zuciyar shi sakat.

“Ka fada musu cikin jikin Layla ba naka bane ba.”

Muryar Ayya ta katse mishi tunanin da yakeyi tana dawo da hankalin shi kanta cike da son fahimtar inda zancen ta ya dosa…

Babi Na Ashirin Da Biyar

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×