Skip to content

Martabarmu | Babi Na Ashirin Da Shida

5
(4)

Karanta Babi Na Ashirin Da Biyar.

Ba idanuwan shi ba, har fuskar shi a kumbure take, yayi kuka har wani yaji-yaji idanuwan shi sukeyi. Duka sallolin shi yau a gida yayi su, abinda ya manta ranar karshe da yayi. Ko bashi da lafiya saiya fita masallaci, ruwa kam banda yanzun da Yaya Ayuba ya tsare shi bai shiga cikin shi ba. Duk yanda Ayya tayi fama da shi kuwa, kai kawai ya dinga girgiza mata, da yake tasan halin shi, ta kuma san bashida wani abokin shawara a wannan yanayin daya wuce Yaya Ayuba shisa ta kira mishi shi, dan tana tunanin ko bai san damuwar su ba, zai ma Abbun fada yasa shi yaci wani abu kar ciwo ya hadar mishi biyu.

Fuskar Yaya Ayuba yake kallo dan tun da ya gama magana Yaya Ayuban yayi shiru baice komai ba. Ji yake kamar Abbu ya watsa mishi ruwan kankara, ya rasa mamaki zaiyi, bacin rai ko tashin hankali. Saboda maganar yake ji tana amsawa a cikin kunnuwan shi har yanzun.

“Layla ciki gareta, cikin Rayyan.”

Lokutta da dama har ran shi yana mantawa Layla da Bilal ba daga jikin Abbu suka fito ba. Shisa maganar ta dake shi ba kadan ba, tana tuna mishi da cewar Layla yar amana ce a hannun Abbu, yar riko ce, marainiya gaba da baya. Baisan wacce irin kwamacala bace wannan da yanda zasu fara bullowa lamarin.

“Kayi shiru…”

Abbu ya fadi zuciyar shi na tafasa.

“Hmm.”

Yaya Ayuba ya iya furtawa yana sake gyara zaman shi, sosai maganar ke yawata mishi, amman duk yanda ta kai cikin kan shi sai yaji wani irin tashin hankali ya tsirga mishi.

“Nayi shiru ne ina so kace mun abinda naji ba dai-dai bane Ahmadi.”

Numfashi mai nauyi Abbu ya sauke, shima tun dazun yake jira, tunda ya dawo dakin shi yake so wani ya same shi yace mishi komai daya faru wasa ne, an gwada shine kawai kuma anga yanda yaran shine raunin shi, amman shiru. Duk dakika da zai wuce saiya kara tabbatar mishi da cewa komai da ya faru da gaske ne.

“Ban san ya zanyi ba, wallahi ban sani ba.”

Cewar Abbu, Yaya Ayuba na jinjina mishi kai.

“Zubar da cikin ba mafita bane ba.”

Wani bugawa zuciyar Abbu tayi, aiko mafita ne ma bai hango za ayi wannan danyen aikin da shi ba, zunuban zasuyi mishi yawa. Laifukan zasuyi mishi nauyin dauka matuqa, yana jin kuma da muryar da Yaya Ayuba yayi magana, bamai kwari bace ba, kamar yana son Abbu ya duba yiwuwar lamarin ne. Kuma hakanne a zuciyar Yaya Ayuba, so yake ya duba in zai yiwu a zubar da cikin, zai saukaka musu abubuwa da yawa, musamman maganganu da surutun mutane idan zancen ya fita, amman a fuskar Abbu yaga yanda babu wannan tsarin a cikin jerin mashalar da yake nema.

“Ina tsoron fitar maganar nan Ahmadi, wallahi ina tsoron ta, mutane zasu fadi komai, zasuyi surutai kala-kala… Ba akan Layla kawai zasu dora ayar tambaya ba, gabaki daya Martabar ahalin Dikko sai ta sami tangarda…”

Kai Abbu ya dafe da duka hannayen shi, a tarihin ahalin su gabaki daya, makamancin wannan bai taba faruwa ba. Ya fahimci tsoron Yaya Ayuba, sai dai maganar mutane mai wucewa ce, tunda gabaki daya rayuwar ma ba mai dorewa bace ba, komai zaizo karshe wata rana. Surutun zai taba zuciyar shine idan akayi shi akan Layla, idan aka dora ayar tambaya kan rikon da suke mata, sosai zuciyar shi take ciwo yanzun da tunanin hakan. Mutane zasu ce bai riketa da kyau ba, zasu ce yayi sakaci da tarbiyar ta, Ayya ma bata fito fili tace haka ba, amman ta fada mishi akwai raunin shi a cikin abinda ya faru.

Idan duk tarin kaunar da take mishi bai hanata fadin abinda ta fada ba, bashi da tabbas akan abinda mutanen da suke jiran kuskuren shi zasu fada, cike da matsananci tsoro Abbu yake kallon Yaya Ayuba.

“Ya zanyi? Me zanyi?”

Dan jim Yaya Ayuba yayi, a cikin abin duka baiga wani zabi mai sauki ba, in dai cikin yana nan basu da tabbas akan tsayawar maganar a tsakanin su kawai. Amman yanzun bayason fadin wani abu da zai kara firgici da fargabar dan uwan nashi, shisa ya zabi fadin.

“Shi Rayyan din ya kamata ya aure ta.”

Kai Abbu ya jinjina cikin aminta da maganar da Yaya Ayuba yayi. Wayar shi da take kan kujera ya dauka yana kiran Ayya.

“Ki kira Rayyan sai kuzo tare.”

Ya fadi tana dagawa, bai jira amsarta ba ya kashe. Mami ma kiranta yayi yace ta taho da Layla.

“Gara su san da maganar.”

Ya fadi yana kallon Yaya Ayuba da baice komai ba, bayason ya tuna ma Abbu ko da za’ayi auren sai bayan ta haihu dole. Sosai yake kara jinjina lamarin. Ayya ce ta fara shigowa dakin da sallama, duk da gefe ta samu ta zauna. Ta kasan idanuwanta Abbu take kallo, yanda fuskar shi take a kumbure na taba zuciyar ta, zata dauke mishi duka wannan tashin hankalin in zata iya. Saida ta koma daki ta zauna ita kadai sannan tasan babu yanda za’ayi ta taba son Mami da Layla, saboda da bata dauko musu yarinyar ba da yanzun suna zaman su lafiya, da bata shigo musu da ita cikin gida ba, da mijinta bai shiga wannan yanayin ba.

Da ta dauko ta din, data riketa yanda ya kamata, da bata barta tabi mata yaro har Zaria ba duk wannan abin da sun kauce mishi. Sai dai in tayi magana yanzun za’a ce ita din bata san kaddara ba, kuma ba haka bane ba, tasan kaddara, ta dai san akwai wadda take tafiya da son zuciya, akwai kuma wadda take hade da sakaci irin wanda Mami tayi kuma Abbu na kallo ya biye mata. Da sun fada mata ita da tasan yanda zata nisanta yaronta daga Layla, watakila da duk basu zo nan ba. Yanzun da taje ta kirawo Rayyan din, zaune ta same shi ya hada kan shi da gwiwa, Bilal ma yana bakin kofar dakin a zaune ya hade na shi kan da gwiwa. Sai bayan ta fito ne ta dafa shi ya dago mata fuskar shi da take a kumbure kamar wanda yaci kuka

“Ka tashi daga nan Bilal, ko dakina ka koma.”

Numfashi ya sauke, da wani yanayi yake kallonta.

“Ki barni anan Ayya, dan Allah ki barni.”

Bata da zuciyar tursasa shi, shisa ta kyale shi din tana tafiya. Yanzun ne tayi mamakin ganin shi ya biyo bayan Rayyan daya juya yana mishi wani irin kallo, yanda yayi tsaye na sanyaya wani abu a zuciyar Ayya, bata san meye take gani a tsakanin yaran nata ba, amman bata son shi, koma mene ne yana kara ma wutar tashin hankalinta fetur. Gefe Rayyan ya karasa yana tsayuwa, Bilal ne ma ya zauna a kasa kusa da Abbu. Yaji me Ayya tace, yaji tana fadama Rayyan din Abbu na kiran shi, sai da ya fito sannan shima ya mike da nufin rufa mishi baya.

“Ina zaka je?”

Rayyan din ya tambaya, ya gwada shiga dakin bayan ya dawo sallar la’asar, ya sake yin magana da Rayyan, ko baice komai ba ya zauna a tare, amman yana daga labulen ya dago yayi mishi wani kallo da ya saka shi mayarwa ya saki. Bayason ganin shi, kamar yanda kowa na gidan yake gab da fara ji a kan shi ya sani, har karshen rayuwar shi zai kasance mai godiya da karamcin su, yanda suka karbe shi suka darajta shi. Ba kuma zai ga laifin su ba, yaci amanar sune shisa, yayi musu kuskuren da ko bakin da zai basu hakuri baida shi.

“Ba zaka dauki laifin da ba kayi ba, ba zan bari ba Hamma.”

Sai da Rayyan din ya dan dafe kan shi sannan ya saki yana kallon Bilal din.

“Karka biyoni Bilal, karka fara biyoni…”

Kamar baiji kashedin Rayyan din ba, yana juyawa, inda ya saka kafar shi nan Bilal ya mayar da tashi, yana tsayawa shima ya tsaya, batare da ya juyo ba wannan karin yace.

“Nace karka biyoni bakaji ko?”

Sun kusan minti daya a tsaye kafin Rayyan din ya sake cigaba da tafiya, wannan karin sai da ya sha kwana sannan Bilal yabi bayan shi. Ba zai zauna ya sake hada Rayyan din da su Abbu ba, bayan abinda yayi, ba zai bari ya kara wani ba. Ko yanzun da Rayyan din ya bishi da wani irin kallo, kan shi kawai ya sadda kasa, ya zauna kusa da Abbu ne saboda ya san damar yin hakan na gab da kwace mishi, zuciyar shi yake ji zaune cikin kirjin shi tana dokawa a hankali a hankali, kamar wadataccen jini baya zagaya mata, suna zaune Mami ta shigo, Layla na bin bayanta, har yanzun tun kayan dazun ne na jikinta, ko hijabin ma bata cire ba.

Inda suka barta bata tashi ba, anan rana ta sameta, anan kuma tabarta, ko sallah batayi ba sai da Magriba da Jabir yazo ya sameta tana zaune anan, shima har zai wuce saiya kasa, ya dawo baya.

“Ki tashi daga nan.”

Taji shi, ko karfin kirki bata da shi balle tayi motsi, hannunta ya kama yana dagata, batayi musu ba ta mike. Janta ya farayi, suka wuce Mami da take zaune a kasa kan kafet, sai da ya kaita dakinta sannan yace,

“Kinyi sallah?”

Kai ta girgiza mishi batare da ta kalle shi ba.

“Tun dazun kina waje Layla? Baki tashi ba? Anan kika zauna rana ta kare akan ki? Baki da hankali ko?”

Idanuwanta taji sun kara cika da hawayen da ta dauka sun kare mata da fadan Jabir din.

“Ki wuce kiyi sallah.”

Batayi mishi musu ba ta shiga bandakin ta dauro alwala ta fito, tana cikin sallah taji shigowar Jabir din kafin ya ajiye kofi yana sake ficewa. Sai da ta gama gabatar da sallolinta duka, zuwa lokacin an kira isha’i shisa tayi, bakinta yayi nauyi, bata san kalar addu’ar da zatayi ba. Dan sallar ma sai take ganin kamar ta makale ne a wani waje, kamar ba zata isa inda za’a karba ba, saboda cikin da yake jikinta, saboda daudar da take ji a tattare da komai nata. Kofin da Jabir ya ajiye ta dauka, shayine mai kauri ya hada mata, sai taji cikinta yayi wani qugi da yunwar da take tattare da ita, ga zazzabi ya sake saukar mata.

Tana kurbar shayin hawaye na zubar mata, batama gama sha ba taji muryar Mami a saman kanta.

“Abbun ku yana kira.”

Mami ta furta tana juyawa, dan shayin da ta samu ya shiga cikinta taji yana barazanar dawowa saboda tashin hankali. Shisa ta dade a zaune kafin ta iya mikewa. Kara hautsinawa cikinta yayi da taga Rayyan din, gefen Mami ta zauna, tana kokarin ganin idanuwan Rayyan ko yayane, amman a tsaye yake ya jingina bayan shi da bango, kan shi a kasa. Wani irin shiru ne a cikin daki da kowa yake ji a jikin shi kamar bargo, ganin Yaya Ayuba bashi da niyyar cewa komai yasa Abbu yanke hukuncin yin magana, ya dauka zai saukaka mishi komai ta hanyar yi ma su Mami bayanin shawarar da suka yanke.

Ya bude bakin shi ya kai sau biyu yana rasa ta inda zai fara ko abinda zai fada din

“Rayyan zai auri Layla.”

Ya furta, maganar na zuwa kunnen shi da wani irin yanayi. Sai lokacin Rayyan ya dago ya kalli Layla, zuciyar shi ciwo take cikin yanayin da bai taba tunanin zatayi ba, ita ma so yake taji abinda yake ji, musamman da ta dago tana sauke nata idanuwan cikin na shi, yau tashin hankali ya korar mishi tsoron idanuwanta da yake ji. So yake taji ciwon da yake ji, taji rabin abinda ta saka yake ji, batare daya dauke idanuwan shi daga cikin nata ba yace,

“Ba zan aure ta ba Abbu.”

Karar rushewar wani abu Layla taji cikin kunnuwanta, amman ta rasa daga inda take fitowa, tashin hankalin da take ciki yanzun yafi duk wani tashin hankali da ta taba cin karo da shi a baya. Dan bata san lokacin da ta kai hannuwanta tana jijjiga Mami da take zaune kusa da ita ba, hawaye ne masu zafi wani nabin wani suke zubar mata.

“Mami ba zai aure ni ba… Hamma ba zai aure ni ba Mami.”

Layla take fadi tashin hankalin duniya yana tarar mata waje daya, yanayin yanda take fadar maganar tana fitar da numfashin da take kokawa da shi da yanda take jijjiga Mami shi Ayya take kallo, kafin ta dubi Rayyan da idanuwan shi suke kafe akan Layla kamar kukan ta baya taba zuciyar shi. Namiji kenan, daga randa Abbu ya hada soyayyarta da ta Mami tasan da gaske baka shaidar namiji, shikenan fa, ya gama da Layla, yana da damar da zaici gaba da rayuwar shi kamar komai bai faru ba, surutun da mutane zasuyi ma da wahala ya bi takan shi. Zai dauki lefin yin cikin da yake jikinta ne kawai.

Abinda Ayya take da yakinin ba zai hana shi auren yarinya kimtsatsiyya ba, amman ita Layla zai hanata auren namiji kamili, ko da ta samu, surutan dangin shi zasuci gaba da binta har karshen rayuwar ta, yaji mata ciwon da samun saukin daukar tabon shi na tare da auren shi ne kawai. Duk da shima din babu tabbacin ba zata fuskanci wulakanci a wajen shi ba, musamman yanzun daya furta ba zai aureta ba. Bata son yarinyar har yanzun, tunaninta a tare da Rayyan na saka cikinta kullewa, amman bai hanata tausaya mata ba, bai kuma hanata tsanar son kan da Rayyan yake sonyi ba.

“Wacce magana kake yi Rayyan?”

Kawu Ayuba ya tambaya yana kallon Rayyan din, shima kallon shi ya yi.

“Ba zan aure ta ba, bana son ta Kawu.”

Ya karasa yana jin zuciyar shi na ihun karyata kalaman, a hade da hakan yana jin ciwon da take yi mishi.

“Bana son yi maka baki Rayyan… Bana…”

Abbu ya fara, Bilal yana katse shi da fadin.

“Abbu…”

Ganin kamar baiji ba yasa shi kara fadin,

“Abbu…”

Cikin yanayin da yasa hankalin kowa ya koma kan Bilal, wannan abin da yake faruwa yanzun ne yasa ba zai bari Rayyan ya dauki wannan laifin ba, ba zai bari su Abbu su fadi maganar da zasuyi dana sani akanta ba kan laifin da baiji ba bai gani ba. Ga kukan da Layla takeyi ya kara daga mishi hankali, shi ya sakata a cikin wannan tashin hankalin, shi ya shiga tsakiyar su ita da Rayyan, abinda bai kamata yayi ba tun daga farko, ko zuciyar shi data doka mata ya dade da sanin bai kamata tayi mishi wannan rashin adalcin ba. Amman cikin watanni kalilan ya fahimci rayuwa bata san wani abu adalci ba, da basu zo inda suke ba yau.

“Ba shi bane Abbu, dan Allah ku saurareni… Layla kiyi magana ke zasu jiki, ki fada musu ba Hamma bane, ki fada musu bashi bane.”

Bilal ya karasa yana kallon Layla da kukanta ya tsananta, kai take girgiza mishi, tana rokon shi a zuciyarta da karya karasa datse sauran igiyar da ta rage a tsakaninta da Rayyan din, shima rokonta yake yi.

“Shirun mu ba zai canza komai ba, dan Allah ki saukaka mana, ki fada musu bashi bane ba.”

Zaninta Ayya ta tattaro tana goge fuskarta da take jin kamar alamun zufa, saboda yanayin maganar Bilal din bata nuna alamar wasa ko son daukar laifi ba. Abbu ma kallon Bilal yake da sabon tashin hankali, kafin daga kasan makoshin shi yace,

“Bilal.”

Abbu ya kalla yana riko hannun shi.

“Ni ne Abbu, ba Hamma bane ba… Ni ne.”

Ya karasa wasu hawaye masu zafi na zubo mishi, komai na jikin Abbu bayason yarda da maganaganun Bilal din, shisa ya kalli Layla duk kuwa da kukan da takeyi tana girgiza mishi kai.

“Layla ki mun magana dan Allah, ku fadamun abinda zan iya dauka.”

Kuka takeyi kamar zata shide, bata roki Bilal komai ba sai shirun shi, bayan duk abinda ya faru. Ya kawota inda ba zata iya juyawa ba, Abbu da kan shine yake rokon ta, a hankali ta daga mishi kai.

“Ba Hamma Rayyan bane.”

Ta iya furtawa da kyar tana kwantar da kanta a jikin Mami hadi da sakin wani kuka da ko sautin shi baya fita.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un.”

Yaya Ayuba ya furta, ba zaice maganar bata dake shi ba tun daga farko. Amman yanzun jijjiga shi tayi tana dagawa ta buga da kasa. Yasan Bilal, ko a yaran shi babu mai natsuwa da hankalin Bilal, babu mai sanin ya kamatan shi. Ya sha aiken Bilal kan abubuwa masu muhimmanci saboda ya aminta da nutsuwar shi. A mafarki idan aka fada mishi Bilal zaiyi abinda yake cewa da kan shi yayi zai karyata, idan ya tashi kuma zaiyi addu’a harma da sadaka. Abbu ya kasa cewa komai, kan shi yayi wani shiru na ban mamaki. Akan Rayyan ya yarda da zancen Ayya, akwai sakacin shi a ciki, akan Bilal fa? Me zaice? Me zata ce ita ma?

Kallon ta yayi, hargitsi ne bayyane akan fuskarta, yaronta take kallo, Bilal dinta take kallo tana yarda da akwai kaddarar da bata da kalaman misaltawa, yanda yake saka hannu yana share hawayen da sunki daina zubar mishi yana saka nata idanuwan cika da hawaye. Abinda yake damun shi kenan, damuwar da yake ta boye mata a watannin nan kenan ashe, bata taba daukar zata yiwa wani uzuri kan lamari irin haka ba sai yau. A tare da Bilal bata bukatar wani bayani, koma meye ya faru kaddara ce, ko menene ya gifta tsakanin shi da Layla tsautsayi ne.

“Bilal.”

Mami da ko kukan ita ta kasayi ta kira, so take ya kalleta dan ta tabbatar da shi dinne, kallon ta yayi, ta kasa tambayar shi, duk da tana son jin bayanin shi kafin ta yanke mishi hukunci, saboda Bilal ne, idan za’a tambayeta shaida akan shi zata fadi cewa duk yanda tasan Ayya tayi kokarin ganin yaran bai kulla alaka da ita ba ya tsallake, baya shakkar dukan da zai sha a hannun Ayya a gabanta yake gaishe da ita, a lokutta da dama ta sha ganin Bilal din ya mata murmushin ban hakuri duk idan Ayya ta sauke mata wata masifar da bata san dalilinta ba. Da yayi hankali har daki yakan bita yana fadin,

“Dan Allah Mami kiyi hakuri, karki sa abin a ranki. Ayya bata nufin duka abinda ta fada, kinsan idan ranta ya baci.”

Ba dan Abbu ba, saboda Bilal ma ta sha kauda kai kan abubuwa da yawa da Ayya zatayi mata. Shisa take son jin bayani daga bakin shi, take son sanin me ya faru, sai dai kafin yayi magana Ayya ta riga shi.

“Karku dora mishi laifi, dan Allah kar kuce wani abu, kuskure ne, Bilal ka fada musu kuskure ne, ni nasan kuskure ne, in dai da gaske ne kuskure ne.”

Hawayen da suka zubo mishi Bilal ya share yana jin kalaman Ayya na saukar mishi, suna ratsa wajaje da yawa a cikin jikin shi, suna kuma sanyaya zuciyar shi da take matukar ciwo. Ayya kenan, Ayyar shi, uzuri take son mishi tun kafin taji bayanin shi, bata da wata tambaya, saboda a idanuwanta ba zaiyi laifi mai girma haka ba, wannan ce girman kaunar da takeyi mishi, kaunar da yake jin ya ha’inta yau, saboda kuka takeyi, shine sanadin kukan da takeyi. A muryarta yaji shisa ya kasa kallonta, Abbu yake kallo da baice komai ba.

“Abbu…”

Bilal ya kira muryar shi na karyewa, Abbu ya kasa kallon shi, ya rasa abinda yake ji, amman so yake kowa yabar shi, ya dan zauna shi kadai, shisa yace,

“Shikenan kai sai ka aure ta… Ku fita dan Allah, ku dan barni.”

Rayyan da yake tsaye yana jin shigi da ficen duk maganganun su batare da sun taba zuciyar shi ba yaji maganganun Abbu sun shiga wajen da suka zauna daram suna kasa fitar mishi. Ya dauka babu wani abu da zasu fada da zai taba shi, ya gama jin su duka daga bakinta da na Bilal. Sai yanzun da yaji Abbu na kiran Bilal ya auri Layla, bayan cikin da yake jikinta da ba nashi ba, yanzun ita din ma ake so ace ba tashi bace ba.

“Abbu”

Rayyan ya kira sauran kalaman na makale mishi.

“Dan Allah ku fita ku barni.”

Abbu ya sake rokon su, saboda muryar Rayyan da yaji na kara saukar mishi da wani yanayi daban. Ganin duk suna mikewa yasa Rayyan sake kallon Abbu cikin tashin hankali, so yake ya fada mishi shifa baice ba zai auri Layla saboda wani abu ba, ya fadane dan shine hanya daya kawai da yake da ita da yasan zataji kalar ciwon da yake ji. Da yace baya son ta ya dauka su duka kamar zuciyar shi sunji karyar da yake yi. Mami ita ta fara barin dakin da Layla a jikinta tana wani irin kuka da yake ji a kasan zuciyar shi.

“Ahmadi”

Yaji Ayya ta kira, tana saka shi kallonta, da zuciyar shi yake rokonta da ta fadama Abbu ya janye kalaman da yayi, amman sai yaji tana fadin.

“Dan Allah kar kaga laifin shi, ka tsaya yayi maka bayani… Bilal kayi mishi bayani kaji.”

Kafin yayi magana Abbu ya kalli Ayya.

“Dan Allah Maimuna, naji iya abinda zai tsaya dani har karshen rayuwata, dan Allah ku barni, kuje ku barni dan girman Allah.”

Hawayenta Ayya ta goge tana mikewa, harta yi taku daya Bilal daya fara magana yana sakata taja ta tsaya cak.

“Ban da uzurin da zan baka Abbu, bani da shi… Nayi laifi na sani. Ko bakin da zance ka yafe mun bani da shi.”

Karasawa tayi ta kama hannun Bilal din tana jan shi, dole ya mike. Zasu dawo ita da Bilal suyiwa Abbu bayani yanda zai fahimta. Suna ficewa Yaya Ayuba ma ya mike, su duka suna bukatar yin bacci kan maganar, gobe ya dawo su kara sanin yanda zasuyi. Ko bankwana baiyi wa Abbu ba ya fice daga dakin. Rayyan ne yayi tsaye, ya kasa tafiya, yana kallon Abbu ya kai hannu ya share kwallar da ta zubo mishi.

“Rayyan bakaji nace ka tafi ba?”

Kai Rayyan ya jinjina mishi, yaji shi, yaji me yace tun da farko, ya kasa tafiya ne saboda akwai tarin maganganu da yake son yi da Abbu, watakila yau ba ita bace ranar daya kamata, amman ya kasa tafiya.

“Abbu baka mamakin ya akayi nake daki daya da kai?”

Dagowa Abbu yayi yana kallon Rayyan din, yau duka bashida wajen mamaki kuma.

“Karka ce in tafi. Abbu karka koreni yau kawai da nake jin zan iya zama daki daya da kai na lokaci mai tsayi batare da iskar wajen ta mun kadan ba.”

Kai Abbu ya jinjina ma Rayyan din. Shi kam zaman ma bashi da karfin yin shi, shisa ya kwanta, duniyar duka na mishi lilo, ya rasa kalar tunanin daya kamata yayi, ya kuma rasa abinda yake faruwa da su haka, abinda yake faruwa da yaran shi. Kafin kalaman Bilal su fara mishi yawo suna saukar mishi da zazzabi. Kuskure shine abinda Ayya ta kira komai da akalar lamarin ta juya kan Bilal, shima bashi da wasu kalamai da zaiyi amfani da su, kalmar iri daya ce da ta Ayya, kuskure. Idanuwan shi ya rufe yana son ya hada ya rufe tare da duk wani tunani amman abin ya faskara. Ya kasa rufe tunanin da yayi mishi cunkus.

Rayyan kam ba zaice ga lokacin daya dauka a tsaye ba, yasan dai kafafuwan shi da kansu suka gaji suna kaishi kasa, da yake akwai kafet cike da dakin nan ya kwanta shima. Ciwo yake ji, ciwon da yake bukatar lallashi ko ya yake, kuka yake nema watakila idan yayi irin wanda Layla takeyi zai samu sauki. Abu daya ne yake mishi yawo, dan yace ba zai auri Layla ba baya nufin yana son ta kusa da wani, balle ace wanin ya kasance Bilal, mutuwa kawai zaiyi ya tabbatar yanzun. Dan kirjin shi kamar an zauna a kai haka yake ji. Me yasa Bilal zai mishi haka? Ya kasa samun wannan amsar, idan kuskure zaiyi me yasa sai akan Layla?

Duk da dazun yana jin surutun da yake yi a bakin kofa, ya zabi yin kamar baiji shi bane ba. Shisa bayason juya kalaman, baya son yin wani tunani da zai hada da yiwa Bilal uzuri, abinda yayi mishi ba zai yafu ba, ba zai iya yafe musu ba daga shi har Layla. Har cikin kasusuwan jikin shi yake jin hakan, yana so suji ciwo kalar wanda shima yake ji. Amman hakan baya nufin yana son ganin Layla a tare da Bilal, yama Abbu zai fara cewa Bilal ya auri Layla. Yana tunanin baccine ya fara fisgar shi, dan kiran sallar farko da akayine ya saka shi bude idanuwan shi dakyar yana tunanin inda yake.

Kafin komai ya dawo mishi yana saka shi dafe kirjin shi da yake ciwo. Da kyar ya iya mikewa, ko ina na jikin shi ma ciwo yakeyi. Abbu da yake kwance ya kalla, sai da yaga ya juya kwanciya sannan ya fice daga dakin. Fitilun gidan duka a kunne suke yau. Dakin su ya nufa, yana shiga zuciyar shi tayi wata irin dokawa da yanayin yanda yaga an fiffido kaya, tun bai karasa cikin dakin ba kafafuwan shi suke rawa, kan tebir din shi yaga takarda a ajiye, ya dauka yana budewa, da daya daga cikin fensiran zanen shi akayi rubutun da yake ganin yana rabe mishi biyu, saida ya runtsa idanuwan shi ya bude su tukunna ya iya karantawa da muryar Bilal a zuciyar shi

“Nayi kuskure na sani, ba zan kara shiga tsakanin ka da Layla fiye da yanda nayi ba Hamma, ba saika yafe mun ba, dan Allah ita ka duba zuciyarka, nasan akwai wajen da zai iya yafe mata, ka yafe mata. Ka dora duka laifin a kaina. Nagode da tarin kaunar ka, ka kula da kan ka, ka kula da Ayya.”

Ya karanta wasikar yafi sau ashirin kafin asalin ma’anar ta ya zauna mishi, cikin wani irin tashin hankali ya fito daga dakin, tun daga bakin kofar yake fadin,

“Ayya!”

Yana kara kwala mata kira harya karasa bakin kofar dakinta inda suka hade saboda daman ba bacci takeyi ba, kiran shi ne ya sata mikewa tana tahowa da sauri, ko da yana yaro kome yake bukata bai taba mata irin wannan kiran ba, yana ganinta kafafuwan shi na kasa daukar shi.

“Ayya ya tafi… Ayya tafiya yayi… Bilal tafiya yayi ya bar ni… Dan ba zan yafe mishi ba sai nace ya tafi? Me yasa zai tafi? Ina ya tafi Ayya?”

Duka zancen shi a baibai take jin shi, jijjigata Rayyan ya fara yi, saboda yasan babu inda Bilal zaice bai fada mata ba, gara ta gaya mishi ya bishi ya dawo da shi.

“Ki fadamun inda ya tafi Ayya… Kinga ni me yace mun…”

Wasikar Ayya ta karanta, fahimtarta ne yake mata wahala saboda babu yanda Bilal zai tafi wani waje bata sani ba, balle ace irin wannan tafiyar, ture Rayyan tayi tana nufar dakin su ya rufa mata baya, kayan Bilal ne tagani a zube, batayi magana ba ta sake fitowa tana jin Rayyan na biye da ita har cikin dakinta inda ta dauki wayarta, tana mamakin yanda komai yayi mata shiru, lambar Bilal ta kira a kashe, duka lambobin shi a kashe, Rayyan ta kalla da shima yaji a kashe ne, kai dai kawai yake girgiza mata, duniyar na kara hargitse mishi, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su da wani irin matsananincin tsoro daya ziyarce shi.

“Ayya dan Allah…”

Cewar Rayyan yana dafa bango ya sulale kasa, a cikin daki yake, amman duniyar duka yake ji tayi mishi fili, babu kowa a cikinta sai shi kadai, bai san inda zai nufa batare da Bilal ba.

“Ayya ki ce mun bai tafi ba, dan Allah kice ya dawo.”

Rayyan yake fadi yana jin iska ta daina kaiwa cikin kan shi, kafin wani irin duhu ya rufe mishi idanuwa ruf, yana saka Ayya tsugunnawa ta riko shi kafin ya karasa kaiwa kasa, kan shi a jikinta yake da wani nauyi da batayi zato ba, nata kan ta dora a na shi, tunda take bata san akwai tashin hankali makamancin wannan ba, a wahalce ta dago, muryar da zatayi amfani da ita wajen neman taimako take nema ta rasa yau.

Babi Na Ashirin Da Bakwai

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×