Skip to content

Martabarmu | Babi Na Ashirin

3
(4)

<< Previous

Lokaci zuwa lokaci wanda yake kujerar kusa da shi a cikin jirgin yakan ja karamin tsaki saboda yanda Rayyan din yake bubbuga kafar shi a kasa cikin kosawa. Gani yake kamar jirgin baya sauri, baisan mene ne a nannade tare da harshen Bappa da kalaman shi ba, amman sunyi tasirin da suka saka shi daukar shawarar shi na tsayawa ya yi abinda ya kaishi Bauchi ya wuce wajen, sai su duba idan akwai jirgin da zai tashi daga Bauchi zuwa Zaria, da yake a yar jakar shi duka katikan shaidar shi suna ciki, na makaranta, katin zabe da kuma katin shaidar dan kasa. Bappa na dubawa kuwa yayi nasarar ganin akwai jirgin da zai tashi karfe biyar da rabi na ranar.

Har suka gama abinda suke yi a camp wajen azahar suka dawo hotel room din Rayyan bai daina mamakin yanda akayi Bappa ya saka shi zama a Bauchi har wannan lokacin ba, saboda gabaki daya hankalin shi ya yi Zaria. Bai sake gwada kiran lambobin su Bilal ba duk ranar, wayar shi dai tana hannun shi, yana gudun kar ya sakata ko da a aljihu ne wani a cikin su ya kira ya zamana bai samu ba. Har airport din ma Bappa ne ya raka shi. A hanya ya tsaya ya sai mishi strawberry yoghurt, da yake yana da sauran biskit a jaka saiya hada ya dan sakama cikin shi, jiri har dibar shi yake idan ya mike, kuma yasan yunwa ce.

Bappa ya zauna da shi har sai da lokacin tantancewa yayi sannan suka mike a tare.

“Na gode. Na gode sosai.”

Rayyan ya tsinci kan shi da furtawa, saboda shine kalaman da zai iya fitowa da su da kalar karamcin da Bappa ya yi mishi. Kai kawai ya jinjina ya furta,

“Sai munyi waya.”

Shima na shi kan ya jinjinawa Bappa, bai tabayin aboki ba balle ya san yanda yake. Amman yanajin da rayuwa ta hada shi da Bappa da wuri, watakila da sun zama abokai. Baya son mutane, amman Bappa yana mishi daban, ba shi da lokacin tunani akan abin saboda su Bilal da suka kara taso mishi suna danne duk wani kwanciyar hankali da yake tare da ita. Da su a manne cikin kan shi suka sauka garin Zaria. Kafafuwan shi kamar basa mishi saurin da ya kamata yau haka yake ji lokacin daya karasa bakin titi da yake da yar tafiya daga cikin airport din. Mashin ya samu zuwa gida.

“Dari biyar.”

Mai mashin din ya fadi, kai kawai ya daga mishi yana hawa.

“Kayi sauri dan Allah.”

Rayyan yayi maganar da wani irin yanayi a muryar shi, har sai da mai mashin din ya dan duba ta mudubi ko zai ga Rayyan din da kyau, ko a cikin abokai lokacin daya fara koyon tukin mashin din “Dan asabe ganganci” ne lakabin shi, yanzun ma sunan Dan Asabe ya bace sai ganganci din, yanda yake jan mashin idan yana tuqi kowa mamakin samun kwastomas din shi yakeyi. Musamman idan ya busa hayaqin wiwi din shi, bakin shi babu hakora wajen biyar saboda hatsarin da yakan yawaita samu. Tabbas yau ko labari yaje ya bayar na cewa wani ya nemi ya kara gudu da shi a mashin babu wanda zai yarda.

Daman ance in da ranka zaka sha kallo, yau ya dauko mahaukaci. Sai yake jin shi a tsorace da Rayyan din, wani mahaukacin tas zaka gan shi, saika saki jiki kaji saukar duka. Haka suka lallaba harya sauke shi. Kafafuwan Rayyan din yaji suna mishi rawa, kamar suna son ce mishi ba zasu iya karasawa da shi cikin gidan ba. Zuciyar shi bata kara gudu ba sai da ya karasa tsakar gidan, har wani numfashin tashin hankali yake fitarwa. Da kyar ya karasa dakin su yana ganin kofar a ture, daga hannu yayi cikin tunanin ya kwankwasa ko ya tura, ko kuma ya gwada saka mukulli. Karshe ya tsaya kan shawarar turawa, yaga dakin ya bude, duk da gidan akwai hasken wutar lantarki, dan ga mutanen cikin gidan nan sunata shige da fice, dan ko sun mishi magana ma bai kula da su ba.

Yana tura dakin ya ga duhu, makoshin shi ya bushe kamar an zuba ya shi, switch ya laluba ya kunna, duk yanda ya sha cin karo da tsayuwar bugun zuciya a karance da kuma a videos bai taba tunanin haka abin yake ba sai yanzun da ganin Bilal a kwance a kasa kamar gawa ya saka tashi zuciyar tsaya na dakika kafin ta soma aiki tana wata irin bugawa. Wannan karin kafafuwan shi duka sunyi sanyi, gwiwoyin shi kamar an buge su da guduma haka yake ji. Kasa ya yi gabaki dayanshi. Da rarrafe ya karasa inda Bilal din yake yana dora hannun shi a jikin Bilal din.

“Bi… Bilal…”

Rayyan ya kira cikin rawar murya, tashin hankalin shi na karuwa, dan gani yayi kamar Bilal din ya rabe mishi gida biyu. Idan zuciyar shi bata daina gudu ba yana gab da sumewa, da kyar ya iya birkito Bilal yana dora hannun shi kan kirjin Bilal din inda yaji zuciyar shi na dokawa a hankali a hankali cikin yanayin daya fara nutsar da na shi bugun zuciyar.

“Bilal…”

Ya sake kira can kasan makoshi, Bilal din da yake jin shi a wata duniya yana bude idanuwan shi da kyar kafin ya sake mayar da su ya rufe. Tun jiya yake nan kwance, da kyar yaja jikin shi da safiyar yau din ya shiga bandaki. Da ya fito ma jiri ya dinga dibar shi har ya karasa daki. Towel din shi na wanka ya ajiye a kasa ya dauki ruwa yai alwalar asuba a kai. Da kyar yayi sallah sabo da ciwon kan da yake fama da shi ko numfashi da kyar yake fitarwa, sanyi yake ji, amman ya mika hannu ya janyo bargo ya kasa, anan yake kwance tun safiyar yana jiran ikon Allah ya cika a kan shi.

Saboda tun jiya ya rigada yasan karshen duniyar shi yazo, baisan har rayuwar tashi gabaki daya tazo karshe ba sai yau. Akan kunnen shi aka kira azahar aka idar, amman ya kasa motsin kirki balle ya gabatar da sallah ko da daga zaune ne. Babu tunanin da baiyi ba. Ayya ita ce tafi kowa tsaya mishi a rai, yana tunanin wanda zai kula mishi da Ayyar shi a lokuttan da shi ka dai ya ke gane tana bukatar kulawa. Wa zai kirata ya yi mata hira, zai so ace ya samu dama, har addu’a ya yi ya samu damar da zai roki Rayyan daya canza in zai iya, ya kula mishi da Ayya, ya kuma yafe mishi.

Ko yanzun zuwan Rayyan din sai yake mishi kamar a mafarki, labban shi sunyi nauyi ne balle yayi magana, daya bude idanuwan shi ma hasken dakin kara mishi ciwon kai ya yi. Sai yaji kamar an soka mishi allurai ta cikin idanuwan, shisa ya mayar da su yana rufewa babu shiri.

“Bilal…”

Rayyan ya sake kira, amman ya ki yin wani kwakkwaran motsi, bawai ciwo bane Bilal bayayi, har yini sun tabayi a asibitin makaranta aka kara mishi ruwa, amman zuwa tara na dare kamar ma baiyi jinya ba. Haka yake hidimar shi, bai taba ganin shi cikin hali irin wannan ba. Tunanin zuwa asibiti ne yazo ran shi, amman bai taba raina karfin shi ba sai da ya daga Bilal dan ya dauke shi yaji kafafuwan shi banda rawa babu abinda suke yi. A hankali ya mayar da Bilal din ya kwantar, da kyar ya karasa mikewa yana fita daga dakin. Ba zaice ga sanda ya cire takalman shi ba, sai da ya taka tsakar gidan su yabi takan ruwan da yaji har tsakiyar kan shi sannan ya gane babu takalma a kafafuwan shi. Abinda ko a daki da wahala ka same shi babu su, akwai wanda yake ajiyewa dan yawo a cikin daki kawai.

Yakan ce Bilal din na tako kasa ya shigo musu da ita, ko idan wani a cikin abokan shi yazo neman shi yana shigowa da kasa, shikuma baya so ya taka kafar shi yaji kasa a cikinta ko ya take.

“Kai da za’a saka a cikin kasa Hamma wanne gudunta kake yi kuma?”

Bilal ya taba fada mishi, ya saka shi kwanaki maganar na mishi yawo, shisa ya daina cewa komai kan shigowa da kasar, amman zai iya sharewa sau goma, kuma da takalma a kafar shi in yana zaune, ko safa wasu lokuttan. Amman yau bashi da wannan lokacin, Abdul kamar yanda yaji Bilal din na kira yaci karo da shi.

“Rayyan”

Abdul din ya fadi cikin gaisuwa.

“Ka taimaka mun, Bilal bashi da lafiya.”

Rayyan ya fadi cikin wani yanayi yana dorawa da, “Zan kai shi asibiti…”

Cikin tashin hankali Abdul yace, “Subhanallah… Bilal din? Yana ina?”

Dan dazun nan suke maganar sun ga motar shi ya yi parking, amman har daki Sulaiman ya ce ya kwankwasa yaji shiru ba ayi magana ba, kuma sun nemi wayar Bilal din a kasha. Sunata mamakin inda ya shiga tun safiyar jiya, saboda shi din na mutane ne, kuma anyi wasan kwallo mai zafi, an lashe club din Barcelona da Bilal din yake bi, sunata neman shi ayi adawa. Amman shiru bai leko su ba, har Abdul din yake cewa,

“Su fa yan Barca haka suke, in su suka ci su addabi kowa, amman basa daukar dabi duk idan aka cinye su.”

Anata dariya da fadin yanda Bilal ya san bambanci dabi irin na kwallon, da kuma yanda baya taba bari gardamar tayi nisan da zai zamana wani yaji babu dadi, in an matsa mishi da yawa yakan ce,

“Ai shikenan, ku bani panadol in watsa ko zanji dama-dama.”

Shikenan gardamar sai tazo karshe a kama dariya kuma. Kaf gidan babu wanda zaice ga rana daya da Bilal ya yi mishi wani abu. Yanzun ma hanyar dakin su Rayyan ya nunawa Abdul da hannu yana juyawa. Har ya fara bin shi ya yi tunanin kiran sauran yan gidan, in har yau Rayyan ya tsaya ya yi magana mai tsayi da shi Bilal din na cikin yanayi sosai. Kafin kace me, kusan duk wanda yake gidan a lokacin ya fito sun nufi dakin su Bilal din har babu wajen da wasu zasu tsaya. Abdul da Rayyan ne suka kama shi. Baima san duniyar da yake ba, daya daga cikin su ya dauki mukullin motar daya gani ajiye kan tebir suka fita da shi, sai dai su shidda suka iya tafiya asibitin duk kuwa tarin mutanen da suke son binsu.

Motar babu waje, mutum biyu ne a baya, sai Bilal na ukku da suka saka a tsakiya. Har Rayyan daya shiga gaba zai kulle kofar yaga wani da zai iya kirga ranakun da magana ta taba hadasu ya kutso, dole ya matsa mishi ya shiga ya rufo suka tafi. Babu fadan da ba’ayi musu ba a asibitin, da yake na kudi kawai suka nufa a maimakon na makaranta. Nan da nan aka fara bawa Bilal din taimakon gaggawa. Rayyan yaso tsayawa cikin dakin, amman baya son yin gardama da likitocin a bata lokaci wajen bawa Bilal taimako. Daga shi sai Sulaiman aka bari dan sauran da suka tabbatar Bilal din ya samu taimako duk sai suka tafi, da zasu barwa Rayyan motar ya girgiza musu kai.

“Ban iya tuki ba, ku tafi da ita kawai…”

Yana kula da kallon mamakin da suke yi mishi, babu dai wanda ya furta komai. Da gaske yau yaga ranar mutane da Bilal kan fada mishi, wajen dubu sha biyar aka bukata tashin farko, shi kuma dubu uku da dari biyu ne a jikin shi tunda jirgi ya biyo, sai dai jakar shi na goye a bayan shi har lokacin. Akwai kuma ATM din shi a ciki, kudin duk ya kwashe ya biya jirgi, sauran dubu takwas a ciki. Kafin yayi wani yunkuri ma su Abdul sun harhada kudin hannun shi, shima saiya kara da dubu ukkun aka bayar.

Zaune suke a dakin shiru daga shi har Sulaiman din suna kallon Bilal, har sai wajen karfe tara na dare, Abdul shi kadai ya dawo, ya kawo musu darduma da kaya guda biyu dan su ya fara gani baisan kona waye a ciki ba. Harda brush ya dauko musu da McLean ya taho da shi. Tare suka mike da Sulaiman suna fadin,

“Allah ya kara sauki yasa kaffara ne, zamu dawo da safe in shaa Allah.”

Kai Rayyan ya jinjina.

“Mun gode…na gode sosai. Na gode.”

Murmushi Abdul ya yi.

“Haba maza ai ana tare.”

Ya fadi suna danyin dariya, sosai Rayyan yaso yayi murmushi amman baya cikin yanayin. Kai kawai ya iya jinjina musu, suna ficewa daga dakin. Mikewa yayi shima ya shiga bandaki ya dauro alwala, magariba da isha’i yayi, yau Bilal kawai yaiwa addu’a ya tashi ya dawo yana jan kujerar sosai ya matsa kusa da gadon Bilal din.

“Me ya same ka haka Bilal?”

Yayi tambayar a zuciyar shi yana sauke numfashi, saboda likita yace mishi jinin Bilal din ya yi wani irin hawa. Har sai da yaji tsoro da yaga takardar. Kwata-kwata Layla ta makale a wani waje cikin kan shi saboda Bilal ya danneta, sai yanzun ne ta fado mishi, wani sabon tashin hankalin na dirar masa, watakila itama bata da lafiyar. Ya laluba wayar shi baiji ta ba, saiya kula cikin kayan da Abdul ya kawo harda wayoyin su shi da Bilal da cajar waya ya hado. Shikam zuwa yanzun baisan kalar godiyar da zai musu ba, sai dai in Bilal ya tashi shi zaifi sanin abinda ya kamata.

Wayar Bilal ya tashi ya saka a caji dan yaganta a kashe, aikam cajin ne babu. Sai da yaga ta dauka sannan ya dawo ya zauna. Gwada lambar Layla yayi inda yai nasara ta shiga, har ta kusa yankewa sannan aka daga, wani irin numfashi ya sauke

“Layla…”

Ya kira daga lungun zuciyar shi, yanajin kamar yabi ta cikin wayar ya leka inda take yaga lafiyar ta.

“Layla…”

Ya sake kira, muryarta can kasa ta amsa,

“Hamma.”

Lumshe idanuwan shi yayi yanajin yanda zuciyar shi ke rawa, nutsuwar da ta kwace mishi yake nema koya take, iya wadda zai samu karfin yi mata magana yaji inda ta shiga haka. Amman ya kasa samu.

“Hamma ban da lafiya.”

Layla ta fadi ta dayan bangaren. Cikin wani mawuyacin yanayi da ya saka Rayyan din mikewa, sai dai ya kasa kara yin motsi saboda Bilal da yake gani a kwance shima. Tunani yake ko akwai hanyar da zaibi ya raba kan shi gida biyu yabar daya anan asibitin dayan kuma yaje wajen Layla, dan sai yake jin kamar kuka take kokarin dannewa. Zuciyar shi ciwo takeyi, ciwon daya kama ta nan take, da kyar ya iya cewa, “Kina ina? Me ya same ki? Waye a wajen ki?”

Ya kusa dakika biyar kafin ta amsa shi.

“Bani da lafiya Hamma…”

Ta sake maimaitawa kamar bataji tambayoyin da yayi mata ba, wannan karin yaji sautin kukanta da ya kara mishi ciwon da zuciyar shi take yi, dan baisan yanda zaiyi ba, baisan wa zai kira ya taimaka mi shi ba. Ya bude baki zai sake yin magana ta riga shi da fadin,

“Anisa…muna asibiti tun da safe. Hamma kana ina?”

Numfashi Rayyan ya sauke, a muryarta yake jin yanda take bukatar shi.

“Ina asibiti, Bilal ba shi da lafiya. Me yasa zaku min haka Layla? Ya kuke so inyi? Ya zaku yi rashin lafiya lokaci daya?”

Ya karasa maganar yana bi da rokon yafiyar Allah dan yaji kamar yayi sabo, kamar yana kokarin dora ayar tambaya akan abinda basu da zabi a kai. Amman da gaske baisan yanda zaiyi ba.

“Ki ba Anisa waya…”

Ya fadi muryar shi na fitowa da gajiyar da yake ji har cikin zuciyar shi.

“Hello…”

Yaji muryar Anisa cikin kunnen shi.

“Anisa ya jikin nata? Me suka ce yana damun ta?”

A nutse Anisa ta ce,

“Zazzabi ne mai zafi, sai sunce tana bukatar samun hutu saboda jininta ya hau, sun mata allurar bacci ne tun da safe, sai yanzun ba dadewa ta tashi, gashi na hada mata shayi zata sha, likita yace za’a karayin wata allurar dan ta kara samun bacci… Da sauki ba kamar yanda muka zo ba.”

Tunda ta fara magana yake saurarenta da dukkan nutsuwar shi, amman ya kasa gane yanda za ayi ace yarinya karama kamar Layla da yanzun ne zata cika shekara ashirin a duniya tana da hawan jinni, ina ta samo shi? Tunanin me take yi? Ko yace tunanin me suke yi daga ita har Bilal da za ace suna da hawan jini haka. Lafiya kalau ya tafi yabar su duka, amman yanzun ya dawo lokaci daya duk sun kwanta. Gara Layla yaji muryarta, ta tashi, amman Bilal har yanzun ko motsi baiyi ba. A ina zasu sami hawan jini?

“Na gode Anisa… Dan Allah ki zauna da ita kafin gobe, ina asibiti wajen Bilal, shima bashi da lafiya.”

Ya karasa yana jin kirjin shi na zafi.

“In shaa Allah…Allah ya basu lafiya.”

Amsawa ya yi da, “Amin.”

Kafin ta mikawa Layla wayar.

“Hamma…”

Ta kira shi tana saka shi jin kamar yayi fuka fuki zuwa inda take

“Kiyi hakuri Layla, Bilal ko motsi bai yi ba har yanzun… Ba zan iya barin shi ba, ba zan iya barin shi inzo wajen ki ba, dan Allah ki kula da kanki, ki sha tea din idan Anisa ta hada, ki kwanta ki huta kinji.”

Muryarta da yake ji can kasa na kara taba shi, kamar bata ji duk abinda ya fada ba, dan ta zabi amsa shine da,

“Ina son ka, wallahi ina son ka da yawa. Dan Allah karka barni, Hamma ina son ka.”

Ta karasa da kukan da ya saka shi fadin,”Ina zanje Layla?”

Dan tun daga dan yatsan kafar shi yake jin babu inda za shi yabarta. Baima san itace mutum na biyu mai matukar muhimmanci a rayuwar shi ba sai yau, Bilal ne na farko, yau yasan matsayin Bilal ba zai taba haduwa dana kowa ba. Yana jin yanda zuciyar shi take zafi da rashin ganin Layla, amman awannin da suka wuce Bilal ya danneta a zuciyar shi da kan shi gabaki daya.

“Ina son ka.”

Ta sake fadi, muryarta na isowa kunnen shi cike da firgici, baisan tsoron da take ji ba, amman ya taba zuciyar shi.

“Ina son ki Layla, watakila yaune rana ta farko kuma ta karshe da zan fada miki, saboda nayi magana mai yawa yau, ina tayi har yanzun. Amman ina son ki, ko da bazan fada ba, zan nuna miki, ina nuna miki, ke ce ba kya gani.”

Ajiyar zuciyar da tayi na nutsar da wani abu a cikin kan shi.

“Mafarki nake yi ko Hamma? Daya daga cikin mafarkina ne yau ma.”

Kai Rayyan ya girgiza mata, baisan soyayyarta na da yawa a tare da shi ba sai yanzun da yake jin kamar zata danne shi.

“Zan sake fadi a karo na biyu, sai ina ganin ki, kafin lokacin ki kula mun da kanki.”

Jin tayi shiru ya sa shi dorawa da,

“Zan iya yarda dake? Zan iya yarda zaki kula mun da kanki?”

Shirun ta sake yi sai sautin numfashin ta da yake tabbatar mishi da kuka take.

“Kasheni kike son yi Layla? Idan banji zaki kula da kanki ba abin zai mun yawa, dan Allah kiyi mun Magana.”

Ya karasa yana kai hannu ya murza kirjin shi, inda zuciyar shi ke ciwo har kaikayi takeyi, amman murzawar baisa yaji kamar ya sosata ba.

“Eh,” ta fadi, kai ya jinjina ba sai ta tsawaita maganar ta ba.

“Idan kin kasa bacci sai ki kirani muyi labari, ki sha tea din yanzun kinji ko?”

Bata amsa ba, amman yasan kai ta daga mishi, da kyar ya raba wayar da kunnen shi yana sauke ajiyar zuciya. Inda wayar Bilal take ya karasa ya kunna, yasan password din shi dan haka ya shigar, ya jira wayar ta gama kawowa, saboda Aisha ta fado mishi a rai. Yasan hankalinta ba’a kwance yake ba, kuma ba zata taba iya tako kafafuwanta gidan su ba, in dai yanda Bilal yake labarinta ne, yana da wannan tabbacin. Missed calls ya gani har guda sittin da bakwai, baibi ta kan su ba, lambar Aisha ya dubo, yana tura mata text.

“Rayyan ne, muna asibiti da Bilal bashi da lafiya. Amman da sauki. Idan ya tashi zai kira ki.”

Karantawa yayi yaga ko yayi sannan ya tura mata, kamar tana jira dan yana shiga tana dawo da amsa.

“Subhanallah, Allah ya bashi lafiya. Dan Allah daya tashi ya kirani, da safe zan kira sai in zo in gan shi.”

Har zai ajiye wayar saiya kula da tarin sakonnin da ta turo babu amsa, guda daya ya karanta.

“Dan girman Allah Nawan ka rufa mun asiri, dan Allah be ok be fine, dan girman Allah.”

Sai ta bashi tausayi, saboda yasan yanda firgicin nan yake.

“In shaa Allah daya tashi zan kiraki sai kuyi magana. Da sauki fa, ki yi bacci.”

Ya sake tura mata, wannan karin yana saka wayar a key, har zai ajiye kira ya shigo. Ya ga Ayya ce, zareta ya yi daga jikin cajin yana dagawa.

“Bilal!”

Muryar Ayya ta daki kunnen shi da wani yanayi.

“Ayya nine.”

Ya furta a gajiye, bakin shi harya gaji, tunda yake ba zai tuna ranar karshe da yayi surutu mai yawan na yau ba, ya gaji da komai, so yake ko dan kwanciya ya yi ko zai samu sauki.

“Rayyan… Ina Bilal? Me ya faru tun jiya nake kira ba’a dagawa? Gobe da sassafe in shaa Allah zamu taho Zaria… Yau babu hali, Abbun mu yace mu jira shi mu taho gabaki daya, saboda akwai taron da suke yi da ba zasu bar shi ba a wajen aiki.”

Sai da ya bari ta gama yi mishi bayani, ya bude baki yaji tana fadin.

“Maryama! Maryama… Ga Rayyan na samu.”

Kamar zata fasa mishi dodon kunne, sannan tayi kasa da muryarta tana sake fadin

“Ina Bilal din?”

Numfashi Rayyan ya sauke.

“Gashi nan muna tare, bashi da lafiya. Muna asibiti, Layla ma bata da lafiya tana asibiti, amman waje daban daban.”

Yana jin salatin da Ayya take yi tana kara wani.

“In shaa Allah gobe da sassafe zamu taho… Allah ya basu lafiya.”

Amin din a zuciyar shi ya amsa wannan karin yana sauke wayar daga kunnen shi hadi da kashewa. Ya jima anan tsugunne kafin ya iya mikewa yana komawa kan kujerar, jakar shi da take gefe ya dauka yana dubawa, ba shi da sigari ko daya, ya zuke ta tas kuma bai samu damar siyan wata ba. Yana bukatar wani abu da zai dan nutsar da shi. Cikin magungunan Bilal da aka siyo ya duba, tunda duk yasan su, akwai sedative a cikin su kuwa. Budewa yayi yana ballar guda shida ya dauki ruwan da su Abdul suka kawo ya fasa ya shanye. Sauran maganin ya saka a cikin jakar shi, da safe yaje ya siyo wani ya yi replacing da wanda ya dauka din.

Badan yana jin bacci ba, ya dai dora kan shine a jikin gadon Bilal din dan yadan huta. Wayar shima a gefe ya ajiye. Yana son Layla ta huta, a lokaci daya kuma yana son ta kasa samun baccin dan ta kira shi ya kara jin muryarta, tunda ba zai iya kiranta ba gara yaji muryarta. Baisan iya lokacin daya dauka a haka ba, amman lokaci zuwa lokaci yakan tashi ya dora hannun shi a kirjin Bilal din yaji ko zuciyar shi na bugawa, sannan kuma ya kara duba wayar shi ko Layla ta kira baiji ba. Kan kunnen shi aka kira sallar asuba, kan shi yake ji yayi nauyi kamar an dora mishi dutse saboda kwanaki biyu kenan rabon shi da samun bacci, sosai ya so ya tambayi Bappa yanda ya yi ya samu bacci, saboda magani guda daya yaga ya sha, kuma bacci ya yi har asuba.

Amman ya adana abinne a bayan zuciyar shi, duk idan ya samu wata dama zai san yanda zaiyi ya tambayi Bappa. Ko a asibiti wajen karbar magani bai taba cin karo da wani ba, Bappa ne mutum na farko da ya gani akan Anti-depressant, duk da yasan akwai dubban mutane da matsalar depression, shi din dai ya fara cin karo da shi. Da tunani barkatai a kan shi ya daura alwalar asuba, da kyar ya iya tattara natsuwa ya kabbara sallah.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×