Skip to content
Part 12 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Kan shi ciwo yake kamar zai rabe gida biyu. Dan bai iya takawa gida ba, sai da ya hau mashin. Da yake ba surutu yake son yi ba, canjin dari da ya baiwa mai mashin dinma da hannu yayi mishi alama daya tafi.

“Allah yasa kar in ga kowa, Allah yasa kar kowa ya ganni.”

Rayyan ya furta a cikin kan shi. Bayason mutane, baya kuma son ‘yan cikin gidan da suke haya fiye da sauran mutane, saboda suna saka shi yanayin magana a lokuttan da ko kadan bayason yi. Gashi yanzun Bilal yace ya dinga yiwa mutane murmushi idan sun mishi magana, baisan ya zai fara ba, motsa labban shi kawai yakeyi wasu lokuttan, tunda bayajin yin fara’a sam-sam. Ya gaisa dasu, baisan kirkin me Bilal yake so ya dinga musu ba.

“Ko rashin lafiya ta kamaka ba fata nake ba, su dinne mutanen farko da zasu taimaka maka tunda kuna gida, kasan abubuwan nan, kasan hakkin makota Hamma.”

Bilal din ya fada mishi.

“Bana son su.”

Shine amsar daya baiwa Bilal din.

“Su ma na tabbata ba son ka sukeyi ba. Ka dinga murmushi dan Allah in zaka gaisa da mutane, ka dan saki fuska ba kamar an maka dole ba.”

Bilal saiya dinga mishi magana kamar baisan dolen akayi mishi yake gaisawa da su ba. Hakkin musulunci kawai yake saukewa. Kamar barawo haka yake sanda wajen shiga gidan, sam baya so wani ya gan shi. Kusan da gudu ya karasa dakin su yana daga labulen ya shiga da sauri.

“Subhanallah…”

Bilal da yake zaune ya bude kular abinci ya fadi, dan sosai Rayyan din ya bashi tsoro.

“Assalamu alaikum…”

Cewar Rayyan, amsawa Bilal din yayi yana girgiza kai kawai. Taliya ce da miya sai soyayyen dankalin turawa, rabon su da dora tukunya a wuta harya manta, sai dai ko in sunyi marmarin shan shayi zasu dafa, amman Aysha na musu kokari matuka ta fannin abinci tunda tazo makarantar. Bilal baiyi mishi tayin abinci ba, tunda yasan sai yayi wanka, aikam ficewa daga dakin Rayyan yayi. Sai bayan yayo wankan ya dawo ya sake kayane ya zauna yana mayar da numfashi Bilal yace,

“Abinci fa?”

Kai Rayyan din ya girgiza mishi.

“Babu abinda kaci fa duk yau.”

Tunda tare suka fita, kuma yasan babu abinda Rayyan din zaici a waje banda biskit, idan ya samu kalar wanda yakeci din kenan.

“Zanci sai anjima.”

Rayyan ya furta yana kwanciya kan katifar da yake zaune a gefe, sai yaji wani dadi a ran shi daya kwanta din, kamar gajiyar daya kwaso ta dan sake shi. Wayar shi da Bilal ya janyone yaga yau din Alhamis, numfashi ya sauke.

“Azumi kakeyi ko?”

Ya tambaya

“Me yasa baka gajiya da surutu? Dan Allah ka kyaleni ni.”

Rayyan yayi maganar cikin alamar gajiya. Murmushi kawai Bilal din yayi. Bai taba gane azumin alhamis da litinin baya wuce Rayyan ba sai wannan dawowar da sukayi. Sai yake tuna ranakun da Rayyan din zai wuni baici komai ba, duk surutun da zai mishi. Sai sun dawo sallar Magriba tukunna, ko in yayo alwala ya shigo daki an kira, Bilal zai ga ya sha ruwa, ko yaci dabino. To bai taba kawo komai a ran shi ba, tunda Rayyan na da shan ruwa, kuma dabino kamar biskit ne a wajen shi, da wahala ka raba jakar shi da su, ko cikin kayan shi ka duba zaka samu.

Zurfin ciki irin na Rayyan baya gajiya da bashi mamaki, shima ranar alhamis din daya san azumi Rayyan yakeyi, alhamis din kuma daya tabbatar da abinda ya dade da sani, wajen Rayyan din yaje daga nasu bangaren, ya same shi a can karkashin wata bishiya, inda yake shimfida darduma ya zauna idan basu da darasi ba kuma yason komawa gida. Tunda wani lokaci ko baiyi niyya ba idan ya zauna cikin aji sai an sami wani mayen yayi mishi magana. Ko mintina biyar da isa baiyi ba sai ga Layla da tun daga nesa take fadin,

“Hamma Rayyann!”

Tana daga mishi hannu da fara’a a fuskarta, yana kallon Rayyan din ya lumshe idanuwan shi yana bude su a kan Layla da take karasowa, doguwar rigace ta atamfa a jikinta, dinkin da ake kira “Fitted gown” a turance, dan tabi jikinta sosai, sai mayafi data dan rataya a wuyanta, ga dauri ta kafa, fuskarta da kwalliya marar nauyi. Da wahala ta wuce ka baka sake kallonta ba, kafin kaga idanuwanta jikinta ne zai fara jan hankalinka, balle kuma idan ka tsayar da hankalinka akan fuskarta da take da wani irin kyau mai sanyi. Dan Bilal sai da yaji jikin shi ya dauki dumi, hakanne yasa shi sauke idanuwan shi daga kanta.

“Hamma…”

Ta sake furtawa tana dariya, kwana biyu bata gan shi ba, Bilal din kuwa kullum sai yaje ya dubata yana tambayar ko tana bukatar wani abu. Amman yau kwana biyu bata saka idanuwanta akan Rayyan ba, tunda suka zo makarantar ita take yawon nemo shi duk rana. Jiya da gangan taki zuwa inda yake, ko shi zai nemeta, amman shiru, yau ta kasa hakuri ne, sai da ta zagaya ta gefen da Rayyan yake tukunna ta kalli Bilal.

“Hamma ina wuni.”

Murmushi yayi mata.

“Layla…”

Ya furta yana yin shiru tunda hankalinta gabaki daya ya koma kan Rayyan.

“Jiya banganka ba.”

Ta fadi tana nazarin fuskar shi, shiru yayi ya kyaleta, baisan ko a satikan nan da tazo Zaria ta fahimci yanda yake matuqar sonta a kusa da shi bane, shisa jiya ta hana mishi ganinta. Kwana yayi yana juyi duniyar ta hade mishi waje daya. Ya gwada kiran wayarta yafi sau ashirin yana fasawa, saboda baisan me zaice mata ba, ba shida wani dalili da zaiyi amfani da shi. Shisa ya hakura. Yau da safe harya nufi hanyar department dinsu sai ya dawo kuma. Shine yanzun take ce mishi jiya bata gan shi ba, kamar bata san inda yake ba idan ta tashi ganin na shi.

“Hamma…”

Ta kira ganin da tayi na cewa yau miskilancin yake ji fiye da ko yaushe, zama tayi gab da shi bata damu da yanda rabin jikinta a kasa yake ba, rike Rayyan ko in hango shi tayi ta rungume shi bai taba damunta ba, hankalinta sam bai taba gaya mata cewar shi din ba muharramin ta bane ba, saboda bata dora abin akan mizanin addini, al’ada kuwa ba damun Layla tayi ba sam. Yanzun ma kanta ta kwantar akan kafadar Rayyan duk da tasan zai iya kwadarta bai hanata ba.

“Hamma…”

Ta furta da wani yanayi a muryarta, tayi kewar shi, jiya kawai da bata gan shi ba kewar shi take ji har cikin ranta. Rayyan bai tsammaci zata kwanta mishi a kafada ba duk da ta zauna kusa da shi, wani irin tsalle zuciyar shi tayi kamar zata fito waje saboda wani irin yanayi da yaji ya tsirga mishi, tureta yayi tana shirin dawowa ya matsa da sauri.

“Azumi nake Layla.”

Yai maganar yana mikewa tsaye gabaki daya, turo labbanta tayi. Shi kuwa Rayyan numfashi yake mayarwa, tun rannan yake tsintar kan shi a wannan yanayin duk idan jikin su ya hadu waje daya. Bilal kallon su yakeyi, zuciyar shi kamar zata fado kasa, idan Rayyan baya kallon Layla da wata fuska data wuce yan uwantaka ya tabbatar ba zai tunanin azumin shi ba dan ta kwanta a jikin shi, tunda tanayi lokutta da dama, bai taba damuwa ba, karshen abinda zaiyi shine ya kamata ya bambare yana fadin.

“Mayya ce ke? Duk wajen nan sai kin hadu da jikina? Me yake damun ki?”

Ita yake fadawa kalaman, amman Bilal sukeyi wa zafi, musamman idan yaga Laylan ta sake komawa ta mannewa Rayyan din duk da zafin kalaman shi da suke shimfide a idanuwanta. Ya rasa yanda zaiyi da su, ya kuma rasa ta ina zai fara hanasu wannan rike-riken junan da sukeyi. Yana kallo Layla ta mike itama tana shirin tafiya.

“Ina zaki je?”

Rayyan ya bukata yana tsareta da idanuwa.

“Ina da lecture, kawai zan ganka ne daman.”

Kai ya jinjina, farar riga ce kal a jikin shi da wandon jeans, saiya dora jacket a sama, ko maballan bai balle ba, kawai ya dora ne, taku hudu yayi yana karasawa inda Layla take tsaye, mayafin da yake wuyanta yaja yana daga shi, wani dan ziriri ne, kai kawai Rayyan ya girgiza. Shi baiga amfanin mayafin ba tunda babu abinda ya rufe, bayason yanda maza suke kallonta duk idan ta wuce, wancen satin da yake wando ta saka saita dora kimono a kai, duk da haka sai da yace wa wani dan ajin su.

“Ko zaka dauke ta hoto ne?”

Ganin irin kallon da yake bin Laylan da shi bayan ta wuce, murmushi kawai gayen yayi yana barin wajen. Kawai bayaso wasu maza na kallon ta, shisa ya bi bayanta, ya taba ganinta da rigar kuma yaga da madauri baisan me yasa bata saka ba. Hannunta ya kama ranar.

“Ina madaurin rigar nan?”

Cike da rashin fahimta tace,

“Yana cikin jakata.”

Jakar ya karba da kanshi ya bude ya dauko, sannan ya mayar mata da jakar cikin hannunta. Da kan shi ya zagaya madaurin yana soka shi a mazaunin shi ya taho da shi ta gaba ya daure mata yanda ya taba ganin ta daure, saida ya rankwashi kanta daya gama yana sakata fadin.

“Wayyoo Hamma!”

Ta dafe wajen dan taji zafi sosai, kara kai mata rankwashi yayi ta kauce, idanuwanta cike taf da hawaye ta kama hanya. Dan sam Rayyan baya damuwa da mutanen da suke waje, bama ya damuwa da yanda saboda idanuwanta yanzun tana cikin ‘yan matan da aka sani a fadin makarantar cikin kankanin lokaci, ga turancinta da yake burge mutane. A ajinsu ma kowa so yakeyi yai kawance da ita, har maza suna mata magana, kawai dai ba kowa take kulawa ba, a matan ma baifi mutum biyu suke yawo tare ba, saboda ta kula duk sunfi kowa wayewa a cikin ajin, kuma daku nan su da juna babu nisa a hostel, floor daya suke, hawa na ukku. Suna ma zuwa wajenta a dakin su.

Jacket din da take jikin shi Rayyan ya cire. Sai da ya rankwasheta.

“Me nayi? Me nayi ni?”

Layla take tambayar shi kamar zata fashe da kuka, rigar ya zagaya yana kafa mata idanuwa,  hannunta ta zira a ciki, tana saka dayan ma, ya gyara mata zaman rigar data sauka tana rufe bayanta sosai, maballi daya ya kama yana ballewa, bude baki tayi zatayi magana ya katseta da fadin,

“Bakin ki zan fasa in kikayi mun surutu…wuce ki bani waje ni.”

Wucewar tayi kuwa, kafin ta juyo tana kallon Bilal da yake zaune yana kallon ikon Allah.

“Hamma sai anjima.”

Kai ya iya daga mata, yana kishin ganinta a haka, bai taba magana a kai ba, bai taba kokarin hanata shigar da takeyi ba, a zuciyar shine bayason abin, amman Rayyan yayi wani abu a kai, a gaban idanuwan shi ya nuna mishi dalilin da yasa idan yana waje Layla bata ganin kowa sai shi. Baisan me yake ji a ran shi ba, ranar kuma da suka koma gida ya manta yake mishi tayin abinci kai ya girgiza yana amsawa da,

“Zanci anjima.”

Sai lokacin Bilal din ya tuna.

“Kana azumi fa ko?”

Kallon shi Rayyan din yayi.

“Ni na fada maka?”

Kai kawai ya girgiza mishi, tun ranar kuma yana kula da shi a ranakun litinin da alhamis, azumi baya wuce shi. Ba dai yason kowa yasani ne tunda badan wani yakeyi ba. Har mamakin mutanen da kamar jira suke ayi musu tayin abinci su sanar cewa suna azumi ne, kamar dan wani suke ibadar. Abinda kakeyi dan Allah, a haka sai ladan yayi tafiya batare da sanin ka ba, idan har ka tsarkake niyyarka, ya kamata ibadunka da ba farilla ba su zamana tsakanin ka da wanda kakeyi domin shi. Abincin Bilal ya karasa cinyewa yana mikewa ya dauko ruwa ya sha hadi dayin hamdala.

*****

Hanjin shi har daurewa yakeyi sanda suka dawo daga sallar Magriba. Gashi baisan abinda zaici ba. Ruwan zafi kawai ya dora a tukunya da nufin ya sha shayi, baiga Bilal ya dauki kulolin Aysha ba sanda zai fita, balle yace watakila in zai dawo zai taho musu da abinci. Baiso a dame shi shisa yana shiga yaja labule ta ciki ya tura kofar dakin, ko babu wuta gara yayi fifita da wani ya dago labule neman Bilal ya saka shi yin maganar da bai shirya ba, balle kuma yau yan nepa suna jin mutunci, tunda suka dawo akwai.

Ya juye ruwan zafi a kofi kenan ya saka Lipton yaji ana Kwankwasawa, karamin tsaki yaja yana yin shiru, idan aka gaji za’a tafi, yasan idan Bilal ne zai tura dakin tunda yasan yana ciki. Sake Kwankwasawa akayi, ya kara jan wani tsakin. A fusace ya mike tsaye yana bude kofar dakin, ga mamakin shi Layla ya gani tsaye sai maida numfashi takeyi, ta rungumo wani kwando da kuloli a ciki, kamar zatayi kuka tace

“Hamma ka amsa, hannuna zai karye.”

Tsautsayine ya sa ta saka riga da siket, da zata hau mashin har kofar gidan su Rayyan. Keken da ta samu kuma yaki shiga da ita lungun. Har ca tayi ta kara mishi kudi saboda kwandon data dauko amman yakiya. Haka ta tako tana tafiya tana kwashe mishi albarka saboda nishin da take dirkawa, ga kwandon hannu daya sai cirewa yakeyi idan ta rike, sai rungume shi tayi. A jigace ta isa gidan su Rayyan din, hannuwanta duk sunyi sanyi.

“Idan ba zaka amsa ba ka matsa daga kofar.”

Tayi maganar cikin tsiwa ganin Rayyan din yana tsaye yana kallonta. Hannun shi daya daga yasata tunanin kwandon zai karba, tallafe mata kai yayi

“Rashin kunya!”

Ya furta yana matsawa, ba zai karba ba tunda tayi mishi surutu, karasawa tayi cikin dakin tana ajiyewa a kasa, inda ya tashi ta zauna tana mayar da numfashi

“Banfa samu mashin har gidan nan ba, akan hanya napep ta ajiyeni, da kafata na shigo wajen nan…”

Dakin Rayyan ya bude saboda yanda zuciyar shi take dokawa ba zai rufe daki daga ita sai shi a ciki ba. Ya rasa lokacin da ganinta ya fara hargitsa tunanin shi har haka, kuma bai saka idanuwan shi cikin nata ba, ya koyi kallon har fuskarta batare da idanuwan shi sun shiga cikin nata ba.

“In da na tashi nan zaki zauna?”

Ya bukata yana karasawa wajen ya rankwafa, hannunta ya kama ya fisga yana dagata.

“Hamma dan Allah, wallahi nagaji, nagaji ni.”

Hannun ya sake rikewa sosai.

“Da daddare kika biyo hanya?”

Duk da ko fita kayi yanzun din za kaita cin karo da mutane, unguwar tasu dalibai sunfi yawa, dare sai kaga kamar rana ne, amman wani abu a zuciyar shi baison yanda ta fito da magriba haka.

“Abinci zan kawo maka, ba kana azumi ba? Dan Allah ka sakeni.”

Ta karasa muryarta na rawa, tun azahar yau ta gama darasinta, tana komawa hostel ta fara aikin yi mishi girkin nan saboda ta siyo kifine sai tayi mishi sauce ta dafa wake da shinkafa. Anisa da suke daki daya taso tayata, tunda wani lokaci har girki sukan hada, tace karta damu zatayi in yaso sai Anisa din tayi wanke-wanke. Ba tsafta bace bata da ita, kawai halin jujun Rayyan ta sani, zai iya tambaya idan ita kadai tayi girkin, kuma ba zata iya kallon shi tayi karya ba, yana ganeta, ta sha gwadawa bakinta yanayin jinni.

“Karya ne.”

Yake fadi a duk lokuttan yana kara kai mata wani dukan, sakar mata hannu yayi yana komawa wajen shi ya zauna. Tsaye tayi a wajen tana murza hannunta, shikuma ita yake jira ta zuba mishi, hakan ta kula da shi, bata dauko faranti ba, a dakin ta samu da cokali, sai da ta dauki ruwan leda tana fita wajen dakin ta daurayo su sannan ta dawo.

“Kazama, a bakin kofa kika zubar mun da ruwa ko?”

Bata kula shi ba, turo labbanta tayi kawai, sai lokacin ta cire hijabin da yake jikinta tana ajiyewa kan teburin da yake cikin dakin. Bai taba mata maganar kayan da take sakawa ba, amman tasan bayaso, har wata zuciyar na fada mata kishi yake shisa, ba karamin dadi take ji ba kuma. Jacket din shi guda hudune a wajenta yanzun, kuma duk idan ta saka kayan da baisone yake bata. Kamar yana yawo da jacket dinne yanzun ko zai ganta da kayan da bayaso, dan kwanaki a jakar shi ya fito da jacket din. Kuma Rayyan sam bai damu da yawan mutanen da suke waje ba idan ya tashi yi mata abu, kamar ma baya ganin su haka yakeyi.

Abincin ta zuba mishi tana neman waje ta zauna, ya fara ci yaga yanda take bin duk cokalin da zai kai a bakin shi da kallo, kai ya girgiza yana ajiye farantin da ya daga, ya gyara zaman shi sosai.

“Me yasa zakiyi girki ba zakici ba?”

Tasan baya tambayeta dan ta bashi amsa bane, shisa tayi shiru, ita batama san tanajin yunwa haka ba sai yanzun da taga yana cin abincin. Cokali ya dauka yana mika mata, zata saka cikin abincin ya dakatar da ita da fadin;

“An taba marin ki cikin ido? Ba zaki tashi ki wanko shi ba, kazama kawai.”

Mikewa tayi tana daukar sauran ruwan da ta ajiye a gefe ta daurayo cokalin ta dawo. Tare suka cinye abincin tana kara zuba musu wani. Abin bai mata wani iri ba, zuwanta makarantar wannan ne karo na wajen biyar da suke cin abinci tare, na farkon ta kusan raba dare data juya yanayin su tare take hangowa sai wani murmushi ya kwace mata da ba zata ce ga dalilin shi ba. Da yake yana cin abinci da sauri, kafin taci guda daya yaci uku, baisan dalilin da zaisa ka tsaya yanga in zakaci abinci ba. Da kanshi ya dauki kular yana kara mata ya zuba mata miya a kai, abincin da yawa tayi.

Yasan Bilal in dai ba wani abu yaci a wajen Aysha ba, zaici, in baici ba da safe sai su dumama suci abinsu. Layla na karasawa, ruwa kawai ta sha, batama gama ba Rayyan ya mike.

“Tashi muje.”

Kallon shi tayi da tashin hankali a fuskata.

“Ina zamu je? Hamma kabari abinci ya tsarga mun, yanzun fa nagama ci.”

Kallon da yayi matane yasata mikewa ta dauki hijabinta tana buga kafarta, duka Rayyan ya kaimata tana kaucewa dan ta gan shi.

“Zaki wuce ko saina kwada miki mari?”

Ya bukata, fita tayi daga dakin, shima takalmi ya zira a kafafuwan shi yana fita, baisan ko Bilal ya dauki mukulli ba, shisa ya janyo kofar kawai, gidan su ba’a taba yin sata ba. Kusan ko yaushe Bilal kan yabi halayyar yan gidan. Ko baka rufe daki ba, wani zai janyo maka. Haka sukeyi, in shanya kayi hadari ya hado ma za’a kwashe maka, inka dawo a kawo maka. Suna da kirki matuqa. Shisa bayajin dadin yanda Rayyan yake hade musu girar sama da ta kasa. Shiya fara yin gaba Layla na biye da shi, cikinta take ji har wuya, inda tasan ba zai bari abinci ya natsa mata ba, da bata cika cikinta haka ba.

Ganin har sun kai titi suna tsallakawa yasa ta fadin,

“In mukai nisa fa ba zamu sama abin hawa ba.”

Dan juyawa Rayyan yayi ya kalleta, hannunta yake shirin kamawa ta kauce.

“A kafa? Hamma a kafa? Tafdin… In dai rakani zakayi nagode…amman ni wal…”

Da sauri yace;

“Karma ki rantse, zakiyi azumi yarinya… Ki zo mu tafi.”

A kafa yake jin tafiya, saboda yana son dan takawa tunda ya cika cikin shi, kuma ko ba haka ba, a ranshi yana jin yin tafiyar tare da ita, ko tana so ko bata so ba matsalar shi bane ba, duk yau ganinta ne yadan nutsar da shi, amman da wani kunci ya wuni, wasu ranakun idan yana azumin yakan ji shi wasai, har Qur’ani yakan dauka ya karanta. Amman wasu ranakun bawai bayaso ya dauka bane, kawai wata irin kasala kan rufe shi duk idan ya yunkura sai ya kasa, haka zai hakura yaita juyi, inya gaji ya kunna sigari ya bukama cikin shi.

“Ni dan Allah kabarni, wallahi nagaji, kuma na saka dogon takalmi.”

Layla ta furta tana shirin yin kuka, tun kafin ta fito take murnar zuwa ta gan shi, amman yanzun harya isheta, ta ina zata fara shafawa a kafa ana zaune lafiya. Zagaye suka fara.

“Layla…”

Ya furta cike da kashedin da yasata tsayawa waje daya, yasan ko bata zagin shi a ranta, tana tunanin hanyoyin da zata jibge shi idan ta samu dama ne saboda kallon da takeyi mishi, hasken wutar lantarki ya sake ma idanuwanta launi, sai da gabanshi ya fadi daya kalle su, musamman da irin kallon da take watsa mishi, hannunta ya damqa yana janta tana tirjewa kamar karamar yarinya. Bai damu ba, cigaba yayi da janta har suka karasa wani shago, yana rike da hannunta har lokacin ya siya silipas, babu karamar lamba, dan koshi sun mishi yawa, sakinta yayi ya fito dasu daga leda yana ajiye mata.

“Ni ce zan saka wannan?”

Ta bukata tana ware mishi ido, kamar duk ranar bataga wani abu daya daga mata hankali irin shi ba, takalman kafafuwan shi dana fata ne yan zire ya cire yana saka silipas din.

“Hamma…”

Cikin ido ya kalleta.

“Kina gwada hakurina Layla, kin sani ko? Wallahi ba zan sake magana dake ba.”

Dogayen takalman kafarta ta cire, ta saka nashin, da kanshi ya kwashe nata ya saka a ledar daya zaro silipas din yana bata, karba tayi ta rike baqar ledar. Hannunta ya sake kamawa suna tafiya. A hankali har suka fara hango makaranta, ba hira sukeyi ba sam balle tace tafiyar tana mata dadi, amman yanayin Rayyan din ya nuna yana cikin nishadi. Musamman yanda ya kalleta yaga tana ta turo baki.

“Ki maida hankali, kilan bakin ki ya rigaki zuwa hostel.”

Ya furta yana kara sauri, yana kallon yanda take kokarin kamo shi tana kara turo baki, sai da tasa murmushi ya kusan kwace mishi, tunda dai babu yanda zatayi da shi. Har kusan kofar hostel din ya karasa da ita, inda sukaci karo da su Bilal su kuma, Aysha zata rako shi, sunyi tsaye suna hira.

“Hamma!”

Ta kwala mishi kira tana murmushi, kallon su Bilal yakeyi da mamaki suna karasowa inda suke, hannun Layla da yake cikin na Rayyan ya kalla, bai amsa Layla ba saboda wani sanannen abu da yaji ya mishi tsaye a makoshi. Kirjin shi harya fara zafin da yakan mishi duk idan ya gansu tare haka.

“Ayshan Hamma”

Layla ta fadi tana mata murmushi.

“Layla…”

Aisha tace cikin gaisuwa, tana kallon Rayyan.

“Ina wuni”

So yakeyi yayi mata murmushi koya ne, amman sam bayajin yi.

“Lafiya kalau. Sannu da kokari, mun gode.”

Ya fadi, yana saka Bilal kallon shi cike da mamaki, Layla ma mamakin takeyi, shi kuma tun rannan yake so yayi mata godiya saboda tana ma Bilal kirki. Tun satin daya wuce yake hada kalaman da zai fada mata in sun hadu, sai yaune ya samu ya fada, baisan me yasa su Bilal suke kallon shi kamar sunga wani abu a fuskar shi.

“Bakomai”

Aisha ta furta a kunyace, Layla zatayi magana Rayyan yaja hannunta sunayin gaba, ta cika surutu, baiga abinda zata fada ba kuma, bayan an gaisa. Tsayawa yayi yana sakinta hadi da fadin.

“Tam sai da safe.”

Kafin ta amsa ya juya, inda su Bilal suke tsaye ya karasa yana dan matsawa gefe hadi da jiran Bilal din, shima hakan yagani yayi sallama da Aisha din yana samun Rayyan. A hanya suka tsaya sunayin sallar isha’i sannan suka nufi gida. Sai da Rayyan ya tsaya wani shago ya siyi sigari.

“Ba zaka daina sha ba ko Hamma?”

Bilal yai tambayar da wani yanayi a muryar shi, sai da Rayyan ya zari kara daya ya kunna yana zuqa ya fitar da hayakin tukunna yace,

“Me yasa kake magana a kai?”

Tunda yasan ba dainawa zaiyi ba, shima ya kamata yabar asarar bakin shi. Ba so ya daina bane bayayi, ko yanzun kamar dole ake mishi haka yake zuqar sigarin, kafin su karasa gida yasha kara hudu, yana shirin daukar ta biyar ne Bilal ya fisge kwalin daga hannun shi yana sakawa a aljihu, Rayyan baice mishi komai ba, haka da suka shiga daki ma baice mishi komai ba. Asalima kan tebir ya zauna ya fara rage tarin assignment din da yake gaban shi, yana kallon Bilal ma yayi nashi kafin ya fara danne-dannen waya da bazai wuce hira yake da Aisha ba. Nan Bilal yayi bacci yabar shi, kwayoyin shi ya sha ganin Bilal din yayi bacci, amman har karfe uku da rabi ko gyangyadi, sai wajen hudu yadan kwanta, yasan ko da babu sallar asuba, da wahala baccin ya wuce awa daya. Rufe idanuwan shi yayi, baya ganin komai sai hotunan Layla kala-kala a cikin kan shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.9 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 11Martabarmu 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×