Skip to content
Part 8 of 34 in the Series Martabarmu by Lubna Sufyan

Da wani yace mishi zai iya shekara daya a wani gari daban, nesa da Bilal, nesa da Layla da bai taba tunanin kewarta zata danne shi haka ba zai karyata. Dare da yawa ya sha farkawa ko shan ruwa da yakan yawan yi ko kuma wani abu daban ya tsinci kan shi da kasa komawa bacci, saboda kawai yana tunanin Layla. Yana tunanin ko tana kewar shi ko batayi, ranar da zai tafi bata neme shi ba sam, yafi mintina talatin a tsaye kofar daki yaki fitowa yana jira ko zata shigo tayi mishi sallama, amman shiru, sai da ya taka ya sameta har bangaren Mami, duk da bai shiga ba a bakin kofa ya tsaya yana kwala mata kira, ko da ta fito sai ya rasa abinda zaice mata.

Lokutta da dama yakan zabi shiru saboda kalaman shi basu da yawa, baisan yanda zai fadi abinda yakeji ba, baisan me ya kamata yace mata ba, shisa ya zabi.

“Tafiya zan yi…”

Kai ta dan daga mishi.

“Allah ya tsare… Zaka dinga zuwa kaman Hamma Haris?”

Dan daga mata kafadu yayi, yana rasa amsar da ta dace ya bata, abubuwa ne masu tarin yawa a ran shi, ya motsa labban shi kenan ta dago idanuwanta tana saka zuciyar shi dokawa. Ya kasa sabawa da kalar su, kamar yanda ko kan hanya yaga giccin mage sai yayi da gaske ne baya zurawa da gudu. Sanin da wahala ya kara cewa komai ya sata yin murmushi.

“Allah ya saukeka lafiya. Banda fada da mutane.”

Baisan murmushi ya kwace mishi ba sai da ta ce,

“Inalillahi… Hamma…murmushi kayi ko wani abune ya fadamun a ido.”

Kai kawai ya girgiza wannan karin har zuciyar shi da yake ji cike da wani irin duhu a lokutta da dama yaji murmushin.

“Kin rainani ko?”

Dariya ta yi mai sauti.

“Ni na isa.”

Numfashi ya sauke mai nauyin gaske, yana kokarin kallon cikin idanuwan ta wannan karin. Ya rasa kalaman da zaiyi amfani da su wajen misalta asalin abinda yake ji. Dakyar ya iya jan kafafuwan shi ya juya yana tafiya. Sanda ya sake waiwayowa sai yaga bata nan. Abin ya mishi wani iri sosai. Yaso ace ta tsaya, yaso ace ta jira shi harya bace mata, amman batayi hakan ba. Bayan tafiyar shi yanayin yana yawan fado mishi a rai, musamman idan yayi kewarta.

A cikin shekara dayan, kusan idan ba karatu bane yayi mishi zafi, duk watan duniya yana hanyar Kano, kawai ya kula da abu dayane a shekarar game da Ayya. Batason yawan zuwan da yakeyi, da ta ganshi zai ga tsoro a cikin idanuwan ta, har magana tayi mishi wani zuwa.

“Rayyan ba zaka natsu waje daya ba ko? Taya zaka fahimci karatu kullum kana hanya?”

Cikin idanuwa ya kalleta, yaso ya fahimci dalilin canzawarta lokaci daya amman ya kasa, yawan magana na saka shi ciwon baki wasu lokuttan, kuma idan maganar tai tsayi zaiji ta fara hau mishi kai, shisa baice mata komai ba, har tayi mitar ta gama. Sai da ya mikene tukunna ya ce,

“Zan gaisheki ne daman.”

Yana juyawa

“Allah ya shiryeka…”

Shine kalamanta da yaji kafin ya fice daga dakin. Bai fasa zuwa ba, gajiyar da yayi jiya ita ta hana mishi tafiya gida, da ciwon kai na gaske ya fito daga wajen jarabawar shi ta kare shekarar farko a jami’ar. Amman a daren ya hada kayan shi yana ajiyewa, yaji dadin hakan dan yana dawowa masallaci wanka ya shiga. Lokacin da yaje babu yanda Haris baiyi dashi ba da su zauna tare a gida daya, amman yaki. Shi sun kama gidane anan Layin Kasuwa. Da Rayyan ya tashi sai ya nema a Rufasi.

Gidan nasu daki shidda ne, guda daya Abbu ya biya mishi shi kadai, sanin halin shi. Banda sallama babu wani abu da yake hada shi da wani a cikin gidan, sau dayane da akace wani Emmanuel bashi da lafiya za’aje duba shi ya bisu. Acan ya barosu saboda baisan ya zai zauna ayi hirar da suke tayi da shi ba. Sunayen su ma bai sani ba, Emmanuel din saida yaje asibitin ya gane shi. Lokacin da yaje ya sami da yawansu a gidan, suke fada mishi yanda suke tsara shara da wankin bandaki, idan wannan yayi wannan ma sai yayi.

Sai dai shi baya jira, shiga biyar idan zaiyi a rana, komin wankin da akayiwa bandakin saiya kara wankewa, ya sha jin suna gulmar shi.

“Dan sarkin masu tsaftar Rufasi da kewaye.”

Daya cikin su ya taba gwada tsokanar shi.

“Gaye sarkin tsafta…”

Kallon “Yaushe muka fara wasan nan” Rayyan yayi mishi ya wuce yana barin shi a wajen batare daya samu damar karashe zancen ba, babu wanda ya sake gwada tsokanar shi a cikin su kaf, koya zakayi mishi fara’a fuskar shi bata canzawa, kullum fuskar shi a hade take, ga cikar gashin girar da yake da ita sai yasa ake kara ganin abinda turawa suke kira da “Frown” bayyane a fuskar tashi. Ko a aji an shaida Rayyan, yakan amsa tambaya idan yana cikin yanayin ko kuma wata rana yayiwa Malami. Amman idan ba kai ka fara mishi magana ba, ko kusa da shi ka zauna zaiyi tamkar bai ganka ba.

Na shi miskilancin daban ne, babu wanda zaice ya taba ganin shi yana yawo da wani, shi kadai yake al’amuran shi a cikin makaranta, duk kuwa yanda wasu a aji suke son kulla abota dashi, daga gaisuwa sai kaci sa’a zaka sake fito da magana daga bakin shi. Ko fita zaiyi daga gida wani lokacin a ranshi yake furta,

“Allah yasa kar wanda yai mun magana yau. Bansan me yasa mutane basa gajiya da magana ba.”

Shisa yau ma yana gama shirin shi tsaf, ya saka wandon jeans, takalmin sneakers ne a kafar shi, sai riga baka da ta amshi farar fatar shi, sai kamshin yakeyi saboda ya yarda da turare, kuma daya fito wanka sai da ya busa sigarin shi. Bilal kance yana warin hayakinta duk idan ya sha, shisa yanzun yafi da ta’ammali da turare, kawai ya tsinci kan shi da kara shinshina jikin shi bayan ya gama shirin, jakar shi daya shirya kaya a ciki ya dauka yana fitowa, mukulli yasa ya kulle dakin, ya saka shi a aljihu kenan kamar daga sama yaji an ce,

“Rayyan ba dai tafiya ba da sassafen nan, kana kewar gida ne da yawa haka?”

Juyawa yayi yaga wanne mai karfin halinne, ya tsani magana da mutane, yafi tsanar magana da mutanen da baisani ba, idan kana so ka bata mishi rai kayi mishi magana da sassafe haka

“Cikin abubuwan da aka haramta ya kamata ace akwai magana da sassafe.”

Ya kan fadima kan shi, kallon gayen yayi, Saminu yaji ana kiran shi, ya rike sunan ne saboda surutun shi, surutun da yasa gayen sam bai mishi ba. Idan yana daki a kwance da daddare muryar shi tafi ta kowa tashi. Lokutta da dama yasha lumshe idanuwan shi ya hasaso ya shiga dakin su Saminu da yake kusa da nashi ya kwada mishi mari.

“Kamar ana korar ka?”

Saminu ya sake fadi yana washe ma Rayyan din hakora kamar ya san shi. Hannu Rayyan ya mika mishi sunayin sallama, yanajin wani yarr a jikin shi saboda hannun Saminun da yake da lema alamun ya taba ruwa, kilan ma baki ya kuskure ya sakada yatsu a ciki yana wankowa. Yatsina fuska Rayyan yayi cike da kyama, yana da bala’in tsantsani, shisa ko a cikin makarantar bako ina yake cin abinci ba, yafi son soyayye kuma, ko ya siyi lemo da biskit yafi mishi natsuwa, akan ya siyi abu yaci zuciyar shi taita tashi a banza da wofi.

Yanzun ma raba Saminu yayi yana ficewa daga gidan. Nufin shi ya fita harya samu acaba da zai kaishi tasha, sai ya tsinci kan shi da takawa yana cigaba da tafiya, kafin wani lokaci ya gan shi kofar gidan su Haris, bayason yaji kamar bai kyauta ba, duk da yanda kasan cuta haka yake avoiding din Haris a cikin makaranta, yana iya hango shi daga nesa ya sake hanya. Duk da Haris din yaki fushi, har aji yakan same shi idan ya kwana biyu bai ganshi ba, wata rana kuma har gidan yakan je da yar kular shi ya kai mishi abinci.

“Ni na dafa, duk me zan kawo maka ni na dafa…”

Haris din ya fadi ranar farko daya kawo mishi abinci, baici ba saida ya tafi, ya kuma ji dadin wake da shinkafar da miyar kifi. Dan ya kwana biyu baici abinci ba a lokacin, to kusan saiya zamana idan yaci abinci ba soyayyen abu ba, to Haris ne ya kawo mishi, ko nashi rishon mai amfani da kalanzir dana wuta bai taba kunnawa ba. Ba ruwan zafi yake wanka dashi ba komin sanyin da akeyi kuwa, ba kuma girki ya iya ba balle ya dafa. Jiyan Haris ya same shi har aji yayi mishi fatan nasara da cewa.

“Naga yau zaku gama jarabawa… Nikam sai ranar laraba in shaa Allah.”

Baisan ya akayi bakin shi yayi nauyin cewa Haris zai tafi gida ba yau, daya huta yanzun. Gashi tsaye a kofar gidan yana tunanin shiga, bama shigar bace ke mishi wahala, abinda zai fada din ne tashin hankalin shi. Yana nan tsaye yayi sa’a Haris ya fito, da mamaki yake kallon Rayyan, dan bai tsammace shi ba, bayan sun gaisa ne yake fadin,

“Sai kayi tsaye a bakin kofa? Da ban fito ba fa? Ka shigo.”

Kai Rayyan ya girgiza.

“Zan tafi gida ne, shine na biyo.”

Murmushi Haris yayi, yaji dadin biyowar kuwa. Dan mutane kanyi mamaki idan yace musu Rayyan din kanin shine, duk da akwai yanayi na kamanni da zai nuna cewa akwai alaka ta jini a tsakanin su, amman halayyarsu tayi hannun riga.

“Ka kyauta daka biyo, nagode da zumunci. Allah ya tsare hanya. Nima in shaa Allah ranar laraba dana fito daga exam zan taho gida.”

Kai kawai Rayyan din ya daga mishi yana juyawa. Jakar shi ya sakewa kafada saboda ta daman ta gaji, anan ya rataya tun fitowar shi. Daga gidan su Haris din kai tsaye titi ya fita yana samun mashin zuwa tasha. Kamar ya runtsa idanuwan shi ya bude su ya ganshi a gida haka yake ji, idan ba kwakwalwar shi ce take mishi karya ba, kamar zumudin zuwa gida yaji yanayi.

*****

Sam tunda Rayyan ya dawo hankalin ta yaki kwanciya. Baccin kirki ma bata samu tayi, gashi hutun yayi mata tsayi, daya tafi makaranta sai taji hankalinta ya kwanta sosai. Ko babu wani abu Rayyan din yayi nisa da gidan, yayi nisa da Mami da Layla. Bikin  Zubaida ma da za’ayi nan da wata biyu bai tsaya mata a rai kamar yanda take so taga Rayyan ya koma makaranta ba. Gashi yanzun yafi da yin nesa da ita, jiya badon Rukayya ba sai girkin da ta dora ya babbake, yanata qauri, sam a hanci ma bataji ba, tazo jikin window din dakin ta daga ciki ta labe tana leke.

Ba karya kunnuwanta sukayi mata ba, tabbas taji muryar Rayyan din yana kiran Layla. Shisa ta labe ko zata ga fitowar ta, taga alama idan ba jan ido ta nuna akayi karamin tashin hankalin da aka kwana biyu ba’ayi irin shi a gidan ba, to Layla ba zata kyale mata yaro ba.

“Shegiya mayya mai zubin yan ruwa. Yarinya baki tafasa ba kina kauri. Wai yar yarinyar nan harta san ta kashewa maza murya. Kai ni Maimuna naga ikon Allah.”

Ta furta ita kadai, dan sambatu shine abokinta tun da Rayyan din ya dawo, kusan kullum zaka ganta manne jikin window, tun yaran na magana har sun kyaleta. Huda takan aika idan bata makaranta tace taje ta dubo mata idan Rayyan yana nan, ko ta saka mata ido idan ta gansu da Layla tazo ta gaya mata, abinka da kuruciya randa ta gansu kuwa tun a gaban shi ta ce,

“Ayya tace dana ganka da Adda Layla inje in fada mata.”

Da gudunta kuwa ta karasa har dakin Ayya din, inda ko mintina biyu bata hada da shiga ba Rayyan din ya rufa mata baya, tana cikin rattafowa Ayya zance, sai da ya kamo hannunta ya juyo da ita sannan ya wanketa da maruka har biyu.

“Karyaki zanyi idan kika sake dibo gulmata kika kawo, kina jina, karyaki zanyi wallahi.”

Yake fadi yana girgiza Huda da take wani irin gigitaccen kuka da ba ita kadai ta rude ba, har Ayya da ta fisgeta, babu wanda Rayyan bai daka ba a gidan, daga Khalifa da sam baya shiga sabgar shi sai kuwa tace Huda, ita kadai ma take ganin yana dan yiwa fara’a wasu lokuttan. Amman ranar saboda ta kawo zancen Layla shisa yake shirin kurmantata.

“Ni zaka daka Rayyan, ba ita zaka daka ba. Ka dakeni saika nuna mun ka girma kafi karfina. Tunda ni na sakata…”

Ayya take fadi tanajin zuciyarta na wani irin zafi.

“Ayya…”

Rayyan ya kira ranshi a bala’in bace, saboda gani yake shi akayiwa laifi, sam bayason gulma, yaga alama kuma Ayya da kanta take so ta koyawa Huda

“Dan ubanka nace ni zaka daka, akan waccen shegiyar yarinyar ne kake neman nakasa kanwarka, kake kuma tsareni da ido”

Kai yasa yana ficewa daga dakin yabarta. Ranar yanda taga dare haka taga rana, washegari sai da tayi wa Bilal zancen

“Wai meye tsakanin Layla da Rayyan? Yarinyar nan duk sai ta lashe muku kurwa ko?”

Da yake kansu a hade yake, dariyar shi ya dinga mata, cikin salo ya canza maganar. Sai ta hakura ta kyale shi, to yanzun Huda da take sakawa ta gano mata me yake faruwa tsoron Rayyan takeyi, ko ta aiketa idanuwanta zasu tara hawaye.

“Hamma zai karyani Ayya… Allah zai dakeni.”

Dole ta kyaleta, sauran yaran ma babu wanda zaije tasani, idan ma sunje din dawowa zasuyi suce mata basu ga komai ba. Mami ta jima tana sakata kwanan zaune, yanzun kuma ta kawo mata alaqaqai tana sakata tuna satin amarcin Mami din da kalar bakin cikin data hadiya.

“Wallahi Maryama ke ba alkhairi bace a rayuwata.”

Ta fadi rannnan da takaici ya qumeta, harda kwallarta. Yanzun kam lissafinta yazo karshe, tunda dai gobe Rayyan din zai tarkata ya koma makaranta, itama ko na kwana talatin ne kafin fitina ta dawo dashi zata samu ta maida hankalinta kan maganar bikin Zubaida. Idan san samune ma Rayyan din yai zaman shi har sai lokacin bikin tukunna. Addu’ar da takeyi baji bagani shine Bilal ya samu gurbin karatu a jami’ar, idan suna tare da Rayyan din acan zaifi dadewa baizo gida ba.

Tana kara gayawa kanta harda rashin Bilal a kusa dashi yasa ya kasa zama waje daya. To Bilal din ya fada mata cewa sunayen farko ya fito babu nashi a ciki, idan Allah ya taimaka sai jeri na biyu da suke tsammani a cikin satin tukunna. Da yake sunyi hutun islamiyya duk suna gida ranar, yaran nata ne suka rage mata tunani, dan suna zaune sunata hira harda Bilal, sai dariya suke. Daga bakin kofa ma zaka iya jiyo rakadin su, Rayyan ya shiga da sallama, yana saka wani irin shiru biyo bayan amsa sallamar tashi da sukayi, kamar basu bane suke ta hira yan dakika da suka wuce.

Kamar yanda baisan taya zai fara hira dasu ba, haka suma basu san abinda ya kamata suyi a gaban shi ba. Duk kuwa tarin kaunar da suke mishi, kowa gudun yin kwakkwaran motsi yakeyi kar su bashi dalilin da zaisa ya juya, dan yana tsaye yaki karasawa.

“Ka shigo mana to, kayi tsaye kamar dan sanda.”

Cewar Bilal, yana saka har Zubaida bin shi da kallo, dan Bilal ne kadai yake da kwarin gwiwar yi ma Rayyan din magana haka, ita ma sai tayi sa’a yake gaishe da ita. Yana iya wucewa ta wuce, zata kuma yi karya idan tace hakan baya bakanta mata rai sosai. Tana shekararta ta karshe a jami’ar Bayero inda take karantar Mass Communication. Mijin da zata aura a makarantar suka hadu lokacin tana shekararta ta biyu, yanzun kuma yana aiki da gidan jaridar Rana. Dan kusan duk bangaren karatun su daya da ita, kawai shi din journalist ne. Wani lokacin har mamaki Zubaida takeyi na yanda ko kadan Rayyan bai damu da su ba.

Tasan kowa abin nacin ran shi, ba dai sa tattaunawa ne, aikam karasawa Rayyan din yayi ya zauna kan hannun kujerar da Bilal yake,  a hankali Bilal din yaci gaba da jansu da hira har kowa ya saki jiki, amman da ido Rayyan yake binsu, yau dai yayi kokari tunda har saida aka kira sallar Magriba tukunna duk suka tashi. Ayya taji dadin shigar tashi, ta manta ranar karshe daya zauna ya hada mintina sha biyar cikakku a cikin dakin nata. Duka abinda basu sani ba shine maganar da Bilal yayi mishi.

“Kai kasan ko na zauna ni bansan me zance ba, ku bakwa gajiya da surutu.”

Rayyan ya fada a takura.

“Ko bakace komai ba idan ka zauna Ayya zataji dadi, saboda Allah ko tausayinta bakaji? Uwa uwa ce (Batul Mamman) Rayyan. Ace sai dai Ayya tazo inda kake, kai ba zakaje ka gaisheta ba idan ba yunwa ce ta koraka ba… Babu wanda zai fada maka baka kyautawa, nima dana fada maka ba lallai ka saurara ba, tunda kai babu wanda ya isa ya saka a hanya.”

Bai amsa Bilal din ba harya fice daga dakin. Da rana ya aiki Layla ta siyo mishi batirin tocila din shi da yake amfani da ita a makaranta, yasan zai iya siya idan yaje, kawai yana son dalilin da zai ganta ne, tunda yasan washegari zai koma makaranta, duk ranar aiken rashin dalili yake kirkira yana mata, sanyinta ne yake mishi wani iri, kamar ba Layla ba yau, harar da takan watsa mishi duk idan tagaji ba taso ta fada mishi tana kuma tunanin baya ganinta yau babu.

Sosai ya dinga sakata kananun abubuwa amman sai yaganta da sanyi-sanyi, shisa da ta kawo mishi battery din ya ce,

“Menene? Me yake damun ki?”

Kallon shi tayi da idanuwanta, itama ba zatace ga asalin abinda yake damunta ba, kamar zatayi zazzabi take ji, ga wani irin ciwo da takeji kasan cikinta nayi, inya tsira mata har cikin bayanta da cinyoyinta da suka rike takeji.

“Kawai bana jin dadine.”

Ta furta a sanyaye,

“Shine baki fadamun ba?”

Cikin ido ta sake kallon shi, yanajin dadin ganin masifar da take cike da idanuwan nata

“Yanzun nake ganin Layla.”

Ya furta a ran shi.

“Idan na fada maka zai hanaka aikena ne?”

Numfashi ya sauke, a ranaku da ba yau ba zai bige bakinta, amman a kasan maganar da tayi yana ganin da gaske bata da lafiya.

“Kai me yake damun ka?”

Ta tambaya saboda yanda ya tattare girar shi yau ya wuce misali, da alama akwai abinda yake ran shi, kafadu yadan daga mata.

“‘Hamma…”

Ta kira a kagauce, inda yasan yanda takeji zai fada mata in yayi niyya koya sallameta taje ta kwanta.

“Ki barni ni dalla can. Bilal ne wai ina zama a dakin Ayya.”

Dariya tadan yi.

“To ka zauna mana, abune me kyau ai.”

Da alamun neman taimako ya kalleta wannan Karin.

“Labari sukeyi in sun zauna. Bansan me zance ba.”

Numfashi ta sauke.

“Ka zauna kawai, ko baka ce komai ba ka zauna.”

Dan jim yayi kafin ya jinjina kai a hankali.

“In tafi shikenan?”

Kallonta yayi, tayi rau-rau da idanuwa.

“Allah Hamma cikina na ciwo.”

Kallon nata dai yaci gaba dayi, a hankali ta dan daga kafarta da ta gaji da tsayuwa tana sake ajiyeta, ta daga dayar ma, yana kallon ta, so takeyi ta tafi.

“Hamma mana”

Layla ta sake fadi kamar zatayi kuka.

“Haka kawai duk inda nayi kina bina, yaune zaki dameni da kina son tafiya?”

Azabar ciwo ta fara damunta, da gaske yau batasan kalar ciwon nan daya addabeta ba. Ganin da yayi idanuwanta na tara hawaye yasa shi fadin.

“Ki kwanta in kinje, kowa ya aike ki kice nace ki kwanta. Idan na hadu dake saina dakeki.”

Juyawa tayi kawai ta fice. Bilal da Layla suka saka shi zuwa dakin Ayya ya zauna yau. Suna kuma dawowa sallar Magriba ba bai koma ba. Nan daki yayi zaman shi, har akayi isha’i ya sake fita, da suka dawo Bilal ne yaje ya dauko musu abinci a bangaren Ayya ya dawo, sukaci, zanen da Bilal din yaga yanayi yasa shi ficewa ya koma dakin Ayya, dan yasan ko maganar duniya zaiyi Bilal din bashi da lokacin shi. Sanda ya dawo ma kwanciya yayi yana barin shi kan takarda. Alamar bacci ma Rayyan bayaji, abinda yake kanshi yake son fitarwa, abinda yayi sati manne a kwakwalwar shi. Hoton Layla, ba wasu kaya bane a jikinta ranar, uniform din islamiyya ne da hijabin take ruwan kasa mai cizawa, tana tsaye nesa da gida kadan ita da Farida, da littafi a hannun Farida din da alama suna duba wani abune, gefen fuskarta kawai yagani, sai yayi mishi kyau sosai, yanayin ta a hakan, da ta kare mishi idanuwanta. Tun ranar hoton yake manne a cikin kanshi, kamar yana son ya fito da shi fili kafin ya bace, ya kyale shine da nufin idanuwanta su tarwatsa mishi hoton, sai dai a satin ta saka idanuwan shi cikin nata yafi a kirga, amman tana barin wajen sai hoton ya dawo mishi, shisa yau yake son fito da shi, yana da tabbacin ba zai gamu a ranar ba, amman zak fito da taswirar, sai yayi sauran aikin ko idan ya koma ne. Ko ba komai zai sami abinyi kafin kewarta ta danne shi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Martabarmu 7Martabarmu 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×