Skip to content

Martabarmu | Babi Na Tara

4
(5)

<< Previous

Shi sam baiga dalilin da Haris zaice tare zasu koma makaranta ba. Ya fahimci zumudin da Bilal yakeyi, duk da baiji shi ba sam a tafiyar farko da zaiyi. Yanzun ne yake jin dadi da Bilal din zai kasance makaranta daya da shi. Amman yana da tabbacin surutun da zasu dingayi shi da Haris kafin su sauka Zaria kan shi yayi ciwo. Shisa ya zabi yau din a matsayin ranar da zai koma, kawai saboda Haris yace zaiyi gaba, amman ya nace ya zauna jiran shi.

Yau ma tunda ya tashi yake jan jiki, duk da hakan na da alaka da hankalin shi gabaki daya da yake kan Layla. Sam baiji motsin ta ba, ya dade a bakin kofa da safe yana ganin shige da ficen yaran gidan har suka tafi makaranta, amman bai ganta ba, yaso ya tambayi wani ko jikin ne yasa bata fito ba, amman gaisuwar da suka dinga mishi ce tasa bakin shi yin nauyi saboda surutun har ya fara hawar mishi kai. Haka ya gaji ya koma, ga kasa da baisan waya shigo da ita dakin ba, sai da ya kara sharewa sau biyu tukunna yaji ya taka tsakar dakin da ya sha tayal ya mishi dai-dai.

“Kai fa muke jira… Kana ganin har biyu ta wuce, dare kake so muyi?”

Bilal ya fadi yana shigowa dakin, kafafuwan shi Rayyan ya bi da kallo

“Kai ka shigo da kasa, ban san sau nawa zance ka dinga cire takalminka a bakin kofa ba, har takalmi na siyo na yawo a daki, amman baka amfani da naka.”

Numfashi Bilal ya sauke, yana zare takalman daga kafar shi, ya saka hannu ya dauka yana fitar dasu bakin kofa, kwana biyu da Rayyan din baya nan wannan ka’idojin na shi duk ya manta su, karasawa yayi ya zauna gefen gado.

“Yanzun ba zaka wanke hannun ka ba, ka taba takalmi haka zaka kama kofi, yasa na daina hada kofuna da kai.”

Numfashi mai nauyi Bilal yaja yana fitar wa

“Hamma ka sama mun lafiya, hannun ka ne ko nawa? Maganar da ake so kayi ba ita zakayi ba, sai kace bakin ka ya gaji da magana, amman baya taba gajiyawa kan tsegumi.”

Duk surutun shi sama-sama Rayyan din yake ji, hankalin shi yayi nisa wajen tunanin ina da ina takalman Bilal din suka taka, wacce kazantar ya kwaso da su ya kuma saka hannu ya damuka, wannan matsalar shi ce kamar yanda ya fada, amman Rayyan din bayason yaje ya taba mishi wani abu da wannan hannun nashi daya dauki takalma. Ya dauka surutu da mutane ne abinda yafi tsana a zamantakewa, sai da ya fara girma yagane kazanta ce abinda yafi tsana, tsantsanin da yake da shi ba karami bane ba.

Lokutta da dama baka raba shi da karance-karance kan kwayoyin cutukan da suke rayuwa da mutane a mu’amalar yau da kullum. Yana son lafiyar shi, yana bala’in ririta lafiyar shi, tana jerin abu na farko da yake roka a dukkan addu’ar shi, shisa yake kara taka tsantsan idan ya tsare da iyawar shi, Allah saiya taimake shi. Dan ya kula mutane basu da wani buri daya wuce su ja mishi amai da gudawa. Haka shekaranjiya da suka dawo daga masallaci Bilal ya siyi wani rake, kuma har yake mishi tayi, tun suna hanya ya fara gabza kamar bashi da hankali.

“Ka tashi dan Allah ka shirya mu tafi.”

Bilal din ya fadi yaba dorawa da

“Hamma…”

Ganin da yayi kamar Rayyan din baya jin shi, sai lokacin ya kalle shi

“Meye? Karka dameni, kuyi gaba da Hamma Haris mana, dole sai kun tafi dani?”

Ya karasa maganar yana mikewa, shi ya gama shiryawa, Layla ce baigani ba

“Ni na gama shiryawa, ka tashi…”

Rayyan ya furta kamar an mishi dole, mikewar yayi, kafin yai wani motsi Haris ya daga labulen dakin tare da yin sallama, idanuwan shi ya tsayar kan Bilal dan yasan ko Rayyan yayi wa magana kai tsaye ba lallai ya amsa shi ba.

“Kun gama? Yamma nayi.”

Kai Bilal ya daga mishi

“Yanzun zan kiraka daman.”

Rayyan kuma Haris din yake kallo, muryar shi can kasan makoshi yace

“Hamma…”

Daga Haris din har Bilal kallon shi sukayi a tare, fuskokin su dauke da mamaki

“Layla fa?”

Ya furta har lokacin muryar shi daga kasan makoshi ta fito, kamar maganar na mishi wahalar gaske.

“Bata da lafiya, ko makaranta bata je ba, tana ta amai jiya da dare, sai da sukaje asibiti da….”

Daga kan kalmar bata da lafiya bayajin wani abu ya kara zuwa kwakwalwar shi, zantukan duk da Haris yakeyi iya kunnuwan shi suka tsaya lokacin daya fara takawa, wuce Haris din da yayi a bakin kofa ya katse mishi maganar da yakeyi, takalma ya zira. A tsayin rayuwar shi ba zai iya tuna ranar karshe da ya taka bangaren Mami ba, ko Layla zai kira daga bakin kofa yake tsayawa ya kwala mata kira, idan bata nan Mami kan fito ko ta aiko a fada mishi bata nan, idan ita ta fito da kanta ta fadi juyawa yakeyi. Itama kamar tasan ba karamin taimako tayi mishi na saukakewa kanta yi mishi magana, haduwa hamsin in zasuyi zai matsa ta wuce ne, fuskarta ma baya kallo balle tasa ran zai gaisheta.

Inda sabo ta saba, a yaran dakin Ayya daga Khalifa sai Bilal ne suke gaishe da ita ko da yaushe, amman sauran sai randa suka ga dama, idan tayi musu magana dai suna amsawa, kuma babu wanda zatace ya taba mata rashin kunya. Amman ta kula ba ita kadai bace, kowane Rayyan baya kulawa, shisa bata taba kullatar shi ba. Amman yau babu wani tunani ya shiga dakin yana fadin,

“Layla…”

Mami da take kitchen tana wanke-wanke sai da taji gabanta ya fadi, dan yau sai taji kamar a cikin dakinta Rayyan yayi magana, hakan ya sata tsame hannuwanta daga cikin ruwa tana fitowa, ganin shi tayi a tsaye, yau ya sauke idanuwan shi akan fuskarta,

“Mami ina Layla?”

Ya furta, yana kara mata mamakin da takeyi, kafin ta iya cewa,

“Tana dakinta.”

Dan yau ikon Allah take gani muraran, bata taba jin sunanta a bakin shi ba, ta manta ranar karshe daya kalli fuskarta yayi magana da ita. Balle kuma ace ya taka dakin ta, amman yau Rayyan ne da kafafuwan shi a cikin dakinta, lallai kam abin babba ne. Shikam harya fara takawa yayi tunanin baisan inda dakin nata yake ba, juyowa yayi, Mami da tasan tambayar da zaiyi ta daga hannunta tana nuna mishi, baice komai ba ya nufi dakin.

“Allah Kai Ka san dai-dai…”

Mami ta furta a hankali tana komawa cikin kitchen dan karasa wanke-wanken ta. Tana barin Rayyan daya taka har kofar dakin da Mami ta nuna mishi yana Kwankwasawa.

“Layla!”

Ya kira yana saka Layla da tun da ta farka cikin dare, magungunan da aka bata a asibiti suka saketa ta rasa abinda yake mata dadi a duniyar gabaki daya. A islamiyya ta sha cin karo da darussan da sukayi magana akan al’ada, menene ita al’adar da hukunce-hukuncen ta a tsari na addinin musulunci. Kuma tun da suke aji biyu a sakandire ta kanji wasu a ajin suna zancen. Sai dai babu wanda taji yana labarin ana shan irin wahalar da take sha tun jiya, mararta take ji tamkar wani ya saka shebir a ciki yana kwashe duk wani abu da bai mishi ba.

Ko numfashi dakyar take iya fitar da shi, bayanta da cinyoyinta a rike su. Har suna sakata tunanin ko jijiyoyin duk dayane suka fara daga bayan nata zuwa cikin cinyoyinta. Ciwo ne da bata taba sanin irin shi ba. Dan ita kabarta da zazzabi, shima sai Mami tayi da gaske zata zauna waje daya. Bata taba wata rashin lafiya da ta kwantar da ita waje daya haka ba. Tana juye-juye ne taji muryar Rayyan, dan kara dakuna fuska tayi dan a tunanin ta cikin kanta ne, dan ko dazun tayi tunanin harya wuce makaranta.

“Layla!!”

Ya kara fadi yana doka kofar fiye da sau daya kamar yanda yayi da farko, bata san lokacin da ta sauko daga kan gadon tana karasawa inda kofa take ba, kama hannun tayi ta murza tana bude mishi.

“Hamma…”

Ta fadi cike da mamaki, da gaske shine.

“Me ya same ki?”

Rayyan ya furta da damuwa kwance a fuskar shi, yanayin da ya dirar mishi da bakunta tunda ba sabawa yayi ba, idanuwanta ta sauke cikin nashi.

“Ki daina kallona!”

Yai maganar a tsawace yana sakata sadda kanta kasa, idanuwanta na fara tara hawaye, nashi idanuwan Rayyan ya lumshe yana bude su a kanta, dai-dai lokacin da mararta tai wata irin murdawa, sai da ta rike kofar tana kiran sunan Allah, ba ita kadai ta rikice ba, hatta shi Rayyan din yanayinta ya ruda shi

“Wai me yake damun ki? Me asibiti suka ce yana damun ki? Kin sha magani?”

Kai kawai ta iya daga mishi, ganin dakyar take a tsaye yasa Rayyan din kama hannunta da yake jikin kofar yana janta suka shiga cikin dakin. Komawa tayi kan gado ta kwanta, yanda duk zata misalta ciwon da take ji ta kasa, ko idanuwanta ta kasa budewa tunda ta kwanta. Tana jin Rayyan ya mika hannu yana daukar mayafin da takan rufa da shi in taji sanyi, duk da ba bargo bane, zanin gadone babba, warware shi yayi yana budewa ya rufa mata. Kafin ya samu wajen zama kan durowar da take gefen gadon. Kallon yanda lokaci zuwa lokaci Layla takan kara runtsa idanuwanta alamun tana cikin azabar ciwo yakeyi.

Jin yanayin yake har cikin ran shi, shi bai taba ganin tayi rashin lafiya haka ba tun tasowar su. Yana nan zaune yana kallon yanayin ta Mami tayi sallamar daya amsa batare daya dauke idanuwan shi daga kan Layla ba.

“Me yake damun ta wai? Ko za’a koma asibiti.”

Murmushi Mami tayi

“Ai da sauki, an bata magunguna kuma ta sha.”

Kai Rayyan yake girgizawa tunda Mami ta fara magana, yana dago kai ya kalleta

“Layla ce Mami. Bata rashin lafiya irin haka… Kinsan bata rashin lafiya irin haka”

Ya karasa maganar da wani yanayi a muryar shi. Kamar baisan yanda zai fadi kalaman ta fahimce shi bane. Itama Mami batasan yanda zata fara gaya mishi ciwon da Layla takeyi bana asibiti bane ba, yanda zai fahimci asibiti sunyi iya nasu kokarin, zai wuce nan da wasu yan kwanaki.

“Nasani, zataji sauki karka damu…”

Kai kawai ya jinjina, tana ganin yanda bai yarda da maganganun ta ba, ya dai mayar da hankalin shi kan Layla ne yana kara gyara zama. Sake ficewa Mami tayi daga dakin, anan tabar Rayyan zaune, sosai ya nutsar da hankalin shi akan Layla, har sai da yaga yanayin ta ya canza da alamar bacci ya dauketa. Amman ko motsi tayi sai gaban shi ya fadi, gabaki daya komai yake ji baya mishi dadi. Kamar daga sama yaji ana fadin,

“Hamma kai muke…”

Hannun shi ya daga guda daya yana dakatar da Bilal, dayan hannun yakai bakin shi da furta,

“Shhh…”

Kafin ya mike tsam yana fitowa wajen dakin, ya dan koma ciki yana fisgo Bilal da ya shiga suka fito, muryar shi can kasa yace

“Meye?”

Kallon shi Bilal yake da mamaki

“Ban gane meye ba, kasan kai muke jira har la’asar tayi ko?”

Numfashi ya sauke, gabaki daya ba yajin yana da natsuwar wata tafiya yau

“Ni kam sai gobe”

Baki Bilal ya bude yana kallon shi, so yake yaga ko dan murmushine a fuskar Rayyan din da zai nuna cewa wasa yake maganar da yayi, amman babu, da dukkan gaskiyar shi ya fadi

“Sai gobe? Kasan Hamma Haris na da abu mai muhimmanci da zaiyi goben ko?”

Cikin idanuwa Rayyan ya kalle shi

“Nace kar ya tafi ne? Ban tuna lokacin da nace wani a cikin ku ya jirani ba, kun tambaya na fada muku yau zan tafi. Yanzun kuma nace sai gobe, me yasa kake da matsala da hakan?”

Ba maganganun bane suka batawa Bilal rai, yanayin da Rayyan din yayi maganar, babu alamun bacin rai ko jin haushi, kamar yana ma karamin yaro bayani, saboda bai dauki abinda yayi a matsayin wani abu ba

“Hakane…”

Bilal ya furta yana juyawa, dan dakuna fuska Rayyan yayi dan yaga kamar ran Bilal din ya baci, bayan a duka maganganun da yayi bai ga abin bacin rai ba. Kiran sallar la’asar da yaji anyi yasa shi ficewa daga bangaren Mami, sai da yaje dakin shi ya daura alwala sannan ya fita masallaci. Yana dawowa kuma kan shi tsaye bangaren Mamin ya kara wucewa, sanda yaje a bandaki ya samu Layla ta tsugunna saboda aman da taji yana taso mata, kuma batama wani ci abinci ba balle tace

“Layla… Amai zakiyi? Amai kikayi?”

Rayyan ya fadi yana jin ruwan da yake takawa a bandakin saboda babu takalma a kafafuwan shi har cikin ran shi, amman wahalar da Layla take ciki tasa ko amsa ta kasa bashi, da kan shi ya tari ruwa a famfo yana janyo bokitin kusa da ita, kofin da yake ciki yai amfani da shi wajen zuba mata ruwa a hannuwanta da ta miko mishi ta wanke fuskarta, shi ya kama hannunta tana mikewa ta ficewa daga bandakin ta koma ta kwanta. A ran shi tunanin inda Mami taje tabarta ita kadai a halin da take ciki yakeyi, ran shi na kara baci.

“Ba dole kiyi rashin lafiya ba, ki kalli bandakin da kike shigowa dan Allah…”

Ya furta, duk da wani zai shiga yagan shi tsaf-tsaf, amman a idanuwan Rayyan yayi mishi datti. Omo daya gani ya dauka ya zuba a bokitin yana wanke bandakin, har karamin tawul din daya gani da baisan kona menene ba ya dauka ya goge bangon bandakin. Ko kadan bayason ganin datti, dan jirwayen ruwan da zaka gani na ruwan wanka a bandaki, na dakin su sam ba zaka gani ba, ya goge ko ina qal-qal. Sai da ya wanke kafafuwan shi sannan ya fito daga bandakin.

*****

“Muje kawai Hamma… Barin wa Ayya sallama, idan mukai la’asar sai mu tafi”

Bilal ya fadi muryar shi a sanyaye, cike da rashin fahimta Haris yace

“Rayyan din fa?”

Kallon shi Bilal yayi

“Yace sai gobe zai tafi, janyo shi zan yi?”

Murmushi Haris yayi, kafin Bilal din ya dan dafe kai yana fadin

“Kayi hakuri…Allah ya batamun rai ne.”

Murmushin dai Haris ya sake fadadawa

“Rayyan manya… Allah ya shirya”

Bandakin su da yake cikin dakin Bilal ya shiga ya daura alwala ya fito

“Kaga ni ina da abinda zanyi a makaranta gobe da safe in shaa Allah. Amman ka jira Rayyan din sai ku taho tare.”

Tun da ya fara magana Bilal yake girgiza mishi kai, ya taho shi kadai kamar yanda yake so. Da tun farko bai wahalar dasu ba yace shi kadai yake son tafiya.

“Ka bar shi Hamma… Da mun dawo sallah tafiya zamuyi…”

Kai Haris ya jinjina yana mikewa. Alwalar yayo shima suna fita masallaci tare, suna dawowa shi ya shiga dan ya fito da jakunkunan su da na Bilal ne guda biyu. Shi kayan shi basu da yawa, Rayyan kuwa jakar shi karama ce, babu abinda yake tafiya da shi. Daga gefen jakar takardun zanen shi ne daya nannade su ya soka. Shi kuma Bilal ya wuce bangaren Ayya inda ya tsaya daga bakin kofa yana fadin,

“Ayya zamu wuce…”

A kasan murmushin alfaharin da tayi akwai damuwa shimfide, gidan har yayi mata wani irin shiru. Da Rayyan ya tafi daman ta saba, dan ko yana cikin gidan sai tayi kwana biyu bata saka shi a idanuwanta ba, amman Bilal, a duk cikin yaranta babu wanda ta shaku da shi kamar Bilal, banda Ahmadi shine namiji na biyu a rayuwarta da yake gane akwai damuwa a fuskarta tun kafin ta furta, yake zama har sai yaga tayi fara’a sannan. Bilal ne kuma ka dai yake dora bukatunta akan nashi. Ko bangaren ya zaba na karatun shi tasan saboda ita ne

“Wai duk cikin ku babu wanda naji yana sha’awar lissafi….ko yar kara ba zakuyi wa Abbun ku ba”

Ta fadi wani lokaci can baya, sosai Bilal yayi dariya, musamman da Zubaida tace

“Wallahi Ayya idan zaki tsareni bansan ya akayi na wuce lissafi a shekarar farko fa, kowa na kallona a matsayin yar Abbu a ajin, suna tunanin zan baro A, dakyar D ta fito…”

Nan aka bude caftar tattauna lissafi, shi bai taba bashi matsala ba, kuma Rayyan yana ganewa matuka, idan waje ya shige mishi duhu daya nunawa Rayyan din yake warware mishi

“Kina son wani ya karanci lissafi ne Ayya?”

Kai ta dan rausayar

“Naga wahala yake baku ai”

Murmushi kawai yayi, sai ranar daya amso takardar samun karbuwa a ABU ne ya nuna mata lissafine gurbin daya samu

“Bilal…”

Ta fadi tana jin kaunar shi har kasan zuciyar ta

“Ki mun addu’a kawai Ayya.”

Shine abinda ya fadi, addu’a kam bata gajiyawa da yi musu ita. Tun da satin tafiyar tashi ya kama take jin yanda zatayi kewar shi. Ko na rana daya Bilal din bai taba zuwa wani waje ya kwana ba, yaran nata girma sukeyi a gaban idanuwanta, amman zuciyarta na kallon su yan kanana. A wajenta har karshen lokacin da Allah ya ara mata tare dasu ba zata daina ganin yarintar su ba.

“Allah ya tsare mun ku, Allah ya baku sa’a a karatun ku. Ka kula da Rayyan kamar yanda ka saba.”

Ta karashe maganar da yanayi mai nauyi a muryarta

“Sai gobe shi, ya fasa tafiya yau.”

Da mamaki Ayya take kallon Bilal

“Saboda me? Bashi ya zabi yau din ba.”

Kallon ‘Rayyan ne Ayya’ Bilal din yayi mata

“Kawai ya fasa tafiya yau din ne.”

Ita fa sam zaman shi a Zaria yanzun ya fiye mata zaman shi a garin Kano. Saboda zai nisanta shi da Mami da kuma Layla. Ko kadan bata kaunar ganin yana wata mu’amala da su

“Yana ina?”

Dan jim Bilal yayi, saboda bayason bata mata rai, yana da tabbacin idan ya fada mata Rayyan na dakin Mami ranta zai baci sosai. Amman a lokaci daya ba zai iya mata karya ba.

“Yana wajen Layla ko?”

Ta tambaya zuciyarta na wani irin zogi, ta rasa ta inda zata fara bullowa al’amarin Rayyan. Shekaranjiya suna tare da Khadi da zuwanta aikin hajji shekaru bakwai da suka wuce yasa duk yan unguwa suna kiranta da Hajiya Dije. Taso tayi mata zancen Rayyan din dan tana da yakinin ba zata rasa shawarar da zata bata ba. Amman sai ta tsinci kanta dayin nauyin baki.

“Bilal tambayar ka nake yi.”

Ayya ta fadi rai a bace, kai ya dan daga mata

“Bata jin dadine, yana bangaren Mami… Mu…”

Ai Ayya bata barshi ya karasa ba, kanta har wani shuu yakeyi saboda tashin hankali. Numfashi kawai Bilal ya sauke yana wucewa dan yasan Haris na can yana jira. Ko baiyi niyya ba zai bi shi Zaria yau, saboda bayason ganin kowanne rikici ne Ayya zatayi a cikin gidan yau. Ita kuwa kanta tsaye dakin Mami da zata kirga iya shigar data tabayi daga zuwanta gidan zuwa yau ta nufa, tana shiga ta fara kwalla mata kira.

“Maryama… Ke kinsan wallahi bokan ki yayi karya… Ke din banza balle kuma yar rikon ki. Ki fito tun wuri ki warware abinda kika kulla.”

Dan tana da tabbacin karatun da Maryama taga Rayyan ya natsu yanayine bata so, shine abinda ya tsokane mata ido yasa take neman sabauta mata yaro. Hango wata kofar daki da tayi a bude yasata takawa tana karasawa. Abinda tagani yana saka duk wata jijiya ta jikinta tsinkewa. Rayyan ne da kayan wankin Layla da tayi bata kwashe ba ta ajiye can gefen gado suka dinga shigar mishi ido, ga kuma zaman da yakeyi. Hakan ya sashi mikewa, idan yana wani abu da hannuwan shi yana rage mishi tunani, ko zane ko aiki, ko karatun makaranta, sosai suke hana kwakwalwar shi tunanin komai sai abinda yakeyi din.

Yana daga wata hijab yaga mp3 din Layla hade da earpiece, shi ya sakama kunnuwan shi ya kunna, kusan wakokin yan kasar sudan da sukayi tashe wato Sahwa ne cike da mp3 din, su yake ji, ya saka mp3 din a aljihun shi. Kayan yake ninkewa a nutse, shisa sam baiji hargagin da Ayya takeyi ba, baima san tana bayan shi ba sai da yaji an dafa shi, juyowa yayi ya cire kunne daya na earpiece din dan yaga kamar magana take yi.

“Uban me kakeyi? Na shiga uku ni Maimuna… Rayyan kayan su naga kana linkewa kamar? Me kakeyi a dakin Maryama? Yaushe ka fara shigowa dakin ta?”

Dakuna fuska yayi yana kama hannun Ayya hadi da janta, bin shi take da matukar mamaki, saboda komai ya kwance mata, suna zuwa tsakiyar falon sukaci karo da Mami da ta yanke karatun azkar din bayan la’asar da takeyi ta fito saboda jin tashin hankalin da Ayya. Hakan nasa Ayya fisge hannunta da Rayyan ya riko

“Maryama ki kiyayeni, wallahi ki fita idona. Kin aure mun miji, kamar hakan bai isheki ba, na saka miki ido akan Bilal, bai isheki ba kin biyo Rayyan? Dauki dai-dai zaki mun kenan.”

Murmushi Mami tayi, ta rasa kalar zargi irin na Ayya. Duk tsayin shekarun nan basu sa ta fahimci cewar bata da lokacin bibiyarta ba. Ko akan Ahmadi batajin zata iya bibiyar Ayyar, duk kuwa tarin kaunar da takeyi mishi. Idan bin Malamai ne Ayya take magana tana da kudin da zata iya basu. Kawai babu abinda ya fiye mata zaman lafiyarta a kabari ne, zata kwammace tabar mata Ahmadi idan za’a bata zabi tsakanin hakan da bin Malamai. Amman a duk rana gani takeyi bibiyarta take yi.

Zuwa yanzun shagunan dinkinta biyu, ana kawo mata dubbanin kudi duk karshen watan duniya, ga hijabai da take dinkawa a cikin gida, sari akeyi garuruwa. Ga hidimar yaranta, sam bata da lokacin wani abu, kawa kwara daya bata da ita da zata nuna tace abokiyar shawara, idan abu yasha mata kai da bata son tattaunawa da Ahmadi, Haris ne abokin shawararta. Yau Rayyan ne kawai zai hanata fadawa Ayya maganar da zata kwana tana juyi. Alkawari ne tayiwa kanta, ko dan zumuncin da ke tsakanin yaran su ba zata taba mayar mata magana a gaban su ba.

Shisa ta girgiza kai kawai yanzun ma tana fadin

“Allah ya kyauta.”

Ta juya

“Na fada miki, ki kyalemun yarana, kome zakiyi ki kyalemun yarana, ba zai miki kyau ba kina bibiyar mun yara.”

Runtsa idanuwan shi Rayyan yayi yana bude su akan Ayya

“Ayya…”

Ya kira muryar shi can kasa, baice yana son Mami ba, bai kuma ce bayason ta ba, bayajin komai a kanta sam-sam. Yanajin abu a game da Ayya da Abbu, amman shi kan shi ba zaice ko meye ba, lokutta da dama idan yagansu zuciyar shi nayin duhu, musamman Abbu, ko gwada magana yayi da shi sai kan shi ya fara sarawa, shisa lokutta da dama yake zabar ya wuce batare da yace mishi komai ba. Ya sha jin tana fadar cewa Mami zata barbada musu abu, shisa bayacin abinta. Lafiyar shi nada muhimmanci a wajen shi, kuma idan Ayya tace za ayi abu, ya tabbata za ayi.

Maganar da suke a tsakanin su bata da yawa, amman bata taba mishi karya ba, ita da Bilal na jerin mutanen da ya aminta ba zasu taba cutar da shi ba. Amman hakan baya nufin yana son hayaniyar da Ayya take yawan yi da Mami din, bai taba mata magana bane kawai. Yafi zabar ya wuce yayi abinda yake gaban shi. Yau dinne yake jin shi sama-sama. Ga Bilal da yaga ran shi ya baci kan maganar da bata kai ta kawo ba, Layla da har yanzun baiga alamar tana jin saukin da Mami ta kira mata ba. Ga Ayya yanzun da tazo tana wasu maganganu

“Ayya dan Allah ki tafi. Kin ga Layla bata da lafiya. Kuma dakyar tayi bacci.”

Kallon shi Ayya take, tsoro bayyane a fuskarta

“Dan ubankan shanyewar da akayi maka har takai haka? Ni kake fadawa dakyar Layla tayi bacci? Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ayya ta karasa kamar zata fasa ihu saboda tashin hankalin da take ciki, abinda ko a mafarki bata hango bane yake faruwa a gabanta

“Ka zo ka wuce ka koma makaranta kafin ranka ya baci wallahi.”

Numfashi Rayyan ya sauke, ran shi ya gama baci, babu wani bacin rai kuma da Ayya zata kira banda wanda yakeji yana taso mishi yanzun

“Zan koma makaranta. Sai gobe in shaa Allah.”

Cikin idanuwa take kallon shi

“Idan na isa, idan ina da wata daraja a idanuwanka zaka wuce ka koma makaranta yau.”

Maganganunta yake ji sun danne shi da wani irin nauyi, amman duhun daya taso mishi na son bijerewa maganar da tayi ya rinjayi koma meye ya fara shirin tasiri akan shi. Hannun ta ya kama yana janta har kofar dakin Mami din

“Zan koma Ayya… Sai gobe zan koma.”

Ya fadi yana juyawa, baki a sake Ayya take kallon Rayyan harya juya yana komawa dakin Layla. A gaban idanuwanta, ba zatace ga yanda akayi ta isa daki ba, amman har wani jiri-jiri take gani saboda tashin hankali. Tana shiga daki a kasa ta zauna dabas, jikinta babu inda baya rawa. Tunda take da Rayyan ko da wasa bai taba gwada tayata wani aiki ba, asalima magana da ita wahala take mishi. Waccen shekarar da tayi jinya ya shiga dakin dai ya zauna, amman baice mata kanzil ba, harta ji sauki haka zai shiga ya samu waje ya zauna.

A fuskar shi babu alamar damuwa ko wani abu, idan ma su Zubaida da suke zaune suna surutu tashi yake ya fice kamar surutun nasu ya fara hawar mishi kai kamar yanda yake fadi. Amman yau Rayyan ne har yake fada mata Layla tana bacci, Rayyan ne da hannun shi tagani ya linke kayan Layla. Wasu hawaye nasu dumi ne suke zubo mata, ta jima a wajen, ko sallar Magriba dakyar ta samu tayi ta, tana zaune tana sharbar kukan ne Ahmadi ya shigo, dan duka yaran suna gidan Yaa Ayuba. Da haka zasu shigo su sameta tana wannan kukan.

Harta fara kewar Bilal tun ba’a kwana ba, tasan shine kawai baya iya daukar awanni bai ganta ba, ko leka kaine sai yayi

“Ayya nace tun dazun banganki bane fa… Kina lafiya dai ko?”

Ba zai taba gane yanda kulawar shi take kara mata son shi ba.

“Subhanallah, Maimuna… Lafiya? Me ya faru?”

Ahmadi ya fadi yana karasawa cikin dakin sosai, kamar haka take jira ta sake fashewa da wani kukan

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Ahmadi ya furta cikin bayanannen tashin hankali

“Duk ina yaran? Suna lafiya? Dan Allah kiyimun magana.”

Dan harya fara zufa saboda tashin hankali, muryar Ayya na shakewa saboda kuka ta soma fadin

“Tunda kake, Ahmadi tunda Rayyan ya mallaki hankalin shi ka taba ganin ya tayani aiki? Ko da shara ce?”

Cike da mamaki Ahmadi yake kallonta, ya dauka sun gama yanke hukunci addu’a ita ce kawai abinda zasu dinga bin Rayyan din da ita, ba zasu kara bata ransu akan shi ba. Idan ma sun bata ran nasu zasu yafe mishi da sun huce ko Allah zai sanyaya zuciyar shi. Tunda fushin su zai kara jefa shi cikin wani yanayin ne, kuma idan bai manta ba yau Bilal yace zasu tafi makaranta, hatta kudin Rayyan din ya hada yaba Bilal, to me zaiyi wa Ayyar haka da take wannan kukan.

“Idan nace maka Rayyan na linkewa wasu can daban kayan da suke sakawa abin ba zai baka mamaki ba?”

Bata ma rufe bakinta ba take ganin wani sabon mamakin karara a fuskar Ahmadi, hannu takai tana share kwallarta, wasu sabbi na samun damar zubowa, kada kai tayi cikin kunar zuciya

“Yanzun zaka yarda dani ko? Yau zaka yarda matarka na bibiyata, zaka yarda yarana take so ta rabani da su. Ahmadi na kauda kai iya yanda zan iya… Da Allah nake rokon ka kayi mata magana ta kyalemun yaro, ta kyalemun yarona”

Ta karasa tana sakin wani gunjin kuka. Tabbas zancenta ya daure mishi kai matuqa. Yasan Rayyan, a cikin yaran shi yanzun babu wanda yake kula da takun shi kamar Rayyan. Idan da gaske Ayya takeyi yana linkewa su Mami kaya to tabbas zargin da takeyi na da tushe, duk da a kasan ranshi yasan Mami ba zata tabayin abinda zai cutar da wanin shi ba.

“Kiyi hakuri, zan mata magana. In shaa Allah babu abinda zai faru. Dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan…”

Ahmadi yake fadi, dan kukan nata ya kara daga mishi hankali, bai fita daga dakin ba har saida ya tabbatar ta daina kukan, da kan shi ya zubo mata abinci ya kawo mata ruwa. Sannan ya nufi bangaren Mami. Duba jikin Layla yayi ya shiga yi, ya samu tana bacci, daga nan ya wuce bangaren shi, bai yiwa Mami zancen ba sai bayan sunci abincin dare harma sun kwanta sannan yace

“Maryama me yake faruwa ne?”

Numfashi ta sauke

“Me kake so ince maka? Na dauka ta gaya maka abinda ya faru.”

Kai ya jinjina

“Baya nufin bana son ji daga bakin ki.”

Murmushin takaici mai sauti Mami tayi, kafin ta labarta mishi iya abinda tasan ya faru tana dorawa da

“Rayyan bai tana shigowa bangarena ba, idan ya taba lokacin yarinta na manta… Amman yau ya shigo saboda Layla… Ina tsoro, har raina ina tsoron wannan kaddarar ko wacce iri ce, saboda ina hango tarin tashin hankalin da yake cikinta.”

Wannan karin Ahmadi ne ya sauke numfashi, gabaki daya abin ya saka jikin shi yayi sanyi, idan da gaske saboda Layla ne Rayyan din ya shigo ba Mami bace kawai a tsorace, shi kanshi zuciyar shi yaji tana rawa.

“Allah karka doramun kaddarar da bazan iya dauka ba, Allah ka dubeni da Rahmar ka ka saukakama yarana kaddarar su…”

Daren kusan Ahmadi, Mami da Ayya kanta kwana sukayi suna juyi. Ayya na jinjina aikin bokan Maryama da yanda ya zame mata dole ta kira Hajiya Dije su tattauna wannan al’amarin. Mami na tunani amanar Layla da take hannunta, tana kuma tsoron abinda zuciyarta take sanar da ita yana faruwa tsakanin Layla da Rayyan din da bata jin sun sani. Ahmadi kuwa gabaki daya lamarin ne yake sanyaya jikin shi, yaran nashine yake ganin kamar sunyi kankanta, kamar ma basu da hankalin hango kaddarar da take bibiyar su.

Rayyan ne kaddarar su Rayyan ne suke tunanin zai zama tushen komai.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×